Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
da Uwais zazzafar soyayya yake yi
wa Amrah ta yadda rayuwarsa ba za ta taba cika babu Amrah ba.
A can gidan Ammi yau ne wuni, don haka duk abokan arzikin Ammi sun zo, ciki har da Hajiya
Asabe shugabar gidan marayu. Hajiya Asabe ta kwance jakarta ta soma fiddo 'yan kulle-kullen
da ta zo da su tana yi wa Ammi bayani, kasancewar 'yar Sokoto ce ita, ta ce ita ga
gudunmawarta kenan kayan gyaran amarya. Ammi ta karba ne kawai ta yi godiya, amma ta
saka a ranta ba za ta bai wa Fahima komai ta ci ba. Matar da hankalin mijin ba ya kanta
sam-sam za'a bai wa maganin mata ya sa ta ciwon mara a banza.
Fahimah ba ta san ta zama matar Uwais ba, da halin da ta samu kanta a ciki yau, da jin cewa
bikin Uwais ake yi da ba ta shige shi ba.
Daga ita sai ubangijinta suka san cewa tana gab da zarewa. Wani dan karamin zaucewa ne ya
same ta a daki sai safa da marwa ta ke a cikin dakinta tana magana ita kadai.
"Yaya Uwais ya yi aure, zai tafi ya barmu... Matarsa mai sa'a ce... Ni ba ni da sa'a... Sai koshin
wahala. In ya tafi gidansa shi ke nan na daina ganinsa... Ganinsa kawai is a blessing because it
heals... Allah ka ba ni juriya, Allah ka ba ni dangana. Allah ka fahimtar da zuciyata ta daina son
abin da ba za ta taba samu ba...". Sai ji ta yi ana bubbuga mata kofa da karfi. Muryar Ammi ce ke kiran sunanta, "Fahimah!
Fahimah! Fito ku yi sallama da su Kawu Shuraim za su tashi yanzu zuwa Sudan".
Ta soma kokarin regaining consciousness dinta don tabbas Ammi ta ganta a wannan halin ba
abin da zai hana ta gano ta... Ta zama zararriya a kan dan ta Uwais, kishinsa na neman hallaka
ta.
Toilet ta fada da gudu ta wanke fuskarta da sabulu ta sanya hijab sannan ta fito, ta bi bayan
Ammi zuwa falo. Duka kawunnin Uwais suka bi ta da kallo har ta samu gefen Ammi ta zauna.
Ta gaishe su, muryarta ba ta fita sosai sabida kukan da ta ci. Baffa Haruna ya hau yi mata
nasihar da ba ta san dalilinta ba, yana fadin ta zauna lafiya da abokiyar zamanta su ba wa
mijinsu hadin kan da zai iya adalci a tsakaninsu. Ta dauki kishiyarta 'yar uwa ba kishiya ba, ta
rike girmanta da Allah ya ba ta.
Fahimah dai ba ta dago ba har zuwa lokacin da Kawu Shuraim ya ce, "Ki yi hakuri da dan
uwanki Uwais, kin san ba da son ransa aka yi aurenku ba. Wannan burin na mahaifiyarsa ne,
don haka tabbas sai kin yi hakuri Fahimah a zamanki tare da Uwais. Don Uwais wani
baudadden mutum ne wanda idan aka yi gabas shi sai ya yi yamma, in aka yi kudu shi sai ya yi
arewa. Hakurin shi ne kadai maslaha har zuwa sanda Allah zai daidaita ku, don haka ba za mu
gaji da cewa ki yi hakuri ba kin ji ko Fahimah?"
A hankali Fahimah ta dago rinannun idanunta ta sauke a kan Ammi Safeeyyah. So ta ke ta
tantance ma'anar kalaman da ke fita daga bakunan kawunnan Uwais, shin ko idanun Ammi za
su ba ta assurance na abin da dattijan nan ke cewa? A zahiri cikinsu babu sa'anta, babu abokin
wasanta balle ta yi zaton wasa ne irin na kaka da jika suke yi mata. Ammi ta gyada mata kai a hankali tana murmushi da ba ta tabbaci daga fararen kwayan
idanunta.
"Uwargidan Uwais!".
In ji Ammi tana mai sanya tattausan hannunta cikin na Fahimah.
"Allah ya ba ku zaman lafiya. Da zuri'a mai albarka. Allah ya kade fitina da dukkan abun ki".
Fahima sai ta samu kanta cikin wani hali na 'fita hayyaci' na wucin gadi. Ta nemi jinta da
ganinta na 'yan dakikai ta rasa. Don haka har su Baffa suka yi sallama da Ammi suka fita
Fahimah ba ta koma cikin hayyacinta ba. Watakila dai mafarki ta ke yi... Irin mafarkin da dan
Adam ke yi idan ya cika sanya tunanin abu a ransa. Mafarkin kasancewa matar Uwais ai ba yau
ta fara ba. Don haka na yau din ma in ta yi hakuri za ta farka ne kada ta yaudari kanta.
Har sai da Ammi ta raka su Baffa ta dawo Fahimah na nan kafe a inda Ammi ta barta, rokon
Allah ta ke yi a zuci ya yi gaggawar farkar da ita daga wannan rudadden mafarki. Ammi na
shigowa ta kama hannunta ta cira ta tsaye suka nufi dakin barcinta.
A gefen gadonta ta zaunar da Fahima wadda zuwa yanzu ta fara ji a jikinta yau ba mafarki ta ke
ba, wani babban alamari ke shirin faruwa da ita, wanda ba za ta ce alkhairi ba ne. Idan
kalamansu gaskiya ne sun aura mata Uwais shin hakan zai haifar da Da mai ido a gare ta?
Wanda ba ya sonka fa bai sonka har abada, kuma ba zai taba sonka ba balle an hada auren da
na matar da yake so, ai kawai in hakan ya tabbata ta amince kawai karshen Fahimah ya zo (the
end of FAHIMAH).
Don dai ta san Uwais ba zai barta da rai da numfashi ba, ba zai barta ta shaki numfashi a
matsayin matarsa ba, balle su hada inuwa daya, inuwar ma wadda ta fi kowacce alfarma wato
inuwar aure.
Maimakon farin ciki duk da mayataccen son da zuciyar Fahimah ke yi wa Uwais, ji ta yi wani irin
tsoro da firgici ya mamaye ta, kada Allah ya nuna mata ranar da za ta kara haduwa da Yaya
Uwais ko da a hanya ne. Kamar yadda suka ce burin na Ammi ne, ta yadda Ammi za ta yi mata
kauna fin haka. Ji ta yi hawaye sun jika fuskarta sharkaf ba tare da ta ankara ba, Ammi gorar
ruwa ta dauko a firji mai sanyi ta zubo a tambulan ta mika wa Fahimah, ganin yadda ta ke
yanka gumi daga zaune kamar wadda ke dakin nakuda duk da rabar iyakwandishan da ta
lullube dakin Ammin.
Kusa da ita Ammi ta zauna, ta ce, kuka Fahimah? Ki yi hakuri in na miki ba daidai ba, ban iya
rabuwa da ke Fahimah zuwa gidan wani, bansan irin kalubalen da zaki fuskanta ba, haka ba
zan iya jurar ki wulakanta a gidan aure ba, a dalilin haka ne na yanke shawarar aura wa Uwais
ke ba tare da neman shawara ko amincewar kowannenku ba don na san ba za ku taba
amincewa ba bisa karan-kanku. Amma Allah shi ne shaidata kan cewa ALHERI nake nufinku da shi, ba za ku gane hakan ba ku
duka sai ranar da bana raye. A yanzu dai ba hadin kanku nake nema ba don abin da nake
nema na same shi, burina ya cika. Fahimah kin dauwama cikin zuriata. Dukkanku kuna bukatar
lokaci kafin ku tantance aya da tsakuwa, ki kwantar da hankalinki in dai a kan Uwais ne ba zan
kai ki gidansa ba sai bisa amincewar zukatanku ku duka.
Ki je ki hada kayanki na sati biyu, gobe insha Allah in an kai masa amaryarsa ni da ke za mu
tashi zuwa umrah, ba za mu dawo ba sai bayan sati biyu.
Jiki a mace Fahimah ta mike amma ta kasa ce da Ammi komai.
Idan na yi miki ba daidai ba, idan hukunci na bai miki daidai ba ki yi hakuri ki yafe min Fahimah.
Da sauri Fahimah ta juyo, tausayin Ammi wadda tsufa ya soma bayyana a gare ta duk sai ya
kamata. Cikin rishin kuka ta ce,
Ammi, ba ki yi min komai ba. Sannan ta sa kai zuwa dakinta.
Burinta a rayuwa komai ya girmansa a yau ya cika. Mafarkanta sun zamo gaskiya, ta zamo wani
bangare na Uwais Shagari, amma abin mamaki ta kasa farin ciki da hakan, watakila don girman
kalubalen da ta ke hangowa ne, watakila kuma don ta san auren ba zabin Uwais ba ne, in ma
ya sani ke nan. Jin kanta ta ke tamkar wadda ta rako dukkan mata duniya sabida rashin saarta
a rayuwa. Gabadaya maganar auren da auren kansa ba ta san a ajin da ya dace ta sanya su
ba.
Da me za ta ji ne a rayuwarta? Maraici, rashin asali and finally BORANCI?
Kodayake Ammi ta ce ba kai ta gidan Uwais za ta yi ba, sai ranar da dukkansu suka amincewa
hakan. Ranar da ta tabbata ba mai zuwa ba ce, sai dai ta dauwama da sunan matar Uwais,
amma auren ba zai taba zama reality ba.
Yadda Fahimah ta ga rana haka ta ga dare a wannan ranar, kitsawa ta ke tana tufkewa sannan
ta warware. Ta rasa makomar rayuwarta. A karshe ta sa a ranta cewa, ya kamata ta yarda
cewa, duk bakinta da Uwais ke fadi yana gorantawa ita ma mace ce kamar sauran mata, wadda
wani namijin bayan Uwais zai iya gani ya ce yana so ya biya sadaki ya dauka ya kai gidansa. In
haka ne kenan ya kamata ta martaba kanta....Ta daina kallon kanta wulakantacciya. Ba kuma ta
kowacce hanya ba face ta yin gefe da UWAIS daga zuciyarta, shi da duk abin da ya shafe shi.
Ta maida komai nasa a bakomai ba, ta maida hankali kadai ga karatun da Ammi ke so ta yi, ta
gina wa kanta future yadda duk ranar da babu Ammi za ta tsaya da kafafunta.
Ta dauki aurenta da Uwais a matsayin shifcin gizo in ba haka ba ita ce a wahale. Ta tsaya ta
nema wa kanta madafa ga rayuwarta ta gaba, wanda ba komai ba ne san yin ilmi da zai ba ta
martabar da kyawun halitta ba ya badawa. Kyawun halittar da ta fi tunanin a kansa ne Uwais bai
sonta. "Goddam Black" kamar yadda yake cewa tana alfahari da bakin fatarta. Ammi ta sha gaya mata Black is beauty a duk lokacin da Yaya Uwais ya ce mata Black, kuma
babu mummuna sam a yaya mata sai wadda ba ta martaba kanta ba.
Da kyar barci ya sace fahimah a wannan daren cike da tunanin da ta kwanta da shi.
******
Washegari Ammi da Fahimah suka tashi Umrah zuwa kasa mai tsarki. Ammi ta yi haka ne don
ta nesanta Fahimah da Uwais na dan lokaci, ya kuma samu lokaci da matar sonsa yadda ya
kamata.
Duk adduar Ammi a Harami da Masjid Nabawy a kan Uwais da Fahimah ne, ita kadai ta san
adadin abubuwan alkhairin da ta ke roka musu.
A can Kano, ango da amarya suna ta barzar amarci babu kama hannun yaro. Uwais ya matukar
jin dadin tafiyar Ammi da Fahimah, don ba ya so ko da kuskure a samu wanda zai gaya wa
Amrah yana da wata matar bayan ita.
Alhaji Umar Dikko ya zuba dukiya a gidan Amrah kamar bai san zafin nema ba. Gidansu komai
ya yi acan-acan, soyayya ruwan zuma gangariya tsakanin Uwais da Amrah ba su taba gundura
da juna.
Kafin Ammi da Fahimah su dawo Saudiyyah ango da amarya har wata yar kiba suka hada a
kumatunansu sabida kwanciyar hankali da samun contentment in life.
Ranar asabar da daddare suka sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Fahimah ta yi wa
kanta sayayya sosai, haka ta yi wa Talatu tsaraba. Ba yadda Ammi ba ta yi da ita ba a kan ta yi
wa Uwais tsaraba ko ta carbi ne, Fahimah ta ki. Yadda ta yi fatali da Uwais daga zuciyarta haka
ta ke fatan ta manta da ko sunansa.
Dan halak din shi ya zo daukarsu zuwa gida, ya sha excelcior fara kal, sai walainiya ya ke. Da
ganin shi ka ga angon daje kan ganiyar sa. Motarshi kamar a nan ne kamfanin Maison Francis
yake. Ga wani farin gilashin PRADA da ya manna ma dogon karan hancinsa. Kallo daya da
Fahimah ta yi masa ba ta kara maimaitawa ba, duk da kuwa cewa zuciyarta ta yi mugun
raurawa. Sakamakon wata irin ilhama da kamala da aure ya kara wa Uwais, gara ita ta kalle shi
sau daya, shi ko sau dayan bai kalle ta ba. Sai da ya mallaki Amrah ya kara gane babu wata
sauran diya mace da za ta kara burge shi a duniya.
Babban tashin hankalinsa a kwanakin nan shi ne in ya tuna Amrah tafiya za ta yi ta barshi shi
kadai a gidansu, aikinsa kuma ba irin na yawo ba ne duk lokacin da aka ga dama. Ya soma da
ya sanin alkawarinsa na barin Amrah ta ci gaba da karatu a jamiar Limkokwing, sai dai ya san
bai isa ba, ya yi kadan, yayi tsararo ya daga wannan alkawarin daga muhallinsa. Amrah ta sangarta shi da abubuwa da yawa a sati uku kacal, ga iya girki, ga tsafta ga
shagwaba sannan uwa-uba ta iya bi da shi a shimfida. Duk da karancin shekarunta.
Suna tafe a kan hanyarsu ta zuwa gida daga airport tsakanin shi da Ammi kawai suke hira a
motar, Fahimah tamkar ba ta gurin a motar, amma har cikin bargonta ta ke jin tasirin muryar
Uwais har tsigar jikinta na tashi, suna isowa gida ko gama parking motar bai yi ba ta bude
murfin motar ta yi cikin gida. Ta gilashin motarsa ya saci kallonta, sanye ta ke da jallabiya kirar Oman ruwan toka da
mayafinsu. Kayan sun karbi choculate colour din jikinta sosai. Sannan ta yi dan haske irin na
kamawar wanka a jikin mace mai tsafta.
Uwais ya dauke kai daga dubanta yana sakin tsaki a ransa. Mace sai fadin ran tsiya kamar
diyar qaruna, nan kuwa diyar kwalin taliyar indomie ce.
Maigadi ya sauke akwatunansu zuwa ckin gida. Da gudu Talatu ta fito tana "oyoyo uwar
dakina", ta rungume Fahima wadda ke ta murmushi don ita ba ta kyalkyala dariya sam,
murmushi kawai ta ke wanda ke maida ita kamar furen fulawa idan ta yi shi sabida bakin
dadashin cikin bakinta da ke bayyana a duk lokacin da ta yi murmushi. Da taimakon Talatu suka
kimtsa duk kayan da suka dawo da su a muhallinsu bayan Fahimah ta ware mata tsarabarta.
Fahimah ba ta san cewa Uwais ya gaya wa Ammi washegari zai kawo Amrah ta yi mata barka
da zuwa ba. Gajiyar tafiya ya sa ta koma barci bayan sallar asubah, ba ta fito ba sai karfe goma
na safe, ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando pakistan ruwan dorawa, ta kame
kakkarfan gashin ta da ribbon kanta babu kallabi, tana tsaye jikin dining tana decorating wurin
da kayan kawata dining area da ta sayo daga Saudiyyah ta ji sallamar mace.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: A hanyarsu ta dawowa Uwais tuki kawai yake ba ya ko
kwakkwaran motsi har suka iso gida. Yana yin parking Fahimah ta fice, har tana tuntube saura
kadan ta fadi, Uwais ya bita da kallon takaici, dakinta ta shige ta murza key. Ta jingina bayan ta
a jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Me ke shirin faruwa ne da rayuwar ta a yau? Ammi na son actualizing wannan auren a
lokacin da daga ita har shi Uwais din ba su shirya ba.
A baya ta ce ne sai lokacin da suka shirya karbar juna a matsayin ma'aurata don kansu.
Abinda su duka biyun suka tabbatar ba mai yiwuwa bane. Amma yau kwatsam! Ta shammaci
kowannen su a lokacin da suka riga suka sakankance cewa auren na su ba mai tabbata bane
sannan ba zai je ko nan da can ba. Yau Ammi ta dauko wata gagarumar rigima wadda baza'a ce rikicin tsufa yayi dalilin ta
ba. Don kuwa bata yi tsufan da zata ce ta manta waye UWAIS ba? Kuma kuma yaya matsayin
ita Fahimah yake a gare shi?
Ta riga ta gama sakankancewa cewa auren ta da Uwais suna ne kawai, sannan a suna
zai kare. Daga ranar da aka daura shi zuwa ranar da zai gaji da ajiyar sa ya bata takardar saki.
Yau ina zata tsoma rayuwar ta idan ta bi Uwais zuwa inda bata san kowa ba? A gaban Ammi
ma ya ta kare da shi balle a bayan idon ta, karkashin mulkin sa da ikon sa?
Kawai sai ta ji hawaye na zubo mata. Hawayen ba na komai ba ne na tausayin kanta ne. Namiji
sai ana rarrashin sa ana kalallamar sa ana nusar da shi a kan ya so ta! Don kawai bata da iyaye
kamar kowa! Ko da ya ke watakila Uwais na kin ta sabida kalar fatar ta ne idan ta yi la'akari da
irin kalaman da ke fita daga bakin sa akan ta duk lokacin da ya bushi iskar izzar sa. Ita wace irin
mara saâa ce a cikin mata? Kuma wace irin kaddara ke bibiyar ta? Daga maraici da rashin
asali.... yanzu kuma zuwa BORANCI!
A wannan lokacin wani irin determination (kudiri) ya kutso ya shigi zuciyar Fahimah Shagari....
Determination na self-defence and self-actualization; abin nufi ta tsaya ta san hakikanin kanta,
ta kuma kare kanta daga farmakin zuciyarta akan Uwais; kada ta bari soyayyar Uwais dake
dankare a zuciyarta ta kassara ta, ta zamo barrier ga farin-cikin ta da cigaban rayuwar ta, ta
zubar da kimarta ta diya mace mai daraja a dalilin soyayya.
Zata yi kokari iyakar yin ta, ta ga cewa ko ta ina aka je aka dawo ta baiwa Yaya Uwais mamaki
sabani ga tunanin sa; she is not begging for his love. Hakannan komai nasa yanzu ya koma ba
komai ba a idanunta (ya daina burgeta). Sannan