Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : Taskar Novels
SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU
QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA
MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har
zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________
Tana kitchen taji ya sake shigowa
"Ki dauko mayafi muje mu kaita" waiwayowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta kauda kai. Wani abune
ke mata yawo a zuciya,ba zata taba manta wannan ranar ba,ranar da banda kiyayewar Allah
babu abinda zai hana ta rasa ranta a abinda Zainab din tayi mata,bayan ta rasa ranta harma ta
rasa ran abinda yake cikinta
"Kuje kawai saikun dawo,zan zauna da yaran tunda dai ba za'a barsu haka gida ba kowa ba"
ido ya zuba mata na wasu sakanni,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice.
Koda ta gama kintsa kitchen din alhassan ta aika ya kirayi su haneefa suka dawo
sashenta,sannan ta saka alhassan din ya kulle sashen zainab din,don yafi haneefa nutsuwa da
hankali,sau tari banda tsaho da ta fishi zaka dauka shine babban.
Falon ta dawo ta zauna lokaci lokaci tana duba wayarta,yaran suna kallon carton,saidai
bari bari da su haneefa din keta sanyata,ba'a samu sauqin abun ba sai da khalil yayi bacci.
Dole ta saka ya qure ac dinsa saboda yanayin da jikinta ke bayarwa da ya soma
dumame motar. Yawun takaici kawai yake hadiyewa,ya rasa me Zainab ke buqata a rayuwa da
zai sanya ta canza halinta. Wasu lokuta yakanji kunyar ace ita din matarsa ce,abinda bai taba ji
ba dangane da ruqayya duk da sunfi dadewa da ita nesa ba kusa ba akan zainab din.
Wani kuka take kwazara mishi babu dadin amo bare dadin sauraro,ita a haka dole
kukan da zai taba ransa yaja hankalinsa,abinda bata sani ba zallar takaici ne ya qumeshi.
"Wallahi na sake yarda da gaske asiri yana tasiri a kanka,na rantse da Allah ko kaffara bazanyi
ba inda ruqayya ke wannan kukan da tuni ka rasa inda zaka tsoma ranka,amma ba komai
akwai Allah"
"Ba zaki rusuna ba kenan ki saita kanki ba"
"Me nayin da har zan rusuna?,saboda kawai idan ba'a sonka idan ka fada ruwa ma sai ace ka
tayar da qura?,kuma ko meye ya sameni ai ta sanadinka ne,duk inayine don na gyara kaina na
samawarwa kaina 'yanci kamar yadda ruqayya ke dashi,don bana son kaucewa hanya nabi
malamai".
"Anzo gurin" ya fada a ransa,cikin zuciyarsa yana fatan ace shiriyarta ce tazo,sai ya sassauta
tuqinsa yana duban titi
"Ai baki kama hanya ba sam zainab,ke din ba makauniya bace amma ta wani fannin kinfi
makaho makanta,ta yaya kike tunanin zaki kamo ruqayya a haka?,bayan kinfi kowa sanin
abubuwan da takeyi wadanda suka kaita matsayin da kike hange?,duk da ina iyakacin bakin
qoqari na na yin adalci a tsakaninku?" Kamar ta banka masa ashariya haka taji,ita da yayi mata
misali ko kwatance da ruqayya gwara ya sakata a daki ya lallasata tayi dumamen jikinta
"Wanne abu takeyi banda zallar kissa da munafunci da bin malaman tsubbu duk don ta
mallakeka?,idanunka ya rufe ka kasa ganin gaskiya?,ni da kullum nake fadi tashin gyara maka
shimfidarka amma qoqarina a banza yake kullum". Kai ya girgiza
"Zaki bawa Allah tabbaci ranar qiyama akan qazafin bin malamai zainab,ki kiyaye harshenki
daga fadar abinda baki da yaqini akai" kuka ta fashe masa dashi
"Ehnnn,an tabo shalelenka ba?,muddin kana irin wannan akan ruqayya wallahi zaman lafiya
tsakanina da ita har abada" ko ya waiwaya ya kalleta bai sakeyi ba,ya sani Zainab tayi nisan da
bazata taba jin kira ba sai wani ikon Allahn.
Sun samu sunga likita,amma yawan gudawar da takeyi yasa likitan yace zata kwana
anan a saka mata drip,gudun kada suje gida cikin dare abun yayi worsening.
Sosai ta sharbe masa tana ci gaba da koke kokenta da babu abinda suke qarawa
saleem sai takaici. Don tuni likita ya gaya masa ya dinga sakata tana kiyaye shan magani
barkatai
"Magungunan nan basu da wata qa'ida ko doka,duk maganin da za'a shashi ba bisa qa'ida ba
dole yayi illa" tuni saleem din ya fahimci maganin meye,ba zata daina halinta ba kenan duk da
tarin gargadin da yayi mata?.
Bai iso dakin da suka batan ba sai daya kira hajiyayye qanwar mahaifiyarta akan tazo
ta kwana da ita sannan ya wuce dakin. Tanajin sallamarsa ta sharbe magashiyyan. Baibi ta
kanta ba tsabar takaici,yaja kujera ya zauna kawai yana danna wayarshi.
Ba dadewa hajiyayye ta iso,ya miqe yana bata gurin zama
"Da kayi zamanka abinka" hajiyayye tace
"Ah dama ke nake jira,tafiya zanyi ni" ido zainab din ta bude da sauri,taci alwashin yau kwanan
asibitin zaiyi,shine abinda zatayi kawai wanda zai quntata ran ruqayya. Yunqurin amai ta fara yi
na qarya,shi da hajiyayyen dukka suka qaraso,saidai babu wani abu data fitar don tuni aman
gasken ya fidda komai daga cikinta
"Idan na fita zan tsaya na yiwa nurses din magana,ko alluran tsaida amai din suzo suyi mata" ya
fadi yana matsawa gurin saman kanta
"Sai da safe zan sake shigowa,banajima zamu kai azahar bamu koma gida ba,Allah ya
sawwaqe " ya fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya ajjiye gefan kanta cikin qoqarin danne
bacin ransa kada duniya ta fahimci halin da suke ciki
"Yanzu ko tausayin halin da nake ciki bakayi tafiya zakayi?" Ta fada da qarfi don hajiyayye taji
harda matso hawaye
"Banda abinki zamansa a nan ai bazaiyiwu ba,kuma me zaiyi miki shi da bashi ke cire ciwo
ba?,jeka abinka gida,Allah ya bamu alkhairi"
"Sai da safe" ya fadi yana ficewa.
Kaman jira takeyi ya fitan ta miqe ta zauna sosai har cannula din hannunta na qoqarin
gocewa
"Banso kikayi magana ba, wallahi hajiyayye na fara gajiya da rashin adalcinsa,qiri qiri mutumin
nan kiga abinda yakeyi,na rantse miki da Allah yau inda ruqayya ce zatayi kwanan asibiti bazai
iya tafiya ya barta ba" kai kawai hajiyayye dake cire hijabinta ta daga ta kalli Zainab. Duk da
tasan wasu abubuwan amma sai tayi kaman bata sani ba ta hanyar tambayarta
"Saboda me?"
"Saboda wani irin mahaukacin kula da yakeyi da ita da wani kulawa da na tabbatar ba ta domin
Allah bace"
"Ke ya akayi kikasan bata Allah bace zainab?" Hajiyayye ta fada tana jawo kujera dab da gadon
Zainab din saboda su biyu ne a dakin,donma daya patient din tayi bacci abinta tuntuni,kuma
abun mamakin ita kadaice babu dan jinya. Sake jan kujerar tayi baya kadan saboda yanayin da
jikin zainab din ke bayarwa taci gaba da kallonta daga nesa nesa
"Yo hajiyayye aiba irin wannan soyayyar a yanzu a wajen mazan wannan zamanin,kana gyara
ma ya ka cika dasu bare baka gyara,nifa kullum cikin fuskantar matsala nakeyi da saleem,kyara
gwasalewa,komai nayi banyi dai dai ba,komai nayi baya nuna wani jib dadi ko kuma wai na
burgeshi,ni kuma a iya sanina macen da bata gyara HQ dinta ita ke fuskantar wannan
matsalar,macen dake gyara take kulawa baji ba gani ai tafi qarfin ayi mata irin wannan tijarar,to
ita ba wani gyara da takeyi matar nan,idan kuwa ba asiri ba banga ta yadda zata mallaki saleem
ba"
"A tunaninki?" Hajiyayye data gama sauraron soki burutsun zainab ta fadi tana dubanta
"Hakane mana" zainab ta amsa mata kai tsaye
"Sam sam" ta sake maida mata tana zama sosai idanunta cikin nata
"Mun sani mafi rinjayen abinda ake kira da aure wannan abunne,to amma shi kansa baya tasiri
baya kuma qayatarwa gami da jan hankalin d'a namiji saikin mallaki wasu
abubuwan,tsafta,ladabi biyayya iya magana tattalin miji da tarairaya duka ina kika barosu?,ina
kika baro iya girki?,ado da gayu?"
"Duk basukai wannan muhimmanci ba hajiyayye,indai sune ke riqe maka miji me yasa saleem
ya auroni idan ka cire matsalar haihuwa?,ita kanta haihuwar ba damun wani namijin tayi ba
indai zai samu wannan gurin da kyau" ta fada tana qoqarin maida kanta ta kwanta,don kwata
kwata maganganun hajiyayye basu samu matsugunni a ranta ba.
Ta dade da sanin Zainab da kafiya da kafirin taurin kai,musu kuwa ba abinda yafi mata
shi sauqi,tunda har bata da intention na ta fahimcetan to ba fahimtarta zatayi ba,zata batawa
kanta baki ne,don haka tace
"Gaskiya ne,hakane,amma akwai gaskiya daya da zan gaya miki,don Allah ki dinga qoqarin
amfani da turare,sannan kodon zirga zirgar da kake wuni kanayi wankanki ki maidashi sau biyu"
"Ke hajiyayye kin ganni nan,saleem bai taba cewa wani abu ba,turare kuwa mu ko munsa ko
bamu saka ba mun wanku fes daga gurin kakanninmu,jikinmu baya komai in gaya miki,ki
qyaleni na huta"
"Hakka" tace da ita kawai tana tura kujerarta baya,ta dauki wayarta ta soma chart
abinda.(hajiyayyen bazawara ce, mijinta ne ya rasu ya barta bata taba haihuwa ba,shekarunta
kuma duka duka basu wuce arba'in da biyu ba).
Idanunta ta rufe saidai maimakon tayi nazarin maganganun hajiyayye a'ah,asarar da
zata tafka ta maganinta take qiyastawa indai shegen likitan nan ya riqeta bai sallameta ba a
gobe
"Aikuwa koda tsiya koda tsiya tsiya dai an sallameni gobe" ta fada tana muskutawa hadi da
gyara kwanciyarta.
"Me kika ce?" Hajiyayye ta daga kanta tana tambayarta
"Ba dake nake ba" ta amsa mata don bata taba zaton zancan zucin da takeyi ya fito fili ba.
Itama bata sake tambayarta ba ta maida kanta ga abinda takeyi.
********Dogon tsaki taja tana gallawa wayar ta data dauki ruri a karo na babu adadi harara
"Kinsan fa ni banason irin wannan abun,waye yake kiranki da baki daga ba bare ki kawo masa
uzuri?" Umma dake zaune a gefanta tana cin tuwon dare ta fada
"Isma'il ne umma"
"To ki daga mana?"
"Haba umma,dame zanji don Allah?,da takaicin shegen yaron nan da na aika ya siyomin
indomie yaje ya zauna koda nacin kiran wayarsa?" Side hannunta data gama cin tuwon umma
ta farayi tana cewa
"Duk dai ke kika jawowa kanki,inda tuwonki kikaci da ba yanzu bakinki alaikum ba,ba wanda
yaji bare ya gani"
"Allah ya sawwaqe,tuwon masara aisaidai a bawa gawata" ta fada tana kyabe baki tare da
gyara zamanta tana ci gaba da hada sabbin syrup da supplements din gyaran jiki dana qiba
data siyo jiya. Gefe kuma ga mayukan saka hasken fata suma data yiwa roba guda.
Dai dai nan yaron ya kwado sallama ya shigo hannunsa da baqar leda
"Kaci uwarka surajo,inda kasan dadewa zakayi uban me yasa ka karbarmin aike?"
"Banason lamarin zagin iyaye na gaya miki malama" umma ta fada tana kwada mata harara
"Layine a wajne wallahi da qyar akazo kaina"
"To kinji ma" umman ta fada ta yunqura tana miqewa da kwanonta ta nufi kitchen.
Jakar umma ta jawo ta zuge,daga can umman ta jiyo qarar zuge jakar
"A'ah fa,ni ba zaki talautani a daren nan ba,na baki kudin indomie me kuma kike nema?"
"Pepsi zai siyomin don Allah,sai kuma ashirin din dana masa alqawari,zan biyaki bashi na ansa"
ta fada tana ciro kudin da sauri ta miqawa surajo din tana masa inkiyar yayi sauri ya fita.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 16
*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*
*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*
*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*
*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*
LOGO
INVITATION CARDS
BANK STICKERS
BUSINESS LOGO
SAVE THE DATE
P.O.S BANNERS
BIRTHDAY CARD
BOOK COVER
DATA FLAYER
BIRTHDAY VIDEOS
VIDEO INVITATION
AI PICTURES
_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_
*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON
DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*
*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku
_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN
MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_
https://wa.me/+2347084515410
_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_í ½í±Œí ¼í¿½í ½í±Œí ¼í¿½í ½í±Œí ¼í¿½í ½í±Œí ¼í¿½
_____________________________
Da gudu surajo ya cilla ya fice daga gidan,saboda yasan indai umman ta fito ta karbi
kudinta to ya shiga uku gurin wasila. Hakanan 'yar naira ashirin dinsa shima ta shiga rububi.
Umma na daga kitchen tana mitar halin wasilan na zabe zaben abinci
"To wai umma idan bakiyimin ba waye zaimin?,kuma ai ansan banason tuwon aka tashi akayi
mana,kinga kuwa bazan kwana da yunwa ba". Suna tsaka da wannan taqaddamar Surajon ya
dawo. Tasa hannu ta karba tana cewa
"Surajo me abun arziqi da na tsiya,yanzu dai sai gaka sharp sharp,to ga kudinka" ta miqa masa
ashrin din. Hannu yasa ya karba yana cewa
"Ana sallama ma sake a waje" fuska tadan bata
"Waye?"
"Isma'il ne" ya bata amsa dai dai sanda umma ke fitowa daga kitchen
"Bawan Allah dan albarka,je kace tana zuwa kaji" juyawa yayi ya fice abinsa,yayin da fuskar
wasila ta canza ta jawo ledarta tana budewa. Kallonta umma tayi
"Nayi tsammanin zakije ki fara saurararsa kada abar mutum haka a tsaye?"
"Ni yunwa nakeji wallahi umma,sai naci abinci tukunna,idan bazai iya jira ba ya tafi"
"A'ah,kedai kiyi da jiki ki gama" umman ta fada tana kade gefan tabarmar da suke kai din ta
sanya hijabinta ta tayar da sallar isha'i.
Da gayya ta dinga laqai laqai harta gama,siririn mayafi kawai ta yafa saman doguwar
rigar jikinta tadan sake shafa turare tayi hanyar soron. Haushin isma'il takeji,wannan shige
matan da yakeyi,sai taga kamar yana nesanta ta ne da irin mazan da take sa muradi,yaqi ya
gane yaqiyin zuciya kuma ya barta.
Kansa a qasa yana danne danne a wayarsa,jin takunta ya sanyashi daga kai daga
abinda yakeyi yana dubanta,sai ya saki qaramin murmushi yana fadin
"Barkanki da fitowa ranki ya dade"
"Yauwa,barka" ta fadi kadaran kadaham. Ita kanta tasan isma'il bashi da wata matsala ko
makusa,amma an riga an gaya mata ba shine alkhairi a tattare da ita ba,kuma itama ta gamsu
da hakan,tunda baikai arziqin da takeson mijinta ace yana da shi ba,yadda take da tarin
magauta din nan,tanason ta auri mijin da idan ta shiga gidansa za'a san yes!,ta auri me
arziqi,mijin da first night dinta zai bata kyautar mota,mijin da zata dinga zuwa umra da aikin hajji
har sai ta gaji,mijin da zai dinga sauya mata kalar motocin da zata ji dadin takota ta shigo
unguwarsu tana fankama da hura hanci,ta bule maqiya da mahassada da qura,ana kiran hajiya
wasila tana kyautar sabbin kudi,dukka tasan isma'il bazai iya affording wannan ba,duk kuwa da
tasan ci sha sutura da wirin zama duk ba zata raza ba,don bai rasa komai din ba,hasalima
Lagos yake zuwa yayi sari na shagonsa me yawa. Ya siya fili kuma gini yakeyi me kyau,amma
yace mata idan bai samu kammalawa ba har lokacin aurensu zai kama musu haya kafin ya
kammala daga bisani sai su tare.
Itakam babban abun kunya ne a gareta ace wai yau ita wasila.......wasila guda tana a
gidan haya,me yafi wannan abun kunya?,duk wadanda duka sanya ido suga ya zaka qare suyi
maka dariya suyi shewa son ransu kenan,Allah sitru buqui inji kishiyar me doro.
Shi ya karba daddumar da ta fito da ita ya shimfida sannan suka zauna akai.
Kusan fiye da rabin hirar shi yakeyi,har zuwa wani lokaci da yaga ta fara hamma da
lumshe idanu duk kuwa da cewa duka duka baifi minti arba'in da zuwa ba
"Yadai?" Ya tambayeta cikin kulawa. Fuska ta yatsina ta danja tsaki
"Bacci nakeji,kuma ma dai yunwa ma nakeji,haka kawai umma tayi mana tuwo yau"
"Subhanallahi" ya fada cikin dan gajeran nazari. Bayan dan shuru da ya biyo baya na sakanni
sai kuma yace
"Ai bai kamata ki kwana da yunwa ba seela ta" ya fada yana fiddo wayarsa a aljihu. Bugu biyu
aka daga suka gaisa
"Ina layin nan dake kallon gurinku........eh takeaway nakeso a hadamin me kyau.......yauwa
komai da komao,ya miqo layin sosai sai yazo gaban wani gida me farin fenti ina daga ciki......
alright na gode" daga haka ya cire wayar a kunnensa ya maida aljihunsa
"Ai da ka barshi wallahi" Ta fada kawai don jin baki
"A'ah,ba za'a yi haka ba ai,so kike nima na kasa bacci?" Murmushi ta saki tana jin dadi a ranta
"Yauwa ni da albishir mafa nazo miki,ga yunwa kuma kina ji,anya albishir din nan zai fadu?"
Wata zaquwa ce ta kamata, zuciyarta na hasaso mata waya zai sauya mata