KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   17 / 24

48K to 51K   out of 69.9K words


kwanciya ciwo wai sai na auri naana 'yar qanin mahaifi na" wani mummunan faduwa gabanta
yayi,qafafunta sukayi sanyi ta kasa cewa komai saici gaba da tayi da kallonsa

"Kiyi haquri don girman Allah,naso qwarai ni dake mu kasance miji da mata don nayi miki irin
gatan da ban taba yiwa kowacce mace...... Amma yanzu ma bata baci ba,ni dake inaso muci
gaba da mu'amala,ko meye kikeso zan kashe miki zan kuma baki".

Hawayen da batasan yadda suka samu bane suka balle mata,ta girgiza kai cikin alhini
tana dubansa

"Amma me yasa duk lokacin nan baka gayamin ba?,ka barni inata bulayi da zaman jiranka?"

"Banason ranki ya baci ne,kuma da farko na dauka zanshawo kanta ashe abun yafi qarfina,kiyi
haquri don Allah karkiga laifina" kasa ci gaba da zama tayi,hankalinta tashe kawai ta miqe tayi
cikin gida,tana iya jiyoshi yana kiranta amma bata ko waiwayeshi ba,kiran da hatta umma ta
jishi,don tana shiga dakin tana binta a baya itama tana tambayarta ba'asi,saidai kukan da takeyi
ya sanya ta gaza bata amsa.


**Da sallama ya shiga sashen bayan barowarsa sashen ruqayya kaman yadda ya saba. Adan
zabure Khalil da haneefa suka amsa sallamar tasa. Idanunsa ya sauke a kansu sanda suketa
qoqarin daga tv plasma din data fado tayi zaman dabaro a qasan tiles.

Ko da bai tambaya ba yasan abinda suka saba ne suka aikata,wato rikito da Tv din
wajen fadace fadacensu da basa qarewa,su biyu kacal amma zaka tsammaci sunyi su goma a
sashen

"Waye yayi wannan aikin?" Ya jefa musu tambayar yana tsaresu da ido

"Wallahi shine daddy.......qarya takeyi daddy itace ni ba ruwana,turani tayi kai" dukka sai suka
kama masa rantse rantse. Ransa yayi qololuwar baci,ya rasa wanne hukunci zaiyi musu?,yo su
idan suna da laifi ma ai kaso mafi yawa laifin na uwarsu ne. Matsawa yayi gaba yasa hannu ua
daga tv din,ransa ya sake baci da ganin yadda tayi kwatsa kwatsa
"Ina mamar taku take?" Ya tambayesu qasan ransa yana mamakin ya za'a yi abu me girma irin
haka ya fado ya fashe amma baka ji ba ballantana ka fito?

"Ta fita tun da rana" Khalil ya fada kansa tsaye. Tsaiwa yayi cak yana dubansa

"Ta fita kuma?,ina taje?" Ya tambayi yaran

"Bamu sani ba,mudau tace mana mu zauna a nan yanzu zataje ta dawo". Wani mugu mugun
bacin rai ne ya sauko masa,a duniya cikin manya manyan abinda ya tsana a wajen matarsa
satar fita, saboda shike haifar da wasu matsalolin da mai yiwuwa ba zasu taba gyaruwa ba.

TV din ya maida duk da shi kansa yasan ta tashi a aiki,bata barnar da sukayi bane
bama yanxu a gabansa,inda zainab ta sanya qafa ta fita bada izininsa ba tunda rana gashi ana
shirye shiryen kiran sallar magariba.

Cikin bacin ran yayi alwala ya wuce sallar magariba yana sanya ran kafin ya dawo ta
dawo,saidai ko sanda ya dawo din ba ita ba dalilinta,dole ya tasa qeyar yaran suka wuce
sassan ruqayya,don kuwa har sun fara jin yunwa,sunce rabonsu da abinci tun da rana,abind
aya sake dugunzumashi kenan. Mutum ne shi da yaqi jinin yunwa ko kadan,wannan ya sanya
baya bari a hora kowa da ita,koda baisan mutum ba bare cikin gidansa kuma 'ya'yansa.

Tana zaune tana lazumi,alhassan da alhussain harma da iftee na zaune suna cin
indomie da sukace sunan sha'awa ta kunna musu qaramin electric da ta ajjiye dama don
saboda su,don wani lokacin qananun dafe dafe sukan iyayi,yaran badai qoqari ba,dafa taliya
haka,shinkafa fara,ruwan zafi ruwan tea,tun uban yana fada da qorafi har ya barsu.
*_KURMAN BAƘI_* ⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 23

https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr

*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA
HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU
QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA
MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har
zuwa girmansu,akwai bonanza time to time da nakeyi,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba
daya_*


Sallamarsu ta amsa tana binsu da kallo cikin mamakin abinda ya shigo dasu dukka
haka a tare

"Ina zainab taje?" Ya tambayeta yana tsareta da kallo cikin salo na tuhuma. Idanu ta zuba masa
na wucin gadi kafin tace

"Bata tayi?" Ta amsa masa da salo na gatse,don ba wannan amsar taso bashi ba. Ya karanci ko
mene a idanunta,maimakon yayi qasa sai yaji ransa ya sake baci,gaba daya kaman sun
rainashi kenan ita da Zainab din

"Kina cikin gidan nan amma abar yara su wuni da yunwa don wulaqanci?,ita ta saka qafa ta fice
bata gayamin inda zata je ba,ke kuma kinsan suna cikin gidan a barsu a guri su kadai,yanzun
inda ace sun taba wani gurin sun hadawa kansu gobara fa?"

"Uhmmm.....Allah sarki" kawai tace dashi taci gaba da jan carbinta. Hakan data masa ya sake
qular dashi,idan ta saba share masa da qin yarda suyi zancan da ya danganci zainab ai issue
din yanzu ya banbanta da na ko yaushe ko?.

"Kai alhassan,ku dauki abincin ku qaro muku ku wuce dakinku kuci tare dasu haneefa"

"To daddy,alhussain dauko plate din,ke haneefa bari a zuba muku naku ke da iftee" sai yaja
yaran suka wuce.

Kallonsa ya maido kanta bayan yaran sun wuce

"Dake nake fa" kai tsaye ta sake kallonsa,duba daya ya fahimci da yunwa ya dawo daga
kasuwa,ita ya kwaso take kuma tunzurashi(muddin kinsan kina barin mijinki da
yunwa......muddin kinsan kina barin mijinki yana jiranki saikin kammala abinci to billahillazi daga
yau ki taimaki kanki ki daina,yunwa tana jawo fushi,shi kuma fushi mabudin dukkan sharri
ne,hanyar da zaki mallaki zuciyar mijinki shine ki kula da cikinsa ki tsare masa shi)

"Wai nikam ajiyarta ka bani?,ko munyi yarjejeniyar zata dinga neman izinina kafin ta fita?"

"To amma ai kece babba cikin gidan ko?,meye amfaninki da har irin hakan zata faru yara su

wuni da yunwa a sashen ba tare da kin sani ba?" Dan qaramin murmushi ne da bata shirya ba
ya subuce mata,tadan girgiza kai kadan

"Allah sarki,yau kuma ni ake baiwa girman ake bani muqamin na saka ido cikin gidan
nan?,bayan togaciya sharadi da iyakokin da aka taba gindayamin a baya?, gaskiya ne.......to
kayi haquri ranka shi dade,indai ba fitina kake nemowa ba kuma,yara dai bansan su kadai bane
a sashensu,da babu i zaa yi na barsu da yunwa,kafi kowa sanin bada abinci ko dafashi bai cikin
matsaloli na.......Abinci ne gashican an basu,ita kuma bansan ta fita ba bansan kuma ina taje
ba,shikenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da idanu itama.

Wani numfashi ya saukar,kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya ya nufi qofa,tana
kallonsa qasan ranta tana hadiye dariya da mamakin halin da namiji,kamar ba'a wannan falon
ya zauna ya qidanya mata dokoki da sharadai akan matarsa shalelensa wadda dangi kaf suka
aza tazo ta cika gidan da 'ya'ya ba,ta nunawa ita ruqayya cewa ita din cikakkiyar juya ce,kaman
bashi ba yanzun ya taho da confidence dinsa zai kawo mata qabli da ba'adi. Tasan yunwa ce
take sasaqarsa,ita kuwa tun a wancan zamanin da ya watsa mata qasa a idanu ta daina bashi
abincinta muddin ba ranar girkinta bane,gashi kuma shi din ba gwanin cin abinci a waje bane.

Har ya isa dab da qofa wayarsa ta dauki burari,ya dakata yana fiddo wayar,ya sake
qufula sanda yaga sunan zainab din.

Koda ya daga wayar saqon da ake gaya masa sai yaji ya girmimi kansa,dole bayan ya
ajjiye wayar ya waiwayo yana duban ruqayya,don ita kadaice yakejin zata tayashi tallafar nauyin
da zuciyarsa da qirjinsa sukayi. Matarsa ta aure?,matarsa ta sunna a kulle a station.

Sanda yake gayawa ruqayyan ita kanta abun sai ya bata mamaki ya girmimi kanta

"Me tayi har ya kaita police station?,yaushe 'yan sanda sukazo da ni da nake cikin gidan nan
banji ba har suka tafi da ita?" Tayi tambayar wadda daga shi har ita basu da amsa

"Wata rigima ya debo na tabbatar da haka" ya fada cikin gamsuwa

"Babu lallai,kaidai ka bincika"

"Wallahi ko kaffara bazanyi ba idan na rantse,nasan halinta ciki da bai,taimaka kizo ki rakani
muje" da sauri ta kada hannunta

"Wa?,ni?,daga qarshe zance ya juye ace ni na saka aka kulleta?,Allah ya tsare hanya a dawo
lafiya" ta fada tana nade abun sallarta. Haka ya tsaya yana binta da kallo harta gama nadewa ta
wuce daki gurin yaran.

Yana tuqi a hanya zuciyarsa tana dada zafi,cikin mintuna qalilan ya isa police station
din. Muryarta ya fara cin karo da ita suna sa'insa da wani dan sanda,fadi yake cewa

"Banda aure dake wuyanki da saikin raina kanki,yanzunma kuma kici gaba da cikama mutane
guri kiga idan ban saka su Monica sun sassaba miki kamanni ba" tasan yadda yake da zafi iya
awannin da sukayi a wajen,don haka ta rage sautinta,saidai kuma bata fasa maganganun ba.

Kunya baqinciki da takaici suka ishi saleem sanda ake karanto masa statement na
dalilin zuwansu gurin

"Maganin mata da shiga har gida su doki mace har dakin mijinta" ji yayi kaman zai mutu saboda
takaici,wanne irin tonon silili ne wannan?. Banda darajar su haneefa da khalil babu abinda zai
hanashi tafiyarta ya barta a wajen ta nemi me belinta,to amma yaran kawai ya tuna ya karbi
belinta harda tararta da sukaci,saidai kuma suna fita farfajiyar gidan yace ta nemi gidan
zuwa,kada ta sake ta dawo masa gida,yaja motarsa ya wuce abinsa.

Sanda ya koma yaran duk har sunyi bacci a dakinsu,shi Khalil dama cikinsa yana
dauka ya haye tattausan gadon alhassan, komai iri daya aka siya aka zuba musu,to amma
rashin kulawa da rashin tsafta yasa yaran suke ganin dakinsu alhassan din kamar yafi nasu
kamar nasu dakin wata aljannar duniya ne.
Wanka tayi data tabbatar sunyi bacci,ta saka rigar material mara nauyi. Abinka da me
yaron ciki sai taji tana son shaqar iskar waje,don haka ta saka qaramin hijabi a kanta,ta dauki
qaramin littafin hisnul muslim da taketa qoqarin haddace wasu addu'o'i masu muhimmanci a ciki
ta fita waje.(akwai addu'o'i masu tarin muhimmanci a ciki,kada ki zauna ace baki haddace
kowacce addu'a ba 'yar uwa,akwai babban hatsari,kaman ka gina gida ne babu qofofi ko
winduna).

Bata jima da zama ba taji hon dinsa,yaron gidansu da bai tafiya sai 12 na dare shi ya
bude masa ya sako motar ciki. Tana zaune har ya saita parking ya tako zuwa cikin gidan kai
tsaye kuma ya nufo sashenta.

Daga kai tayi tana amsa sallamar sa tare da nazarin ganinsa shi daya

"Ya na ganka kai kadai?,ko ta wuce ciki?" Ta tambayeshi tana gyara zamanta cikin kujera. Kai
ya dauke gefe guda

"Me zanyi mata?,na karbo ta amma saidai ta wuce gidansu,don ni bazan iya zama da ita ba da
wannan abun kunyar da ta jawomin"

"Ban fahimceka ba,kaman yaaya?" Ta tambayeshi fuskarta a dan yamutse

"Eh nace ta tafi gidansu" kai ta ya shiga girgizawa

"A'ah, bazaiyiwu ba,ta tafi gidansu ta barwa waye yaranta?,haka kawai mace na gidanta ka

sallameta?"

"Au haka kawai ne ma?"

"Eh mana,don tayi laifi?,waye baya kuskure?"

"Ganganci ne wannan zallar taurin kai da rashin jin magana"

"Hakanan zakayi haquri da ita,amma ba inda zataje,don ban shirya riqon dan kowa ba,koda nan
gaba aure ka qara to ka saka a ranka mutu ka raba kai da ita,nima nawa ban gama wahalarsu
ba"

"Sai naga ta yadda zakimin dole" ya fada yana shirin wucewa sashenta

"Bafa kwanana bane,kada ka shigarmin gida ka tayarmin da yara" ta fada tana miqewa tsaye.

A zafafe ya waiwayo yana dubanta,yana jin kamar tanason tunzurashi ne,wai wacce
irin macace ita?wasu matan suna murna suna jiran irin wannan damar?,amma ita ta samu tana
tankwabewa?.

Baikai ga cewa komai ba aka buda can qofar get aka shigo. Akwai wadatar hasken
fitilu a farfajiyar,don haka kana iya gano zainab.

Dakatawa yayi da shirin shiga ya nufota rai bace

"Ba gida nace ki wuce ba?"

"Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba, tsautsayi ne wannan ma"

"Banason na sakejin komai daga bakinki,gida nace ki tafi"

"Bafa inda zataje,waye baya kuskure?,sai ka zauna ka fahimceta ai,idan da hali a bata uzuri
ko?" Shi da zainab din dukansu ita suka kalla,zainab din bata taba kawo zata sanya baki ko ta
bata kariya ba,amma duk da hakan da tayi bataji ta burgeta ba

"Wannan ba hukuncin ki bane ba kuma huruminki bane,hukunci na riga na yanke"

"Eh haka ne.....to jirani nima na hado nawa kayan mu tafi tare" ruqayya tace tana juyawa zuwa
cikin gidan. A yadda taga tayi maganar ya tabbatar tana nufin abinda ta fada din,ya waiwaya ya
dubi ruqayya sake shigewa ciki ya kalli Zainab dake tsaye saroro

"Ki wuce ciki,amma wallahi saikin gane kurenki don bazan lamunci wannan zubda mutuncin ba"
baqinciki da farinciki ne dukka suka gaurayar mata lokaci daya,tabbas badon ita ko domin Allah

saleem ya barta ta koma dakinta ba. Yanzun kamar ita ace albarkacin kishiya taci?,wanne irin
babban abun takaici da abun kunya ne wannan?.

Wannan abun yayi wata wawuyar tsaiwa a zuciyar Zainab,a daren ranar baccinta
ragaggge ne,duk sanda ta juya sai abun ya fado mata,wutar qiyayyar ruqayya ce kawai take
sake ruruwa a zuciyarta.

To wai banda don a gallaza mata a tozartata me yakai saleem aurota yasan ruqayya
nada wadannan qualities din?,wato amfaninta kadai a wajensa dai dai yake da machine na
haifar yara?,eh mana......tazo ne kawai kenan don ta cike masa gibin haihuwa?,a yanzun kuma
da haihuwar ta samu daga gurin ruqayyan sai komai ya sake zama wani iri. Ya akayi a komai
sai ruqayya ta fita ne?,iya cikin jikinta kadai ya isa abunda yake hana ma zuciyarta da
kwanyarta nutsuwa da kwanciyar hankali. A daren taji burinta na qarshe a rayuwa shine taga
bayan ruqayya,ta tabbatar shine abinda zaya sama mata nutsuwa da kwanciyar rai.

******Cikin kwanakin gaba daya damuwa ta yiwa wasila yawa,duk idan ka ganta zakasan bata
cikin nutsuwarta,faisal yayi mata dukkan wata bazata da bata taba kawowa ba. Da ruqayya
kadai tayi zancan bayan ummanta,saboda da ruqayyan ta amince,don kowa kallonsa take a
matsayin wanda zai iya zaka mata hannu a lalacewar maganar aurenta. Duk yadd kaso ga
bawa wasilan shawara ba lallai tayi tasiri,don haka iya gwargwadon hali ruqayya ta lallasheta ne
tare da bata shawarar dagewa da addu'a,duk da tasan babu lallai addu'ar tayi mata tasiri tunda
ta riga ta raba qafa. Dan man da take shafawa kwana biyu ta aje saboda bacin rai,hakan ta fada
qibar ta dan janye kadan.

Cikin wannan lokacin yara suka kammala exams, za'a yi musu hutu,hakanan an
gayyaci dukkan iyayen yara don su halarci makarantar za'a yi taron tafiya hutu da bada
kyaututuka ga haziqan dalibai.

Farko ruqayya cewa tayi ba zataje ba,tunda duka makarantar yaran nasu daya ne
Zainab din ta wakilceta kawai. Saleem ne yace a'ah,dukkansu suje kawai,bataso zuwa din ba
don cikin yazo mata da zaman daki zuwa falo,batason leqawa ko ina,amma hakanan dai tunda
yace aje din ta kira wasila tace tazo suje tare tayi mata rakiya.
Kowa a motarsa zashi,don haka koda ta tashi tafiya bata cewa Zainab din komai ba.
Tunda ta lura ta dauki wata gagarumar gaba da ita tun daga ranar da tace zata bita suyi yaji
tare,sai itama ta sake kama kanta fiye da baya,don a nata ganin meye nata a ciki?,fadanta
dama tsakaninta da mijinta ne,abinda ya sanya harta sanya baki ma shine ganin za'a bar mata
wahalar yara,wanda ba ita ta fara tarbiyyarsu ba,so

17 / 24