KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   10 / 24

27K to 30K   out of 69.9K words

hana kanta fita
amma hakan ya gagara,saita waiwayo ta kallo alhassan

"Kada ku fito ina zuwa" ta cire key din motar ta fita tana dosar motar.

Daga baya baya ta tsaya tayi musu knocking,dukka su biyun suka leqo ita da
saurayin,saidai kuma kamar yadda taso wasilar ce ta ganta sosai.

Sosai fuskarta ta nuna mamakin ganin ruqayya da dan shock kadan,amma saita daure
ta bude murfin motar ta fito

"Ya na ganki a nan?" Wasilan ta tambaya

"Ke za'a yiwa wannan tambayar ai wasila,umma tasan da fitowarki?"

"A'ah don ba jimawa zanyi ba" haushi da takaici suka cika zuciyar ruqayya. Ranta idan yayi
dubu ya baci

"Yanzu don girman Allah hakan mutunci da martabar ahalinmu kika siya mana ko sarayarwa
kikayi?" Ta mata tambayar hannunta goye a qirjinta. Hannu wasilan ta yarfar tana dan buga
qafa

"Kin cika matsala wallahi ruqayya,yanzun wani abun kikaga inayi?,kun hanani karbar waya na
haqura,yanzu 'yar pizza da shawarma din ma da zan karba sai ace a'ah don me?"

"Idan yaa Bashir ya ganki kuma kice masa me?" Ta tambayeta tana ritsata da idanu

"Yayi miki fada kice an matsa miki ko?"

"yanxu yanzu zan koma,don ma sun jima wanda muka saka order din wajensa bai kawo ba da
bazaki sameni a nan ba bare akai ga yaa bashir" kai ruqayya ta jinjina cikin zafin rai,dai dai
sanda saurayin ya leqo yana cewa

"Baby zo mu wuce gashi an kawo" wani kallon bamza ruqayya ta watsa masa,sannan taja
hannun wasila kai tsaye ba tare data tsaya saurarenta ba ta wuce mota da ita.

Kaman qaramar yarinya ta bude mata seat din baya ta turata,itama ta koma
mazauninta ta balbaleta da masifa. Tun wasilan na kare kanta har ta kasa cewa komai sai shuru
da tayi tana bin ruqayyan da kallo

"A irin wannan abun kinsan 'yan mata nawa ne suka rasa budurcinsu?,kinsan yammata nawa
aka yiwa ciki wasu suka haihu?,kinsan cewa daga zarar kin daga qafa kin shiga motar saurayi
baki da guarantee akaran kanki dama abinda zai sameki?,kuma ko meye ya sameki ke kika
rattaba hannu akan hakan"
"ki daina wannan batun mana haba,nace na daina"

"Kindai fada yanzu,kuma tabbas kinsan maso abinka ai ya fika dabara ko?"

"Don Allah mana ruqayya" inda taga wasila na kalla ta maida hankalinta,sai taga saleem ke
tahowa,alamu suna nuna batason yaji zancan

"Saina gaya masa ai kima daina wani boye boye"

"Ki rufan asiri karku cinyeni,ki barni na dan karbo pizza din mana na saka rai"

"Ko mayya ce ke saidai ki mutu" ruqayya ta fada tana tayar da motar kafin saleem ya qaraso ya
bude ya shige.

Baice komai ba sanda tace zasu aje wasila gida duk da yasan ba tare suka fito
ba,mutum ne shi da ba akan komai yake magana ba musamman akan lamuran ruqayya,ya sani
duk da dan adam ajizi ne amma komai tana yinsa ne bisa doron hankali da sanin abinda ya
kamata.
Sai da suka sauketa ta dauki tata ledar da saleem ya bata ta miqa wasilan taja motar
suka wuce.

*_ZAINAB_*

Tunda ta isa gida ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda wani mugun kartawa da cikinta
yakeyi. A iya tunaninta a gidan sunan yau duka bata ma wani ci cikakken abinci ba,saboda

batason cikinta yayi cushewar da magungunanta zasu kasa samun matsugunni a cikinta.

Duk da kartawar cikinta amma hakan bai hanata dage labule lokaci lokaci ba tana
hangen gurbin da ruqayya kan aje motarta,har yanzu bata dawo ba,kuma yaran sun gaya mata
ga abbansu can ya fita sanda suke shigowa gidan a tata motar.

Koda ba ranar girkinta bane ta tsani taga saleem din sun fita da ruqayya,takanji
zuciyarta kamar zata faso qirjinta. Tasha gwada su fita din itama dashi amma sai ya noqe ko ya
kawo uzurin rashin kudin yanzun sai yace sai wani lokacin

"Amma inda ruqayya ce ba wanda zaiji bari ya gani,saidai mutum kawai yaga ka shigo yi masa
sallama,kuma lokacin da nake waje ai baka taba kawomin uzuri ba idan na buqaci mu fita,sai
yanzun da ka gama cin moriyar ganga ko?" A lokacin tashi yayi sosai yana dubanta. Harshenta
kullum a tsaye yake carrr kamar wadda ak yiwa gorin harshe. Yana mamakin tarin rashin
hankali irin na Zainab din,a lokacin da take maganar kudade masu yawa ya kashe a ranar ya
gyaro mata wayarta data barwa yara suka jefata a ruwa,ko awanni biyu ba'a cika ba amma take
wannan qorafin

"Itama duk sanda kikaga mun fita din cikin ribar business dinta ne,kinga baki da bakin yin
qorafi,tunda dai tare na raba muku jarin nan,amma naki har yau bansan ina yake ba,bansan
kuma taqamaimen abinda kikayi dashi ba" fuskarta ta bata sosai. Tayi mugu mugun tsanar ayi
mata zancan ruqayya bare jarin da tamkar bakin wuta aka bata. Duk da tasan ina ta zuba kudin
suka narke,amma baqincikinta yadda ta saka rai kudin zasu jawo ninkinsu amma sai abun ya
tabarbare mata kudin yabi ruwa.

"Ni ina ruwana da wani business dinta?,nidai abinda na sani kawai cikin gidan nan sam ba'a
kwata adalci ba,inda kasan ba zaka iya ba da barina kayi gaban iyayena baka nuna duk duniya
babu yani ka tattagoni ka kawoni gidanka ka hadani da makirar matarka me shegiyar kissa da
kisisina wadda babu Allah a ranta" daga wannan maganar ta miqe ta fice daga bedroom din
nasa, ficewar da bata sake dawowa ba sai da safe.

Ko kadan bai wani damu ba,bajewa yayi abinsa yayi kwanciyarsa. Don a ranar dama
tuwo tayi musu,miyar ta cika daddawa har tayi baqi warinta yayi yawa. Da zanin data gama
madaqalar tuwon dashi ta shigo masa bedroom,ba niyyar wanka bare brush. Tunda ya kwanta
bai tashi ba sai da safe,kullum dai baya gajiya da mamakin yadda kishi ke rufe idanun zainab
din ta gaza koyi da abinda zai amfaneta.

Horn din motar da taji ya sanyata miqewa daga kujerar da ta tattakure,zanin atamfar
jikinta ne tayi daurin qirji dashi sai dankwalin data daure kanta shima dashi. Ko kadan bata
damu da kayan jikinta masu tsada bane,idan ta dawo unguwa ta nema masu sauqin ta saka ba,
hakanan zata wayi gari dasu taci gaba da sabgoginta,ita da cire zanin har sai ita a karan kanta
ta tabbatar yayi dauda yadda ya kamata.

"Umma ni bana hangowa" khalil da yabi ta qasan uwar ya fada yana tura kai jikin window din da
zainab ta yaye labulen tana son ganin tare da waye ruqayya ta dawo?. Daidai sannan cikinta ya
sake kartawa tasa hannu ya dafe amma duk da haka taqi gusawa daga wajen sai taga abinda
takeson ganin.
*HUGUMA*👑

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 13


https://www.mkdatasarvices.com.ng


*MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽

*_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA
KADAI DON AMFANIN KANSU?_*

*_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_*

*_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA
RANGWAME_*

https://www.mkdatasarvices.com.ng


_Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number
wayar_

08038258489


*ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾



Sam ba wanda yama lura da tsaiwarta a gurin,don hidimar gabansu kawai sukeyi. Su
alhassan suka fara fitowa sai ta miqa musu iftee tace suyi gaba ta duqa ta dauko musu sauran
ledojinsu tunda ita ta bada tata tayi gaba tana cewa

"Sai ka taho" saboda tasan zai fara da shiga sassan zainab ne. Labulen ta saka tana jan qwafa
bayan ta gama irga ledojin hannun ruqayyan sannan ya nufo nata sashen,zamewa tayi ta zauna
kan kujerar tana jiran shigowarsa ta kuma ga da me ya shigo matan.

Da sallama ya shigo sashen,khalil dake tsaye har yanzu saman kujerar ya diro ya
nufoshi da gudu yana kiran

"Daddy" daukansa yayi ya daga sama yana dubansa

"Ya rigarka yake a jiqe?" Ya tambayeshi yana tattaba gaban rigar

"Lemo nasha"

"Oya jeka cireta ka canza wata" ya fada yana ajjiyeshi.

"Baki iya sannu da zuwa ba?" Ya fada yana saka hannunsa daya a aljihun rigarsa yana duban
haneefa dake tattaba ledar da ya shigo da ita. Magana yayi me harshen damo,ya aika saqonne
har zuwa ga Zainab wadda banda sallamar da ta amsa da qyar bata ko sake kallonsa ba

"Au sannu da zuwa daddy"

"Yauwa,daga yau kada ki bari na sake tuna miki,be a good girl hanee"

"To daddy" miqa musu ledar hannun nasa kawai yayi,suka karba suka kici kicin budewa. Kasa
daurewa tayi don ta tabbatar suka bude din saisun cinye abinda ke ciki,tadan ciza lebanta tana
cewa

"Kuka bude sai kunci ubanku,kun koma kamar agololin gida,sai a wuce da leda biyu uku ku sai
a baku daya" sosai ransa ya baci,don zagin baiyi kama da yaran takewa shi ba

"Ku dauka ka tafi dakinku dashi naku ne" ya fada yana kallon yaran. Da farincikinsu suka miqe
suka cilla dakin nasu kuwa. Maida dubansa yayi kanta idanunsa suna nuna bacin ran dake kan
fuskarsa

"Daga yau ya zama rana ta qarshe da zaki zagarmin yara a gabana,duk randa kuma kika
kuskura kika sake aikata hakan to ki kuka da kanki" yayi maganar yana nunata da yatsa.

"A'ah wallah,na me?,bayan kun gama cin amanar tawa ka zagaye kaje ka daukota saboda ita
bada qafafun yin tuqi ta dawo gida shine ni kuma yanzu zaka sauke a kaina?,bashi yiwuwa" ta
fada tana miqewa,saidai kuma dole ta duqa saboda wani azababben gudawa da taji yana
taruwa waje daya a cikinta.

"Anci amanar taki,kema idan kin iya kici tamu" ya bata amsar a zafafe yana motsawa don barin
gurin. Idanunta dake rufe ta bude ta bishi da kallo,wani abu ya tsaya mata a maqoshi,bataso
maganar nan ta tsaya iya haka saboda takai maqura da abinda akeyi mata,rashin adalcinsa a
kanta ya fara isarta,yanzun inda ranar girkinta ne yaje yiwa ruqayyan sallama yana iya kwashe
minti talatin bai fito ba,amma ita gashinan ko zama baikai ga yi ba

"Wanda ya cuci wani Allah ya saka masa"

"Ameen" ya fadi ba tare da ya waiwayo ba,saidai cikin ransa yanajin tabbas zaiyi maganin
wannan rashin mutuncin nata.

Ransa a bace ya koma sassan ruqayyan,taga hakan saman fuskarsa amma sai ta
share bata tambayeshi ba,ta shiga hidimar shirya masa abinci da kunna room Heather saboda
dakin yadan qara yin dumi don yau din akwai alamun sanyi sanyi. Tasan koma meye tsakaninsa
da matarsa ne,ita kuma wannan ba huruminta bane.
Pyjama dinsa ta cire masa ta dawo gefansa ta ajjiye masa tana kallon fuskarsa,har cikin
ranta tana jin ba dadi to amma meye nata a ciki?,duk wanda ya debo da zafi bakinsa ai.

Daga kai yayi suka hada ido sai tayi saurin dauke nata idanun tana warware kayan
data dauko. A hankali ya kama hannunta ya riqe yana kallon kayan. Tare ya siyosu ya ajjiye
wasu a bedroom dinsa na sashen zainab,amma tuni wadanda ke sashen zainab din suka zama
tarihi,don daga qarshe da kansa ya bayar dasu sakamakon komawar da sukayi basu da
maraba da tsumma

"Anya ko da gaske kike kin yafemin?"

"Da akayi me fa?" Ta fadu tana dubansa fuskarta na nuna rashin fahimta

"Abubuwa marasa dadi keta faruwa,tunda na auro Zainab na kasa jin dadin zama da ita ko na
kwana daya ne,wasu abubuwan ban taba zaton mace tana iya aikatawa miji ba sai zuwanta
gidan nan,idan kace zaka kai qorafi saika zama........"

"Saika zama qaramin mutum,haka zaka ci gaba da haqurin" ta fada tana miqewa tsaye daga
saman gadon ba tare data kalli qwayar idanunsa ba

"Zainab kwata kwata......."

"Please mana habeeb......" Ta katsi numfashinsa tana fadi qwayar idanunta carr cikin tashi

"Banason naji please,inaso wannan daren,banason abinda zai batashi" kansa ya girgiza yana
kallonta

"Kinga bacin rai da damuwa akan fuskata amma baki damu kin tambaya ba,da abun yayimun
yawa kuma nake gaya miki da kaina nan ma ruqayya ba zaki fahimceni ba?,ba zaki bani
shawaran da zata zamemin fitila akan matsalata ba?" Wani murmushi me ciwo ne ya qwace
mata,ta kauda kanta gefe tana tuna wasu abubuwa masu ciwo da suka wuce. Tana mamakin
halin maza qwarai,mace zaki iya cinye daci da zugin radadin da namiji ya banka miki,amma shi
bai iya dauke radadi da ciwo. Yana samunsa yanzun zai ɓara kowa sai yaji.

Ta kusa minti biyu a haka ba wansa yace da dan uwansa wani abu,shi ya kafeta da
ido ita kuma ta kawar da kanta tana kallon wani gurin na daban tare da qoqarin hadiye abinda
takeji sannan ta waiwayo tana dubansa

"Ka tashi ka canza kaya muje kaci abincinka"

"Bazanci ba,ba wannan maganar akeyi ba"

"Maganar da akeyi din ai bata da muhalli a gurina,ba hurumina bane"

"Eh ba huruminki bane amma na sakaki a ciki". Ta lura da gasken gaske so yake ya tsomata a
ciki,yanaso ya sanyata yin abinda taketa dannewa,sai ta saki kayan hannunta zatayi gaba tabar
dakin amma sai ya damqi hannunta ya dawo za ita ya zaunar

"Amma baicikin aikin mace ta sanyaya zuciyar mijinta?,shima bada shawarar laifi ne?"

"Wacce shawara kake buqata?,sanda kake da buqatar shawarar ka nemeta ne?,ko ka manta
sanda nazo da shawarar?,ka tuna abinda ka gayamin?,na cika kishi,duk zancan magauta ne kai
baka da haufi akan yarinyar ka manta?,kana da tabbaci da yaqini a kanta so yanzun bai kamata
kayi loosing wannan courage din ba,ba hurumina bane sulhuntaku ko na shiga maganarku
ba,ko shawara ma ba dole bane na baka indai akan abinda ya shafi iyalinka ne,na roqeka ka
fiddani daga sha'aninku" ta fada tana hade hannuwanta guri guda,qwalla na cika mata
idanu,don tabbas ya taba Mata tsohon mikinta. Kasa cewa komai yayi,wannan ya bata qwarin
gwiwar miqewa a nutse ta fita daga dakin.

Tana jin mahaukacin kishinsa cikin kowacce gaba da sashe na jikinta amma ya gaza
gane hakan,komai tana yinsa bisa qarfafawa kai gwiwa da kuma jagorancin addu'ar da kullum
takeyi dare da rana akan Allah ya bata ikon mallakar zuciyarta,kada Allah ya bata ikon cutar da
zainab ko kasa yiwa saleem biyayya,tanayi maamanta tana tayata,ta tabbatar wannan shine
ginshiqi na farko da yayi mata katanga daga bin son zuciyarta.

Binta yayi da kallo jikinsa a sanyaye har ta gama ficewa ba tare da ya iya dakatar da ita
ba. Iska me zafi ya furzar daga hunhunsa yana maida bayansa jikin gadon ya kwantar yana
tariyo abubuwan da suka shude shekarun baya. A lokacin da idanunsa suka rufe yaji duk
duniya ba abinda yakeso ya gani illa d'an kansa. A baya tunaninsa sassauqa ne akan
wannan,amma tasirin kalaman mahaifiya da na qanne yasa sannu a hankali ya jarabtu dason

qara aure don ya samu haihuwa kamar kowanne cikakken namiji yadda ake gaya masa.
Mahaifiyarsa tayi masa nuni da Zainab cikin 'yammatan danginsa. Farar fatarta da yawan
iyayinta yasa yaji kaman zata dace da yanayinsa.

Duk macen da aka yiwa kishiya tasan zafi da rudanin da zuciya ke fuskanta a wannan
lokacin, ruqayyan ma taji haka,duk da nata za'a iya cewa ragaggge ne bayan tasan wacece
Zainab din. Taso qwarai ta kwatanta masa amma a sannan suna ganiyar buga soyayyar da
babu kama hannun yaro.
Ko kadan babu nufin hanashi qara aure a tattare da ita,duk da inda ace zai fasa zataji
dadin hakan,to amma taso ya bata dama wajen zabowa kansa da ita abokiyar zama ta gari,da
hakan zata kasance da farincikinta ya qaru.

"Kin cika zafin kishi ne kawai,amma duk wanda yace ga illar zee to saidai munafuki ko wanda
bai mata farin sani ba,ita din bakiga yadda take maganarki ba,kuma an gayamin girmamaki take
duk sanda kuka hadu a wani taro,to me ya rage me kikeso indai ba masifa da fitina ba?" Ya
fada a sannan hannunsa riqe da wayarsa yana replying watsapp massages na zainab din
"Ki cirewa kanki fitina da damuwa don Allah,ta kusa shigowa komai yazo qarshe ma"
maganarsa ta qarshe tafi kowacce bata mata ranta,don zatayi gyara don ta sama masa
nutsuwa da farinciki ga duk auren da zai qaro sai abun ya juye kanta?. Ita ta sani bawai alfahari
ba,bata tsoron karawa da kowacce macce indai ba daga aljanna aka sauko da ita ba,to

10 / 24