Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : Taskar Novels
ya sanya ya bude motar ya fito hannunsa
dauke da ledoji,qarar rufe murfin motar yaja hankalin zainab dake kitchen,ta ajjiye ludayin
miyarta da sassarfa ta fito daga kitchen din ta isa window din da yakw sadata da kowanne kallo
da ya danganci harabar gidan.
Kamar zuciyarta zata fado sanda yake nufar sashen ruqayya,abinda tafi tsana kenan a
rayuwarta,duk kuwa da cewa ita dinma hakan yake musu,baya taba shallake sashenta idan ya
shigo sai ya fara dubata sanann ya wuce wajen ruqayyan yadda al'adarsa take kenan duk
sanda ya kasance kece da girki. A nutse ta sauke idanunta ga ledar hannunsa,tanaso tasan
meye a ciki?,saidai duk iya qwaqwarta ta kasa tantancewa saboda ledar baqace me duhu
babba da qarama.
Sakin labulen tayi yana jan tsaki,ta waiwayo ga haneefa wadda suketa wasan guje
guje,wasan guje gujen da ya qarasa hargitsa gyaran 'yar burum burum din da ta yiwa falon.
Tsawa ta doka mata sannan ta narka mata ashar
"Ga babanku can yayi sashensu alhassan,bishi ki ga me ya shigo da shi a baqar ledar
hannunsa" yarinyar kamar ba zataje ba,sai kuma ta zumbura baki tayi gaba
"Zakici ubanki da shegen rashin son aike" ta sake binta da zagin idanunta kamar zasu fado
saboda harara,sai kuma taja qwafa ta wuce bandaki a gurguje tanason watsa ruwa kafin yakai
ga shigowa.
Wani sassanyan yanayi ne da parlor din wanda ko yaushe baya rabo da shi saboda
tsaftar da ya kamashi. Komai na tsaftace ne akan tsari da sanin darajar muhalli.
Sassauqar doguwar riga ce a jikinta ta wani yadi maras nauyi ruwan madara me haske
sosai,kusan duk shigarta tana yinta ne bisa tsari da favourite colours na saleem din. Alhassan
da alhussain na zaune daga qasan carfet saman qananun duddumansu,kowanne jallabiyya ne
a jikinsa farare da qananun hulunan tashi ka fiya naci. Kyau yaran sukayi kuma duk wanda ya
kallesu dole su bashi sha'awa.
Sallamar uban ta sanyasu hankulansu yowa kansa,al_hussain shi ya fara yo gaba
yana qoqarin karbar ledar hannunsa hadi da fadin
"Abba sannu da zuwa" wadda suka furtata kusan lokaci daya da al_hussain dake daukema
abban nasu pillow daga saman kujerar don ya samu wajen zama.
A duk sanda ya sanya qafafunsa a sassanta yakan jishi tamkar cikin wani muhalli na
daban yake ba'a cikin gidan ba. Sau tari yakan tambayi kansa da kansa
"Me yasa ya qaro aure?" Wani lokaci zuciyarsa da kwanyarsa kanyi hadin gwiwar bashi amsar
"Rabo". Kamar ko yaushe a yau ma amsar da ta bashi din kenan,wanda yayi dai dai da ajjiye
kaskon turaren wutan dake hannunta,ta kuma sauko daga dining area din yana gyara zaman
dankwalin kanta me sulbi tana fadin
"Barka da warhaka"
"Barka kadai" ya amsa mata yana bin su alhussain da kallo wadanda suka nade abun sallarsu
suka wuce dakinsu.
Hannun 3sitter din da yake kai zaune ta zauna itama,idonsa ya dawo dashi kanta
lokacin da ta miqa hannu ta jawo gorar ruwa me matsakaicin sanyi ta zuba glass cup tana miqa
masa. Sai da ya saki murmushi sannan ya miqa hannu ya karba,ya shanye tas sannan ya miqa
mata cup din
"Na rasa wacce irin baiwa ce dake da har kike gane yunwata da qishirwata ba tare da na furta
ba" murmushin ta kuma sakar masa
"Da kallo guda daya tak da zanwa idanunka na gama samun amsar komai" kai ya gyada cikin
gamsuwa tare da jin matsayinta yana sake zarcewa wani madaukakin muhalli a zuciyarsa.
Kullum wayewar gari sai ya godewa Allah da bai bawa shaidan galaba a kansa a shekarun
baya ya ingizashin da zai zama sanadiyyar rasa ruqayya ba,inda hakan ta faru?,yanzu da a
wanne gurbi yake a rayuwa?.
"Amma,me yasa ba kowacce mace ke da wannan baiwar ba?" Idanunta ta dan janye daga
kansa,jikinta ya bata inda maganarsa keson dosa,don haka tadan juya ido kadan
"Ya danganta da yadd kika zabi ki fuskanci mijinki ko ki mu'amalanceshi,hakanan ya danganta
da iya adadin lokacinki da kuma kulawar da kika bashi".
"Sai yaushe zainab zata dinga fahimtar irin wadan nan abubuwan tayi koyi dake ta kuma
canza?" Dauke kanta ta sakeyi a karo na biyu. Duk girman matsin da zaya shiga muddin akan
zainab ne bata da sha'awar ta shiga lamarinsu,lamarin miji da mata sai Allah,duk yadda take
gani a yanzun a wata ranar tana iya ganin sauyin hakan a tattare dashi,duk da cewa zuwa
yanzu ta jima da mance wannan lamarin
"Ba'a sassa na kake ba,kada maman haneefa taga ka jima da yawa" ta fada tana miqewa,
miqewar da taja hankalinsa har ya gaza dauke dubansa daga kanta
"Au korata ma kikeyi?" Ya jefa mata tambayar da kafin ta bashi amsa turo qofa da shigowar
haneefa taja hankalinsu.
Rarraba ido ta fara yi tsakanin fuskar abban nasu da ruqayyan. Har cikin ranta
ruqayyan tana jin babu dadi. Yadda yanayin tarbiyya haneefa take a gidan,akwai sakaci na
bala'i daga wajen mahaifiyar da bata cancanci zama uwa ba. Duk da haneefa ta girmewa su
alhussain nesa ba kusa ba,amma akwai nisan tazara me yawa a tsakaninsu,tun daga
hankalinta zuwa nutsuwarta.
Tsuke fuska saleem yayi ransa na baci,a tsawace yayi mata magana
*HUGUMA*í ½í±‘
https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 04
"Halan baki iya sallama ba bare gaisuwa haneefa?" Ta tsorata ainun,don duk yadda
yake sakewa da iyalansa amma sun sani,muddin ya dauki zafi da kai ko fushi to zakaji babu
dadi
"Sannu da zuwa abba,ina wuni?" Ta fada tana hade maganganun duka guri daya
"Koma kiyi sallama" ruqayya ta fada a sanyaye. Sakin labulen yarinyar tayi ta juya zuwa
waje,haushin tsawar da akayi mata tana cikata,tana ji a ranta maamantata ce ta jawo mata.
Irin yadda taga su alhussain din sukayi haka tayi,ya amsa yana dauke kai,saidai cikin
ransa yaci alwashi bazai dauki wannan sakarce sakarcen da yayi imanin laifin na Zainab
ne,dole ya zauna da ita ya kafa mata sharudda da qa'idojin da zata yawaita tunawa kanta bazai
dauki irin wanann ba.
Ledar hannunsa ya miqawa ruqayya babbar
"Ga mutanen naki" murmushi ta saki cikin jin dadi,kamar yasan a daren tana da buqatarsu,duk
da al'adarsa ce tunda kayan suka zama abebadan shanta
"Na Gode qwarai qwarai,kaima Allah ya faranta maka ya qara budi da wadata"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu, your prayers are my strength" ya fada yana dan lumshe ido.
Idanunta ta kada masa tana murmushi,ya zare nasa idon da sauri yana yin gaba
"Inda zan zauna n qara awa daya tak zaki cikamin kunne da magiyar na tashi na tafi yanzun
kuma kina yin abubuwan da sun saba doka da qa'ida irin ta yau" dariya ya bata sosai,sai ta
rungume ledar ta juya zuwa cikin kitchen don ta wanke kayan ta kuma adanasu cikin fridge.
Shigowar haneefa ya sanyata dungure man data dauko zata shafa ta waiwayo tana
bada hankalinta ga yarinyar. Tun kafin ya gama shigowa ta kasa jumurin jira
"Me ya shigar musu dashi?,ina ledar?" Baki haneefa din ta tura alamun dake nuna tsiwa ta
zauna mata sosai a jikinta
"Ina zamana kin saka anyimin fada harda tsawa"
"Ba wannan na tambayeki ba leda nake tambaya" ta fadi tana zaro idanu cikin takaicinta tana
duban haneefar
"Ya bata" ta amsa mata a a taqaice
"Ya bawa wa?" Zainab ta fada tana zaro idanu cikin jin bala'i da tashin hankali
"Mommyn alhassan"
"Lallai yau an taro fitina a gidan nan,wallahi bazan dauki irin wannan abun ba" ta fada tana jin
kamar zata dora hannu a kai ta rusa kuka. Tako ina saleem cikin jawo abubuwan da zasu kawo
rudani a zamansu yakeyi,rashin adalci tako ina yake gwadawa rayuwarta,duk qoqarin da ita din
keyi na ganin sun zauna lafiya ita kuma ta faranta masa.
Tana tsayen da daurin qirjinta hannunta riqe a qugu ya tura qofar dakin hadi da
sallama ya shigo.
Kamar me ciwon wuya haka ta waiwayo da qyar tana amsa sallamar,bakinta zaka dauka
ya cusa lomar biredi ne data hanata yin magana da kyau.
Tuna fadan da ya gama yi mata yanzu yanzu ya sanya haneefa juyawa ta fice a dakin.
A nutse ya qara takowa ciki yana karantar yanayin dakin. Mutum ne shi me wani irin
qaqqarfar halittar jiyo qamshi ko warin abu,don haka a yanzun ma kusan abinda hancinsa ke
jiyo masa sam baiyi daidai da abinda zuciyarsa keso da muradi ji cikin gidan sa ba.
Mayar da dubansa yayi gareta,tana tsaye qerere tana binsa da kallon da baisan daga
ina ta samoshi ba. Cikin daurin qirji,gashin kanta me tsaho da laushi ya samu guri ya cure
abinsa saman kanta,wanda hakan ke nufin akwai dauda da rashin tajewa da ya zama silar
wanzuwarsa a haka. Kauda idanunsa yayi,don idan da sabo za'a iya cewa ya riga ya saba.
Cikin ranakun mako guda bakwai zaiyi wahala zainab din ta tsallake kwana biyu ba tare da ya
ganta da daurin qirjin ba,walau da safe ko da dare kamar haka,ko yanzunma yasan qilan dashi
ta wuni,bayan tasan babu abinda yafi tsana irinsa
_Note:Da yawan maza sun tsani wannan al'adar,domin bata da wani alfanu sai canzawa mace
yanayi,musamman idan ta hadu da nau'i na qazanta irin ta zainab,akwai wasu lokuta da mace
kanyi daurin qirjin don jan hankalin miji,in a stylish way,ta yadda zaki daure bakin zanin a
tsakiyar qirjinki kamar kin qulle abu,ki koma sassauto da zanin zuwa rabin qirjinki wanda hakan
zai bashi damar gano pant da wasu sashe na breast dinki,bawai daurin qirji irin wannan na
gargajiya mara ma'ana ba da fallen zani me dauda_
"Sannu da zuwa" ta fada da qyar a hakanma tana tausar zuciyarta ne gudun kada daren yau din
ta sake tafka asara kamar yadda tayi a jiya
"Yauwa,ya gidan ya yaran"
"Lafiya lau.....mu ina tamu ledar?" Ta tambayeshi kai tsaye tamkar ita ta aikeshi. Daga kai yayi
ya dubeta yana maimaita tambayar da tayi masan,qasan ransa mamaki yana cin ran nasa. Ya
akayi tasan ya shigo da leda?,har yanzu bata daina wannan dabi'ar tata ba kenan ta shegen
sanya idanu a shige da ficen kowa na gidan?.
"Oh wadda kika aikeni da ita?" Dan sararawa tayi kadan,saboda amsarsa ta bata hasken inda
ya dosa
"A'ah,ni ban aikeka ba,wai saboda naga yara sun ganka da leda ya kamata suma ace an basu
ko tunda suma 'ya'ya ne kamar kowa" ta fada tana murmushin yaqe.
Takaici ya qumeshi sosai,wai ita a hakan fa ta qure dukkan iyawarta ta gaya masa
magana me dadi kenan. Miqewa yayi daga dosana zaman da yayi saman stool dinta
"Abinda yake ciki ba cimarki bane,fruits ne,ke kuma nasan babu daya a ciki da kike ci,itace me
ta'ammali dasu kullum shi yasa nakai mata na dibarwa su haneefa,duk da su dinma sun koya
ba lallai su iya shanyewa" ya bata amsar yana nufar qofa.
Kallo ta bishi dashi tana tabe baki,a ranta tana jin kawai zallar mugunta ta sanya
ruqayya ta sakashi siyo fruit din. Wannan shan fruit da cin ganyayyakin nata yana masifar qona
mata rai,aikinta kenan kullum kamar wata raquma
"Ni bazan zauna ina fama da 'ya'yan itace ba,nafi qarfin gaban nan,mu saidai mu rungumi
qwaryar qwayoyi musha muyi tatil mu gigita mutum" ta fada qasa qasa tana shafe fuskarta da
mai,koda ta gama kuma bata nemi powder ba bare turare ta fara laluben kayan da zata saka.
A gajiye ya tura qofar dakin nasa da shirin fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa ya wuce
masallaci yayi aallar magariba. Cikin qasa sa second biyar dukkan wannan karsashin nasa da
dokin ya fita a kansa gaba daya.
Yadda ya fita yabar dakin da safe haka ya sameshi,babu wani abu da ya sauya. Hatta
da comb da ya taje kansa kafin ya fita yana zaune abinsa dungurgur saman madubin. Numfashi
ya zuqa ya kuma fesar zuciyarsa na wani irin tafasa. Ya sha gaya mata,a duk sanda qazantarta
ta motsa taje ta qarata,tunda yayi iya yinsa,to amma ta tabbatar qazantar bata shafi komai nasa
ba.
Murfin qofar ya saki bayan ya jingine briefcase dinsa jikin bango ya koma da baya falo
inda yabar yaran. Duban ledar da ya ajjiye musu yayi,sun gutsutstsura fruit din kawai sun barshi
sai ma bata gurin da suka sakeyi. Daga khalil dake da shekara shida har haneefa din dake da
shekara goma cikin ta sha daya rasa me hankali yayi a cikinsu. Alhassan da alhussain dake da
shekaru takwas cikin ta tara ya tuna,a wadan nan shekarun nasu sun iya share guri suyi
mopping fes,sun iya wanke wanke da wanke qananun undies dinsu na mamansu dana
qanwarsu,a yawancin lokuta har fada yakan yiwa ruqayya,saidai ta langabar da kanta
"Ka bari sunyi mana daddynsu,idan basuyimin ba wa nake da da zaiyimin,sannan wataranma fa
suma mazan auren wasu ne,idan suka iya ai kaga har matan da zasu aura sun huta
suma,wataran sayi karba a aikin gidan,ko kuma wata lalurar idan ta samu matayen ko?" Hanci
ya lakace mata
"A fakaice dai ni kike zagewa fa rukky" dariya ta saki tana riqe yatsunsa
"A'ah wallahi daddy,rainon inna ne fa kai?,kaima ai koda bata koya maka aikin gida ba aita koya
maka abinda yafi wannan muhimmanci,iya kula da iyali,zuciyar soyayya da tausasawa da kuma
kyautatawa" yadda kalaman suka fita a bakinta sun sake ninka kimarta a zuciyarsa,sun kuma
sanyashi yana sake jin nauyinta da kuma rashin son tuna wasu abubuwa da suka wuce a baya.
"Kiramin mamarku" yace da khalil,bayan ya wuce ya kalli haneefa
"Haneefa"
"Daddy" ta amsa
"Ki tattare wannan abinda kukaci din ki sakasu a fridge,sauran ki saka a shara,duk abinda
bakuci idan na kawo ku daina lalatashi irin haka,saboda qannenki zasu gani su koya ne"
"Tom" kawai tace tana miqewa cikin sakalci ta soma gyaran wajen,wanda kana gani kasan bata
saba ba kwata kwata.
Kanshi ya girgiza kawai ya koma bedroom din nasa. Tsaho wasu mintuna bata iso
ba,har ransa yaso ya soma baci,sai kawai ya miqe ya soma rage kayan jikinsa yana dorasu
saman wadanda ya ciresu da safe.
Sai da ya kammala sannan yaji ta turo qofar,still da uban daurin qirjinta na dazu,ya rasa
me takeyi tun shigarsa dakin da fitowarsa kawo yanzu da bata nema wani abun ta saka ba ta
raba kanta da daurin qirjin nan
"Gani" ta fada tanason nemo dakiya a ranta,saboda tun shigowarta ta gama gano abinda ya
farun. Shaf ta manta da wani batun gyaran dakinsa gaba daya,tunda ta zauna yau qoqarin
neman maganin da zaiyi mata aiki sharp sharp shi da ita takeyi,kuma ko yanzun alhamdulillah
ta fara jin alamun hakan cikin jikinta,saura shi.
Waiwayo yayi yana qoqarin hadiye bacin ransa ya dubeta,sai ya hangi khalil kusa da
ita
"Wuce falo wajen haneefa" yace da yaron,bacin ransa yana sake tasiri. Kwata kwata basu da
tsarin shiga guri daga shi har 'yar uwarsa,ko ina ma suna iya bin iyayen ko su shiga ba tare da
rarrabe dacewa ko rashin dacewar hakan ba,yau ya kawo qarshe kuma dole ya sanyata ta
gyara ginin data bata,bazai bari suci gaba da girma akan haka ba.
"Haka ya kamata dakina ya zama?" Ya fada yana tsareta da kallon tuhuma bayan ficewar khalil
din. Hannu ta saka ta sosa kanta
"Wallahi na sha'afa ne inata aiki tun safe"
"Eh naga alama a gidan ai" ya amsa yana juyawa abinda ya shige bandakin.
Bai iya wanka a ciki ba saboda Allah ya zuba masa tsantsami,sai daya zazzaga garin
klien hypo da ruwan izal ya wanke toilet din fes da kansa sannan ya hada ruwan wanka. A
gurguje yayi wankan saboda gudun qwacewar lokaci,saidai duk yadda yaso ya fita akan karin
sai da lokacin ya kusa qwace masa,abu na biyu daya tsana ya rasa jam'i,yana fitowa ya zura
jallabiyya kawai a gaggauce ya fice.
Bazai iya tuna randa yayi missing sallahr magariba ba duk sanda yake sashen
ruqayya,saboda komai da tasan yanaso tana tanadar masa