Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : Taskar Novels
kafin yazo ga buqatarsa. Akwai
banbancin da tazara me dinmbin yawa tsakaninta da ita,yana dukka iyakar qoqarinsa ne kawai
wajen kamanta adalci da boye hakan a mu'amalarsa da su gwargwadon iyawarsa,amma ko sau
daya zainab din idanunta basa gani.
A kullum zancanta daya ne zuwa biyu,ruqayya ta mallakeshi shi yasa sai abinda takeso
ake gani,baya kamanta adalci a tsakaninsu duk da qoqarin kyautata masa da takeyi. Ya rasa
wanne adalci take bida bayan wannan?,me takeso yayi mata?,da wannan tunanin ya isa
masallacin ya zare takalmin qafarsa ya shiga.
Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i,don gaba daya bashi da wani karsashi da
dokin zama a gidan gaba daya.
Kallon takaici kawai yabi dakin dashi,ya kada kai yana wucewa ciki ya ajjiye abun
sallarsa. Sanda ya dawo falon da niyyar zama ba komai dake kai kawo sai qaurin abinci,ya kalli
kitchen din kaman zaiyi magana sai kuma ya sake dauke idonsa. Wannan na daya daga cikin
dalilan da ya sanya kullum ta Allah muddin zai zagaya backyard na kitchen dinta sai ya taras da
uban lalataccen qanzo,qudaje da sauran qananun qwari suna parade akai iya son ransu. Duk
yadda zaiyi wajen kwatanta mata ta daina amma hakan ya gagara,a taqaice ma abicin store
dinta shine yake fara qarewa cikin gidan. Bama abincin ba,zai iya cewa kusan komai ma.
Kamar ko yaushe a nutse ta shirya cikin wani sassauqan riga da wando na pakistan
masi taushi da hasken launi,dan qaramin mayafin da kayan yazo dashi mai qarancin kaurin da
kana iya hangen gashinta dake gyare a matse cikin band ta lullubawa kanta,ta lakaci oil
perfume dinta ta shafe jikinta da shi sannan ta soma nufar qofar dakin.
Tuntuni saleem ya sanya haneefa ta kirayi yaran,har fateema iftee ta bisu. Su da yake
yara ne ba kasafai suke damuwa da yanayin dandanon abinci ba,koda sun gane dinma ba
wanda ke mata maganar don bata basu fuskar dauko zance su gaya mata ba.
Cikin rawar kai da karsashi taketa kai kawon jera abincin saman table mat din da suke
shimfidawa a qasa suci abinci. Yau din tana da hope tana kuma da mafi rinjayen yaqinin zata
shayar da saleem din abinda baya taba samu daga gurin ruqayya.
Hankalinsa na kan waya yana amsa kiran sanda take zirganiyarta. Maimakon qamshi
ya zamana abokin rakiyarta a duk lokacin da zata gifta din saidai akasin hakan ya biyo baya.
Duk da tayi wanka saidai za'a iya kiran wankan da jiqa jiqa kai tsaye,uwa uba ta hada gumi
wajen kammala girkin waje daya,bata saka koda alum ba bare turare,sai rigar data cire jiya ta
maida jikinta,a cewarta tunda dare ne kuma kwanciya zasuyi,ba sai tayi asarar ware wankakkun
kayanta ba. Gumin ya cakude da tsumammiyar rigar wanann yasa wani abu me kama da qari
qari ke tashi kadan kadan.
Dai dai sanda ya gama wayar ruqayyan tayi sallama a tausashe. Ya kashe wayar ya
ajjiye ta a gefe yana dan murmushi. Itama fuskarta a sake ta qaraso
"Sannu da gida maman haneefa" ta fadi da zuciya daya
"Yauwa" ta amsa mata saboda darajar idanun saleem din,sai dai a gajarce murya can qasa,
zuciyarta na quntata da ganinta a gurin. A son ranta taso ya qyaleta ko da iya yau kadai ne suci
abincinsu su biyu.
Daga gefe ta zauna,sannan tayi masa barka da warhaka a tausashe. Idanunsa yadan
lumshe yana amsa mata cikin kulawa,abinda ya motsa zuciyar zainab,sai ta dire masa plate din
abincin tana guna guni qasa qasa. Tayi bala'in tsanar dressing din ruqayya,takanji inama tana
da dama da kuma iko,da tabbas zata cinnawa sutturunta wuta ne su kama su qone qurmus.
Tanaso tayi bore akan hakan,amma tasan koda tayi aikin banza ne wai harara a
duhu,ranar data fara magantuwa akan hakan tayi qara wajen saleem amsarsa batayi mata da
kyau ba
"Nifa ban fahimci kwalliyar da maman alhassan ke shigowa da ita ba,bayan cin abinci akwai
akace tazo tayi ba nuna ado ba" ta fada fuskarta babu digon walwala a kai,don ba abinda ke
mata yawo a lokacin sai kallon da saleem yabi ruqayya dashi. Tasha jin ana cewa baqaqen
kaya basa yiwa baqi kyau,amma yau ita da kanta ta qaryata hakan saboda yadda baqar
atamfar tayi mata wani irin mahaukacin kyau
"Kaman yaya?,dama ita tsafta tana da ranakun yinta ne a taki fahimtar?" Sarai ta fahimci kamar
magana yakeson gasa mata,saita waiwayo itama tana dubansa tare da sake tsuke fuska
"Idan taso ta zama agwagwa ma sarkin wanka,amma ta tsaya iya ranakun girkinta,ban shiga
hurumin kowa ba,nima ba za'a shiga nawa ba"
"Bazan taba ce mata ta daina kwalliya ba idan ma wannan shine burinki,kema idan zakiyi babu
wanda zai hanaki,hasalima ina maraba da hakan kuma sai nafi kowa farinciki,haka siddan
kinason zama qadangaren bakin tulu "sai ya wuce toilet ya barta kawai.
"Kadangaren bakin tulu" tayita maimaita kalma,kasancewarta macace me bala'in tsarguwa da
sawa rai abu. Wayarta ta dauko saboda ta kasa nutsuwa da abinda yace. Ta bude data ta shiga
group dinsu ta kuma antaya tambayar bayan taqaitaccen bayanin abinda ya farun.
Cikin qasa da minti biyar kalolin amsoshi suka dinga fitowa,kasancewar group din group
ne da baya rabo da jama'a,amsoshin da kai tsaye suka fito mata da ma'anar abinda saleem din
ke nufi. Wayar ta ajiye ta koma gaban madubi ta zauna tana duban kanta. Har rana wayau ta
kasa gane me tayi wai da ya saka mata da tsanani yake mata kallon qazama,dame ruqayyan ta
fita banda baqar fata?.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 05
Ci gaba tayi da gunaguni,Kusan wannan dabi'arta ce,ta qware wajen mita da gunagunin
mai da magana a ciki. Nata ta zuba daban,sai ruqayya ta saka hannu tayi bismillah ta dauki
plate din ta soma zubawa tana fatar ta iya kai abincin cikin cikinta.
Allah ya sani har cikin zuciyarta tana jin qyamar Zainab,saboda ita din macace da
qazantarta bata boyuwa ko kadan. Mafi yawa duk farar mace qazantarta tafi saurin bayyana
saboda hasken guraben boye datti da take dashi. Misali yatsu da faratanta zuwa duga
dugi,zaka samesu a dafe ne ko yaushe,saboda bata damu data sanyawa qafarta lalle ba koda
qanqani,hasalima duk sanda me lallen ruqayya tazo yi musu kallon sakarkaru takeyi su
dukka,takan tabe baki tana juya kai da kafada,har cikin zuciyarta tana jin cewa ita dince mace
cikakkiya. Kamar wata rana da tayi subutar baki bayan saleem ya gaza daure kyan lallen cikin
dogayen yatsun ruqayya masu tsaho duk kuwa da cewa fatarta me dan duhu ce,amma sunyi
ma yatsun nata kyau sosai,ya yaba irin yabawar da har zuciyarta taji dadin hakan,sai taji ko
nawa ta kashe wajen yin lallen bata fadi ba
"Uhmmm,bonono,ana gyaran badini malam wa yake ta zahiri?,an bar qofar gari babu tsaro
amma an tafi ana gyaran cikin birni" a nutse ta daga kai ta kalli Zainab. Sau tari tana yawan
sake mata magana,saidai ita har zuciyarta tana jin cewa bata da lokacinta,muddin ta biye mata
kenan hakan yana nufin ita da ita basu da banbanci kenan.
Ba kasafai ta fiya sakin jiki ko hira da saleem ba duk ranar girkin Zainab din. Don a gurin
Zainab hakan ma duka laifi ne. Banda tsaiwar ruqayya da baiwa banza ajiyar zainab din,hatta
da kwalliyarta bataso saleem ya gani,bayan ita din koda kwalli da zai nuna anihin zatin kyan
mace bai dameta ba.
Wani irin zaman cin abinci suke mara armashi duk randa ya zamana ita ke da
girki,ruqayya na tafiya bisa tsarin hakanne bawai don tana tsoron zainab ba,a'ah......tun asali ita
din macace marason hayaniya da kuma tashin hankali,tana da wata irin nutsuwa da hankali
wanda ke sake fusgar saleem a tare da ita. Hatta da shi din da ya zama miji a gareta shekaru
kusan shida kenan,kusan komai nata da wani irin aji takeyinsa da zai nuna maka meye ainihin
ma'anar sanin ciwon kai.
K'ididdigaggun lomomi yayi yaji abincin yakai masa ko ina. Yasan dama za'a rina,a
lokuttan irin wannan yafi ta'ammali da fruit masu yawa da kuma damammiyar fura. Ko a yanzun
ma aje cokalin yayi
"Ina nonon da na aiko isma'il ya kawo?" ya fada yana zuba ruwa a cup
"Ba'a dama ba" bai damu ba don ya saba da hakan
"Dauko ki damamin inaso nasha" sai data cika bakinta da lomar abincin,kamar batasan meye
dandanon dadi bisa harshenta ba sannan tace
"Kamar fa yara sun shanyeta dazun,sun iso daga makaranta suna jin yunwa aiki yasha
kaina,ban ankara ba" ruwan ya dakata da sha yana dubanta. Ba sau daya ba sau biyu ba yasha
yaja mata kunne kan irin wannan dabi'ar tata
"Sau nawa zan gaya miki ne zainab?,duk sanda yara sukayi amfani da abinda bace a ajjiyemin
ki dinga daukan waya kina gayamin kafin na dawo gida na buqaci amfani dashi don na taho da
wani?" Kai ta langabe tanason gwada kissar da taga sauran mata nayi,duk da can qasan
zuciyarta fal take da haushi,komai fa ruqayya tana gani,kuma uwa uba a yadda take mace me
jajircewa da gyaran kanta dukkan ire iren wadannan tirjiyar bai kamata ta dinga fuskantarsu
daga saleem din ba
"To gashi na musanya maka da zobo ko?,kayi haquri ka sha" ta fada tana miqa masa bayan ta
zuba.
Duk da ransa ya riga ya baci,amma ya sani abune mai bata rai qwarai mace tayi abu
don saboda kai ka wofantar kaqi amfani da shi,don haka ya danne zuciyarsa ya amsa din.
Sanda ya fara shi ji tayi kaman anyi mata bushara da aljanna,farincikinta ya gaza
boyuwa har saman fuskarta
"Lallai da alama yau bazanyi asarar kudina ba" ta fada cikin zuciyarta tana jin wani dadi yana
ratsata.
Duk yadda tazo taci abicin ya gaza wuce mata saboda zallar rashin ma'anarsa,dole ta
ajjiye ta dauki wayarta dake ajjiye gefe tana fadin
"Nidai zan wuce,sai da safenku" cup din ya dire ya miqe kaman yadda ya saba
"Muje na taka muku" maganar ta fusgi zainab, fargabar kada yaje ya jima wani abu ya faru ya
sanyata miqewa
"Nikam dama kin tafi dasu haneefa wallahi" tayi maganar cikin son cusa wasi wasi a zuciyar
ruqayyan
"Ba school ne gobe?,nakega bacci ya kamata su kwanta ko?" Saleem din ya fada yana duba
agogon wayarsa. Ido ta kanne masa guda daya,ta matsa dab dashi sosai suna gogar juna
"Na maka tanadi ne dear,inason space" dan dauke kansa yayi gefe kadan ya kuma yi taku biyu
baya kadan ya rabeta yana yin gaba idanunsa akan ruqayya wadda har tayi gaba abinta. Yana
mamakin yadda gaba daya baki da jikinta baya cikin damuwar da zata zanya damuwarta a
kanta,baisan dsga safe har zuwa dare me takeyi da zata gagara tsaiwa gyara jiki da bakinta ba
"Suyi kwanansu a nan din" ya gadi yana qarasa ficewa. Qwafa taja tana dauke kanta daga
bakin qofar,bata karanci komai a fuskar ruqayya ba dangane da maganar ds tayi,taso qwarai
taga adadin tasirin da maganar tayi mata,taso ta kwana da abun ya hanata bacci, gobe da safe
kuma taga sauyin da zai qarasa gigitata.
Zaune yake daga gefan gadonsa,calculator da wasu qananun takardu ne a hannunsa
yana lissafin kasuwa. Sallama zainab tayi cikin doki tana shigowa dakin bayan ta kora su
haneefa dakinsu.
Kai ya daga ya kalleta yana amsa sallamar,bai qara koda second biyu ba ya ajjiye kan
nashi yaci gaba da aikinsa. Gaba gadi taci gaba da takowa cikin dakin da daurin qirjin da ta
sakeyi bayan ta cire rigar data maqala a dazun. Har ta gama abinda zatayi ta wuce gadon ta
sheme bai motsa ba yana qarasa lissafinsa.
"Daddyn haneefa.....kai nake jira fa,ka ajjiye aikin ka tashi ka cire kayanka mu kwanta" ta fada
tana daga kwancen. Kansa ya daga haushi da takaici yana taso masa,kamar wanda zasuyi
aikin gini ko na kauda itace,tana magana gatsau ba wani salo me jan hankalin miji a ciki?.
Idanunsa yakai kan qafafunta dake saman cotton bedsheet din nasa,wanda asali ruqayya ce ta
siyesu har guda shida tace ga guda daya kyauta ta bashi,saidai kuma a duk sanda yake
kwananta ne ire irensu take canza masa a bedroom dinsa dake sashenta.
Ba komai a qafartata face baqi da datti kwance qasan tafin qafartata,ga kaushi da
qananun faso da suka tsatsagata suka bawa datti muhallin zama me kyau. Daga saman
singalalin qafarta kuwa shima kaushinne da fata kanyi sanadin busawar sanyi sanyi da kuma
rashin bata muhimmanci wajen shafa mata mai akai akai.
Da ya maida dubansa ga zanin jikinta kuwa,farin siririn layin dake qasan bakin kowacce
atamfa dake dauke da sunan atamfar ya sirka laifinsa. Alamu dake nuna dattin atamfa da kuma
neman agajin wanki da takeyi. Hannunta na ajjiye daga qugunta,fararen faratanta da babu
digon Jan lalle ko baqi ko misqala zarratin na shimfide a jikinta. Sake gyara kwanciyarta tayi
tana jin farinciki cikin ranta,kallon da yake mata sai zuciyarta ta fara qissimamata lallai maganin
ke aiki a jikinsa. Eh zai iya cewa tunda ya zauna a gurin yakejin sauyin a jikinsa,saidai kuma a
yanzun da yake kallonta ya rasa wani abu guda da zaiyi masa tasirin da zai shauqantu zuwa
gareta. Tana murmushin haqoranta da suka komawa ruwan madara qarfi fa yaji suka
bayyana,ta miqa hannunta tana sosai gashinta dake a cunkushe wanda yaci arziqi saboda
zuwanta ta shafeshi da man gelo fes,abinda yasa yake fesar da wani qamshi mara dadi kenan
"Yanzu kin gama shirin bacci kenan?" Idanunta ta fiddo waje
"Eh mana,kai nake jira" ta fada tana murmushi dadi yana ratsata. Kansa ya mayar ga aikinsa
yana jin buqata tana tasiri a jikinsa
"Ki shiga toilet dina kiyi wanka ki fidda zanin nan,ki bude wardrobe dina akwai wata rigar bacci
black and white,ki dauki black din.
"Wanka kuma yanzu?,bayan tuni nayi wanka na?, gaskiya dare yayi" ta fada tana jin wata
muguwar ganda da qyuya tana ratsata. Ita batasan me yake damun saleem ba,ya fiya zafafawa
da yawa,shegen sanabe da tsafta kamar d'an kwad'i
"Umarni nake baki" ya fadi bayan ya dago idonsa ya zube a kanta.
Batason tayi asarar kudinta shine babban dalilin da ya sanyata ta jawo jikinta ta sauko
ba don taso ba. Ya bita da kallo yana girgiza kai. Wanka ma na shiga dakin miji sai ance da
mace tayi,wacce irin rayuwa ce a wannan. A sassan ruqayya shi ake sanyawa yayi
wankana,amma a nan sashen abun yasha banban.
Ko minti hudu batayi ba sai gata ta fito daure da maqalallen zanin da ya rasa na
meye,ta qarasa wardrobe din ta ciro rigunan kamar yadda yace,ta farke baqar tana dagata
sannan ta dubeshi
"Daddyn haneefa,rigace wannan ko matacin koko?"
"Shafa kiji" kawai yace mata saboda takaici,abinda yakeji cikin jikinsa zuwa yanzu ya fara
haukata,sai ya fara tattare kayan aikin nasa yana zubawa a bedside drawer dinsa.
"Nifa wadan nan rigunan banga wani amfaninsu ba,banda asarar kudi,abu kamar sange(ragar
net),da kudin aka baka ka qaro maganin harka da baifi ba wannan me zata tsinana maka,bakaci
a bakinka ba ba baka matsa a qasanka ba sai kuma ace tana da amfani" ta fada cikin qunaquni.
Qunaqunin da tsaf ya jita amma yayi banza da ita. Sai data gama qananun mitocinta sannan ta
saka rigar. Rigar tayi sama abinta,saboda bata bada hankalinta wajen daidaitata a jikinta
ba,gurin breast curves din yayi sama breast din kuma yana a qasanshi. Gwanace gurin shan
magungunan mata,amma sai bata taba lura da cewa breast na daya daga cikin abinda ke tafiya
da hankalin saleem din ba,itadai can qasan shine muhallin harinta ko da yaushe.
Duk wani lungu da saqo dake isar da saqo a jikin mace yayi qoqarin ya aika saqo
can,saidai da ya cusa kai ko harshensa wani qaqqarfan abu ke ingizoshi waje. Yayi wani irin
rudewa da gigicewar da shi kansa ya dinga tuhumar kansa abinda ke faruwa,saboda a yadda
yasan jikinsa yanayin da yake cikin ya wuce dabi'arsa. Duk sanda aka koroshin sai zuciyarsa ta
tunasar dashi BA RUQAYYA BACE. dole daga qarshe ya haqura da nufin aika zafafan saqonnin
ya koma kan hanyar da itama zainab din ta baje take jira ya isa ga gurin,a