Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
zo ta gyara masa daki. Tsaki yayi yana fadin "da abinda tafi
dacewa kenan ai (aikatau) ba matar masu gida ba".
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Washegari da safe Fahimah ta shirya masa breakfast, sabida
Talatu ta yi sammako zuwa kauyen su Jahun 'yar ta ta haihu. Kunun gyada tayi masa fari kal
mai gardi sai kosan dankalin turawa da ruwan shayin da ya zamewa al'ummar gidan duka
farillah. Ya fito cikin casual - dress din sa na suit din ma'aikatan bankin GT misalin karfe bakwai dai-dai
na safe. One thing shine baya wasa da cikin sa sabida fadin kirjin sa (physique) da motsa jiki da
yake yi da Asubah yasa baya iya fita ba tare da ya karya ba.
A jikin dining din ya sameta tana jera abincin, rigar barci ce a jikin ta da 'yar hula a kanta ta dora
zanin atampa a saman rigar. Yana zuwa ya ja kujera ya zauna, ba tareda ya dubeta ba. Juyawa
tayi ta bar wurin jin zata sake yin barin tangaranm ita kuma tayi alkawarin ta daina bada kanta
gaban Uwais. Yayi tsammanin zata gaishe shi ne ya baiwa banza ajiyar ta. Ga madaukakin
mamakin sa sai ta juya zuwa dakin ta ba tareda ta ko kalle shi ba.
"Kin rufawa kan ki asiri".
Ya fada yana tsiyaya kunun a kofi. Ko daga kyan kunun a ido ya tabbatar zai yi gardi a baki.
"Kin taimaki mijin ki na gaba (idan Uwais ya sake ki) da kika tsaya kika iya girki. Don zaman
Ammi kike yi ba nawa ba. Banda abun Ammi wannan Blakin ai sai ta dinga firgita mutum cikin
dare. Gara da ta rike abar ta a gefen ta bata yi gigin kawo masa ita gida ba. La-shakkah da
Amrah ta samu Kuku. Don bazai taba bude baki ya iya cewa Amrah yana da wata macen a
duniya bayan ita ba. Bai yaudari Amrah ba, don da gaske har cikin zuciyar sa bai da wata mace
bayan ita.
Sama-sama ya ci abincin ya wuce dakin Ammi, tana zaune bisa darduma tana azkar din ta na
safiya. "Na fito Ammi, sai na dawo. Sabahul khair". Daga masa kai ta yi ya juya ya fita.
****
Yau Fahimah zata fara registration, don haka tare suka tafi da Ammi, kuma fannin da Ammi ke
koyarwa shi ta zabar mata, don tace a fannin ne kawai zata iya dinga taimaka mata a gida wato
tsimi da tanadi (economics).
Kasancewar yanzu abu ake na sanayya, Fahimah bata sha wahalar samun gurbi fannin na tsimi
da tanadi ba kamar sauran dalibai, duk da wahalar da yakeyi, tunda tana da uwa a gindin
murhu.
Da taimakon Ammi ta fara registration, kullum da safe tare suke tafiya, yau da suka fito akan
titin su na komawa gida Ammi ta ce "Fahimah, is high time ki fara koyon tukin mota don ki dinga
taimaka min kina taimakon kanki, tunda Surajo ya tsufa baya iya gani sosai, yanzu kuma ke
matar aure ce, bai kamata ga mijin ki zaune a gida in dauko wani kato ya dinga kai ki
makaranta ba, nikuma ba kullum nake shiga Campus ba, tafiyar mu zata saba in kika fara
daukar lacca".
Fahimah ta ce "Ammi to waye zai koya mini?" "Ni dai kin san bani da lokaci, tunda an shiga
sabon semester, amma zan wa Uwais magana ya dinga koya miki a karshen mako".
Ammi ta kirkiro zancen koyon mota ne don ta samar da kusanci ko yaya tsakanin Uwais da
Fahimah don ta ga abin nasu ba mai alamar karewa bane. Kada kuma auren ya lalace a haka.
Lokacin da Ammi ta furta masa wannan umarnin, fuskar Uwais komawa ta yi kamar hadarin da
ya nausa yayi gabas. "In koya mata mota fa kika ce Ammi?" "Eh, abinda nace kenan" bai san
sanda ya ce "Ammi muharramata ce?" Don shi shaf! Ya mance da wata Fahimah balle auren ta
dake kansa. Ammi dunkule yatsunta tayi ta mika masa "ungo nan (dakuwa). A'ah ba muharramar ka bace,
kanwar tsohon ka dake kabari ce".
"Yau sabida Fahimah har Baban shi an zaga". Tashi yayi fuuuu! Ya wuce dakin sa. Abincin ma
ya fasa ci. Ammi tana kai shi bango da yawa akan Fahimah yana hakuri ne kawai don UWA ta fi
gaban wasa ammma da tuni Fahimah ta dade da komawa orphanage.
Washegari Ammi ta samu waya daga babban dan Kawu Shuraim wato Mahdi, cikin kuka mai
tsanani Mahdi yace.
"Allah ya yi wa Abbu rasuwa yau din nan".
"Innalilllahi wainna ilaihi rajioun".
Ammi Safeeyah ta fada tana karawa.
Ashe shiyasa ya dage ya zo ya yi wa Uwais aure? Ashe sallama ce ya yi musu, ashe rabuwar
kenan, ashe daga wannan lokacin Uwais yayi rashin Kawun sa mai son sa da kaunar sa...
Allahu akbar!
Muryar Ammi kadai ya ji ya tabbatar kuka take yi. Uwais a zaune yake akan kujerar sa amma
bai san sanda ya mike tsaye ba makale da wayar a kunnuwan sa, kansa ya kama ya dafe da
hannayensa biyu a lokacin da Ammi ta fada masa rasuwar Kawu Shuraim. Babu irin kokarin da
bai yi ba don ya samu excuse daga Banki ya bi Ammi Sudan amma bai samu ba, domin already
yana daga cikin manyan ma'aikatan GT da zasu halarci seminar ta organization din nasu
gabadaya, wadda suke yi duk karshen shekara a babban reshen su da ke jihar Lagos, zasu tafi
cikin satinnan kuma an riga an mika sunan sa.
Ammi ta so tafiya da Fahimah, amma ga nata karatun da bai gama nuna ba, kuma tana so ta
jima a Khartoum wannan karon kasancewar ta dade bata je ba. Don haka dole ta bar ta a gida.
Da daddare bayan Uwais ya dawo take tambayar sa "yaya ka samu excuse din ne zamu tafi
tare ko yaya?" Ya kalli Ammi da tausayin ganin yadda mutuwar dan uwan ta ta buge ta, ta
fyadar da ita a wuni guda, Ammi har ramewa ta yi. Idanun ta sun yi jazur sabida kuka. Ya ce a
hankali "ban samu ba Ammi, don an tura ni cikin masu tafi seminar a Lagos nan da kwana uku,
zan yi kwanaki ukku, sai dai idan na dawo, zan yi matukar kokari na samu adduar bakwai".
Ammi ta ce yaushene tafiya Lagos din? Yace jibi Juma'ah, zamu dawo Lahadi don mu samu
ofis litinin, sai in yi kokari a bar ni in zo Sudan ko na kwana biyune kacal".
Ammi ta ce "to Yaya za'a yi da Fahimah? Don ni zan yi akalla sati biyu kuma tana zuwa
makaranta, ga Talatu bata dawo ba har yau, don haka tunda Juma'ah, Asabar da Lahadi ne ka
tafi tare da ita Lagos din, bazan barta ita kadai a gidannan ba.
In kuka dawo ka samu izni daga ofis din sai ku taho Sudan tare ku samu addu'ar bakwai ku
dawo tare, tunda dukkan ku kuna da passport na kasar Sudan".
Wani gumi ne ya shiga barkowa Uwais daga kowacce kafa mai tsatstsafar da gumi ta jikin sa.
Bai san san da ya kira sunan Ammi da hanzari ba.
"AMMI!"
Tune din muryar kamar na wanda zai fashe da kuka. "Muharrama ta ce da zan tafi da ita wani
gari har kwanaki?" Ammi bata san sanda ta kai masa bugu da filon hannun ta ba, ta ce "idan ka
sake yi min wannan tambayar ta rainin hankali wai ko Fahimah muharramarka ce sai na
sassaba maka kamanni. A'a ba muharramarka bace, karuwa ce nace ka dauka ka tafi da ita. Kuma ka kula da marainiyar Allah Uwais, cin ta, shan ta da walwalarta. In ka ci amanata kai da
Allah".
Uwais ya mike yana rangaji ya bar falon, bakin ciki kamar ya hadiye zuciyar sa. Wai me ke
damun Ammi ne? Idan da yana tunanin Dimentia ne yanzu kam ya tabbatar lafiya kalau take,
tana matukar son hada rayuwar sa da yarinyar nan, yarinyar data riga tasan ita kadai take son
abarta. Ya dauketa ya shiga da ita cikin abokan aikin sa ma ya ce matar sa ce ai ya sayowa
kansa raini a wurin ta da wurin su. Wannan matar leburori ce da marassa gata ba irin tashi
bace. Shi fa ba abunda bai so ma a duniya irin ganin black fuskarta, balle yasa ta a gefensa
yana yawo da ita cikin Nigeria wai har ma da wajen ta (Sudan).
Idan Amrah ta samu labari fa cewa he is with another woman me zata dauke shi? Hakan bai
zama yaudara da cin amanar soyayyah ba? Zuciyar sa ta tambaya. Sannan ba tare da bata
lokaci ba daya zuciyar ta halarto da amsa...
Bai zama cin amana ba, tunda itama ka biya sadakin ta, matsalar tun farko bai kamata ka
boyewa Amrah ba. In har tana son ka zata baka goyon ne baya kayi biyayya ga mahaifiyar ka.
Yadda zuciyar sa zata iya jure hada muhalli da Fahimah a bakon wuri inda basu san kowa ba
har na tsayin wasu kwanaki shine babbar damuwa a gare shi.
****
Ya cigaba da yiwa Ammi shirin tafiya Sudan a yinin ranar duk da cewa he's frustrated amma
bazaka taba ganin hakan akan fuskarsa ba, yana da charisma na boye fushi, ya saya mata tikiti,
a lokaci guda yana nashi shirin na tafiya Lagos. Yayi waya da duka 'ya'yan Kawu Shuraim yayi
musu ta'aziyyah musamman Mahdi, ya gaya musu uzurin sa na rashin biyo Ammi. A yau da
daddare Ammi zata tashi, tun jiya Fahimah ta hada mata kayan da zata bukata a babbar jakar
matafiya, bata san me ke faruwa tsakanin Ammi da Uwais akan ta ba.
Karfe shidda na yamma Ammi ta shigo dakin ta, ta zauna dab da ita, sannan tace.
"Fahimah, ban miki bayani ba tun jiya, na bari sai yau da zan tafi, ki hada kayan ki kamar kala
shidda, idan na tafi yau, ku kuma gobe da safe zaku tashi zuwa Ikko".
"Ni da wa Ammi.. wa muka sani a Lagos?"
"Ke da mijin ki zaku tafi, ko akwai damuwa ne a cikin hakan?"
Ta yi mata tambayar tana mai tsatstsareta da ido, don kada ta bata damar cewa komai.
Fahimah ta ji miyan bakin ta ya kafe, ta fiddo idanuwa kawai zuruuu! Tana kallon Ammi. Wani
abu ya shiga kan Ammi da alama. Ammi ta fahimci kallon da take mata sarai don haka tayi
murmushi ta ce. "Kalle ni da kyau ki kara, lafiya ta sumul-kalau, a kullum ina addu'ar Allah ya kawo sanadin da
shakuwa ko yaya zata shiga tsakanin ki da Uwais. Wannan nesa-nesan da kuke da juna shi
yake bada babbar gudunmuwa wajen nesanta zukatanku da juna.
Na baku lokaci, ban zaci abin naku zai kai haka ba, amma na fahimci in za'a shekara a haka
zaku zauna har auren ya lalace. Ban ce lallai sai kun zauna gida daya ba, ni in dai zaku amsa
sunan miji da mata ko a gidannan ne kiyi ta zama Fahimah, ki haifa min jikoki masu irin
tarbiyyar ki, masu kama da ku, wadanda ni Allah bai bani da yawa ba. Uwais in dai irin halittar marigayi mahaifin sa gare shi, wallahi bai iya tsallake wannan tarkon
dana dana masa. Ina nufin (bai iya yin kwanaki masu yawa babu mace). Don haka wuyar ta ku
fahimci juna shike nan ina tabbatar miki komai zai wuce kamar ba'a yi shi ba. Sai tattali da
soyayya da zasu biyo baya. Soyayya zata yi kanta a zukatanku duk da yanzun ma bani da tabbacin kiyayya ce kuke wa
juna. In ma kiyayyar ce sai dai daga Uwais amma banda ke Fahimah. Na ga soyayya mai yawa
cikin kwarar idanun ki....shiyasa ma na jajirce na hada wannan auren, don idan mace na son
namiji, to kuwa tabbas zata yi hakuri da shi duk rintsi, ta rike shi matsayin uban 'ya'yan ta
albarkacin wannan so da ta ke masa.
Don haka bisa umarni na Fahimah, tashi ki hada kayan ki ki bi mijin ki zuwa inda duk yasa kafa
wajen neman abincin sa. Allah yayi muku albarka".
Fahimah bata ce komai ba, abinda bata son yi agaban Ammi shi ya zo (tears). Ammi da kanta
ta shiga zabo mata kayan da ya kamata ta dauka daga cikin na lefen ta da aka dinko. Hatta
kayan shafa dana kwalliya duk a acikin na lefen ta ta diba mata, ta hada mata su a
matsakaiciyar trolley. Fahimah sai bin ta take da jikakkun ido har ta gama. Ta dube ta tana daga
zaune a bakin gado duk jikin ta ya mutu. Ta yi kamar bata gane halin data ke ciki ba na zullumi
da anxiousness. "In da abinda kike bukata na amfanin ki sai ki kara, na gaya miki kwana uku
zaku yi, kuma in kun dawo da kwana biyu zaku biyo ni Sudan.
Bakin Fahimah sai motsi yake tana so ta tambayi Ammi. "Shin Yaya Uwais ya amince da
wannan tsarin nata?" Amma ta kasa furtawa har Ammi ta bar dakin.
Ba abinda ta kara kan kayan da Ammi ta hada mata sai inner wears, sannan ta dauki pad,
kasancewar tasan ta kusa yin period.
Ita da Uwais din ne suka raka Ammi airport, karfe takwas na dare, kasancewar boarding flight
zata bi. Suna can har karfe goma Uwais na shige da fice da kayan da Ammi zata tafi dasu gun
(screening) kafin lokacin tashin su yayi.
Gab da zasu tashi ya iso inda suke zaune itada Fahimah akan kujerun silver, yace.
"Everything is set Ammi, Allah ya kiyaye hanya, safe journey".
Ammi ta daga ido ta dube shi da murmushi, daidai lokacin da aka soma kiran pasinjan Sudan
da su shiga jirgi. "Ina fatan kafin in dawo, komai zai zama tarihi Uwais. I mean tsakanin ka da
Fahimah. Za ka rungumi auren ka da hannu bubbiyu, ka yarda Fahimah amanar Allah ce a
hannun mu Uwais. Idan kana ganin takurawa ce na yi maka kayi hakuri ka bani dama, just give
it a try, ni na haifeka Uwais don haka ka yarda bazan cutar da kai ba, komai na yi maka sai dai
ya zamo taimako da soyayya.
Kai da kanka watarana zaka zo kana gaya mini WACECE FAHIMAH? Wadanne irin baiwarwaki
Allah yayi mata nayi maka wannan alkawarin. Kyal-kyal banza ya daina diban ka. Halin mutum
shine abinda yake sawa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba...
Above all this black da kake cewa is but expensive beauty, but only ta BRAVE MEN Uwais......".
Ta karasa da murmushi, sannan ta mike tsaye don kowa ya shige ya barta,
"I'm hoping that my son to be among them".
Sannan ta kama hannun Fahimah wadda kanta ke sunkuye tana hawaye, ta sanya cikin
tattausan hannun Uwais. Ta dunkule su ta cure wuri guda, sannan ta dauki hand bag dinta ta
wuce zuwa terminal.
Ya dade yana kalon bayan Ammi, sannan ya sauke ido akan hannun Fahimah dake dunkule
cikin nasa, wadda tunda ta sunkuyar da kai hawaye take zubarwa bata dago ba. Ji take kamar
ta bi Ammi, kamar Ammi sallama take musu, kamar in ta tafi ta bar su su kenan bazata dawo
ba! Ta barta da miskilallen dan ta a inda bata da kowa. Kalaman Ammi Safeeyah sun luguiguita
zuciyarta; wai namiji akewa wannan rokon akan ya so ta ita wace irin mara sa'a ce a rayuwar
ta? Ta shiga ittikafin adadin soyayyar da Ammi ke mata....wadda duk itace silar hakan.
Ko don wannan kauna da soyayya na Ammi Safeeyah, ta ci alwashin zama karkashin igiyoyin
auren Uwais no matter what, sannan against all odds, ko da zai dinga zaftarar naman jikin ta ne
kullum yana sawa a miya saboda kiyayya.
Mu karasa a littafi na 2.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A daidai wannan lokacin Amrah na can cikin Aunties dinta ana yi
mata kwalliya. Kasa daga kiran ta yi da ta ga sunansa ke yawo a screen din, domin Amrah
yarinya ce mai alkunya. Aunty Murjanatu ta ce, Amrah ba kiranki ake bane?"
Aunty Wasila ta ce,
"Maybe angon ne ake jin kunyarmu".
Ita dai ba ta tanka su ba har wayar ta katse. Yau ji ta ke ba wanda ta ke jin nauyi duk duniya irin
Uwais. Aunty Wasila ta ce, "Amrah a haka za ki kama mijin? Yo yanzu wa yake kunyar amsa
wayar mijinsa a ko ina? Zauna nan kina fulako, matan waje su kwace, wannan mijin naki wanke
hannu ka taba".
Duk aka yi dariya har make up artist din dake yi mata kwalliya. Still Amrah ta kasa daga wayar
Uwais duk da sai kira yake har sau uku. Daga karshe ya turo text. Shi ma sai da ta saci idon su
Aunty Murja sannan ta karanta.
"Finally Mrs. Shagari.
May this moment mark the beginning of the series of our blessings... May Allah's rahma cover
us forever. I promised you eternal love Amrah and all the happiness that love can bring... I love
you Amrah!"
Uwais Shagari.
Amrah ta yi catching numfashinta a hankali tana satar kallon yayyanta ko da wanda ya gane
yadda sakon Uwais ya tafiyar da numfashinta na wucin gadi? Dukkansu hankalinsu ba ya kanta
yana kan hirar dinner da za a yi yau da daddare. Ta yi ajiyar zuciya tana tunanin da idanun da
za ta iya kara duban Uwais a sabon matsayinsa na miji a gare ta. Amrah na son Uwais, amma soyayyar Uwais ta fi ta Amrah yawa. Probably za ta iya ci gaba da
rayuwarta normally ko babu Uwais ko da akwai shi. Yayin