Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : Taskar Novels
haka ne,zaki iya ci gaba
da bashi dukkan abinda yakeso daidai da wanda yake binki sau da qafa?" Kai ta girgiza alamun
a'ah,sai ruqayya ta gyara zamanta
"Sama da haka kikeyiwa Allah ta'addanci shin kin sani?,ya baki lafiya wadda bai bawa bayinsa
miliyoyi da suka fiki yi masa biyayya,ya baki ilimi hankali ya kyautata surarki wadda bayinsa
masu yawa da suka fiki binsa bai basu ba,kome kikeso ya baki shi kyauta ba da kudinki
ba,amma ya shata miki wasu layuka 'yan kadan yace kada ki tsallake sai kikayi kunnen uwar
shegu dasu. Kinsan cewa qarya kadai da kikeyi tana iya hanaki samun duk wani alkhairi a
rayuwarki?,SHAFA MAI DON KIYI HASKE da magungunan qarin qiba da kike sha kinsan su
kadai taka hurumi da dokar Allah ne?,SAKA FARCE KO AJJIYE FARCW A HANNU,QARIN
GASHI DAMA KO MEYE da kikeyi bakisan haramun bane?,ba mijinki ba,ko waye zaki yiwa da
sunan ado HARAMUNNE HARAMUNNE HARAMUNNE,kuma billahillazi la'ilaha illa huwa
yadda annabi yace meyi ba zatashiga aljanna ba bazataji qamshinta ba,idan duk duniya gatanki
ne ba wanda ya isa ya sanyaki shiga aljanna,bare uwa uba zuwa wurin malami ko dame yake
aiki muddin zai gaya miki abinda yake gaibu ko abinda yake a boye,don wasu suna rudarku da
ajjiye qur'ani da litattafan addini da rawani da carbi"
"Nima tunda nake ban taba shiga jeji ko zuwa gurin wani malami me kayan shirka ba sai wanda
na ganshi da litattafan addini........"
"Suma mushrikai ne,suna sanya litattafannne saboda ado su jawo hankalin mata masu sauran
imani,duk duniya ki gayamin WAYE YASAN GAIBU?,sai Allah shi daya sai kuma annabawa
yakan sanar dasu cikin abinda yayi niyyar su sani,SANIN GAIBU SAI ALLAH.......
*_ZAFAFAN DAI_*
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA
ALLAH_*❤❤❤
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA
HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN
MARUBUTA_*
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN
AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR... ZAFAFA BIYAR NAKU
NE_*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 28
________________________________
*_ZAFAFAN DAI_*
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA
ALLAH_*❤❤❤
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA
HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN
MARUBUTA_*
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN
AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR... ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
_____________________________
"mu'amala dasu bata qarawa bawa komai face cire masa imani da yaqini da
ubangijinsa,ta fidda maka dukka wani hasken tauhidi,ta cire maka wani ginshiqi cikin ginshiqin
imani wato yadda da qaddara me kyau da mara kyau,wasila.....ki kiyaye dokokin Allah sai Allah
ya kiyaye duk wani abu da kikeso,kiyi kishin Allah sai Allah yayi kishinki,ki gwada wasila da
iklasi da tsarkake niyya,wallahi wallahi wallahi Allah bazai baki kunya ba bazai bani kunya ba"
sai ruqayya ta zare hannunta a hankali daga cikin na wasila tana kallon tsakiyar idanun wasilan
wadda sannu a hankali maganganun ruqayya taji suna samun wani matsugunni me kyau a
ranta,irin matsugunnin da basu taba samu daga gareta ba.
Washegari da safe da hannunta ta tarkata duk wasu abubuwa da tasan tana ta'ammali
dasu ta qona,irinsu jan farce nail polish,ribbon din attachment,shi kansa gashin da ake mata
kitso dashi,ta cire sarqa qafa uban barimomin kunnenta,magungunanta da duk wasu takardu na
rubuce rubuce da malamanta suka bata sukace tayi amfani dasu, supplement dinta na qarin
qiba da haske dukka ta tattarasu ta qonesu. Bata cewa ruqayya komai ba,saidai ruqayyan taji
dadin hakan ta kuma tabbatar da cewa lallai komai yana da lokacinsa,yau dare daya wasila taji
nasiharta?.
Ko bayan sun gama buda baki a ranar saita kalli ruqayya
"Me dame kike ganin ya kamata na riqe a yanzu?" Sosai ruqayya taji dadin tambayar,ta saki
murmushi
"Muna lokaci na amsa addu'a,ki riqe istigfari ba kuma iya a baki kawai ba,duk sanda kikayi
istigfari din kiji har zuciyarki kina yine saboda neman yafiyar ubangiji akan zunubanki,kuma kina
yine saboda samun kusanci da Allah,ki yawaita ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika
astgis,Allahumma rahmatika arju,fala takilni ila nafsy darfata ainin,wa'aslihi li sha'ani kullahu
la'ilaha illa anta,sai uwa uba kuma shakundum salatin annabi muhammad S A W ko shi kika
riqe da istigfari sun isheki komai basai kinje gurin kowa ba,amma akwai babban abu muhimmi
guda daya wanda da yawan mutane basu sanshi ba....."
"Menene shi ruky?" Wasila tayi tambayar tana kallon fuskar ruqayya
"Husnul kulq wato kyakkyawar mu'amala"
"Kaman yaya?"
"Ma sha Allah" ruqayya ta fada tana gyara zamanta
"Ubangiji yana masifar kishin bayinsa,duk yadda kikai ga ibada da kusanta kanki da Allah
muddin baki da mu'amala me kyau tsakaninki da mutane bayin Allah to za'a iya cewa ibadarki ta
tashi a banza" idanu wasila ta fidda
"Kaman yaya?"
"Yauwa,zan baki wata kissa,watarana annabi S A W yana zaune da sahabbansa,sai akazo
wucewa da gawar wata mata,sai sahabbai suke fadin irin halayen matar,macace me azumi ga
ibada ga sadaka ga kuma tsaiwar dare,amma maqotanta basu tsira daga cutarwarta ba,sai
annabi yace wajabat,wato tabbata akanta,da sahabbai suka tambayi ma'aiki akan hakan sai ya
shaida musu ta tabe,yar wuta ce,kinga azuminta da ibadarta basu amfaneta da komai ba tunda
bata da mu'amala,sau da dama mutumin da yake da mu'amala me kyau da mutane yana iya
samun rahamar Allah bayan ya mutu koda kuwa shi din me yawan zunubi ne,sai yaci albarkacin
kyautata zamantakewa da bayin Allah" sosai jikin wasila ya sake sanyaya,tayi shuru tana
nazari,matan yayyenta duk da tana kyautata musu amma suna yawan kuka da halinta,kamar
ruqayyan tasan me take tunani ta sake cewa
"Abinda ka raina sai kaga ranar gobe babban abune a wajen Allah,ki zauna da kowa lafiya da
kyakkyawar zuciya"
"In sha Allah" ta amsa mata a sanyaye.
Tun daga ranar komai na wasilan ya canza,hatta da magana me yawa ta rage duk da
ita din gwanar surutu ce,ko yaushe zaka sameta da counter a hannu,koda ta sha'afa an fara
doguwar hira zata koma istigfar dinta da salatinta. Sannu a hankali sai ta dinga jin wata nutsuwa
tana saukar mata irin nutsuwar da tunda take yawan bin gifan malamai suke bata wurdodi bata
taba jin makamanciyarta ba,dukka damuwarta akan zaid sai taji tana gushewa,tsananin tunanin
zaid da takeji kaman zai zautar da ita sai ya fara raguwa a ranta,tana iya wuni ba tare data
tunashi bama. Har a ranta kuma takejin zata iya daukar kowacce qaddarar rayuwa da zata
sameta,samun zaid ko rasashi,taci gaba da addu'ar samun nagartaccen miji kadai wanda zai
zamewa rayuwarta alkhairi.
*_ZAINAB_*
Ko sau daya bata taba kaiwa hankalinta ga yadda dinkinta ya dinga zarewa zaren yana
ficewa ba tun baikai ace ta warke ba,ranar da taga zaren farko ta yanke abinta tana murnar
"Dinkinnan yayi mugun saurin warkewa,ga zare nan ya fice da kansa?, gaskiya ina da sa'a"
tsananin qazanta ya hanata jin tashi tashin da wajen ya farayi. Abun tun safina bata fara jinsa
ba har ta fara yi mata complain,sannu a hankali itama ta fara ji saidai kadan kadan,sai kawai ta
bagarar ta azawa ranta qaranta amfani da ruwan dumin da akace tayi amfani dashi da takeyi ne
ya jawo haka. Wannan ya sanya kullum sau daya a rana zata cika baho da ruwan dumi ta shiga
ta fito,a hankali ta soma jin qaiqayi,qaiqayin da yasa ta sake imanin dinkinta warkewa yakeyi
fes,abin yayi mata dadi saboda yazo ne dai dai sanda ya rage saura kwanaki biyar saleem ya
dawo.
******Zuwa lokacin ta fara jin sauqin laulayinta sosai,tana iya wasu abubuwa da yawa da
kanta,hakanan azuminta taba bakin qoqari taga takai,sam bata sanyawa kanta irin son jiki na
matan yanzu ba,wadanda daga ciki su da azumi sunyi hannun riga,idan ya sake zagayowa
kuma suce shayarwa,wata shekarar kuma an samu wani cikin,sai ka wayi gari da yawa yawan
mata suna wasa da ibadar azumi,wanda babbar masifa ce muke jefa kawunanmu,muna kuma
kwashewa yaran albarka don ta silarsu muke fakewa da qinyin azumin.
Tsaf wasila ta tayata sukayi kwalemar sashenta,don kada su jigata duka sai ansha
ruwa sukeyi. Gwanar tattali ce ita,kuma uwa uba tana Sana'a,gashi cikin watan da ciniki yake
yawaita,don haka cikin ribarta da abinda ta tattala din tayi siye siye,kusan tafi rinjiyar da komai
ga gyaran dakin saleem din,burinta ya dawo ya samu komai ya banbanta da sanda ya tafin. Tun
daga bedsheet blanket dinsa zuwa qananun underwears na ciki da curtains na dakinsa.
Kwanaki biyu ya rage ya dawo ta kirayi me qunshinta ta ta zuba mata jan lalle ita da iftee,aka
yiwa wasila itama a mazaunin qunshin sallarta,bayan ansha ruwa taje akayi mata wankin
kai,take gashinta ya qara tsaho da sheqi ta hadeshi cikin ribbon gwanin sha'awa.
*_ZAINAB_*
Kusan tunda lissafin kwanakin dawowar saleem ya fara matsowa nata dokin ya ninka
na kowa saidai ana iya cewa dokin banxa tunda nata tunanin yasha banban da na kowacce
mace me hankali. Gaba daya tafi karkata tunaninta wajen neman magungunan mata da zata
sake tsuma kanta da kanta a cewarta,dai dai da gyaran sashen ba abinda ta iya tsinanawa
banda dakin saleem din data gyara a daddafe,tana gamawa ta sharbe a wajen,bata sake
motsawa ba har sai da safina ta tasheta bayan ansha ruwa.
Da dan hanzarinta taso miqewa,saidai hakan ya gagara kwata kwata saboda wani
mugun riqewa da qugunta yayi.
"Wayyo na shiga uku" ta fada tana dafe qugunta hadi da ware idanu.
"Lafiya?" Safina ta fada tana kallonta,don ita kanta zuwa yanzu ta fara gajiyawa da abubuwa da
yawa na Zainab,Allah Allah take mijinta ya dawo ta tarkata ta barsu
"Mugun ciwo marata takeyi" ta fada tana yarfar da hannu
"Sannu,ki daure ki tashi saikisha ruwa kisha magani" ta fada tana kallonta. Ta jimaa haka kafin
ya saketa,ta miqe tana dafawa da qyar ta isa bandaki.
Saman tiles ta tsugunna zatayi fitsari duk da yadda safina ke masifa idan ta wanke
toilet din duk wanda ya mata fitsari a qasa. Maimakon ruwan fitsari sai ga jini yana fita da wani
butaci butaci
"Kaddai period ne yazo?" Ta tambayi kanta da kanta bayan ta gama fisarin. Cikin ranta ta
gamsu shi dinne,saidai kuma yadda taji jini yana bin jikinta sai abun yadan bata mamaki
"Koma meye kafin nan da ranar da zai dawo na gama period din nan,duk da ba haka naso ba
amma ba matsala" ta fada a ranta tana duba tsummokaran da take period dasu,don kudin
always dinta na watan shima ta sakashi a layin kudin magani.
Tana sakawa ba dadewa ya jiqe,sanda ta fiddo tsumman yawan jinin da wari warin da
yakeyi yasa ita kanta ta yamutsa fuska,a ranta tana tunanin maganin da ta shane da asuba
bayan ta gama sahur. Wasu tsumman ta ninka sukayi tudu sosai sannan ta samu yadan zauna
a jikinta.
Bata wani jima dashi ba shima taji ta fara leaking,sosai hankalinta ya fara tashi da
ganin yadda take bleeding. Daga daren zuwa safiya ita kanta tasan ta zubda jini sosai,cikin
zuciyarta kawai taji taqi yarda ko gamsuwa da zubar jinin, zuciyarta ta shiga raya mata akwai
wata a qasa,don haka ta jawo wayarta ta kirayi raliya abokiyar shawara.
Sun jima suna waya da raliyan,kuma dukka maganganun data gaya mata sun zauna
sosai a rai da zuciyarta,ta gamsu da maganar raliya,lallai ba makawa asiri ne,jifanta akayi,kuma
ba kowa bace da wannan aikin sai ruqayya,da alama ta lura da shirin da taketa yi da gyaran HQ
dinta don sake samun fada a wajen saleem,lallai kam wannan karon ba zata bari ba,koda bata
taba bin malamai ba a wannan karon saita taba ruqayya don ta nuna mata ba tsoronta takeji
ba,ba kuma wai finta sanin hanyar gidan malamai tayi ba,sai ta sanya an zubda cikin da take
taqama da shi,sannan kuma ta sanya a saka mata warin jaba ta yadda ko dosota saleem
bazaiyi marmarin yi ba,idan yaso ita da itan dukka su rasa ayi mutuwar kasko.
Tana saman kujera tana faman kada qafa hadi da lissafin dokin rano safina ta shigo
falon. Kallon safinan tayi sama sama ta sake maida hankalinta ga lissafinta,itama safinan bata
bi ta kanta ba ta samu waje ta zauna tana cewa
"Ba wani gyara ne da za'a yi umman haneefa?" Dan maida kanta kadan tayi ga safina
"Gyaran me?,wani abu ya lalace ne a gidan nan?" Kai ta mirgina cikin takaici amma ta danne
don har ga Allah tanason ta gyara din
"A'ah,ba babansu haneefa saura kwana biyu ya dawo ba?,banga kin canza komai ba"
"Me kuma zan canza?,dakinsa ne na shareshi yana kulle babu me shiga" haushi ya sake
kamata,ko ita da take budurwa ai tasan abinda idan mace tayi zai dadadawa miji matafiyi
"Haba ke kuma anty Zainab don Allah,share daki wani abune?,dakinma da daga shara ko goge
goge bakiyi masa ba?,bakiga momynsu alhassan ba?,bakiga har qunshi akazo akayi musu
ba?,ta wanke kanta ta gyare sashen har curtains naga ta canza......"
"To baqar munafuka" zainab ta fada tana gyara zamanta hadi da ajjiye wayar hannunta a gefe
"Da alama idan nayi baccin rana satar jiki kikeyi ki shiga wajenta ko?"
"Kinsan inda zan shiga idanunki biyu ma shiga zanyi.....ita tsafta ai bata boyuwa hakama
akasinta,ko kai makaho ne kazo gidan nan ka zauna zakasan matar tana da tsafta,don ko ta
sashenta kazo giftawa zakaji qamshin sashenta daban yake,kwalliyarta daban haka sutturar da
yaranta suke sawa ma atsaftace take"
*_Mu hadu anjima in sha Allah new page_*
*_ZAFAFAN DAI_*
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA
ALLAH_*❤❤❤
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA
HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN
MARUBUTA_*
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN
AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR... ZAFAFA BIYAR NAKU
NE_*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 29
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_Hanzarta kiyi joining group dina domin samun kaya masu tsananin kyau da quality akan
farashi me sauqi,siyan d'aya d'aya na cikin gida ko kuma sari kikeyi?, AKWAI RAGI DA DAMA
TA MUSAMMAN DAGA WAJEN MASU SARI,KAYANMU MU MUKE KAWOSU DAGA TURKEY
DA CHINA_*
*_Akwak bonanza da nakeyi time to time na kayana idan dama ta samu_*
"kin gama?" Zainab ta fada tana tsire safina da ido,safinar bata damu ba ta dora da fadin
"Kina ganin kamar maganin mata kad'ai shine sirrin mallakar miji?,wallahi ba anan take ba,shi
maganin mata shima ba kowanne iri ba ingantacce amintacce wani ciko ne na kwaskwarimar
halitta ga d'iya mace tunda hausawa sunce ko kana da kyau ka qara da wanka,wani namijin
kome zakiyi masa ba zaki burgeshi ba matuqar baki da tsafta baki da kalami baki da ladabi da
qanqan da kai,wani namijin kuma muddin baki iya abinci ba babu abinda zakiyi ki burgeshi don
a nan tasa jarabawar take,bawai gyaran can ciki bane