Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
duk yadda ta kai da son sa a baya, daga
lokacin da aka sanar da ita an yi musu aure duk wani infatuation sai da ya kama gaban sa. Su
ci gaba da zama a yadda suke a duk inda za su je ba damuwar ta ba ne matukar zata rike
determination dinnan nata. Uwais ya rike duk abinda yake takama da shi itama daga yau ta koyi
sarrafa kanta akan sa. Abinda Ammi ke fatan ya kasance insha Allah ba zai kasance ba,
karewa ma ita yau ta fara period kuma sai ta yi kusan kwana hudu yake daukewa. Kuma an ce
tafiyar ta kwanaki uku ce.
Tunanin hakan da ta yi ya sa ta jin wani irin relief a zuciyarta. Ta bar bakin kofar zuwa toilet ta
sakar wa kanta shower mai dumi kamar yadda ake a alâadarta kullum kafin ta kwanta barci.
A duk lokacin da tayi hakan zata yi barci mai dadi ne har da saleba.
To yau ma hakan. Domin kwata-kwata ta cire damuwar tafiyar daga ran ta. Sai sake-sake da
kintace-kintacen abinda zai faru.
Bayan sallahr asubah ta sake wanka ta shirya cikin koriyar atamparta vlisco, ba ta san
takamai-mai karfe nawa za su tafi ba, don haka ta kishingide a kan gado da zummar kafin cikar
karfe takwas na safe ta sake bincikawa in ma tafiya yayi ya barta ta sani, tayi abinda ke
gabanta. Ai kuwa barci mai nauyi ya sadado ya yi awon gaba da ita. Don jiya tunani da sake-saken
yadda tafiyar ta da Uwais zata kasance kadai bai barta ta yi barci yadda ya kamata ba.
Can! Cikin barcinta ta ji ana buga mata kofa da dan karfi, kamar za'a jijjigeta. âWho is this?"
Fahimah Ta tambaya cikin mamaki da mutstsike ido.
Shiru ba amsa, tamkar da dutse take magana, nan jikin ta ya bata ko waye, saukowa ta yi daga
gadon ta bude kofar don ganin wanda ke mata wannan bugun kamar ana binta bashi.
Uwais ta gani harde da hannuwa a kirji sai huci yake kamar mesa, ya hade cikin jamfa da
wando na wani tattausan voyel sky blue, as usual hular kansa ta nitse cikin tsakiyar sumar
kansa. Wani kallo ya yi mata kamar fararen kwayar idanunsa za su fado don harara, sannan ya
nuna mata agogon hannunsa. âAre you awareâ? an lika min ke kuma zaki bata min lokaci ki ka shige daki kina ta barci?
Me za mu ci kafin mu bar gida ko ni ki ke jira in je in girka miki?â?
Fahimah ta tsuke baki, sannan ta murguda shi gefe ta rabe ta gefensa ta wuce zuwa kitchen ba
tare da ta tanka masa ba. Ya saki baki yana kallonta da madaukakin mamaki har ta shige
kitchen, shi ta ke murguda wa baki?
Girgiza kai ya yi ya bi ta kitchen din. Cikin hargagi yace.
âYou Goddam Black, 15 minutes na baki ki sama min abin da zan ci, bana hawa jirgi ban ci
komai ba, cikina hautsinewa yake yiâ?.
Fahimah dai bata amsa ba, ta baiwa banza ajiyar sa, sai kokarin kunna heater din dafa ruwan
zafi da ta ke yi. Da alama so yake ta tanka ya ji dadin bata mata rai, ya ci mutuncin ta a banza
bata da mai tare mata, to ba za ta tanka shi ba. Don an ce karfe daya baya amo.
âIrin ga dan iska din nan ko, ina magana kin bai wa banza ajiyata?â?
Fahimah ta ga in ba ta amsa ba zai iya yin zuciya ya shigo ya makure ta, ko ya samu ya huce
haushin manna masa ita da Ammi ta yi, ga shi su biyu kacal a cikin gida babu mai ceton ta. Sai
ta ga gara ta tanka, don ya san ta daina tsoronsa yanzu, kuma tana iya mallakar kanta a
gabansa. Sannan ba zamansa take yi ba zaman Ammi take yi.
âDon Allah ka sarara min mana! Kafin 15 minutes din ma zan kawoâ?. Ta fada ciki-ciki
kamar mai kunkuni. Babu tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba. Tsiwa take so tayi masa amma tana
tsoro.
Fatanta ya bar mata kicin din. Ko ta samu ta saita bugun zuciyar ta. Kada tayi abind ta saba yi a
gaban sa.
Tsayuwarsa a wurin na maida ita unease, jikinta ya ki sakewa ya yi aiki yadda ya kamata.
Kamar wadda ke cikin sanyin kankara a dalilin kasancewar sa a wurin tare da ita. Daurewa
kawai take yi don tsira da determination din ta akan Uwais Shagari.
Amma ga mamakinta Uwais ya ki tafiya, karewa ma shigowa ya yi kitchen din ya haye kan
island ya yi zamansa. So yake ya gargasa mata magana ko yaya ne kafin ya yarda ya dauketa
su tafi, wadda har ta koma ga mahaliccinta ba za ta mance ba ya sonta ba.
"Yanzu ke kin yarda Ammi ta rusa miki rayuwa da mijin da ba ya sonki, bai taba sonki ba, kuma
ba zai taba sonki ba? Me ya sa ba ki yi wata hobbasa don kwatar wa kanki âyanci ba? Ba ki
da masaniyar ina da mata ne, wadda nake matukar so kamar na ba ta raina?â?
Tunda ya fara maganar Fahimah ba ta dago ba, firar dankali ta ke, amma da ya zo sentence
dinsa na karshe sai ji ta yi ta tafi da tsokar hannunta, wato ta yanke hannunta da kakkaifar
wukar da ke hannunta.
âIna da matar da nake so, kamar na ba ta rainaâ?.
Wani statement ne wanda shi a wurinsa ba komai ba. Amma a gare ta tamkar digar ruwan
dalma ne a kan fatar jikinta. Tana so ta ba shi amsa, daidai da wadda ta dace da munanan
maganganunsa sai ta tuna UWAIS ne. Wani kwayan mutum guda daya da zuciya da ruhinta ke
so, wanda ta yi wa kanta alkawarin zama da shi da kasancewa tare da shi against all odds koda
zai yi ta yankar tsokar naman jikin ta yana sanyawa a miya albarkacin Ammi Safeeyyah -
Basudaniyyah. Balle common bakar magana akan matar da yake so.
Sai ta saki wukar da ke hannunta kasa, hade da dankalin ganin jini yana fita. Ta kudire ko
dukanta Uwais zai yi cikin gidannan ba za ta soya masa dankalin nan ba, ko dai ya tafi da
yunwarsa, ko ya kirawo matar da zai iya bai wa rai ta soya masa daga Malaysia.
Ta kashe komai ta wuce ta gabansa hannun ta nan digar jini ba tare da ta ce da shi komai ba.
Murmushin mugunta ya yi, ko ba komai ya ci nasara, ya yi spoiling mood dinta ita ga amarya
zata bi miji Ikko, ta samu miji a bagas sabida ba Amrah, kuma gashi ya janyo ta yanke hannu.
Sai yaji bai ji dadi ba daga kasan ransa saboda ko kadan ba ya son ganin jini ko yaya daga jikin
dan Adam. Don haka ya sauya shawara ya bi bayanta zuwa dakinta ba tare da ta san ya biyo ta
ba.
Toilet ta shige ta sakar wa hannun famfo a sink, tana kalon jinin jikin ta na gudu treda ruwan
tana hawaye, sai jin motsin mutum ta yi daga bayanta. Da sauri ta juya a tsorace, ashe har ya
iso gab da ita sai da ta bigi kirjinsa. Da sauri ta ja baya. Dan farin bandeji ne a hannunsa na
nade ciwo da ruwan hydrogen, daya dauko a dakin Ammi, sabida bata wasa da first aid ita, ba
tare da ya ce komai ba ya kama yatsan ya zuba hydrogen a kan yankan, sannan ya soma
kokarin daurewa da bandejin.
Fahimah, ta kusa suma a wannan lokacin sabida kyakkyawan closeness din da ya shiga
tsakanin ta da Uwais. Wanda hakan bai taba faruwa ba koda da kuskure. Ita da Uwais sai kallo
daga nesa. Wani irin sassanyar kamshi yake yi na Maison Francis (Baccarat Rouge) dake tashi
a hankali daga jikin sa. Shi kuwa Uwais bai yi don wata manufa ba, sai don tunawa da ya yi da
kalaman Ammi.
âFahimah amanar Allah ce tsakaninmu Uwaisâ? na ba ka amanartaâ? idan ka cutar da ita
kai da Allahâ¦â?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ita in wani ne ya gaya mata a baya cewa Uwais na magana haka
ma, ba za ta taba yarda ba. He is not that miskili to such an extent kamar yadda ta dauka a
baya, kawai dai magana sai ya ga damar yin ta, kuma in ya so yana yin abar sa sosai ko da
bazaka bashi amsa ba. Uwais Shagari, ya fara sassauta wa ransa kiyayyar Fahima a bisa
dalilai da dama.....
Muhimmi shi ne, ganewa da ya yi ita din is a source of geniune happiness na mahaifiyar sa
wadda in ya zauna da ita ko da ba ya kyautata mata in disguise Ammi za ta yi ta farin ciki da shi
ne, tareda sanya masa albarka.
Sannan auren su wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa) wanda bazai iya tsallakewa
ba, watakila har abada, don ba zai taba iya mikawa Ammi takardar saki ko ta wata mace daban,
balle wannan wadda take so kamar ita ta haifa ba.
In haka ne kenan takurawa rai da kiyayyar da babu riba a cikin ta aikin banza ne.
Zai zauna da Fahimah koda har abada ba zaya so ta ba. Sai ta zauna zaman Ladan Noma (as
he called it). Tunda haka Ammi ta zaba mata.
A kullum yana tuna dawainiyar da Ammi ta yi da shi tun yana yaro, da dawainiyar ilminsa a
bayan ran mahaifinsa ba tare da taimakon kowa ba. Ita ke kaishi makaranta ta dauko shi tun
daga primary har secondary bata yarda kowa yayi mata wannan aikin.
Yau ga shi yana ta cin gajiyar ilmin ta koâina, sannan ta bar shi ya auri Amrah duk da yakinin
da yake da shi na ba ta sonta, amma ta kwatanta adalci ko a fuska ba ta taba nunawa Amrah
ko wani ba.
Ammi na da wasu irin principles (doctrines) akan akan karan-kanta, wadanda ta dora Fahimah a
kai, wanda su ne ta ke masa kwadayi, amma ya kasa ganewa da gangan. Yana can ga
kyale-kyalen da baya lasting. Tana da tabbacin watarana zai gane din, tana raye ko bata raye,
cewa Fahimah matar rufin asiri ce kuma babban alkhairi a gareshi, har ma ya zo ya gode mata
da dukkan godiyar da zai iya. What he needs most is time ....and closeness ga Fahimah.
Bayan fitarsa Fahimah ta ga ya dace ta sauya sutturar jikinta ko da ba ta yi kwalliyar da Ammi
ke so ba, don haka ta yi wankanta a nitse, da Olay shower gel (goats' milk), ta fito ta zauna
shafa, sannan ta fiddo wani jan material da aka yi wa fitted gown ta sanya, yana da ratsin
golden da baki a jikinsa. Ta yi daurin kai ya zauna cif, sannan ta matsa gaban mudubi tana duba
turarukan da Uwais ya ajiye a wajen har guda uku. Ashe sunan turaren Uwais ke nan (Maison
Francis, Baccarat Rouge).
Kwarai ta dade tana son kamshin, domin kuwa kamshinsa na mannewa a zuciya ne tamkar
maganadisu, musamman ga ruhin diya mace ma'abociyar soyayyar da bata samu martani ba.
Ba ta san lokacin da ta kai turaren ga bakinta ta sumbata ba, and it feels likeâ?.. like Uwais din
himself ta ji ta sumbata apparently. Wanda hakan ya aika wani irin sako cikin ruhinta, wanda ta ji
shi tun daga kwakwalwa har zuwa toe wato babban yatsar kafar ta.
Something like emotion mai narka zuciya, da sanya wani irin daddadan feeling..... Fahimah ta
shiga waiwaye ko da wanda ya ga abun kunyar da ta yi (sumbatar turaren Uwais). Ga dukkan
taimakon Allah, sai ya kasance babu kowa. Daga ita sai Ubangijin ta kadai, sune kuma kadai
suka san adadin son da ta ke yi wa Uwais Shagari. Tana kuma rokonSa Azza Wa Jallah a kan
in son da ta ke yi wa Uwais, ba alkhairi ba ne a gare ta to ya yaye mata bakidaya ko ya
sassauta mata.
Akuyar cikinta ta yi kukan da ke tuna mata rabonta da abinci tun jiya. And cikinta na da nasa
hakkin a kanta ba soyayyar Uwais kadai ba. Wadda ta zamo mafi rinjayen abin da ke
consuming lokacin ta.
Idan ta lula a duniyar tunanin Uwais, ba ta sanin cewa lokaci na tafiya, sai ta farga da awannin
da ta karar ba tare da ta san me ta ke yi ba. Hormones dinta suna da karfi, da ba su sabbaba
mata ciwon tunani a kan Uwais ba.
She then decided to prayâ? wato ta yanke shawarar komawa ga addu'a akan Uwais Shagari,
tunda an ce adduâa maganin komai ce.
Addu'ar data dukufa yi a yau itace. Idan son da ta ke wa Uwais alkhairi ne, Allah ya juyo da
hankalinsa kanta cikin gaggawa. Idan ba alkhairi ba ne a gare ta, Allah ya nesanta zuciyarta
daga kansa Ya raba ta da wannan koshin wahala.
Karfe biyu aka kawo mata abinci mai rai da motsi taci sama-sama daga nan kuma barci mai
dadi ya dauke ta, barci sosai ta yi wanda ba ta farka ba har Uwais ya dawo.
Karar sautin talabijin shi ya sanar da ita dawowarsa. Da ta bude ido ta dubi inda yake zaune
yana shan lemun power horse daga shi sai farar singlet da dogon wandon suit din da ya cire.
Jikinsa ne ya gaya masa tana kallon shi, ya juya ya sakar mata harara a ran shi yana fadin ta
kafe shi da ido kamar mayya, ko sun hada jini da maitar ma wa ya sani ne? Kunya sosai ta ji da
ya kama ta kane-kane a cikin kallonsa.
âAre you not praying ne ke? (Ke ba kya sallah ne)? Tunda muka zo ban ga kin dungura
goshinki gaban Ubangiji ba, sai kallon mazan mutane kamar kya cinye su?â?
Fahimah ta tsuke baki da fuska cikin bacin ran kalaman sa, sannan ta mike daga kwanciyar. Ya
dan bi ta da kallo tana wucewa ta gabansa, sai ya ji kamshin turaren sa na tashi a jikin ta
kadan-kadan.
"Lallai ma yarinyar nan ta fara raina ni". Uwais ya fada a ransa. Amma bai furta mata ba dai in
ma ta yi ne don ya tanka. Anyway jan kayan nan sun mata kyau as black as she is, sannan
sheâs tall, slim and well-structured. Bar ta dai da 'bakin ta' da ke munana ta (dark-skinned).
But even her lips are looking luscious, succulent and irresitable to every tensed manâ?" da
sauri Uwais ya shafo sumar kansa cike da fargabar Allah ya sa ba a fili ya fadi wadannan
baranbaramar kalaman ba.
Daidai lokacin da ta fito daga toilet fuskarta da damshin ruwa, sai ya ga ruwan ba ya mannewa
a kan fatarta sabida sulbinta. Sai digewa yake dis-dis. Da sauri ya kauda kansa da suka hada
ido, yana tambayar kansa, me yake kallo ne haka???
Duhu ya shigo, bayan ya yi sallar isha ya ji yana da bukatar fita supermarket, akwai abubuwan
bukata da yake son sayo musu. Ya mike ya maida rigar sa, ya dau wayarsa ya sa a aljihu ya
durfafi kofa.
Fahimah ta fahimci Uwais fita zai sake yi a daren nan, ba ta san lokacin da ta zari mayafinta ta
rufa masa baya ba saura kadan su yi karo a bakin kofa.
âKe lafiya? Ina za ki haka?â?
Ai kawai ba ta san sanda ta rike gefen rigarsa ba.
âZan jira ka a waje ka je ka dawo, dazu bayan ka fita aka yi ta kwankwasa min kofa. Ni
gaskiya tsoro nake ji an ce Lagos ana kidnappingâ?.
Ta fada da iyakar gaskiyarta.
Uwais ya rasa me zai ce, sai ya kalli hannunta da ya rike masa riga gam!
âTo cika ni tukunna ko?â?
Ta sake shi cikin jin kunyar abin da ta yi, har ga Allah tsoro ta ji, ba ta san lokacin da ta yi hakan
ba.
Juyawa ya yi ya fita ta rufa masa baya, ya rufe kofar dakin. Suna sauka ta lifter yana kiran
direbansu da ke zirga-zirga da su, don haka suka samu direban ya yi parking kofar reception
yana jiransu.
âPlease take us to the nearest supermarketâ?.
âItâs done, Sir.â?
Tafiyar mintuna sha biyar suka yi ya kai su wani supermarket shahararre a nan Ikoyi. Fahimah
ba ta yi niyyar fita ba, amma da ta tuna pad dinta saura uku sai kawai ta balle murfin mota ta bi
shi a baya ba tare da ya sani ba.
Shi dai sai hango ta ya yi a wani bangare daban na shagon tana daukar abu. Ya yi kamar bai
ganta ba ya ci gaba da sayayyarsa. Duk abin da za su bukata da ma wanda ba za su bukata ba
sai da ya daukar musu daga nan Lagos har zuwa Sudan. Ta ja gefe ta tsaya tana ta kallon
mutane wadanda yawancinsu couples ne da yaransu suke sayayya gwanin shaâawa. Da ta ga ya doshi wajen biyan kudi, sai tayi maza ta bi shi a baya tana dan bobboye abin da ta
dauko.
Daga bayansa ta tsaya, ya yi kamar bai ganta ba. Da aka fara lissafa kayansa ya juya yana
amsa waya, sai ta yi wuf! Ta jefa always pad din data dauko cikin kayan.
Da ATM card ya biya aka dauko masa kayan zuwa mota. Suna shiga wayar Ammi na shigo
masa.
âKa ce in ka koma gida za ka ba ni Fahimah kuma na ji shiruâ?.
âIâm sorry Ammi, mun dan fita ne zuwa supermarket, bari mu karasa masauki zan kira in
ba taâ?.
âTo lallai gobe ka duba lafiyar wayar ta, haka kawai Fahima ba ta kashe waya, gara da waya
a kusa ko da ba ka nan za ta iya kiraâ?.
Suna ajewa direba ya ja motar.
A can Khartoum Haj. Safeeyyah-Basudaniyyah sai ta dungura goshinta cikin hali na sujjadah ta
godiya ga Ubangiji.
Ko ma dai ya ya ne, ko ba shiri suke ba, ko ba soyayya suke ba, ko babu