KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   9 / 24

24K to 27K   out of 69.9K words

da mutane nagartattu guda biyu akansa sannan ka zartar" .

Kai wasila ta kawar tadan mele baki sannan ta dawo da dubanta ga ruqayya

"Na gode da tunasarwa,amma na jima ina yin wannan ai,sannan shi kansa abinda ke faruwa
jifana akayi,mutum kusan biyar suna gayamin asirin akayimin don kada na auru,ina da magauta
da yawa da maqiya,duk wanda naje gurinsa cewa yakeyi a gaba aka sakoni"

"Babu wanda yasan gaibu sai Allah,amma asiri gaskiya ne yana kuma iya kama mutum,saidai

bisa amincewar Allah ne,ba wanda ya isa ya cutar dakai sai Allah yaga dama,akwai kuma ayoyi
daga alqur'ani da tsafatattun hanyoyin warware sihiri da kuma kare kai daga sake kamuwa
dashi,kamar cikin suratul a'araf......"

"Duk fa inayinsu amma.....hmmmm" sarai ruqayya ta fahimci me takeson cewa,sai ta gyara
zama

"Eh bata karbu ba kikeson cewa?,ko kin dade kinayi ba nasara ko?,to bari kiji wani abu da baki
sani ba,ita kanta addu'a tana da qa'idojin yinta da amsata.....indai zakiji a ranki addu'arki bata
karbu ba to kin wargazata,indai zakiyi......"

"Kinga rubutamin addu'o'in saina hada dasu" ta fada tana zaro biro da memo ta miqa
mata,sannan ta miqe tana fidda kayan jikinta.

"An kusa kiran sallah,akwai hayaqin da zanyi kada lokaci ya wuce,ina zuwa" ta fada tana daura
zanin fallen atamfa tana fita a gaggauce daga dakin.

Da kallo kawai ruqayya ta bita dashi,saita girgiza kanta takaici yana kamata,cikin qasa
da minti biyu qaurin hayaqi ya risketa a nan inda ta barta a zaune.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 11


https://www.mkdatasarvices.com.ng


*MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽

*_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA
KADAI DON AMFANIN KANSU?_*

*_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_*

*_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA
RANGWAME_*

https://www.mkdatasarvices.com.ng


_Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number

wayar_

08038258489


*ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾



Tana saka kanta a tsakar gidan umma tayi sallama

"A'ah,baqi mukayi?" Umman ta fada cikin fara'a. Tun asali ita din macace me kirki da qoqarin
zumunci,saidai ubangiji ya jarabceta da dabi'ar son 'ya'ya. Irin matan nan ne da basa iya boye
soyayyar yaransu,wannan ya sanya abubuwa da yawa da yaran zasu aikata ba kasafai suke iya
tsawatar musu akai ko su hanasu ba.
"Sannu da zuwa umma" ruqayya ta fada tana murmushi,a ranta tana jin dadi me yiwuwa
umman yanzu data shigo ta taras da uban qauri hayaqin turaren ta yiwa wasila fada,iya zallar
qaurin ta isa ta sanya ka samu matsala idan kana da cutar asma

"Tun yaushe kika zo?,munyi sabani naje barka 'yar hannatu ce ta haihu" ruqayya na qaramar
dariya taja kujerar 'yar tsugunno ta zauna kusa da umma da ita ta zauna saman kujerar bayan
ta fidda mayafinta ta rataye jikin igiya

"Ahhhh,umma hannatu ce yanzu da jika?,lallai rayuwa tana gudu"

"Uhmm,kedai bari kawai,shi yasa yanzu gaba daya hankalina ha koma kan 'yar uwarku,ta samu
itama tabar gidan nan,kada na mutu banga aurenta ba" umman ta fada cikin karyewar murya.
Gyara zamanta ruqayya tayi

"Umma kada ki damu,muddin kina mata addu'a akwai lokaci shi aure kaman haihuwa yake
muddin yazo sai anyishi ba abinda zai canza,lokacinta ne kawai itama baiyi ba" baki umman
tadan tabe kadan fuskarta fal alhini

"Uhmmm,mutanene yanzu sun zama abinda suka zama,baka takawa mutum ba baka barar
masa ba amma sai ya saka ka a gaba sai yaga bayanka,nidai tunda nake ban tana jifan dan
wani da ko Allah wadai ba,amma ni tawa diyar ita kenam qwaya daya an hanata ta motsa" cira
kai ruqayya tayi tana kallon umman,alamu dukka sun nuna itama ta yarda da cewa jifa aka yiwa
wasila,itama nata idanun sun rufe da tarin kura kurai da dabi'u da ya kamata wasilan ta fara
gyarawa saboda ta samu tsakaninta da ubangijinta yayi kyau ta yadda addu'arta zatafi shiga.
Sau tari mune sila na rashin karbuwar addu'o'inmu,amma saimu danganta sanadin ga wani ko
wata.

"Don Allah umma kada ki saka wannan a ranki,hadisi ne guda daga ma'aiki cewa,idan da dukka
mutanen duniya zasu taru don su cutar da kai,ba zasu iya cutar da kai ba sai abinda Allah ya
rubuta a gareka,hakanan idan da dukkansu zasu taru don su amfanar da kai basu isa su
amfanar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka zai sameka"
"Uhmm,kedai Allah ya rufa asiri kawai,ina kishiyar tawa da masu gidan nawa?" Kamar jira suke
umman tayi tambayar sai ga sallamarsu,suna gaba yusra na bayansu.

Da gudu suka qarasa shigowa kamar wadanda suka shekara basu ga mamar tasu ba. A
jikinta suka zube iftee ta haye cinyarta

"Ku dagani hakanan ku gaida umma" ruqayya ta fada bayan duk sun gama ifce ifcen.

Daya bayan suka durqusa suka gaidata har ifteehal da take qarama. Umman ta amsa
tana shafa kawunansu sannan tace

"Allah ya nuna mana yaran wasila haka,da tuni itama nata yaran sunkai haka"

"Lokaci dai umma" ruqayya ta fada tana wucewa bakin famfo don yin alwala.

Tana fitowa ta ji umman na magana da waseelar,waseelan tana sake mata bayanin
abinda malamin ya gaya mata

"Wallahi umma da kin barni na tambayeshi,ya gayamin su waye da waye,na rantse da Allah duk
randa aurena ya tashi kaf sai na tambayi sunansu,sai naci(ta dura ashar),kuma wallahi wallahi
ba wanda zai moreni,ba wanda zaici arziqina,kada ma daga baya kice ai ya wuce na yiwa
wance kaza na yiwa wance kaza,arziqin mijina nawa ne saike sai 'ya'yana da wanda naga
dama" ta fada tana shanye ragowar rubutun dake cikin leda ta jefa ledar cikin kurfetunsu na
girki

"Ki barsu da mugun nufinsu,duk wanda yayi na gari kansa ai ko?". Sake cika da mamaki
ruqayya tayi,gaba daya wasilan ta sake canzawa,duk wasu halaye da ruqayya tasan wasila
dasu ta ninko wasu a kai wasu kima ta sauyasu gaba daya.

Tana salla amma mamaki ya gaza barin kanta,ita wasila dake wannan zancan har ma
tasan me kudi zata aura kenan da take zancan ba wanda zaici arziqinta. Kafin ta gama sallar
wasila ta shigo dakin,ta nade saman katifarta tanata amsa waya,ko muryarta ma ba'a ji iya ji
sosai saboda tsabar sanabe da langwashe murya. Waiwayawa kadan tayi ta kalleta sai kuma ta
dauke kai tana ci gaba da lazuminta tana sauraron kusur kusur din wasila saboda bata iya jin
muryarta sosai. A gaban umma ta fara wayar,sai daga bisani ta tashi,tana mamakin yadda take
iya zance tsaf da saurayi a waya a gaban umman ko yayyenta,ba tun yau ba ta saba hakan
dabi'arta ce.

Dai dai sanda ta shafa addu'a wasilan ta saki siririyar qara

"Da gaske don Allah?.....wow......bari na shirya" ta fadi tana katse wayar gami da saukowa daga
katifar

"Ki tayani murna 'yar uwa, iphon 13promax yanzun nan za'a kawomin ita" wasila ta fadi tana
bude wardrobe dinta tana zubo da kayan ciki qasa.

"Toooo.......isma'il dinne?" Waiwayowa wasila tayi ta zabga mata harara

"A'ah sulaiman ba isma'il ba,kina da abun haushi wallahi.....wannan wani guy ne irin type dina
wallahi" ajjiye carbin hannunta ruqayya tayi ta tallafe habarta

"A'ah,amma yanzu kk ce baki samu wanda kikeso ba ko saboda jifanki akeyi" rigar atamfar ta
zaro ta dawo gefan gadon ta zauna tana kallon ruqayya

"Inason mutumin nan ruqayya,amma na masa maganar ya fito yakai sau goma har yanzu
shuru,malamai biyu sun gayamin jifan da akeyimin ne yake hanashi turowa,shima yana
shafarsa" kai tadan gyada

"Kuma kin tabbatar yana sonki kema?"

"Sosai,ke kinga hidimar da yakeyimin ne?,kuma inda baya sona ai da tuni ya tafi,wata nawa
muna tare,munfi shekara fa". Shuru ta sakeyi tana nazari,duk da ita da wasilan tamkar ciki daya
suka fito haka suka tashi,kuma ko yanzun dukansu suna iya yiwa juna katsalandan akan abinda
ya shafi rayuwar daya,saidai zuciya da kuma shaidan batasan ta fiya challenging wasilan.
"Au,bari na gayawa umma ta tura wani yaron ma ya siyo masa lemo" wasila ta fadi tana fita da
sauri a dakin.

Minti daya kacal ta soma jin muryar umman tana magana

"Bazaiyiwu ba,tunda kinsan ko kin karba Bashir sai ya saka an maida masa,bayan uban fadan
dazai hada ni dake yayi mana"

"Don Allah umma ki manta da yaa Bashir,shi wallahi ya fiya tsanani,waini qaramar yarinya ce da
zatayi abinda bai kamata ba?,nasan fa abinda nakeyi da hankalina,waya me tsada kamar
wannan ina gani umma kice kada a kawo?, gaskiya kiyi haquri umma,yaa bashir dai tunda ba'a
gidan nan yake ba sai naso ma zaisan wacce irin wayace a hannu na".
"Nidai ba ruwana na gaya miki"

"Haba umma,haba umma" wasila ta fadi tana buga qafarta,sannan kuma rai a bace ta dawo

dakin.

"Wasila" ruqayya ta kira sunanta

"Inajinki" ta amsa mata tana zama gefan gadon

"Abinda ya bashir fa yayi dai dai ne,sannan dadewa da saurayi da kuma yi miki hidima ba shine
tabbacin ingancin halaye da dabu'unsa ba,hakanan ba shine tabbacin yana sonki ba,babu
soyayyar data wuce mutum ya aiko gidanku ayi maganar aure tsakaninki da shi"

"To amma meye hadin waccar matsalar da wannan,kawai sai ace kyautar wayar ma ba za'a
karba ba,komai an maka izini kamar dan qaramin yaro?"

"Kudin iphone 13ya isa fa ya kawo kudin aurenki harda sadaki fa wasila,mutuncinki suke kare
miki" juyawa tayi kawai ta kwanta rub da ciki ba tare data sake cewa da ruqayya komai ba,sai
qananun gunaguni data ci gaba da yi,kana ta jawo wayarta tahau yin waya.

Tata wayarce itama tahau tsuwwa,koda ta duba sai taga saleem ne. A nutse ta daga
tana daidaita muryarta tamkar budurwar da zatayi magana da saurayinta da suke sharafin
ganiyar soyayya

"Habibee,hala munyi dare ko?,ayi mana afuwa umma dince ban samu ba sai dana jirata"

"Kada ki dami habibtee,nima ina komawa na fito,zan qaraso saimu dawo tare,da motarki kika
fita?"

"Eh da ita ne"

"To sai na qaraso"

"Allah ya kawomin kai lafiya"

"Ameen habibtee" ya amsa mata.

Ajiye wayar tayi tana fita gurin umma,ta sameta tsakiyar su iftee ta sakasu a gaba suna
cin alkubus da miyar ganye,sunata zuba mata surutu tana biye musu.

Sake gaisawa sukayi a nutse sannan suka shiga hirar duniya wadda kusan duka ta
zumunci ne. Akwai zumunci sosai tsakanin mahaifiyar ruqayya da umman data kasance qanwa
ga mahaifiyar ruqayya. Suna tsaka da hira kiran saleem din ya shigo wayarta, saita duba tana
cewa da alhassan
"Duba ko abbanku ne a waje,yace zai qaraso mu wuce gida tare"

"Asshsha,kya barshi a waje,jeki shigo dashi mana"umman ta fadi,sai ruqayyan ta miqe ta fice.

Tare suka shigo tana zolayarsa,yayi kyau cikin yadin voyel fari qal yana zuba qamshi

"Kodai kodai anya kuwa?" Murmushi ne ma ya qwace mishi,ita ta tafi dashi saboda daurin data
lanqwasa kanta,fararen idanunta kuma sun fito tarwai a hasken qwan lantarkin da ya haske
gidan gaba daya amma ita tsokanarsa take qoqarin yi

"Kodai me?"

"Zance kaje ka biyo ta nan" ta fadi tana qaramar dariya me jan hankali saboda sautin da take
bayarwa ma daban yake. Hakanan ita kanta ta saba,idan tana tare da saleem komai nata yakan
canza,takan rikide daga ainihin ruqayyanta zuwa habibtee dinsa.

Sosai umma ta tarbeshi,don kafin su iso ma ta masa shimfidar dadduma. Hira sukayi
kadaran kadaham,don yafi sakewa da ita ma akan maama mahaifiyar ruqayya. Wasila ta saka
ta zubo masa alkubus,amna kuma baici ba yace ya qoshi,don ba kasafai yakecin abinci a wani
guri ba muddin girkin ruqayya ne. Ko kadan bayason yayi missing girkinta,gurin hajiya
mahaifiyarsa kawai yake iya karbar abinci yaci indai tayi masa tayi ranar girkin ruqayyan.

Koda zasu tafi umman ta juye masa abincin

"Ku tafi dashi ruqaiya" umman ta fadi. A gurguje ruqayya ta leqa don yiwa wasila da bata sake
ganin gilmawarta ba sallama,saidai bata cikin dakin,bata kawo komai ranta ba ta fita suka wuce.


*HUGUMA*👑

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 12


Hannu ga miqa mata zai karba key din,sai ta langabe kai tana dubansa qasa qasa

"Ranka ya dade yi zamanka kawai ka huta,yau ni zan tuqaka,nasan daka koma gida baka kai
ga zama ba ka sake fitowa" shima nasa kan ya karyar

"Allah ya taimakeki ayi haka?" Girarta ta dage duka biyun

"Me zai hana?"

"Lallai na cika dan gata" ya fada yana murmushi.

A nutse take tuqin yana daga gefanta,har cikin jikinsa yakejin bambancin komai da
komai ma tsakaninta da zainab. Ya taba zama irin haka yace Zainab ta tuqasu,budar bakinta sai
tace

"Tabdijan,kamar wata driver?,wannan ai aikinka ne" ta jefa masa key din,abinda ya jawo ya bata
mata rai kenan shima. Yana da sauqin kai yana da daukar wasu abubuwan da yawan maza
suke kallonshi a mazaunin raini,amma shi sam bai dauki hakan a bakin komai ba,saidai abu
guda da baya iya dauka shine,ki kawo masa raini ko maganar banza ko ta rashin girmamawa
gaban 'ya'yansa ko yaran da suke aiki qarqashinsa ko qannensa.

Dabi'un Zainab wasu irin dabi'u ne masu daure kai da ban mamaki. Ya jima yana
mamakin halayenta,saboda shi ko kadan ba haka ya saba gani ba daga wajen ruqayya. Bazai
iya cewa ga wata rana guda daya da ta gaya masa magana gatsau kwatankwacin ta Zainab ba.
Tsahon shekarun da suka dauka da zainab din duk wani abu da ya kamata yayi don gyara
bakinta yanayin mu'amala da tsaftarta yayi amma a banza. Sau tari hajiyarsa ke haqurqurtar
dashi daga kawo wasu qorafe qorafen,a danneshi duk da sunan 'yaruwarsa ce yayi haquri.

Bai taba kawowa auren zumunci da nasa illolin ba sai yanzu. Wasu lokutan yakan
tambayi kansa da kansa. Shin wai me yasa yayi gaggawar qara aure?,da ya tashi qara auren
kuma me yasa ya auri Zainab?. Duk sanda yayi wannan tunanin sai yayi istigfari,don ya
tabbatar Rabon haneefa da khaleel dake jikinta nasa ne,kuma dole sai ta haifa masa Kota halin
qaqa.

Farkon aurensu ya dauka zata daina zata kuma gyara,amma zuwa yanzu ya riga yayi giving
up,saidai bazai gaji ba bazai kuma daina saitata ba,hakanan bazai iya jurar wasu abubuwan
nata ba.

Hira sukeyi mai dadi da armashi tsakanin shi da ita da yaran. Irin hirar da yayi
tsammanin daga sanda ya kawo zainab din gidan ta gushe a tsakaninsu,saidai a'ah hakan bata
faru ba,duk da akwai abubuwa da yawa da har yanzun tunda ruqayyan ta ajesu a gefe
tsakaninta da shi bata dawo dasu ba. Abubuwa ne masu yawa da yayi missing dinsu sosai,ya
kuma saba da su,bai kuma taba zaton zata daina ba. Duk da bata cusguna masa ko hanashi
qara aurensa ba,amma hakan sai yake ganin kamar wani horo tayi masa me kama da turin
mutuwa,kuma har yau har gobe idan ya dauko zancan ta daina kaza bata taba bari suyi
maganar da shi.

A wani suya spot yace ta tsaida motar,ya buda murfin yana kallonta yana cewa

"Bari na siyo tashi watstsake" kunya ta kamata,saita kawar da kanta gefe tana murmushi.

Hannu ya miqa ya mintsina gefen cinyarta kadan yadda ba zataji zafi ba yace

"Kin ajemin saqo ne ai,kuma saqon ya isa inda ya kamata yaje...."

"Please su alhassan fa" ta fada tana kare fuskarta da hanun nata,sai ya qara girgiza kai ya buda
murfin motar yana ficewa.

Waiwayawa tayi ta yiwa su alhassan daketa hayaniya maganar su rage hayaniyar tayi
yawa,juyowar da zatayi kamar ance mata kalli gefenki. Kyakkyawan gani ta yiwa wasila zaune
cikin farar motar dake daura da su. Tana zaune a gaban motar ta bada dukka attention dinta ga
matashin saurayin dake zaune mazaunin driver shima yana dubanta.
Chiffon gown ce a jikinta sai yalolon mayafin da ya dace da material din,kanta ba hula ba
dankwali kana iya ganin gaban gashinta.

Wani malolon abune ya taso ya tokare mata wuya,duk yadda taso ta

9 / 24