KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   6 / 24

15K to 18K   out of 69.9K words

inda zai cusa hancinsa AMINCI zai tarar da marabta me kyau. Gaba daya zainab din
ma a tsarinta ire iren wadan nan abubuwan bata lokaci ne,gwara a dinga tafiya zuwa ga babbar
headquarter din gaba daya.

"Banajin dadi ne" ya fada shima cikin narkewar da baima san yayita ba,kawai wani farinciki yaji
yana saukar masa tamkar mutumin dake tsakiyar kogo me duhu masu agaji suka riskeshi don
fiddashi hakanan yaji.

"Ya salam" ta fada tana nuna zallar alhini a fuskarta tana kuma takowa da sassarfa zuwa
kujerar da ya zauna din a kai,yanayin yadda take takun ya bawa qirjinta damar motsawa,wanda
ya ciko yayi fam saboda baiwar aqirji da take dashi,uwa uba kuma tana using push off brazier
don bahaushe yace idan kana da kyau ka qara da wanka. Ita kanta tana alfahari da baiwar
beast da hips da Allah ya bata,ita din baqace ko ace wankan tarwada,zainab ta fita fari da
tsahon gashi sosai,farin da a baya yaso ya zame.mata tarnaqi kuma kalmar da akaso ayita
cusguna mata da ita. Bata taba mance lokacin auren zainab,zuciyarta ce kadai ta rage bata
buga ba,amma hawan jini kashi kashi ta yishi. Hasken fata da tsahon gashi tayi imani kawai
zainab ta fita,saidai ita kuma Allah sai ya qareta ta bangarorin da take da tabbas ta yiwa zainab
rata me tarin yawan da bazata lissafu ba.

A hannun kujerar da yake kai ta zauna tana duban fuskarsa

"Habba amma ya kamata na sani ko?" Ta fadi a shagwabe tana tura baki gaba. Murmushi ya
saki yana kauda idanunsa saboda ta fara tadoshi sosai

"Am sorry" ya fada a taqaice saboda tsaiwar Zainab a wajen wadda kamar zata fashe

"Alright,muje na qarasa wannan jinyar gaskiya,wannan amarci an cishi yadda ya dace,har
ruwan dumi zan maka na gasaka da kyau,kaga nima sai naji dadin diban nawa tsumammen
uwargidancin" ta qarasa maganar tana kashe masa ido daya hadi da cije lip's dinsa na qasa
abinda ya sanya tsigar jikinsa zubawa.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 07


"Ba inda zaije,bashi da lafiya,kuma har yanzu kwanana ne" a nutse ruqayya ta waiwaya ta
dubeta sama da qasa,ta ganta wata harikicibayya cikin zanin wata atamfa da yayi musu waccan
sallar,ta Zainab din ruwan madara ne,atamfar kudinta duk daya ta doshi dubu goma sha takwas
amma cikin qasa da wata goma tata har ta doshi hanyar zama tsumma,ta rune daga milk ta
koma brown brown da torches na dattin abubuwa mabanbanta,bakin zanin yayi leb'atu wani ya
zarta wani yana lilo

"Haba amarsu bakya laifi,baki lura bane azahar har ta gota?,ko kin manta ke kika tsara mana
hakan dama?,kiyi haquri kwana biyu rak zan dawo miki dashi da kaina" ta fada mata tana
murmushi dariyar daurin dankwalijta yake a jirkice yana kama ruqayya. Sau tari bata fiya jin
kishin zainab cancan ba, saboda tasan bata da abinda zata kara da ita,saidai hali kawai irin na
zuciya da kuma abinda takeso.

Miqewa saleem din yayi yace

"Minti daya"

"A fito lafiya" ta amsa masa tana maida dubanta ga tv din dake aiki, wadda rabinta tayi baqi
saboda yadda su haneefa suka ragargajeta duk girmanta kuwa,shi kuma yayi rantsuwar bazai
canza mata wata ba,saboda bayan wadda ya siya musu ita da ruqayya ya sauya mata
wata,wannan din shine karo na biyu kenan da yake sauya musun bayan ta farko.
"Ba inda zashi,yana nan" zainab din ta fada tana juyawa tabi bayanshi dakin.

Aikin da ya gagara bai gama jiya ba yake hada kan takardun nasa sai yaji
motsinta,koda ya waiwayo ta fara zare t.shirt da zanin jikinta,ta fara takowa inda yake tana
girgiza kafadunta

"Mene hakan?" Ya fada a mamakance,take fuskarta ta sauya kamar yadda bata iya cinye bacin
ranta ba

"Ragowar haqqina nake buqata,kuma kaima aina lura bawai ka gama nutsuwa bane" Dariya ce
ma taso kamashi,yadan kauda kai daga nan yana jiyo yadda smell na jikinta ya canza da alamu
tana da buqatar tayi wanka amma ta kasa gane hakan. Abu na biyu kuma ya fahimci tana so ne
tayi abinda zata batawa ruqayya lokaci,saidai kash bata iya durfafar miji da salon zai dauke
masa hankalin ba tare dashi kansa yasan ya akayi hakan ta faru ba

"Lokaci ya fice yanzun kema kin sani"

"Eh amma hakkina ne ai a wuyanka ko?" Tsaiwa yayi yana kallonta kafin daga bisani ya girgiza
kai yaci gaba da hada takardunsa. Maganganu ta shiga yi na bacin rai har ya gama,ya miqe
tsaye yana zuba mata idanunsa abinda ya sanyata rage kaifi bakinta

"Kiyi qoqari ki tabbatar ba wani abun kika zubamin jiya ba,don muddin na gano hakan kinsan
sai na hukuntaki tabbas!" Ya qarashe maganar yana kewayeta ya fice,saboda yasha mata
gargadi akan hakan,yayi dukkan abinda zaiyi ya koya mata hade haden vegetables din da
ruqayya keyi masa da suke da matuqar amfani ga lafiyarsa da auratayyarsu,amma tsabar son
jiki ta kasa tsaiwa ta dinga yi masa a kullum kamar yadda yake da buqatar ya dinga ci din.

Har wani sakakken numfashi ya saki sanda suka isa sashen nata,wata ni'ima da
nutsuwa suna saukar masa. Ruwa me dumin sosai ta hada masa kamar yadda tace,koda ya
sanya hannu cirewa yayi da sauri yana dariya

"Wai ashe da gasken kike gasanin zakiyi?,na dauka kin fada ne kawai saboda kishi?" Yadda ya
rutsata da ido yana tambayarta sai abun ya bata dariya,ta murmusa tana qoqarin danne
kishinsa da takeji yana cin qasan zuciyarta

"Amma dai kafi kowa sanin ruqayya,idan tace eh tana nufin eh din,idan tace a'ah shima tana
nufin hakan" murmushi ya saki yakai hannu yana shafar dukiyar fulaninta da yanayin dinkin da
akayi mata ya fidda shape dinsu sosai. Har yanzun yanajin wannan yanayin a jikinsa,saidai
hankalinsa na kwanciya idan ya tuna ya fado hannun da zai samu dukkan kowacce irin
nutsuwa.

"Naji sashen shuru ina duka yaran"ya tambayeta sanda take taimaka masa yana fidda kayan
jikinsa don ya samu yayi wankan,har yau har gobe muddin tana free irin haka itace ke taimaka
masa da wannan,hakama shirin muddin ta gama nata ayyukan

"Na korasu gidan kakaninsu don nayi jinyar daddynsu da kyau" wafta ya kawo mata,ya jawo
qugunta ya riqeta suna musayar numfashi. Idonsa cikin nata,hakanan duk wani fitar
numfashinta sai ya hado da sassanyan qamshinta. Sai ya tuna wata rana irin hakan da ya
gwada yiwa zainab hakan,daga qarshe da hannunsa ya saketa saboda bala'in rashin tsaftar

baki,wanda hatta da numfashinta da irin wannan yanayin yake hadowa ya fito.

"Wannan jinyar ta tsaye miki a rai ko?,to kada ki damu,kema yau ki daure ki jinyatani hakan
mana" ya fada yana kashe mata ido daya. Hannu biyu ta sanya ta turashi baya tana dariya

"To bismillah ko an gaya maka raguwa ce?,ai dai kafi kowa sanin wace ni" dariya ya saki yana
kai mata cafka,sai ta zame ta fice,don sam ba zata yarda ya rabeta daga barowarsa sassan
zainab ba,tafi son ya tsaftace jikinsa duk da fes yake,amma hakanan take da wannan kishin a
zuciyarta.
Kafin ya fito ta hada masa hadin salad na musamman,bricole,spinach,cocumber,parsley
cabbage lettuce cornflower,ta yayyankasu ta wankesu da ruwan gishiri,ta diga masa mai kadan.
Tuni ta haramta zuba maggi me yawa a abincinsa bare akai ga farin magi,don haka gishiri ta
zuba mishi kadan da yaji wanda tasirinsa bazai fito ba bare ya dameka. Blender dinta ta jona ta
markada kabewa dabino da kanunfari yayi laushi qwarai kaman yoghurt ta wadatashi da zuma.

Duk inda ta gifta saita aje masa qamshinta,hakanan tasirin maganin jiya da bai bar
jikinsa ba ya dinga tsomoshi. Sai data gama shirya masa komai sannan ta dawo ta zauna tana
dubansa cikin wani lallausan kallo data aje kawai saboda shi,zata iya cewa duk duniya ba
wanda ya taba ganin makamancin kallo irin wannan a idanunta saishi daya tal
"Ga abinci ya kammala,ka fara tabawa kafin na dora girkin dare" kumatunta yaja yana
murmushi

"Emergency kika hadamin ne?,naga harda pumpkin smoothie" farrr tayi da idanunta tana
murmushi

"A'ah,ya za'a yi mu hadu muyita tara maka gajiya?,so nake kaci ka qoshi ka kwanta ka
huta,qwarin jikinka ya dawo" mintsininta yayi kadan yana murmushi, muryarsa qasa qasa yace

"Ban yarda ba,tunda kikace kin tafi gidan aunty deeja nasan there's something special yau,naga
wani abu me zaqi zaqi ma a fridge dinki" idanu ta fiddo tana kallonsa

"Sai kuma kasha?" Kai ya girgiza yana langabe mata shima

"Dandanawa kayi nayi fa,Allah bansha ba" shagwabe masa tayi sosai kaman zata saki kuka

"Amma dai daddynmu kasan ba kyau bincike dai ko?" Dariya ta qwace masa

"Ni ruwa naje sha ba bincike nayi ba" ya fadi yana daga hannunsa sama duka biyun yana dariya

"To nidai na yafe yau din,an baka hutu" ta qarashe maganar idanunta nakan labulen window
dinta dake ta veranda din waje. Idan idanunta sun nuna mata gaskiya shatin tsaiwar mutum

take hangowa,karon farko kuma taji zuciyarta tafi kakata da cewa zainab ce. Sau uku qanwarta
da maqociyarta suna gaya mata Zainab din tana mata labe,amma bata taba daukan abun da
muhimmanci ba tunda bata taba kamata ba.

"Ni kuma ban yafe ba" ya fada yana matsa hannunta dake da wani sulbi da taushi.

Tana sane ta saki wata shagwababbiyar qara idanunta nakan labulen

"Allah dear......ka bari don Allah,tun ba'a yi nisa ba kada kasa na kasa komai"

"Na bari,amma mu fara salla tukunna kafin muci abincin"

"Yes sir" ta fada tana miqewa. Sai data fara wucewa kitchen ta fiddo sumammen ruwa ta juye a
wata roba sannan ta wuce toilet ta shirya masa ruwan yadda zaizo da dumi bayan tayi tata
alwalar ta kuma shimfida abun sallah sannan ta zarce kitchen din.

"Na daina raga miki" ruqayya ta fada qasa qasa tana dariya mugunta hannunta dauke da robar
ta dawo falon din.

Sake gyara tsaiwarta tayi da kyau zuciyarta na sake tafasa da bacin rai. Ba zata bar
wajen nan ba har sai taji uban me dame sukeyi tas a cikin falon. Gumin fuskarta ta goge tana jin
kamar ta rushe da kuka. Babu ta yadda za'a yi ma ta yarda cewa ruqayya ba asiri ta yiwa
saleem ba,don bataga wani abu guda daya da zaisa saleem din ya dinga wannan rawar jikin a
kanta ba,bayan itace tafi cancanta da hakan.

Ai bata dire tunaninta ba taji saukar ruwan qanqarar da ya kusa tafiya da numfashinta
gaba daya. Ta taqarqare ta kunzuma ihu ta mance ma shaf da muhallin da take a tsaye. Da
sauri ruqayya ta bankade labulen da qofar gaba daya ta fito tana salati

"Jar uba!,ni kika jiqa da ruwan qanqara,wallahi tallahi yau ko sama da qasa zasu hade bazan
yarda ba" ta fada tana gyara daurin qirjin da tayi a saman zanin atamfar jikinta. Wata dariya ta
tasowa ruqayyan yadda tayi tsamo tsamo da ruwan har tana rawar dari,amma dai sake gyara
masoyinta takeyi wato daurin qirji
"Aike za'a tambaya,me kikeyi a nan gurin?" Tambayar data daukewa Zainab din wuta difff
musamman da tambayar ta fado dai dai sanda saleem yake fitowa daga falon saboda ihun
zainab din daya riskeshi har bandaki.

Ido tahau rabawa, ganin yadda shi da ita gaba daya suka zuba mata ido suna sauraren
amsarta sai tahau tafa hannu

"Ni zaki yiwa wannan tambayar?,ko kin manta yadda gidan nan yake naki nima haka yake a
wajena?,ko wucewar ma mutum bazaiyi ba saboda window din daki ne?"

"Wucewar ce harda kujera?" Saleem ya sake jefa mata tambayar yana nuna mata kujerar data
aje a wajen. Dif wuta ta dauke mata,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta yana hadiye wani
abu me tauri.

"Allah ya kyauta" ruqayya ta fadi tana kewayeshi ta wuce ciki abinta,ko babu komai ya gani da
idanunsa,bata bude baki ta fadi ba bare ace sharri ne da yarfe irin na kishiyoyi.

Batasan yadda suka qare ba,saidai har alwalarta ta bushe bai shigo ba,sai daga bisani
ya shigo yana ware hannun rigarsa,fuskar nan cike fal da bacin rai,saidai bata bari hakan yaci
gaba da damunsa ba ,don bayan sun gama sallar sai data tabbatar ta mantar dashi komai ta
hanyar biye masa ya sauke sauran nauyin da Zainab ta dibga ma cikinsa ba tare daya sani
ba,sannan ta shiriritar dashi suna wata daddadan hirar gado wadda ta musammance data
warewa lokuta irin wannan. Lokutan da suka gama kasancewa da juna a lokaci irin wannan da
babu kowa daga shi sai ita. Yanason irin wannan moment din da take creating musu,yana sakin
jiki qwarai yayi sirrika masu tarin yawa da ita,suyi shawara da juna ta kuma sauke masa
damuwar da yakejin duk duniya ita daya keda wannan power din.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 08


GIDAN HAJIYAR MATA daya daga cikin jerin gidaje guda goma sha biyar kenan dake
layin.

Faffadan gida ne dake da soro makeke guda,yalwataccen tsakar gida dake da bishiyar
mangwaro a tsakiyar gidan,sai dakuna guda biyar manya,wanda kowanne cike yake da kayan
jere na alatu wadanda suka fi qarfin a zubasu a gida kamar wannan,duk da gidan fes yake,baya
rabo da fenti da 'yan gyare gyare kodon saboda baqi dake yawan zirga zirga a gidan.
Kusan duk sanda zaka shiga gidan zaka samu dakuna hudun nan a rufe,musamman
uku daga cikinsu,har gwara dayan ana yawan budeshi saboda baqi dake zuwar mata. Daki
guda kuwa kulli yaumin yana a bude,saboda shine ainihin ma'assasar neman kudi da dukka
wata taqama na hajiya zeena din. Akwai masu aikin dake zirganiya daga dakin zuwa tsakar
gidan sanye da riguna koraye masu dauke da tambarin HAJIYAR MATA musamman idan ta
kammala hada magungunanta za'a yi packaging.

Saidai ko su din akwai wasu kebantattun lokutta da bata barinsu shiga dakin har sai ta
kamala hada magungunanta saboda boye sirrin kasuwa kamar yadda takance

"Mutane ba amana,kasuwa ai sirri ce"

Ko a yau din ma masu aikin nata na zaune a tsakar gida suna hirarrakinsu tare da jiran
hajiyan dake dakin ta sallami baquwarta ta kuma gama hada magungunan nata su shiga suyi
aikinsu,don yau din akwai kaya da yawa tace musu akwai matar da zata sara.

Daga cikin fallen babban dakin da yafi kowanne girma mata ne zaune saman kujeru
guda biyu,dayar kana kallonta kasan itace matar gidan,don kanta daurin ture kaga tsiya ne
tayi,qwaiwayayyen gashinta ya bullutso ta qasan daurin,yayin da d'ayar ke sanye da hijabinta
saidai ta sabashi saman kafada
"Shi carwash din yanzun saidai botiki uku?,botiki biyar naso saboda zanyi sabulun tsarki dashi
me yawa wallahi"

"Masu nema ne sukayi yawa hajiya,kuma kalolin da za'a sakawa koren ne babu,ke kuma koren
kike da buqatar yayi ko?"

"Eh mana,yo banda abinki ta yaya za'a yarda sabulun magarya ne babu koriyar kala?"

"Ba matsala zanyi qoqarin hada miki cikin satin nan in sha Allahu"

"Shikenan,zan jalauta haka" ta fada tana ninke takardar lissafin nasu,ta jawo wata lalita a
qugunta ta zuge ta lissafo kudade ta miqa mata

"Gashi babu kare bin damo,idan kin kawo sauran koren na baki kudinsa iya shi kadai" kudin ta
jujjuya a hannunta

"Haba hajiya,na zaci zaki bani kudinsa shima kafin na kawo"

"Kije kiyimin irin ta wancan lokacin ko?,saiji nayi kin bawa wata,to kar nake kallonki"

"Karmuyi haka dake mana,duk zaman nan ace ba aminci tsakaninmu?,kudin nan fa kafin ki
tashi a nan na tabbatar kin maida ninkin baninkin dinsu" daurin dankwalinta ta sake turowa
gaba ta bararraje tana jawo wani farin botiki dake cike da garin masara me azabar fari da laushi
da yasha tankada da kyau,hakan ya nunawa matar da take kira da saude ba zata cika mata din
ba

"Kinga miqomin botikin zumar can" dariya saude ta sheqe dashi

"Zuma ko dafaffen sugar cakude da dan zaqi?(sweetner)" Baki ta tabe cikin nuna halin ko in
kula

"Koma menene ke kika sani,miqomin nayi nayi na hada,basira zata shigo sari tace akwai gidan
sunan da zata je yau din"

"Hajiyar mata hajiyar mata" saude ta fada gana dire mata botikin.

"Ahto,meye amfanin sana'ar da babu riba,tunda dai sunyi imani kuma yana musu aiki aimu
alhamdulillahi......ina fiddausi?,zoki hada dan matsin nan yasha iska kafin anjima" ta qwalawa
biyu daga cikin amintattun masu aikin nata kira.

Wani kwali ta jawo dake dauke da zanen mace babu komai a jikinta sai pant,an fiddo
abinda zai nuna maka tallan abubuwan da zasu qara masa girma akeyi

"Balle capsule dinnan ki watsa a hadin garin qara girman nonon can za'a kai niqa"

"Kinsan sirrin kasuwa hajiya" saude dake dariya ta fada

"Yo mu din na wasa ne?,ke kinga yadda mata suke wasoson garurrukana?,to kina sha zai fara
aiki,su dama haka sukeso,wannan

6 / 24