KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   11 / 24

30K to 33K   out of 69.9K words

amma
me?,saleem din ya sota matuqar soyayyar da ta tabbatar zai wahala wata diya mace ta samu
kwatankwacinta. Banda maganar aure data taso yanzu bai taba wani abu don ya cutar da ita ko
ya cusguna mata ba,wannan yasa take masa laluben macen da zai samu nutsuwa da ita,wadda
itama ba zata daga mata hankali kota rabata da nata farincikin ba. To amma saboda idanunsa
sun rufe,ya kuma yi nisan da bayajin kira bai hango abinda ta hango masa din ba ita.

Bayan gama tuna dimbin laifuka da abubuwan da yayi mata na rashin kyautawa bai
zaci dawowarta dakin ba a sannan. Sai kawai ya tsinci tattausar muryarta daga bakin qofa tana
fadin

"Daddy abincinka har ya gaji da jiranka,muma kaga dare yanayi kai muke jira" Da ya daga kai
ya kalleta murmushi ne saman fuskarta kaman ba itace ta fita da fushi ba. Daya daga cikin
abinda yake burgeshi da ita kenan,kuma guda cikin failure na zainab.

Ita muddin ya bata mata rai sai ta bata masa,muddin tayi fushi ko ranta ya baci saita
nuna ta kuma furta maka

"Ko sai nazo na qarasa shiryaka ranka ya dade?" Ta fada tana rungume hannunta a qirji
idanunta a kansa

"Me yasa na damu na kasa juriya da qaddara,na shiga neman aure ido rufe?,don kawai ruqayya

bata haihu ba?,yanzu ita ke da twins har da tsarabar diya mace guda,lallai rashin haquri da
juriya na gaggauto mana da wasu abubuwa da lokacin riskarsu zuwa garemu.ma baiyi ba" yana
gama wannan tunanin tana isowa,kaman jiranta yakeyi yasa hannu ya fusgota zuwa
jikinsa,wanann sassanyan qamshin nata yayi ma hancinsa kyakkyawan maraba
"Kiyi haquri da bata miki rai da nayi"

"Nasan bakayi don kana sani ba,kayine saboda relief kakeson samu a sannan daga abinda
kakeji,kayi haquri nima, wani yanayi ne da bana iya controlling kaina"

"Laifi nane,amma bazan sake ba in sha Allah,zan fuskanci consequences din ni kadai"

"Ya wuce fa,tashi ka shirya,yara har sunci nasu sun wuce". Ita ta taimaka masa ya shirya
din,duk bayan sakanni sai ya jawota ya shaqi qamshinta. Har fargaba yakeyi daren qarshe a
ranakun girkinta su fita,don gobe warhaka yasan makomarsa.

K'arin abun mamakin koda da kudinsa ya siya turaren yace a saka masa iya dakinsa
idan ma ita bata da buqata to fa bazai samu hakan ba,ya rasa dalili kamar me aljannun da suke
gaba da turare.

Da suka zauna alhassan ta aika kiran Zainab din

"Jeka kira ummanku,kace tazo muyi dinner" amsa mata yaron yayi ya juya ya fice,ita kuma ta
maida hankali wajen fara serving saleem. Tana zuba masan suna hira qasa qasa,yana bin
hannuwanta dake jujjuyawa wajen zuba masa abincin da kallo saboda jan lallen da tasha tun
shekaran jiya,an mata ratsin baqi a farcenta. Sau da yawa akan ruqayya ne baya yarda da
cewar lalle baya kyau a hannun baqaqen mata,bai sani ba ko don yakan manta da kalar lalle
idan ba hannunta ba?,don idan kaga Zainab din da lalle to kan tabbatar lallai akwai biki a dangi.

*HUGUMA*👑

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 14


*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*

*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*

*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*

*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*

LOGO
INVITATION CARDS
BANK STICKERS
BUSINESS LOGO
SAVE THE DATE
P.O.S BANNERS
BIRTHDAY CARD
BOOK COVER
DATA FLAYER
BIRTHDAY VIDEOS
VIDEO INVITATION
AI PICTURES

_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_

*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON
DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*

*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku

_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN
MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_

https://wa.me/+2347084515410

_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽
________________________________


"akwai maganar da nakeson muyi,saidai bansan yadda zaku fahimceta ba" saleem din
ya fada a tausashe yana jan plate din data ajjiye masa a gabansa don ya qagu ya fara cin
abincin,iya qamshin abincin kadai ya isa ya sa ka zaqu kakai bakinka,kada ma ayi maganar
farfesun kayan cikin da yaji spices.
Zama tayi sosai a gabansa kaman zata koma cikinsa ko kuma an bata gadinsa tana
dubansa da wani tattausan kallo. Idonsa ya lumshe ya sake budewa duka lokaci guda yana
dubanta qamshinta yana kai masa ko ina

"Uwargida sarautar mata" ya samu bakinsa da fadi. Wani shagalallen murmushi mai qaramin
sauti ta saki tana watsa idanunta

"Itace maganar da kace zakayi din?" Kai ya girgiza

"Bansan ya akayi bakina ya subuce ba"

"To ka gyara bakinka tun kafin umman haneefa ta iso,don nidai ba ruwana"

"Laifinki ne hajjaju,irin wanann kallon na rantse tsaf zai hanani cin abincin nan,bari kiga tun baki
cikamin cikina da soyayya ba" rausayar da kai tayi tana sake sakin siririyar dariyar. Itakam har
abada koyon kyawawan dabi'un da zasuja hankalin miji ba shakka sun biyata,don ko yaushe
suna wanketa ne a idanun saleem,koda bata sanyawa jikinta komai da zaija hankalinsa din
ba,iya kallonta kawai ya wadatar.

"Umara nakeson muje gaba daya,ni dake da hajiya sai zainab,to amma kudin hannuna basu
cika ba,kudin tafiyar mutum uku ne ba kadan,kinga mutum daya bai samu ba"

"Kai,kai ma sha Allah" ruqayyan ta fadi tana langwashe qafafunta

"Amma naji dadi qwarai da gaske,Allah ya qara budi,inda duk allura ta fita Allah ya naidata
dutse"

"Ameen ameen,duka wannan addu'ar haka bayan baki da tabacin kina cikin masu zuwan?"
Murmushi tayi masa me kama da harara

"Zakaje,hajiya zata je,to meye ya ragemin?,kamar nayi rabin zuwa kenan,rabin kuma sai ranar
da ubangiji yayi kirana" zamansa ya gyara yana jinjina kai,ko da yaushe maslaharta itace
tasa,koda yaushe buqatunsa take sakawa a gaban nata(maza nason irin wadan nan matan),to
shikam me yayi masa saura game da matar kirki?.
"Amma sai hajiya tace ko ita zata haqura naje daku,ita wata shekarar idan da yawan rai tunda
alhaji me rasuwa ya taba kaita hajji" Kai ruqayya ke girgizawa da sauri tana dubansa

"Kai yanzun koda tace hakan sai kayi hakan?,da yake mu muka haifa mata kai?,sam ba za'a yi
haka ba,mu ya kamata mu haqura din,mune qasa da ita,yanzun ni ko Zainab wani a cikinmu
zaiso idan su alhassan da khalil sun girma hakan ta faru tsakaninmu da matansu?".

Kai ya girgiza yana jin wani sanyi a cikin ransa,lallai ya samu mace ta garin da annabi
ya suffanta,yana cikin mazan da suka shigo duniya a sa'a.

"Wai da ina ganin zanyi mata gyaran gida ne kafin mu tafin shi yasa"

"Dukka ta cancanta daddy,ta cancanci abinda yafi haka ma,hasalima inda zata buqaci ranka ka
ciro ka bata baka saka mata da komai ba" ta fadu tana dubansa. Wata ajiyar zuciya ya saki

yana jinjina kai cike da gamsuwa,wata irin daraja da kimarta suna linkuwa a ransa,ruqayya
macace daya tamkar da dubu lallai ya shaida wannan.

Takun Zainab taf taf shine yana hankulansu,suka waiwaya gaba daya suna dubanta.
Idanunta akan ruqayya suke,ji takeyi kaman ta shaqota,taji komai a labewar da tayi,banda baqin
hali da baqar zuciya da ya cakuda da baqinciki ai ita taso yiwa mugunta. Saudiyyan nan daga
ruqayya din har hajiyan ai sunje,shine don tsabar hassada da qyashi me makon ita da tunda
tazo duniya ba'a taba zuwa da ita ba tace a dauketa sai tace a barsu?.

"Amma dai wannan shawarar ba komai a cikinta sai zallar rashin adalci da qyashi da hassada"
Zainab ta fada fuskarta na nuna tsantsar bacin rai. Daga zaunen saleem ya daga kai ya bita da
kallo. Tsaiwarta a gurin kawai ya canza atmosphere na wajen. Daurin qirjin nan ne dai na gado
sai armless shirt daga ciki,qafafunta tsage tsage a waje kamar sunyi d'ai d'ai
"Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar. Cikinta ne ya juya abinda ya Sanya yawu taruwa a
bakinta kenan,sai ta juya gefan hagunta ta fesar da yawun tasa bayan hannunta ta goge
ragowar da ya bata mata baki. Da sauri ruqayya ta kawar da kanta gefe tana a'uziyya zuciyarta
na tashi saboda tsantsami.
Juyowa Zainab din tayi tana duban saleem

"Ta yaya zakayi shawara da ita ita kadai,bayan ba ita kadaice matarka ba?,ba ita kadaice take
da haqqi a kanka ba,sai nayi magana kuma aga na cika qorafi bayan adalcinne sam ba'a yishi
ba?"

"Ni kika tsayawa akai kina gayan ban miki adalci ba?" Yadda yayi mata tambayar ta bugar mata
da gwiwa,amma rashin son gaskiya da jin tafi qarfin ayi mata fada sunyi mata katutu saita
kauda kanta gefe ta fara halin nata wato gunaguni

"Eh ai azzaluma ka tambaya gashi tana batun ni da ita duka mu rasa ku tafi kai da hajiya
saboda tsabar muguntar kowama ya rasa,bayan ko hajiyarma ta taba zuwa ai,nice ba inda na
taba leqawa a qa'ida......" Ta fada hannunta a qugunta ba tare data dubeshi ba.

"Idan baki matsamin akai ba sai ranki yayi mummunan baci,sakara mara wayo" maganar ta
girmi kunnenta don bai taba gwada fadin hakan ba

"Um um daddynsu,ya isa don Allah" ruqayya ta fadi qasa qasa tana tausarsa saboda ta hangi
fushin da ya fara tasiri a idanunsa

"Ki qyaleni na fadi mata,naji ta fara sako batun hajiya ne,ta dauka yanzun daa ne da zan dauki
iskancinta akan uwata,wanda kikayi a baya ma na kasa tsawatar miki istigfari nakeyi har yanzu"
can qasan zuciyar ruqayya cewa kawai tayi uhmmmm. Zuwan Zainab gidan tana amarya ba ita
ba,hatta hajiyan ta shuka mata iskanci kala kala,ba zaka taba zaton akwai wata alaqa ta jini

tsakaninta da hajiyan ba,a lokacin bai cewa komai,shi yasa ruqayyan tayi qoqari ta kama
mutunci sosai a lokacin (kira ga uwayen gidaje,ina qara gaya muku sau tari ku kike siyawa
kanku daraja da mutunci a farkon zuwan abokan zamanku,kuma kuke basu fuska da qofar
rainaku tun farko,ki watsar da ita da me gidan gaba daya ki basu space ki maida kanki busy a
lokacin da suke ganiyar cin amarcinsu,hakan shine zaifi zame miki alkhairi akan sanya idanu
akan duk wani motsi nasu,ranki zaiyita baci ne kina ganin abubuwan da babu lallai suyi miki
dadi,ke kuma babu tabbas din zuciyarki zata iya jurewa).

Wannan kame kan shine abinda ya jawo har yau duk iya iskancin Zainab da ganin
ruqayyan ta tare mata gaba ta tare mata baya ba komai take iya tunkararta da shi ba.

"To ai saika dauki mataki yanzu ma bata baci ba" ta fadi a zafafe,saidai gama fadin keda wuya
wani zazzafan amai ya biyo baya.

Dan janye jiki ruqayya tayi cikin mamaki,zubewar da taga zainab din tayi a wajen ya
sanyata miqewa tana fadin

"Subhanallahi lafiya?" Qarasowa tayi dab da ita tana qoqarin riqota,saidai wani yanayi dake
tashi a jikinta ya sanyata matsawa gefe ta tsugunna tana mata sannu.

Mugun galabaita ta fara yi,ita da saleem din suna tsaye a kanta. Wannan abun ya sake
bawa zainab dama ta sake ragwabewa sosai ta narke kamar matacciya

"Dauko mata hijabi mu tafi asibiti" tsam ta miqe tana juya yadda Zainab din ta sake gaba daga
yin amai?. Eh tayi wani irin amai mai yawa a gurin amma baici ace ta sassake haka ba.

Sau biyu tana sallama yaran basuji ba saboda sun qure qarar tv sunata kuma damben
fada akan abun wasa,harda haneefa da ya kamata ace a shekarunta ba wannan abun yakeyi
ba,ita ke kula ma da khaleel.

Sanda suka farga da kallo suka bita baki sake saboda ba zasu iya cewa ga ranar
qarshe data tako sashen nasu ba. Tunda ta shiga falon yanayin falon taji sam baiyi mata
ba,haka ta dinga takawa cikin tsantsani don ko ina datti ne,bata tunanin jiya ya samu
kyakkyawar shara,yau kuwa dama tunda tana sauri biki ya samu tayi imanin inda zata leqa
kitchen dinta ko wanke wanke batayi ba.

Kusan ginin nasu iri daya ne,wannan ya sanya bata sha wahalar gane inda bedroom
dinta yake ba

"Karki shigarwa ummanmu daki fa" haneefa ta fada tana kallon ruqayya. Sosai abun ya bawa
ruqayya mamaki,ta juyo tana duban yarinyar. Har tasan wani kishiya kada ta shigarwa kishiya
daki?, komai ma wai zama zainab takeyi da yaran ta gaya musu?.

Hannu ruqayya ta saka ta yafitota tana murmushi

"Zoki nunan kayan ummanki zan dauko mata zani da hijab,asibiti daddynku zai kaita" tsalle tayo
ta sauko daga saman kujerar da sun jima da cin ubanta ta nufo ruqayyan ba tare da ta maida
hankali ga batun zuwa asibiti ba

"Zakisha wahala,dauko kayan ummanmu akwai wahala,don itama kullum saidai ta gaji ta dauko
wanda ta gani ta mayar da sauran" bata cewa yarinyar komai ba tabi bayanta.

Kusan idan ka ganta cikin dakin Zainab haihuwa tayi,rabonta da bedroom dinta tun
haihuwar khalil. Tayi mamaki har fiye da zato na yadda ta zamu dakin nata a hargitse,hatta da
shimfidar gadon a harmutse take,harda qasa qasa a kai,panties nata Brazier da cup harda
spoon ma. Qasan dakin kuwa baja baja yake da karikice da bazata ma iya tsaiwa tantancesu
ba. Dakin ba abinda yakeyi sai wani irin hamami hamami kamar warin dauda cakude da warin
hammata. Bata sani ba amma qila tsabar tashi da jiki da hammatar Zainab din keyi da
annakiyar da dakin yake da ita ne ya sanya a madadin qamshin turare... Nata turaren ya zama
wadannan warika ne gud biyu. Bandaki shima na buso tashi gudunmawar qarni da zarnin ta
qoofar bandakin dake a wangale.

Gaba daya kayane jibge a rataye tun daga murfin sif din zuwa kan qofar
bandakin,zannuwanta ne panties da riguna.

Haneefa ce ta bude sif din hankalin ruqayya nakan wani tsadajjen turarensu data gani
yashe a qasa an tattara kwalbar an shareta acan matse matsi mudubi,ta yiwu dazun da tana
saurin zata fice ne ya fashe garin ta saka,ita kuma ba zata iya tsaiwa ba ta tattareshi gefe da
zummar saita dawo,data dawo din kuma bata da lokacin bi ta kansa sai ranar da Allah yakai
tsintsiyar shararta gurin.

Zubowar kaya kawai ruqayya taji yiiiiiiffffff kamar an saki buhu. Gefe ta matsa da sauri
adan tsorace,haneefa ta sheqe da dariya

"Haka ummanmu takeyi kullum idan zata saka kaya,ki zabar mata saiki barsu a gurin saikin
dawo,ko natayaki mu mayar" yarinyar ta fada hankalinta kwance cikin nishadi kamar me bada
labarin abun arziqi.

Tsaf ruqayya ta qarewa kayan kallo,tama kasa tantance meye da meye,don basu da
maraba kwashen dilar kayan gwanjo

"Ke da nace kaya aiba wanki za'a kai ba,ba kayan dauda ba wankakku asibiti zataje" baki ta
saki tana kallon ruqayya

"Ai sune wadannan,idan aka kawosu daga wanki watsasu mukeyi,idan muka cire kuma indai
laundry basket dinmu ya cika sai mu ajjiye ciki idan an tashi kai wanki a kwaso,rannan ma

daddy yace duka kayan ciki tsami sukeyi" ta fadi tana toshe hanci cikin son gwada yadda yayin
a ranar tana dariya abinta don maganar har yau dariya take bata

"Ya isa,ina hanaki fadin abu ko an tambayeki bare ba'a tambayeki ba,mu kwashe kayan mu
mayar" tace da haneefan.

Tana tilar kayan tana dauke numfashi da kau da kanta,haka ta dunga diba tana
cusasu yadda ta gansu haneefa na tayata. Kafin su gama cikinta ya gama gurbata,da qyar ta
iya gano zani da hijabi ta fito dasu a hannunta amma zuciyarta fal qyanqyami.

A nan ta samesu,ta ajjiyewa zainab din kayan amma sai tayi talau alamun ba zata iya
sakawa ba. Saleem dinne ya karba ya fara saka mata. Da ya gama saka matan ya riqeta suka
fita farfajiyar gidan Zainab din tana layi kaman zata fadi.

Kwanukan abincinta ta fara tattarawa tana daukesu a wajen kafin suma su fita a
kanta.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 15

https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39


*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA
HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE

11 / 24