FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 20

57K to 59.2K   out of 59.2K words

cire ba ka daina kamshin (Maison
Francis)�.

Ya ce, “Ai kuwa sai dai a yi wacce za a yi, amma ban da wannan yarenâ€?.


Sun yi shirin kwanciya, zullumi da damuwa duk sun ishi Amrah, ba da wasa ta ke ba turarensa
hawa kanta yake, a baya babu kamshin da ta ke so irin na Uwais amma banda yanzu.
Uwais na sanya tafukansa a bayan wuyanta ya hada goshinsu zai lallashe ta don ya ji actual
abin da ke damunta ta ke ta wannan yamutse-yamutsen fuskar. Ai kuwa ta kelayo masa wani
uban amai, mai karni. Ya yi maza ya ja baya ita kuma ta ci gaba da amayar da spicy chicken din
da ta ci tas! Sai da ta amayar da ita. A daren ya ce su tafi asibiti, ita kuma ta dage ba ta zuwa ko’ina. Ai ta gaya masa turarensa
ne ba ta so ya ki jin magana. Ya ki ya bar mata dakin.

Washegari sai da ya yi mata jan ido sannan ta yarda suka tafi asibitin standard. Awo na fitsari a
tashin farko ya nuna ciki na watanni uku.
Tunda suka dauko hanyar dawowa Amrah ke kuka, kuka kashirban. Kamar ba ita bace a baya
ta ce ta yi surrender ba. Bata taba tsammatarwa kanta ciki a wannan lokacin ba. Ta rantse ba ta
shirya wa haihuwa yanzu ba, karatunta zai salwanta. Uwais sabida tsananin bacin rai ga
kalaman Amrah a kan kyautar da Allah ya yi masa cewa ya yi,
“Wallahi in ki ka zubda cikin nan da gangan, to a bakin aurenkiâ€?.

Amrah ta zaro ido tana kallon Uwais, kallon mamaki da tsoro, ina soyayyar da yake ikirarin yana
yi mata? Yanzu har ya fi son dan da zai haifa a kanta? Da ma Daddy ya ce soyayya karya ce,
ka yi aure kawai don bukatarka ta dan Adam da cika sunnar Annabi, amma ba don soyayya ba,
sabida it never exist in nowadays men, even if it exists da zarar sun gano wata za ta yi fading.
Shin Daddy da gaske yake? Ko dai Uwais ya gano watan ne shi ya sa komai nata ke fading a
idanunsa??? Ba za ta yi mamakin kowacce barazana daga gare shi ba, don ya nuna yana son
cikinsa. Amma barazana da igiyar aurenta abin ya ba ta mamaki da tsoro sosai, ya kuma kara
sagar mata da gwiwa akan canje-canjen data ta gani daga gare shi.

Tunda suka dawo kuwa ta raba daki da shi, shi ma bai kara takura mata ba. Yanzu lallabawa zai
yi ta haife masa dansa ko ‘yarsa lafiya ya daina neman komai a wurinta. All thanks to AMMI
yana da precious gem dinsa a gefe, a virtous wife who her priçe is far above rubies wadda sai
yadda ya ga damar sarrafa ta (naïve and innocent FAH-HIMAH SHAGARI). Yau da bai san
ina zai sa kansa ba da wannan takunkumin na Amrah.
Wuni guda Amrah ba ta kulla komai a gidan ba, ga shi duk ya yi kura, kasancewar an kwana
biyu ba'a ciki, tunda suka zo sai abincin sayarwa yake ta faman sayo musu. Har ya fara gajiya
da daukan mota yana fita yana dawowa.

Ita da kanta dattin gidan ya ishe ta, ta fito ta same shi a falo yana kallon ball da kungiyar da
yake so Arsenal, yana shan wankakken inabi da ke kan tebirin gabansa. Daga can nesa da shi
ta tsaya tana toshe hanci.
“Habiby, ina wannan yarinyar ta gidanku?â€?
Ya kalle ta cikin takaicin yadda ta ke toshe masa hanci kamar wani mushe, ya ce,
"Wace yarinya? Mu gidanmu da yarinya ne?�
Ta ce, “Wannan budurwar nake nufi, baka, mai kyau haka, mai jan class din nanâ€?.

Gaban Uwais ne ya bada wani irin damm! Ya bude ido kawai yana kallon ta.
Ta ce, “Don Allah don Annabi ka je ka dauko min ita ta taimaka min in kintsa gidan nan, ta yi
min miya ko ta sati daya ce in sa a firji don wallahi ba ni son warin albasa�.
Uwais ji ya yi tamkar Amrah ta yi masa gafara, zaman nan da ya yi yana shan inab tunaninta
yake yi, ba ya son Amrah ta samu wani clue ne kasancewar Fahimah matar sa a yanzu,
musamman cikin halin nan da ta ke ciki komai zai iya faruwa.
Ya yi niyyar gaya mata gaskiya tun kafin ya baro gidan Ammi, amma sai ga bayyanar maganar
cikin, don haka ya fasa sai cikinta ya yi kwari. Ta yadda ko me ye zai biyo baya ba zai shafi
lafiyar babynsa ba. Amma anya Fahimah za ta yarda ta zo gidansa?
Kuma in ya yi hakan ya yi wa Ammi da ita kanta Fahimar daidai duk da Amrah taimako ta
nema?
Amma Amrah ta kafa naci, ta kasa ta tsare ita lallai ya je ya zo mata da mai aikin Ammi. Da ya
rasa yadda zai mata bayani, sai ya fiddo wayarsa ya binciko lambar Ammi ta kasar Sudan ya
kira.
Wayar na shiga ya mika mata, “Ungo nemi iznin Ammi da kankiâ€?.
Tana karba ta yi sallama, “Salamu alaikum, Ammi ni ce Amrahâ€?.
Ammi ta ce, “Maraba da mutanen Malaysia, ya ya karatun?â€?

“Ammi na samu mid-term break na sati biyu shi ne kawai na taho Kano. Amma Ammi ba ni
da lafiya, ba na iya aikin gida da girki, shi ne na roke shi ya dauko min aron yarinyar wajenki
kafin ki dawo, lokacin ne nima zan koma makaranta, tunda ita ma cikin kadaici ta ke, sai mu
zauna tare ta taimaka mun har ki dawo, sai ya ce wai sai dai in tambaye ki da kaina. Don Allah
Ammi a yi min alfarma�.
Ammi ta yi jimmmm! Kafin ta ce, “Babu laifi, zan masa magana ya dauko ta ya kawo miki,
amma ku bari in fara magana da ita tukunna in nemi amincewar ta. Don Fahimah ba wai ta
saba da shiga mutane ba ne�.
Amrah ta ce, “Ki roka min ita Ammi, ki gaya mata I’m not boring, ba zan dinga damunta ba
sam, hira in ba tana so ba ba za mu yi ba, ni ma ba dadi nake ji ba kullum ina daki, sabida warin
komai sai in ji shi ba daidai ba…â€?.
Ammi ta yi murmushi, ta ce, “A hankali komai zai dawo daidai, zan lallashi Fahimah ta zauna
da ku din har in dawo�.

A zuciyarta kuma addu’a ta yi, Allah ya bai wa Fahimah nata rabon itama cikin gaggawa. Ta
rasa dalilinsa na kin gaya wa Amrah gaskiya cewa Fahimah kishiyar ta ce, amma ta san Uwais
sarai ta san halayensa, ko me yake yi yana sane, kuma sai ya tabbata yana da hujja.
Kafin ta kira Fahimah sai da ta fara kiran Uwais a lokacin da ta tabbatar yana office. Ta ce,
“Uwais me zai hana ka gaya mata gaskiya in ya so Fahimah ta tare gabadaya su yi zaman
mai dalili? Ni bana son abu na rashin gaskiya ko kankani, kada nan gaba ta gane ta ce mun
yaudare ta".
Uwais ya ce, “Ammi ki rabu da Amrah kawai, zan gaya mata amma ba yanzu ba, don ba son
cikin jikinta ta ke ba. Idan na gaya mata yanzu komai zai iya faruwa.
Za ta iya yin komai don ta huce wanda zai kare ne a kan cikin nan, don hakan sai nan da
watanni hudu a gaba zan gaya mata. Lokacin na gama yi wa Fahimah gininta. Ita kuma cikin ya
kusa isa haihuwa. Don yanzu na aza harsashin ginin�.
Ammi ta fahimce shi, as she has no option, ta ce, “To Allah ya kade fitina ya hada
hankulansu in ka tashi sai ka biya ka tafi mata da Fahimar zan kira ta yanzu in mata bayani".

Fahimah ta fito wanka kenan tana shafa a gaban mudubi kiran Ammi ya shigo mata. Ta mika
hannu ta daga da sallama, Ammi ta ce, “Ya ya na ji muryarki so pale? Are you alright?â€?
Fahimah ta ce, “Lafiya nake Ammi, barci ne bai ishe ni baâ€?.
Ammi ta ce, “To ki kwanta zuwa lokacin tashin Uwais zai zo ku tafi gidansa. Amrah ta roke ni
kan ba ta da lafiya ki je ku zauna tare kafin na dawo.
Ki sa a ranki Amrah ba kishiya ba ce a gare ki, kanwa ce. Ko babu aure tsakaninki da Uwais in
tana cikin lalura hakkinmu ne mu taimaka mata tunda iyayenta ba a gari suke ba�.

Fahimah ta ji kanta ya yi wani irin gingiringim. Idan kuma Uwais ya bada wata kafa da Amrah za
ta fahimci something in between a tsakaninsu fa? Tunda daga shi har Ammi ba su shirya
bayyana matsayinta ga Amrah ba? A kan dalilinsu da ba za ta ce mene ne shi ba? Amma
matsayin Ammi ya wuce ta yi umarni ta saba, ko da bai yi daidai da son ranta ba. Ammi ba ta yi haka don ta kaskantata ba, sai don ta zamo uwa mai adalci ga kowa (zuciyarta ta
tunasar).

Sai kawai ta mike ta hau shiri, tana addu’a a cikin ranta, Allah ya ba ta juriya a zama da
Amrah da zata je ta yi, ya rage mata kishinta da ke damun ranta.
Sanda Uwais ya shigo gidan a falo ya tadda ita jingine jikin jakar kayanta da ta hada. Ya tafi
gaba-gadi da sassarfa ya yi mata wata kyakkyawar runguma tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya
ta. Ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya bayyanawa ba. Sai ya shiga nuna mata practically
yadda ya yi kewan nata har abin ya bai wa Fahimah mamaki da tsoro. Tsoron nata bai je
ko’ina ba ta ji Uwais ya sure ta bai aje ta ko’ina ba sai tsakiyar gadon dakinsa.

It was kind of gentle romance wanda ya motsa zuciya da ruhin Fahimah har sai da hawaye
suka fito daga idanunta. Hawayen da ta tabbatar na farin ciki ne, farin cikin cikar buri, burin
mallakar Uwais a rayuwarta, ta tabbata da ba ta samu Uwais ba rayuwarta ba za ta taba
komawa cikakka, kuma mai dadi ba kamar yadda ta faro a baya.
A bangaren Uwais 100% satisfaction irin wanda bai taba samu a rayuwarsa ba. Da komai ya
lafa a tsakaninsu ya koma gefe tallafe da kansa yana kallon Fahimah daga karshen idanunsa
yana mamaki yana tu’ajjibi a cikin ransa na yadda ta juya masa rayuwa cikin dan lokaci
kalilan. Ya manta da asalin, ya manta da kalar fatar da ba ya son, ita din kadai yake son
kasancewa da, fiye da kowa a halin yanzu. Ita ce sirrinsa marufar asirin sa. Inda yake jin zai iya
sauke duk wani urge da bukatun sa babu shamaki.
Hannu ya sa ya janyo ta gaba daya ta dawo samansa. Ya ce, “Fahhimah, yau hira za mu yi,
madallah da Ammi na, uwata wadda ta fi ta kowa, da ta mallaka min this rare gem. Fahhimah ki
ba ni labarin duk da ya shafe ki da na rayuwarki, ina kuma son sanin duk abin da ki ke so da
wanda ba kya so…â€?. Fahimah ta ce, “I have a very short biography wanda ka fi ni saninsa. Na tashi na gan ni a
duniya ban san kowa ba bansan komai ba sai AMMI. Don haka na shiga tsananin kidima da
Ammi ta dauke ni ta baka Ya Uwais, babu wanda zai so dansa ya auri mara asali, ‘yar da ba
a da tabbacin ko shegiya ceâ€?....â€?. Hawaye suka fito idonta, Uwais ya sa tafin hannunsa yana share mata ya ce, “You are a
darling (ke abar so ce) ko da kuwa a ce daga sama ne ki ka fado, ba dan Adam ne ya haife ki
ba!
Ki yarda da ni Fahhimah� and I promise you LOVE and protection till my last breadth.
Ko kin ga iyayenki watarana, ko ba ki gansu ba har abada, Fahhima zan rayu da ke matsayin
uwargidana kuma uwar 'ya'yan da zan haifa a gaba, daga gidan duniya har gidan aljannah�.
Kalaman Uwais sun narka zuciyar Fahimah, sai ta rungume shi sosai tana hawaye. Ta ce,
“Ya Uwais na dade ina sonka, ina son kasancewa da kai, your odd behaviours ba su taba
sanya min tsanarka ba. Kullum gaya wa kaina nake I didn’t deserve to be loved shi ya sa ka
ke maltreating dina�....�.
Uwais ya sanya tafin hannunsa ya toshe mata baki yana girgiza kai, ya ce, “Actually
Fahhimahâ€? iâ€? I’m jeolous of you. Sabida son da Ammi ta ke miki, bayan wannan sai
kuma ganewa da na zo na yi Ammi daga gidan marayu ta dauko ki,
I’m sorry Fahhimah, amma ki yarda soyayya ba ta yin kanta, sai lokacin da Allah ya nufa. A
yau na samu kaina dumu-dumu a so da kaunarki, wanda nake fatan har mutuwa ta dauke mu

tare, mu tashi tare a aljannah matsayin miji da mata ranar gobe kiyamah…â€?.
Fahimah sarkin kuka, kalaman Uwais sabida dadin da suke mata hawaye kawai suke sanya ta.
Ba su suka bar gidan ba sai wajejejn karfe goma na dare, Amrah ta yi kira har ta gaji ba ta
same shi ba don tun shigarsa gidan Ammi ya kashe wayar sa.

20 / 20