KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  Taskar Novels

Chapter   1 / 24

1 to 3K   out of 69.9K words




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_KURMAN BAK'I_*

*H U G U M A*

PAGE 01


_Akwai saqonni masu tarin yawa a ciki,saidai kuma KURMAN BAQI ne me wuyar fassaruwa,ga
duk me nisan zangon hankali da tunani zai tsinkayi hakan,DAN JAGORA NE ga
mata,musamman masu KISHIYA,kuma hannunka me sanda ne ga masu sana'a data shafi
labarin dake cikin littafin_
*NOTE:qirqirarren labari ne wanda ya dace da matsalolin da mata ke fuskanta a yanzu,komai
dake ciki qirqirarre ne,idan ya dace da zahirin rayuwar wata to arashi aka samu*


Zaune take zaman farar stool din dake ajjiye gaban dressing table din dakin. K'afarta
daya kan daya tana kuma karkadasu da wani irin sauri. Kallo daya tak zaka yiwa fuskarta ka
fahimci akwai zallar bacin rai mai mugun yawa shinfide a saman fuskarta,bacin ran da ko
shakka babu yana yiwa zuciyarta wani irin fusga da kud'a me ciwo.
Hatta da launin idanunta zuwa fuskarta sun sauya,abinda zai alamta maka kuka tasha
bana wasa ba,da alamu kuma ba wani lokaci me tsaho ta dauka da gama kukan ba.

Har cikin zuciyarta takejin wani irin masifa da tashin hankali suna sadakarta. Qoqari take
tayi ta taushi zuciyarta amma kuma kamar hakan yana neman gagararta.

Ita din tana cikin jerin sahun matan da basu iya cinye fushi da bacin rai ba tare da
zukatansu sun furta ko sun furzar da shi ga dukka wanda yayi silar afkwarsu a wannan yanayin
ba.

"Idan ba damuwa don Allah zan dan fita yau din,amma bazan wuce awanni biyu ba zan dawo in
sha Allah" Sautin muryar dake tashi sama sama ya ratso ta cikin windows dinta,ya kuma keta
labulayenta ya isa ga kunnuwanta.

Isar sautin muryar kadai ga kunnuwanta amma sai taji kamar an sakar mata guduma
cikin tsakiyar zuciyarta. Tana da muradin jin amsar da wanda akayi maganar dominsa zai
bayar,wannan ya sanyata miqewa zumbur ta kuma kai ga labulen ta yaye a zafafe.

Fes take iya hango mutum biyun wanda ke magana cikin wata irin nutsuwa a
tsakaninsu. Tsayayyen namiji ne wanda ke tafe da tsaho da kuma qibarsa gaba daya,wanda
hakan ya bashi wani irin kyakkyawan murjajjen jiki da ya qara masa kyau da cikar zatin da kai
tsaye ya isa ya amsa sunan NAMIJI. Duk kuwa da cewa shi din ba wani mugun kyakkyawa
bane,amma sam sam bai hada koda hanya da kalmar MUNI BA. Baqi ne da bahaushe kan kira
da wankan tarwada,wanda yayi wani irin kyau me cike da nutsuwa cikin wani lallausan yadi
ruwan sararin samaniya a jikinsa. Ganinka na farko da shi zaka tabbatar da cewa shi din
gwanine wajen iya murza hula da sanya sutura ta zauna a jikinsa,hakanan telansa ya qware
qwarai da gaske gurin baiwa dinki haqqinsa,dukka wadannan abubuwa suna da cikin abubuwan
da suka hadu suka qarawa SALEEM kwarjini da cikae kamala da kuma siffa.

Matar dake a gefansa kuwa duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da takwas
ba,idan tayi nisa da yawa ashirin da Tara zuwa talatin. Ita dinma baqa ce kamarsa,saidai nata
baqin har yafi nashi gogewa,chocolate color ce sosai,mai matsakaicin tsaho,ba gajeriya
bace,saidai kuma bata kai tsahonsa ba sam sam. Tana da manyan idanu masu matsaikatan
girma,hakanan hancinta yana da tsaho da tudu. Komai nata matsakaici ne,itama tana da wani
kyau na daban,wanda baiyi yawa ba.

"Ina zuwa kenan?" Ya tambayeta yana duban fuskarta da murmushi ya subuce mata

"Gidan aunty khadija mana" kai ya jinjina yana murmushi

"A dawo lafiya Allah ya tsare" ya fada yana same fadada murmushinsa. Qaramar dariya ce ta
qwace mata

"Da sauri haka?,saboda kaji gidan aunty deeja ne?" Ido ya fiddo yana sakin wani murmushin

"Ta yaya zan hanaki zuwa nan?,ai nasan ta samu ne" ya fadi qasa qasa. Siririyar dariyar da ta
ajjiyeta musamman saboda shi ta saki,cikin salon nuna jin kunya tace

"Ni bance ba,amma dai sirri ne"

"I know,bance sai naji ba nima,Karki jima please" ya fada cikin tausasawa yana takawa zuwa
muhallin ajiyar mota na gidan dake dauke da motoci gida uku kamar yadda iya adadin abinda
zai iya dauka din kenan

"Nasan ba ka son yin dare a waje daddynsu,ba zan kuma saba ba in sha Allah" dakatawa yayi
da tafiyar ya waiwayo yana dubanta. Wani murmushi ne saman fuskarsa wanda ya sani bai isa
ya hanashi fita daga fuskar tasa ba. Tattausan murmushin itama ta saki sannan tadan rausaya
kanta cikin alamun jin nauyin kallon da yake matan. Tamkar an saya hannu an finciko zuciyarta
daga qirjinta haka ZAINAB taji. Taji na zata iya qara koda second daya a tsaye tana kallon
wannan abun ba. Sai ta saki labulen da sauri ta kuma juya da sassarfa tana rufar qofa zuciyarta

na sake soyewa da wani irin zafi da radadi.

Ya za'a yi mutumin da tun daren jiya ta rasa ganin walwala koda qanqani saman
fuskarsa?,hatta da abincin darensa ma bai samu ci ba,ya kuma gaya mata baijin dadi ne a haka
suka kwana amma shine yake rausaya da idanu da wani irin shu'umin kallo irin haka?. Bayan
ko yau da safe a tsaitsaye ya shirya,ko fuskantarta suyi magana ya kasa yi,sai baya da ya juya
mata,ya gama shirinsa a gaggauce ya fice?. Ta dauka ya jima da barin gidan ma,ashe yana tare
da wannan makirar baqar matar tasa.

"Allah ya bada sa'a,ya tsare mana kai,ya baka ikon nemo halak ka ciyar damu da ita,a dawo
lafiya" idanunsa ya lumshe kadan,addu'arta tana masa tasiri har tsakiyar zuciyarsa. Wanann
addu'ar na cikin jerin abubuwan dake faranta zuciyarsa duk safiya,ta kuma yi masa rakiya har
zuwa shagonsa na kasuwa.
Da fara'ar shimfide akan fuskarsa ya bude idanunsa yana motsa labbansa. Sai idanun
nasa suka sauka akan zainab wadda ke tsaye tana numfarfashi nata idanun itama a kansa.
Janye dubansa yayi daga kanta ya mayar ga RUQAYYA yana cewa

"Ameen ameen,na gode qwarai,Allah yayi albarka"

"Ameen" ta amsa masa tana shafa tafukan hannuwanta dukka biyun saman fuskarta,sannan
tayi taku biyu taja baya daga kusa da zainab din,ba tare data dubeta ba saboda sanin cewa ko
meye zata gani saman fuska da idanunta ba alkhairi bane,sai ta saka kai cikin gidan tana
zarcewa sashenta.
"Har ka warke kenan?" Zainab ta jefa masa tambayar kai tsaye tana ci gaba da dubansa,
tambayar da tazo da salo ma titsiye da kuma son qure mutum

"Dama ai ba ciwo nakeyi ba,nace dai miki bana jin dadi ne kawai,kuma kowa yana tsintar kansa
a irin wannan yanayin"Ya fada yana janye dubansa daga kanta,baqinciki na lasar zuciyarsa. Ita
sam kwata kwata ma kamar bata kishin kanta?,bata taba damuwa da ta sauya wasu abubuwa
ba ko don ruqayya. Ruqayya din bata taba zamar mata abar kwatance ba,tafi bawa abu guda
daya muhimmanci,sannan wannan abu dayan tafi bashi himma kima da darajar data zarce ace
an bashi din.

"Kaji dai tsoron Allah kada ranar qiyama ka tashi da shanyayyen barin jiki wallahi.....koda yake
ba laifinka bane,kaci ka sha,duk da shima asirin ai yana tadda hali ne" ta fada a zafafe sannan
ta juya abinta tana komawa cikin gidan da sauri saurinta.

Bai dakata da kallonta ba har ta bacewa ganinsa,ya sauke numfashi mai nauyi ya zura
key yana qoqarin bude motarsa yana girgiza kai hadi da jan wani qaramin tsaki. Ba abinda ke
yawo a idanunsa sai rigar baccin jikinta wadda duk dalli dallin maiqo ne a jikinta,abinka da abu
silk jirwaye da maiqo bashi da wuyar nunawa a tattare dashi. Iya tsaiwarta a wajen,qamshin

jikin ruqayya ya baje ya koma inda ya fito,ba komai a wajen sai wani yanayi dake nuni da lokaci
yayi da gangar jikin mutum ta fara buqatuwa zuwa ga wanka,wankan da yayi imanin koda za'a
yishi to saifa idan ya dawo ko kuma yana dab da dawowa idan an tafka sa'a a ranar.

Zuciyarsa cike da qiyasce qiyasce da juya al'amuran zainab ya tashi motarsa sannan
ya sulale ya fice a gidan yana son daidaita nutsuwarsa kota halin qaqa.

A nutse ta tura qofar parlor din nata da bata gama rufewa ba saboda tana sauri ta
cimmasa ta gaya masa zata fita din a yau. Ko ina a gyare yake tsaf a killace,sai ka rantse bata
da yaro ko guda ko kuma amarya ce,saboda sassanyan qamshin turaren wuta da burner din
dake kunne take bayarwa. Gurin burner din ta isa ta kasheta,ta gama bata qamshin da takeso
ta kuma biya mata buqatarta. Sassanyan qamshin da tasan saleem din yafiso a ko yaushe bata
taba yarda ta rabu dashi,bata damu ba da ranar girkinta ne ko ba ita ke da girki ba,itadai burinta
a ko yaushe wannan qamshin ya zamana shine abu na qarshe da ya shaqa dag wajenta don ya
zama abokin tayashi tunata tsahon yinin da zaiyi gurin neman halal dinsa.

A nutse ta buda daya daga cikin qofofin dake parlor din. Madaidaicin dakin yara ne me
dauke da qananun gadaje guda uku,cikin dayan gadon yarinya ce ke kwance tana bacci. Sai
data leqata ta tabbatar babu wata matsala sanann ta dawo a nutse ta rufe qofar,ta isa ga
madaidaicin dining dinta me kujera hudu tana tattare plates din da ta gama breakfast. Yau duka
tayi abincin karin tare da yara ta diba nata saboda tanason fita din,batason tsaiwa hada wani
lokaci ya qurace mata.

Tsaf ta gama hada plates din da cups din,zata debe ta wuce kitchen taji an banko qofar
babu zato ba tsammani,abinda ya sanyata waiwayowa da sauri tana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakil,waye haka?"

Kanta tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba ta ratso cikin falon tana kallon ruqayya. Kallo
na tsantsar qiyayya da tsana muraran. A kaf fadin duniya batajin akwai wata halitta da zuciyarta
ta tsana bayan ita. Idanunta ta kuma saukewa akan plates da cups din dake riqe a hannun
ruqayya,wannan ya sake bata tabbacin eh lallai,bayan ya tsallake breakfast din data shirya
masa a nan yazo yayi karin kumallo?.

Ta hadiye wani abu me tauri da ya tsaye mata a wuya me mugun radadi,sannan ta
watsawa ruqayya wani mummunan kallo.

"Nice nan,zuwa nayi na gaya miki abinda kika kasa ganewa,tunda baki da tsoron Allahn da zai
ganar dake hakan,inason ki sani ke din baki isa komai ba kamar yadda baki isa ki rabani da
saleem ba,duk yadda kike ganin bokanki tsafinki da tsubbace tsubbancenki sunayin
tasiri,wallahi baki isa ki raba alaqar da Allaj ya hada ba,kuma a juri zuwa rafi da tulu da diban
ruwa,dole wataran zai fashe" tana kaiwa nan ta juya a zafafe tana jin inama zai yiwu ta rufe
ruqayyan da mummunan dukan da zai sanya a rasa gane ainihin halitattarta. Duk kuwa da tayi

imanin babu wani kyau dake rudar saleem tattare da ruqayyan,face zallar tsafi da tsubbace
tsubbace,tunda dai indai ana batu na kyan fuska da hasken farar fata,ko kusa ko alama ruqayya
bata isa ta matso koda gefanta ba,wannan abun shi yake sake bata tabbaci a ko yaushe iyawa
da gogewa a bun malamai da 'yan bori suke sanyawa ruqayyan ke shan gabanta a zuciyar
saleem,wanda dukkan me dogon nazari da tsinkaye koda ba'a gaya masa hakan ba shi da
kansa zai fahimta.

Kasa ce mata komai ruqayya tayi face binta da kallo data ci gaba da yi har ta bacewa
ganinta. Taja numfashi sosai sannan kuma ta sauke tana rausayar da kai. Koda sau daya bata
taba tsaiwa ta biyewa shirmen zainab ba,amma a yau abun yayi ta'azzarar da har ta samu
qwarin gwiwar shigo mata sashe?.
Karamin tsaki taja ganin qananun tunane tunanen matsalolin Zainab da basu taba
qarewa cikin gidan ba suna neman bata mata lokaci,saita juya zuwa kitchen zuciyarta na sake
fadada da tunani da mamakin halayen Zainab din. Me yasa har yanzu IDON ZUCIYARTA ya
kasa budewa?,ta gaza fahimtar abinda ke gabanta a bayyane?.
Da irin wadannan tunane tunanen ta kammala dauraye plates da cups din da wanke
kowanne kwano da aka bata da abinci ya zame mata jiki a duk sanda aka gama cin abincin,ta
goge ko ina da kitchen towel ta sakayo qofar.

Tsaftataccen killataccen bedroom dinta ta buda ta shiga,ta kalli agogo,sai ta bude
wardrobe dinta ta ciro mayafinta daya dace da da A shape din atamfar dake jikinta a dan
gaggauce ganin lokaci ya fara ja,tanason taje ta dawo da wuri kafin yaran su dawo daga
makaranta,don ta dade da yiwa kanta alwashin muddin ba wani babban uzuri ba ta daina barwa
zainab su saboda wani dalili.

Ta dakin yaran ta biya ta dauki baby fatima dake barci ta sakata a kafada sannan ta
maida lallausan mini blanket din yariyar ya lullubeta ta fito.



*FREE BOOK NE,KU SAKI JIKI KUSHA KARATU*😂😂🙌🏼🙌🏼🙌🏼

*_FOLLOW MY AREWABOOKS ACCOUNT_*

*HUGUMA*👑
*_KURMAN BAƘI_*

*H U G U M A*

PAGE 02

Muhallin da ta tashi dazun a dakin shi ta koma ta zauna,har yanzu babu wani sassauci
data samu ko qanqani,duk da cewa daga ruqayya har saleem ta barwa kowa a cikinsu saqo.
Sam bata damu da tarin qazantar dake a sashen nata ba bare hankalinta ya dauku wajen ganin
ta tsaftace shi,duk kuwa da cewa rana ta fara yi,kuma lokaci ne da ya kamata ace gurin ya
kasance cikin kintsi da gyara. Ba abinda yafi damunta irin uban kudadenta data kashe,ta siya
magunguna masu tarin yawa na mata,magungunan da aka bata tabbacin sunansu KAFI
MALLAKA. Kuma muddin tayi amfani dasu ba saleem ba,duk wani wanda yake rayuwa da
saleem ma zaya zama qarqashinta ikonta da zabinta ne. Sai gashi gaba daya daga kudin har
maganin babu abinda ta amfana dashi,maganin da yake na kwana biyu ne,tayi asarar dare
daya,saura dare daya ya rage mata,wanda bata da wani hope a kanshi,saboda bahaushe ma
ya fadi juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Irin rabuwar da sukayi da saleem a
yau bata tunanin zai nema wani abu daga wajenta a daren yau din,ita kuma batajin koda zatayi
asarar kudin data zuba zata iya saukar da kanta ta nemeshi,muddin ba shine akayi katari ya
saukar da kanshi ba. Koda bai bata haquri ba tana iya sallamawa,saboda kaf kudaden da ya
basu ne saboda siyayyar sallah tasu data yara ta narka a ciki cike da yaqini da imanin zata
maida mafiyinsu muddin tayi amfani da maganin.

Kamar wadda aka tsunkula ta miqe da sauri,ta sanya hannu tana jawo locker din
madubinta. Tarin ledoji ne da tarkacen da zakayi tsammanin qaramar bolar mahaukata ce dake
cunkushe da karikice,wasu a leda,wasu a kwalaye,wasu a takarda,wasu ma saboda rashin
gyara da kintsin gurin sun fashe sun barbade a cikin locker din.
Da kallo tabi locker wani takaici yana sake ninkuwa a zuciyarta

"Wai dame na gaza da har yau na kasa ture wannan baqar matar tasa?,dame ruqayya ta fini
ne?" Ta tambayi kanta tana qarewa locker din kallo,tako ina bata wasa da gyaran HQ dinta,duk
wami magani da zata gani ana tallatawa,ko taji labarin kyan ingancinsa da aikinsa a gurin
qawaye saita tabbatar ta mallakeshi hankalinta yake kwanciya,amma har yanzu ta gaza samun
nasarar da take hangowa kanta.

Hannu ta saka ta dauko baqar ledar dake ajjiye daga gefe tana jan tsaki,kunceta tayi
saman madubi,wasu qullukan garurruka ne da dunqulallun wasu abubuwa guda hudu. Daya
brown daya baqi daya fari tas dayan kuma kore. Tsaki ta sake ja

"Fiye da rabin ma da akace nayi inserting nasu ashe nayi,banajin wadan nan ragowar zasu
samar min da abinda nakeso" ta qarashe maganar tana maida ledar ta qulle. Gwara ta samo
wani abun da zai cikashe mata gibin da zata samu.

Saman hautsinannen gadonta ta miqa hannunta,ta cusa shi qasan pillow dinta ta ciro
wayarta. Kai tsaye data dinta ta kunna,sannan ta hau watsapp dinta.

Tarin saqwanni ne suka shiga shigowa,duk da jiyan raba dare tayi tana chart kafin ta

rufe tabi saleem din bedroom dinsa.

Fitsarin da ya cika mata mara ya sanyata ajjiye wayar a gefan gadonta,sannan ta miqe
da sauri ta tura qofar toilet dinta ta shige.

1 / 24