Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : Taskar Novels
wani tarkace da zai dinga kawo masa tsaiko,ba
dattu da qananun abubuwa bisa hanyar. Ruqayya kadai tasan salon kalaman dake sanyashi
yaji ana tsinka masa tunani,kalaman da koda baiyi niyyar kasancewa da ita ba ya dawo babu
shiri,kalaman da koda cikin kasuwa yake ta furta masa su zaiji bashi da sauran burin da ya
wuce ya dawo gida ya kasance da ita,kalaman da zaijishi tamkar an daukeshi daga duniyar da
yake ciki zuwa wata ta daban (sune dirty talk,a hausance ana kiransu da kalaman batsa,Yake
budurwa?,kina yiwa saurayinki su koda shi zaki aura?,❌❌❌❌,hakan babban kuskure
ne,MIJI shi kadai ake gayawa maganganu na batsa,zaki samu tarin lada me dinmbin
yawa,nasan zakice kai?,a batsar za'a samu lada?. Eh tabbas!!!,muddin ga mijin da yake da
igiyoyin aurenki ne guda uku,BANCE SAURAYI BA!❌. BANCE WANDA KUKA KUSA KUYI
AURE BA!!!❌❌❌. Su wadannan yin wannan maganganun dasu ba abinda yake gadarwa
face zallar zunubi da tarun fushin Allah,UWAYEN GIDA DA AMARE KU BIYONI)
(Kowacce zuciya meson bin rudin shaidan ce da kuma son jin gard'in sabon Allah,dukkanmu
abinda ke mana waigi ahine tairon Allah tare da tsoron haduwa da fushinsa a ranar gobe. Duk
mace ko nakijij da kika basa sabon Allah,bawai don basa so bane,ko don ba zasu iya aikatawa
ba,aah.....zallar tairon Allah ne yasa akewa zukata waigi daga aikata hakan. To a wannan
zamanin wata fitina ta samemu,Allah S W T ya kawomu wani lalataccen zamanin da wai DIYA
MACE BUDURWA DA AKA SANTA DA TSANANIN KUNYA DA KAMEWA, KUNYAR DA HAR
AKE SUFFANTA KUNYAR MA'AIKI DA MISALIN KUNYAR BUDURWA saboda sanin tsananin
kunya da kamun kai da duk wata 'ya mace budurwa ke da ita. Amma anzo zamanin da yarinya
zata iya baje jikinta me tarin daraja tayi hoton tsiraicinta ta turawa wani,anzo zamanin da diya
macen da magana ke mata wuya gaban d'a namijin da yake ba muharraminta ba amma yanzu
zata iya baje baki suyi magana akan abubuwan da wata matar auren ko zaki saka kanta gabas
ba zata iya fadinsu ga mijinta ba!!!. Idan kika ga chart dinsu da ita saikin kisa sumewa. Toke
ladingo kina aikin me?,ke baki b'aro zantuka ba ga ladidi can tana ware miki tufka?,me take
gaya masa da ke ba zaki murje kunyarki ki gaya masa ba,BAKI AKA FIKI?,KO IYA GAYAWA
MIJI BATSA AKA FIKI?.
Ita zuciya tana da so da kwadayin sabon Allah duk kamewarta,saidai tuna girman Allah
da girman azabarsa zai sanya ka dinga tanqwarata kana hanata abinda takeso,ME ZAI SA BA
ZAKI TAIMKAKESHI BA?. Idan ma irin wamnan charts din ke burgeshi kuna zaune a falo kowa
da wayarsa amma irin charts din kukeyi ke dashi. A bedroom(kuyi haqiri ta kama na gaya muku
ne,saboda akwai mata da yawa da idan kikayi magana dasu akan wannan zasuce miki wallahi
basusan ma anayi ba,su kunya sukeji da sauransu) irin wadannan kalaman batsan da zaki
dinga fitowa baro baro kina gaya masa yana bala'in qarawa musu karsashi da kuzari me azabar
yawa,sau da yawa wasu guraren cikin littafi(nawa bansan na wasu ba) zakuji nace ya rada
mata wasu kalamai a kunnenta da suka bata kunya/ko ta qunshe kanta/kota gagara tsaiwa/ko
ta rada masa wasu kalamai da suka sanyashi sakin murmushi/ko ya qanqameta da
sauransu,dukka irin wadan nan kalamanne da bazaiyiwu ka fito ka rubutasu baro baro ba
sabanin yadda wasu marubutan ke rubutasun gayansu(muna musu fata da addu'ar Allah ya
ganar dasu gudun kada rubutunsu yayi waiwaye bayan dogon zamani ya tadda yara da
jikokinsu ya zame musu qaiqayi koma kan masheqiya ya ruguza ginin tarbiyyar da suke gani
sun bayar). Kunyar me zakiji ke da suke halal a bakinki tsakaninki da mijinki?,KIN GWAMMACE
WATA TAYI MIKI SHUKAR DA BA TATA BA?. Gwara ki tare ko ina,ki tare komai. Da masu
farautar sun fara gaya masa zaiga meye sabo a ciki?,ai wance tana gaya min su(kuma bayan
kin gama gayan masan kin kunna abinki ga magani a gefe zaki saukeshi,wadancan kuwa idan
abun yazo da sauqi basu da abinda zasu saukeshi dashi ta hanyar data dace kaman ke) zaiga
meye sabo a ciki?(idan ke zazzafa ce ma kin fisu iya tsara kalaman masu tayar da hankali zaiga
bashi da sauran lokacinsu). Mu cire kunya game da mazajenmu ta wannan fannin don
Allah,tako wacce siga mu dinga updating muna daidaita kanmu da zamani,KOWANNE NAMIJI
DAN DUNIYA NE(ba ina nufin duka 'yan iska bane a'ah,amma kowanne namiji yanason
rayuwa yana son holewa duk taurin kansa duk miskilancinsa) kada kiga mijinki ustaz ne ko
shuru shuru kice ai wane ba ruwansa wallahi KI GWADA KI GANI ZAKISHA MAMAKI
MUSAMMAN A OTHER ROOM sanda al'amura suka fara tafiya(DON ALLAH KARKICE KIN
TSUFA,KO MISKILI NE wallahi za'a yi babu ke,namiji baya tsufa shikam wallahil azeem,me
yasa idan sun auro sa'annin jikokinsu sai kiga sun zama tabararru kuyita zaginsa?,tana masa
abinda ke kike ganin tsufa yazo ba zaki masa ba,bayan cikin bedroom dinnan daga ke
saishi,ba'a taron assembly kuke ba....ku yafemin mommies). Wanda bakinsu haya
shuru kuma bance ki bawa kowa labari ba bayan kin gwada,kiyita blushing abinki idan
assignment dinki ya samu nasara,ki sake fidda wasu hanyoyin kuma a kanki,sai shawara da
zaki iya baiwa ga kowacce mace ta tsaftataccen harshe ba tare da kin bankadawa kanki asiri
ba. Allah ya dawwamar damu da mazajenmu,wadanda basu da aure ya basu ikon kame kansu
ya hadasu da mazaje salihai nagartattu.
*Ruwan wanka me kyau ta hada ta fara wanka farko. Ta sake hada wani zata sakeyi,har ta
dauko sabulunta yau kadai taji qamshinsa baiyi mata ba,ya tsaya mata a hanci da qirji,saita
maida ta buda shower gel dinta ta matsa ta fara wanke jikinta. Ita dinma hakanan taji kamar
wari wari takeyi mata,amma sai ta kauda kai cikin hanzari taci gaba da wankan tana Allah Allah
ta gama.
*********Tana zaune saman gadon asibitin bayanta jingine da bango. Tun a daren jiya kawo yau
idanunta da hanakalinta yana kan matar da suka kasance su biyu ne a dakin. Matar da qyar
take takawa cikin takatsantsan duk sanda zata shiga bandaki,amma jikinta da bakinta sun nuna
ras take,hakanan babu wani me jinyarta koda mutum daya ne,sai wasu nurses guda biyu dake
shigowa suyi hira su fice. Yadda suke magana da nurses din yasa ta fahimci kamar qawayenta
ne,kuma cikin maganar tasu ta fuskanci kamar dinki aka yiwa matar,saidai kuma dinki wanne
iri?,shine abinda hankalinta yafi karkata akai kenan taketa da kwadayin jin dinkin meye akayi
mata?.
Bata tashi fahimta ba saida nurse din tazo duba dinkin. Mamaki sosai ya kamata,iya
saninta masu haihuwa akewa dinki a wannan wajen,to amma ita wannan ai sam bataga alamun
ciki ko haihuwa tattare da ita ba. Hasalima batayi mata kama da matan aure ba,tafi mata kama
da irin matannan 'yan duniya.
Bata gushe ba tana ci gaba bin qwwqwafin matar,sai ta lura manyan wayoyi ne a
hannunta,hakanan manyan kudade take fiddawa tana kashewa ko a jikinta.
Tuni zuciyarta tayi nisa gurin son sanin wace matar?,wanne sirrine a tattare da
ita?,tayita Allah Allah hajiyayye ta fita,don ta shirya tunkarar matar qila ta samu wani haske
daga gareta.
Cikin sa'a hajiyayye kuwa ta fita dubiya can ward na yara,da sauri ta sauka a gadon
tana daura dankwalinta ta zura slippers dinta ta tunkari gadon.
Tana kashingide tana danna iphone14 dinta hankali kwance,sai ta daga kai tana amsa
sallamar zainab din tana binta da wani kallo.
"Sannu ya jiki?"
"Da sauqi" ta amsa ciki ciki tana ci gaba danna wayarta
"Ni sunana zainab,kuma nice nake jinya a dakinnan" ta fada tana murmushi
"Ayyah sannu" ta sake fada ciki ciki
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 19
https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA
HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU
QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA
MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har
zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________
Ta amsa ciki ciki tana maida hankalinta akan wayarta.
"Tambaya ce dani idan bazaki damu ba"
"Inajinki" ta fada ba tare data sake kallonta ba
"Don Allah kiyimin taimako ki gayamin meye amfanin wannan dinkin da akayi miki bayan ba
haihuwa kikayi ba?" Ta qarasa fada cikin d'ari d'ari tana dubanta.
Wani kallon tara saura ta watsa mata,don itakam tunda ta zauna a gurin hamamin jikinta
ya addabeta,batasan uwar da tasa ta kwaso jiki tazo zata dameta ba. Ta buda baki zatayi
magana daya daga cikin qawayenta nurses suka shigo
"Jimmy,ya dai?,baquwa kikayi?" Maida kallonta kan nurse din tayi
"Ni bansan me yake damun mutane da shiga sha'anin da bai shafesu ba....."
"Wallahi ba haka bane,ina cikin kaidin kishiya ne,mafita nake nema don Allah ki taimaka ki
gayamin" ta fada gabanta yana faduwa,kada taqi mata bayani wannan damar ta subuce mata.
"Malama me kikeso?" Nurse din ta fada cikin sakewar fuska
"Dinkin da aka yiwa qawarki nakeso ayimin bayani" murmushi ta saka suka hada ido da jimmy
din,sai ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar zainab
"Wannan dinki shine kankat a fannin matsi,babu wani magani da zaiyi miki abinda kikeso sama
dashi,yanansake tsuke gaban mace ya maidata tamkar budurwa 'yar sha hudu" . Tuni jikin
zainab ya dauki rawa,gaba daya hanakalinta ya daga,yanzun duk wayewarta a fannin matsi
akwai wani abu da yayi saura wanda batasan da shi ba?,ashe duk wayewarta bata kai
ba?,koda yake dai dama shi ilimi ance kogi ne.
"Don Allah malama ki taimakeni,nima inason ayimin,wallahi akwai matsala,na rasa hanyar da
zan mallaki hankalin mijina,duk wani abu da mace zata yiwa namiji don ta mallakeshi ta hanyar
shimfida nayi amma a banza,komai kyan magani nayi amfani da shi bana ganewa,idan kinga ya
nuna jin dadinsa to sanda ya fita hayyacinsa ne bazai iya mallakar kansa ba wajen nunan jin
dadin. Ni nafiso koda ba ranar girkina bane hankalinsa ya zamana yana tare dani,yana d'okin
dawomin,wasu matan naga har satar kwana akeyi a kansu,amma ni koda wasa bai taba yi
ba,tunda muka cinye amarci shikenan. Mijina ya auroni yana sona,ya auroni kuma don ya samu
'ya'ya dani,ni na fara haifa masa yara,amma bayan haihuwata ina yayewa saiga matsiyaciyar da
ciki,wai data tashi haihuwa saiga twince,ina sake haife na biyu saiga wani cikij still ta sake
haihuwa itama,wallahi malama asiri ne,ko cikin data samu aita hanyar tsubbu ne, mace batasan
gyaran HQ dinta ba,batasan komai ba......kunsan Allah na fita hasken fata nesa da kusa ba,ita
ko irin dan man nan da ake gogawa a murtsike baqi bata sawa jikinta,ko gashi ma wallahi
gashinta baifi rabin nawa ba...." Tana cewa gashi jimmy data saki baki tana kallon yadda take
zuba ratata kamar an kunna famfo ta maida kallonta ga sumartata. Baki ta tabe,ko ita da take
mace tsantsami ta bata ta yaya zata burge namiji?,aba a qudundune?.
"Don Allah nurse ki gayan bakya tsuke guri baka damsasashi ta yaya miji zai soki?"
"A'ah babu fa zee baby" nurse ta fada tana qarewa zainab kallo a fakaice dariya da takaici suna
kamata
"To kin gani.....yanzu yaushe za'a yimin dinkin?,kuma nawa ne?" Ido nurse din ta dan juya
"Eh to,ke zaki zabi watanni,dinkin kuma na musamman ne ai,a qalla zaki ajjiye dubu tamanin
haka,don idan akayi miki kuma shikenan keda neman maganin matsi har abada,shi kansa oga
idan ya kawo ziyara kullum inajin saikin taimaka masa zai samu gurbi" Duk da kudin da nurse
din ta cika mata yayi yawan da bata dasu amma kuma amfanin dinkin take dubawa. Fuskarta ta
yalwata sosai da fara'a
"To shikenan,yanzu dai bani da wannan kudin a hannuna,amma mai gidan zai tafi umra inajin
nan da kwana goma ne ko sati biyu,yana tafiya da sati daya za'a yimin kafin nan na hada
kudin,sannan ma zai kasance kafin ya dawo na warke,zansan yadda zanyi zan lissafa kwanakin
yabar qasar nan cikin kwanakina,yadda idan ya dawo kwanana ne "
"To shikenan,ba laifi " nurse din ta fada. Godiya sosai zainab ta dinga kwarara mata,tana ji a
jikinta lokaci yayi na maganin matsalarta. Wannan karon indai ta samu yadda takeso hatta
saleem sai ta garashi yadda takeso,ba kullum zai samu ba,don ta tabbatar muddin yaji yadda ta
sake komawa sai abinda hali yayi.
Bayan zainab ta wuce bandaki duban nurse din jimmy tayi
"Amma dai talatu baki da imani,yanzu don Allah don Allah inake ina wani dinki bayan ke kanki
kinsan ba'a nan akayi dinkinnan ba?,nazo ne kawai nan na warke saboda kawar da hankulan
jama'a?" Gyara zamanta tayi tana dariya
"Allah ne kawai ya kawomin rabona har gida, karba zanyi na kankareta na dinke abinda ya
samu"
"Amma dai da kin gaya mata gaskiya ina ganin da shi zaifi,taje ta fara gyara jikinta,baiiji irin
samamin da take bugawa ba?" Dariya talatu ta kece da ita har sai data kama bakinta ta riqe
gam bayan data tuna zainab din tana bandakin
"ke ni Allah yasa ma na iya bankadata,don wallahi wannan da alama can wajen ma ba
sauqi,danqari!" Ta sake fada tana dariya.
Tabe baki jimmy tayi tana gyara zamanta
"Kyaji dashi dai,ni mijinne ma nake ganin qoqarinsa da yake iya maaja din jikinsa da nata"
"Ke qazaman matannan ai jarababbun maza ne,yo ita ai na tabbatar miki ko abinci ya hanata ba
lallai ta damu ba akan ya hanata abinsa,shan HARKA MEDICINE ai yafi musu komai
muhimmanci koda sallah bata fiya samun lokacinsu haka ba" baki ta sake tabewa
"Lallai,irin wannan ba dole mu qadangarun bariki 'yan kwalta mu qwace musu maza ba,kiga
mace kamar tsohuwar jaka a gidanta amma wai a haka take so ta mallaki miji?,wata macen ko
ke bakya bata burgeki wallahi bare miji. Jikina talatu duk wata sai nayi masa gyara,gyaran fata
kawai fa na dubu hamsin,a turarani,a qamsasa ni,to ta yaya maza ba zasu liqemin ba?,kazo
nan kaji lumus,can qamshi can taushi,ka koma gida ka tarar da qamaya maya........Da anyi
motsi mace take miki namiji bashi da adalci,namiji dan kunama ne,namiji bashi da
mutunci,namiji batulu ne da sauransu,bayan ke kika siyawa kanki,habba.....muddin akwai mata
irinsu zainab a duniya to kasuwar karuwai ba zata taba mutuwa ba" Dariya talatu ta saka
"Yo yanzu wannan kika jera da ita ai cewa za'a yi 'yar aikinki ce"
"Allah ya kiyaye,wallahi ko masu aikina basu isa su zauna da irin wannan qazantar ba" jimmy ta
fada tana kyabe baki alamun mugun tsantsami ya kamata.
Ranta fes ta koma gadonta,duk bayan mintuna biyu saita kalli jimmy ta sakar mata
murmushi tare da yi mata sannu. Gaba daya jimmy ta gama tafiya da ita,jikinta ya bata tsabar
yadda HQ dinta ke a gyare ne take juya gidanta, don da ganin kura taci mutum,yadda jimmy din
keta wayoyi cikin isa da qasaita y tabbatar mata isassar macace ita a gidanta,kuma komai tace
tanaso zataji nurse tayi sallama ta miqo tace inji wane,hakan kadai ya isheta amsa.
Murmushi ya kubce mata,Allah ya nuna mata wannan ranar,ranar da saleem zai dawo
tafin hannunta,dole ruqayya ta dandana kudarta yadda ya kamata.
Tare suka jero shi da ita cikin asibitin,yana riqe da kwandon kayan abincin tana a
gefansa. Kallonta yayi kadan ta gefan ido
"Yane?,tunda muka shigo naga kinata faman toshe hanci?" Fuska ta yamutsa tana sake jan
gyalenta zuwa hancinta
"Warin asibitinne baiyimin ba,sai shigarmin hanci yakeyi yana damuna" ta fada tana jin har
cikinta yadda yake hautsina mata 'yan hanji.
"Sannu,ai ba jimawa zamuyi ba,nasan sallama likitan zaiyi"
"Ba komai" ta amsa masa tana sake toshe hancinta da kyau.
Sallamarsu ita ta farkar da ita daga saqar da takeyi cikin mugun zare. Tare suka daga
kai da jimmy kowa ya amsa sallamar gwargwadon muryarsa.
Fuska zainab din ta tsuke ganinsu tare,ranta ya raya mata ita ta riqeshi basu fito ba sai
yanzu har qarfe goma. Qarasawa ruqayyan tayi ta jawo kujerar da hajiyayye ta tashi dazu a kai
zuwa gaban gadon tana cewa da saleem
"Bismillah" kwandon ya ajjiye
"Kai haba,nifa namiji ne,zauna kedai"
"Muna gaisawa zan baku guri ai,ka zauna kafijin dadin dubata"
"Dubiyar kukazo ko wasan kwaikwayo?,ko baqincikin daka saba cusan na jiya da ba'a cusan ba
aka biyoni asibiti a cusamin" zainab ta fada tana hade fuska kaman zataci babu.
Bai dubeta ba yaja kujerar ya zauna,ruqayya ta matsa gaba kadan tana cewa
"Sannu maman haneefa,ya jikin?,Allah ya mayar kaffara"
"Gani me tulin zunubi ba,dole ki kiramin kaffara ga bijirarriyar musulma" ta maida mata cikin
zafi. Kullum sai taga wata sabuwar suturar a jikin ruqayya,kullum walau a cikin gida ko a waje
ruqayyan cikin ado da sauya suttura take.