KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   5 / 24

12K to 15K   out of 69.9K words

wajenta duk wadan
nan abubuwan da yakeyi din bata lokaci ne kawai,tafi ganewa kai tsaye a shiga karatun.

A yadda komai ke tafiya ya saka farinciki a zuciyarta ya kuma tabbatar mata da lallai
yau din taci kudinta. Saidai a gefen saleem tun yana fahimtar abubuwan suna masa yadda
yakeso har ya fara shiga wani yanayi na mamaki. Buqatuwarsa ta yau ta wuce ta kullum,abinda

bai taba tsintar kansa a ciki ba muddin yana tare da Zainab dinne. Lokaci da qa'ida daya
kamata ace komai ya lafa yazo qarshe sai ya kasa dakatawa. A hankali jikinsa ya fara
weakening bugun zuciyarsa yayi mugun linkuwa,abinda ya haifar masa da haki da wani
mahaukacin gumi.
Bazai iya cewa ga yadda akayi ba,shi dai ya samu kansa da yin wani dummmm,kafin
daga bisani yaji kamar jijiyoyin jikinsa basa aiki,ya sulale a hankali yayi kwance a gefe yana
fidda numfashi.

A qalla ya kusa mintuna goma a haka,sam bata lura ba tana daga kwance ta sheme
tana sakin murmushi hadi da kada idanu,lallai yau akwai babbar kyauta da zata samu daga
wajen saleem. Komai ya gudanar cikin wani irin zafi da kalar buqatuwar da takeso kullum ta
ganshi a ciki.
A hankali numfashinsa ya fara dai daita saidai yanzu kansa bai sauka daga nauyin da
yayi masa ba,hakanan gangar jikinsa babu wata gaba dake da qarfi ko kadan.

Miqewa yayi ya zauna yaja jikinsa da qyar ya wuce bandaki,da kallo ta bishi tana gyara
kwanciyarta murmushi yana sake fita a fuskarta. Har ya fito tana kwance,ya goge jikinsa da
towel ya sanya baqin gajeran wando da singlet ya dawo gefen gadon yana takawa a hankali ya
zauna yana bata baya.
"Tashi" yace da ita. Wannan ba sabon abu bane,duk sanda mu'amala ta shiga tsakaninsu shike
fama da ita akan ta tashi ta tsaftace jikinta,har yau har kwanan gobe kuma bata canza ba,koda
alwala kadai sai yayi yaqi takeyi bare wanka da sai da safe ma wani zubin sannan ta rattaba
sallarta ta kuma hau shirya yara zuwa makaranta,wannan ya zama silar da duk sanda wani abu
ya shiga tsakaninsu sai yara sun makara a makaranta,koda su alhassan sun shirya da wuri
kuwa,tunda tare driver yake kaisu. Wannan ya sanya tun hankalin ruqayya baikai ba har ta
fahimci abinda ke jawo hakan,saidai koda wasa koda saleem din bata taba nuna masa tasan
dalili ba har yau har gobe.

"Ni gaskiya bazan iya tashi ba,haba kaman ba kaga rashin imanin daka yimin ba yau,alwalar
ma idan Allah ya kaimu asuba nayi" ta fada tana wani narkewa.

"Me kika bani na sha zainab?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ya waiwayo ba.

Ido ta fidda waje hadi da tashi ta zauna ba tare data shirya ba

"Me kuwa zan baka daddyn haneefa,me ya faru?" Waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa
da suka sauya launi saboda kansa da yakeji ya masa nauyi

"Yanayina ya canza,ba haka nake ba"

"Okay,inda a tattare da ruqayya ka samu hakan ba zakace komai ba,saini saboda ban cika
macen da za'a ji haka tare da ita ba?" Sai ta fashe masa da kuka. Can qasan ranta tasan
tabbas ta kusa jawowa kanta matsala ne kawai,dose din maganin qwaya daya ne amma ta
saka uku,kuma taji suna shaqiyanci a group din tare da gargadin masu wuce gona da iri din
irinta ko ita a yanzun bawai ta gama sauka bane,amm bataga ta bakin cewa komai ba gudun
tabbatar masa da zarginsa.

Zazzabi yakeji a jikinsa baya kuma buqatar wata doguwar hayaniya ko qorafi,don haka
ya dauke kansa yaja jikinsa ya koma saman gadon yana rufa da blanket idanunsa a rufe yana
ambatar ALLAH qasa qasa.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 06


*****Kamar kowacce rana da zata karba girki,duk sanda ka ganta tana gyare gyare zaka
tsammaci wata tafiya me nisa saleem din yayi yake shirin dawowa. Kusan komai na dakin sai ta
tabashi,wani ta canza masa guri wani ta gogeshi wani ta sauyashi gaba daya. Kafin azahar sai
ta tabbata komai na dakin ya sauya daga ainihin yadda saleem ya fita ya barshi.
Sha daya na rana ta fito daga dakin bayan ta gama kintsashi. Qofar ta murda ta bude
ta fito parlor dinta hannunta riqe da qaramin towel da tayi goge goge dashi.

Alhassan da alhussain ne zaune sun sanya tv a gaba,sun wani nutsu har abun yaso
nata dariya. Ta jima bataga yatan dake masifar son kallon cartoon ba irinsu

"Yadda kuka nutsu kuna wannan kallon,kada ku yarda anjima nazo karban hadda naci
gyaranku". Yare suka dago kai suka kalleta suna dariya,alhussain ne ya fara cewa

"Ni ko yanzu ma mommy ki karba Allah na shirya"

"Nima din ai na shirya yaro" alhassan ya fada. Take 'yar musu ta barke a tsakaninsu. Gaba tayi
ta barsu a gurin,don irin wanann qananun rigingimun nasu a rana har bata iya riga adadin sau
nawa sukeyi,saidai fadan baya nisa ake watsewa,shi yasa ba kasafai ta fiya damun kanta da
rabo ba.
Gaban fridge dinta ta qarasa,ta saka hannu ta bude tana ciro wata doguwar gora me
kyau,sai ta azata saman Fridge tana kallon agogo da dan mamaki a fuskarta. Tun dazun take
mamakin rashin jin motsin saleem,duk da bata son zurafafawa kanta da tunanin abinda ya
hanashi shigowa dubasu tunda hakan ba sabonsa bane,tanata son kiransa ko tabi ba'asin jinsa
shurun amma zuciyarta tana kwabarta. Batason abun rigima da fitina,ko kuma taje ta gano ko ta

jiyo abinda zai motsa kishin da taketa qoqarin ganin ta mallaki zuciyarta a kansa.

Sai da yadan huce sannan ta bude gorar,take qamshin kanunfari da sauran kayan
qamshi suka cika gurin. Tun kafin takai bakinta yawunta ya tsinke,ingantaccen tsumi ne data
zauna ta dafashi da kanta jiya da sanannun saqe saqi da danginsu rake mazarqwaila harma da
zuma a ciki. Cup daya ta cikashi dashi ta fara sha a hankali. Idonta ta lumshe tana jin dadinsa
har saman harshenta,sai data shanye a nutse sannan ta kife cup din wanda yayi dai dai da
kwada sallamar Zainab,sannan kai tsaye ta danno cikin parlor din.

Hannu ruqayya ta sanya ta dauke gorar tsumin nata tana qoqarin maidawa fridge,duk
da ba wani abu bane don Zainab din ta gani ba,koda ta gani tasan ba lallai ta fahimci meye
ba,to amma ita din mutum ce da ba komai take bari idanun kishiyarta yakai kai ba (hakan ba
laifi bane,yana da kyau ki iya takunki wajen kishiya,ba komai kike bari tana sani naki ba,koda
kuwa me kyau ne,akwai abubuwan da sukan zama tamkar wani sirri ne naki,kuma makaminki
da kike naki yaqin cikin gidan tsakaninki da mijinki,barin kishiya tasan da wannan sirrin ko
makamin tamkar wargazawa kanki da kanki shiri ne). Tuni idanunta suka kai din,tunda itan tana
cikin jerin sahun matan da komai kayi suna da buqatar sani ko gani,amma tunaninta sai ya tafi
ga wani abun daban

"Ana nan ana fama da coca-cola" ta fadi qasa qasa. Bata damu da kallon da ta bita dashi ba,ta
gyara zaman tsumin ta maida fridge dinta ta rufe tana amsa sallamar tata

"Aron mopper zaki ban yara sun karya min tawa" ta fada tana riqe hannu a qugu. Sau tari tana
mamakin Zainab har ba iyaka,duka yara biyu amma idan kaga barnar da ake a sashen nata
zaka dauka wasu gayyar yara gareta. Duk tsananin baqin kishinta kuma bata kunyar aron abu
daga hannun kishiya?,wani abu guda daya tal da ruqayya zata iya bugar qirji tace bata taba yi
ba(zubda kaine aron abu a wajen kishiya,muddin ba wai ta kama bane ko ba yadda
zakiyi,komai da kikasan zaku buqata keda yara siya ki ajjiye,gwara ke a ara a hannunki).

Waiwayowa tayi ga alhassan ta sanyashi shiga store ya dauko mata,saidai sanda ta
maido dubanta ga zainab din sai ta sameta tana sana'ar tata wato sanya ido. A duk sanda wani
uzuri ya kaita ga shigowa sassan nata to ba zata taba fita ba sai ta yiwa parlor din nata kallon
tsaf!,in sha Allah duk abinda ta gani sabo ko baqo sai tayi qoqarin siyan makamancinsa. Abun
tun yana bawa ruqayya mamaki har ma sai ya koma bata dariya.

"Nikam daddynsu lafiya na jishi shuru bai leqo ba?" Tambayar da tayiwa Zainab mugun dadi,sai
ta waiwayo tana sakin murmushi

"Angoncinne ya motsa,don da qyar na lallabashi ya fita sallar asuba saboda jiya bamu samu
isashen bacci ba ni dashi duka,saboda tsabar duniya ta masa dadi harda wani guntun zazzabin
shagwaba" Girma sosai maganar ta yiwa ruqayya,takai idanunta da sauri kan alhassan da
alhussain iftee dama baccinta takeyi saman kujera. Allah ya taimaketa hankulansu gaba daya
ya tafi kan cartoon din sosai,da alama kunnuwansu basuyi wannan baqin jin ba,sai ta daga ido

ta maida dubanta ga zainab.

Idanun zainab din fes kan fuskar ruqayyan tanason ganin bacin ran da ta qiyasta zata
gani din,saidai ga mamakinta murmushi ruqayyan ta saki bayan ta tako zuwa sashen da take
don ta kaucewa kunnuwan yaran jin abinda bai shafesu ba

"Ayyah,kayya kiyi masa sannu,ai ban sani ba,bai kamata ace har wannan lokacin ba'a shiga an
dubashi ba,amma ina nan shigowa na duba angon naki,irin wannan dattijon amarci ga shekaru
ga kuma bar muku sudi?,da kin sani ai aikomin kikayi dasu haneefan,kinga ni lokacin nawa
amarcin duk girman gidan nan daga shi sai ni,baccin shekara ma sai muyi babu me tashinmu".
Baki Zainab din ta tabe,maimakon ran ruqayyan ya baci sai tata zuciyar ta soma motsawa

"Ah ai kunsha bacci,shi yasa tsabar bacci aka dauka juya ya auro"

"Sai kuma ga mazaje har guda biyu sun wanke sunan ummansu daga juya zuwa uwar maza
ba" ta maida mata amsar tana tsuntsira dariya abinta hankali kwance.

Baki yasan abinda zai furta saidai kuma bashi da masaniyar amsar da za'a bashi.
Maganar ta sake tunzura Zainab din,sai ta juya tana ficewa a gurin

"Ki bar mopper din a wajenki idan kin gama" ruqayyan ta sake fadi,saidai ko waiwayowa zainab
batayi ba ta qara gaba. K'aramar dariya ruqayya ta saki,kwata kwata wautar zainab take
gani,idan tasan halittar ta saurin fushi,tunzura da rashin iya cinye bacin rai,to ya kamata ta
kiyaye shiga ko faro maganganun da amsarsu ba zasu mata dadi ba,ta dinga kame kanta da
hana kanta da kanta shiga hurumin da bai shafeta ba,ke da aka yiwa tambayar me gida kurum
saiki zaqe?,bayan kinsan zuciya da fuskarki duka basu da baiwar iya shanye bacin rai da maida
komai ba komai ba

"Kadanma kika gani,na fiki iya iskanci" ruqayya ta fada tana komawa ciki.

Kitchen kawai ta shige abinta,ta canza shawarar shiga dubashi din,a maimakon hakan sai
ta jawo wayarta ta tura masa tex tana masa sannu da jiki. Yana fahimtar ta qwarai,tasan ko iya
tex din ya wadatar. Data tabbatar ya shiga saita bude fridge ta ciro lafiyayyen kifi mara wadatar
qaya ta kwara masa ruwan zafi sannan ta fara aikin sarrafashi.
Nau'in kifin da saleem yafiso ne,kuma ita din bata taba rabo dashi koda wanda ya siyo
ya qare,tana siya da kudinta ta zuba a fridge din. Jin dadin hakan ya sanya duk sanda yazo
yaga ta zuba din zai biyata kudinta harma wasu lokutan ya qara mata. Abun na masa dadi
qwarai,saboda na gefin Zainab sau tari saidai yaga an zubda a shara ya lalace,don ba damuwa
ta fiyayi da kunna Fridge din kayan miya ba kwata kwata,ko ta kwashe ta bayar kyauta don
kawai tayi bajinta.

Kafin ta gama aikin ta kira qanwarta

"Kizo ku tafi dasu alhassan su kwana gobe sauka idan jikin abbansu yayi sauqi na samu fitowa
saimu dawo tare,tun jiya dama na tambayar musu" ba jimawa ta iso gidan,saita sakar mata
gyaran kitchen din,ita kuma ta wuce bedroom dinta.

Wankanta wani abune da bata wasa dashi,kowanne lungu da saqo da tasan maboyar
datti ce sai tabi ta qalqale,ramin cibiya,qasan mama duk da tana da baiwar tsayayyun
mama,matse matsin mazaunai,matse matsin cinyoyi,bayan kunne harma da cikin kunnen da
qasan mara.
Cikin mintuna talatin ta fito fes cikin doguwar rigar atamfa chocolate color din fatartan
nan tayi luf cikin qamshi da cream masu taushi,daurin dankwalin kuma ya zauna mata sosai a
kanta. Sai da tayi sallar azahar sannan ta dawo parlor din.

A falo ta samu anata daru da iftee tace itama sai taje,da farko sai ta qyaleta tanata
saka turaren wuta a burner tare da jona humidifier dinta,har ta gama bata bar kukan ba
yarinyar,duk da ba'a jima da dawowa da ita gidan daga yaye ba, dole ta hada mata kala dayan
itama ta bisu din.
Kitchen ta wuce,ta ciro dafaffiyar budurwar kazarta da tasha hadin saqe saqi,kazar
da take dafata da hannunta da ingatantattun saqe saqi da kayan da suke bawa jiki garkuwa da
lafiya su kuma magance ciwon sanyi. Dan dumamata tayi kadan sannan ta zauna a nutse ta
fara ci hankali kwance saboda sashen nata ya dauki shuru. Minti goma sha biyar ta gama,sai ta
wuce da kwanon kitchen,ta koma dakinta tayi brush sannan ta dawo ta sake mulke jikinta da
turaren da ba kasafai take amfani da shi ba idan ba lokacin kwanciya bacci ba saboda yadda
saleem din ke matuqar sonsa.

Bata yafa komai ba sai wani dan siririn gyale da yafi kama da mayafin yara wanda ya
dace da atamfar jikinta ta fito daga sashen nata ta ratsa babban falonsu da yaron dake musu
aike aike cikin gidan tuni ya gama tsaftaceshi ya wuce sabgar gabansa,ta doshi qofar falon
sashen zainab din.
Tun bata qarasa ba take jiyo ifce ifcen haneefa da khalil,da alama ma fada sukeyi,don
tana jiyo muryar uwar tana kwarara musu tsawa wanda sauran kadan ta barke da ashar,tana
tuna cewa saleem din yana gidanne da tuntuni ta hadasu data maguzawa,tunda a cewarta ta
lura sunfi ganeta.
Duk da tayi sallama ba wanda ya jiyota,sun kacame da dambe. Ta sanya qafarta da
hanzari don ta isa ta rabasu,saudai tayi kyakkyawan Katarin taka wani abu me danqo. Koda ta
dube sai taga ashe tea ne aka watsar har ya fara kama gurin ya soma bushewa. Tsigar jikinta ta
zuba,ta janye qafarta tana takata saman carfet din falon saidai a nan ma qasa ta cabo a qasan
qafartata. Dubanta ta maida ga tafin qafartata kafin ta dago kai saleem da hayaniyar ta isheshi
har ta tayat dashi a bacci ya fito a dakin.

Dif sukayi kowanne na neman gurin buya,sai suka fara qoqarin barin parlor din. Bai
lura da ita ba saboda baiyi tsammanin shigowarta ba,saidai sassanyan qamshin da ya gauraye
parlor din yake shiga masa hanci ya sanyashi wara idanunsa a parlor din. Qamshine da a jikin
mutum guda ya sanshi,qamshine da duk sanda ya jishi ya tabbatar zai samu wani irin tarairaya
da soyayya me girma,qamshin dake nuni da zai shiga wata duniya me cike da tarin nutsuwa.

Ido suka hada daidai da fitowar Zainab daga kitchen wadda ke mamakin me ya sanya
haneefa da Kahlil din nutsuwa lokaci guda?.

Sarai ruqayya ta ganta amma ko da ido bata nuna mata hakan ba,sai tafi maida
hankalinta ga saleem din.

"Zuwa nayi na tafi da ango,ban sani ba ko angoncin daka balle jiya ya hanaka gane hanya shi
yasa har yanzu baka samu shigowa ba" ta fada a tausashe tana murmushi. Hannu yasa ya
shafi sumar kansa,har yanzu baya jinsa ya koma dai dai,kuma har yanzun idan ya tuna jiyan ya
kasa nutsuwa haka siddan ya koma haka,ba abinda zai iya dorarwa me shauqin da zaice yayi
matuqar qayatar dashi da zai tsaya masa a rai,face wasu irin abubuwa da hancinsa ya shaqa.
Idanunsa sun rufe ya zurfafa hancinsa cikin jikinta,abinda dama ba kasafai ya fiya yi ba,wannan
din wani sirrinsa ne da ba mahaluqin da ya sani,ruqayyan kadai yake iya yiwa hakan,saboda
yasan duk

5 / 24