FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 20

45K to 48K   out of 59.2K words

yi rub-da-ciki yana
waya. Daga yadda yake magana kasa-kasa da tausasa murya ta fahimci shi da matarsa ne.
Sun gama fadan kuma sun shirya.
Maganganun da ta ji ana yi cikin wayar sun girmi kwakwalwarta, don haka ta ga gara ta fita ta
ba su fili kafin ta samu heart attack. Uwais har da gayya yake fadin,
“Zan iya hakuri mana Amrah? Amma na kwana arba’in, daga nan duk ‘yar akwalar da
na samu zan yi maneji da ita, da yardar ki ko babu, kada ki ga laifina in ki ka dawo ki ka same ni
da sabon aure…â€?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Murjanatu ta ce, "Ki yi wa mijinki kyakkyawan zato Amrah, Uwais
mutumin kirki ne a fili da boye as far as i know, bana zarginsa da wannan. Amma lallai ne
Amrah in kina son aurenki ya dore, kuma martabarki ta dore a idon Uwais to ki sake shawara a
kan karatun ki. Tunda ya fito fili ya nuna miki ba zai iya hakuri ba, bana jiye miki matan waje don
Uwais ba irin nasu bane. Amma ina jiye miki kishiya da kuruciyar ki…â€?.

Gaban Amrah ya yi bala’in yankewa ya fadi da kalaman Murjanatu na karshe, wani abu da
ba za ta taba iya yarda da shi ba (tarayya da wata a kan Uwais), gara mata ranar mutuwar ta da
ganin wannan ranar.
Amrah ta dubi Antin ta Murja cikin karaya, ta ce, “Aunty Murja, ba ni ce abun ji ba, Daddy ne,
kuma dai kin san yadda karatun likita yake a kasar nan sai ka yi shekaru goma ma ba su
sallame ka ba, sannan gaskiyar magana Uwais yana da takura, mayata har da hayyata. Tafiyata
na dan lokaci ba ki ji hutawar da na yi ba da sararawar da na yi. Sannan ni ba zan iya karatu a
Kano ba, gaskiya na riga na saba da Malaysia�.

Aunty Murja ta ce, “To Bamaleshiya, haifaffar Malay, sai kuwa ki baiwa Uwais dama ya yi
aure shi ne kadai mafita ga matsalolin ku�.
Amrah ta kankance ido tana duban Murjanatu, ta ce,
"Over my dead body!".
Murjanatu ta ce, "Ki daina fadin haka kada ki fada da bakin Mala'iku Amrah, kuma ki mutun, a
zo a yi, gara ma a yi kina rayen, kowacce ta murza kambunta, in ya so wadda ta fi son mijin ta
kwace, don ina tantamar soyayyar ki ga Uwais idan ba ta fi cikin cokali ba. Ki yarda kin fi
muhimmanta karatu da aure Amrah. Sannan kina son kan ki da yawa, kuma irin ku masu gudun
kishiya an fi yi muku wallahi".
Maganganun Murja sun ki yi mata dadi ko kankami, domin Murjanatu irin mutanen nan ne masu
tsage gaskiya komai dacinta. Don haka Amrah ta tashi ta bar mata falon tana kunkuni, cikin
kunkunin fadin ta ke,
"Aunty Murja ba ta sonta, tunda ta ke mata fatan kishiya".
Murjanatu ta bi ta da kallo cike da tausayinta, ta san upbringing na gidansu shi ne babban
abinda yake wahalar da ita, ita ma haka ta sha wahala da Jabeer don shi cewa ya yi ko
haihuwa ba za su fara ba sai sun yi shekara goma da aure. So many challenges ta fuskance su
a kan Jabeer irin na Amrah a kan tsananin bokon su. Farkon aurensu ko sallar asubah sai ya
gama shirin ofis yake yinta don kada ya makara ofis. Sai da ta dage wajen kyautatawa da
lallashi cikin hikima ya koma yarda ta tada shi sallar asubah. Amma har yanzu in yana wasu
abubuwan za ka fahimci sun fi bai wa boko muhimmanci a kan addini.

Tana tausaya wa Amrah, musamman da ta fahimci weakness din mijinta, kwace mata shi daga
wajen sauran mata na ciki ko na waje ba zai zamo abu mai wahala ba. Wai Hausawa suka ce
kwace goruba a hannun kuturu ba wahala......

****


KHARTOUM
Ammi ce ta kira wayar Uwais ganin shiru-shiru har azahar ba su ba alamar su a main house. Ga
shi Mahdi ya ce mata Fahimah ce ba ta jin dadi, don haka hankalinta ya ki kwanciya sam.
Uwais na dagawa, ta ce, "Ya ya jikin Fahimah? Ko dai a kawo ni mu je asibiti?"
Uwais ya shafo lallausar sumar kansa cikin jin nauyi, ya ce, "Ammi ta wartsake fah, wanka ma
ta ke yi yanzun, muna nan tafe zuwa karfe hudu".
Ammi ta ce, "To alhamdu lillah, abinci fa?"
Uwais ya ce, "Kada ki damu Ammi na yi order a nan an kawo mana tun dazun".

Hawayen farin ciki suka cicciko a idon Ammi, don ta gama gane ciwon na Fahimah ta ce, "Allah
ya yi muku albarka Uwais, Allah ya jikan mahaifinka, yadda ka yi min biyayya Allah ya ba ka
masu yi maka, yadda ka faranta min kai ma Allah ya faranta maka".

Tunda yake da Ammi ba ta taba yi masa addu'ar da ya ji dadi, kuma mai tsayi kamar wannan
ba. Ko don ya ci gaba da samun wannan tofin albarkar ya yi alkawarin rike auren Fahimah da
amana da hannaye bibbiyu. A ransa fadi ya ke, "Ammi ai gata ki ka yi mun, you gave me a
precious gem, wanda ba zan gushe ba ina nema miki rahmar Ubangiji da gafarar sa a kansa.
Fahimah ta fito daga toilet, ta yi wanka amma ta dauko kayan da ta tube ta maka, kasancewar
ta manta bata shiga da wadanda za ta canza ba, kuma ba za ta iya fitowa daure da tawul a
gaban Uwais ba. Ya daga lumsassun idanunsa yana kallonta, her radiant black skin sai wani
sheki ta ke kamar ta matan kasar Ghana, ta wani fannin kuma Somalis. Ta fiddo doguwar riga
ruwan makuba kirar Dammam daga cikin kayan ta za ta saka, ba ta san lokacin da Uwais ya
taso ya iso gabanta ba.
Fuskarta da ruwa bai iya zama sosai sabida santsinta ya dan shafo, sannan ya hau kici-kicin
cire mata rigar da ta mako.
"Ya Uwais lafiya?"
Ta fada cikin kidima, don yanzu Uwais ya zame mata dodo. Yesterday night will forever remain
fresh in her memory kuma bazata gushe ba tana tuno komai da ya wakana cikin daren ba a duk
lokacin da Uwais ya kusance ta.
Cikin kokarin kwantar mata da hankali da rage mata karfin tsoron da ya gani cikin idanun ta a
kansa ya tausasa murya ya ce.
"Nothing as you expect, daga nan har dare kina da hutu, kawai kayan zan canza miki da kaina
don ki sani yanzu ke da Uwais, babu sauran shamaki, ki daina wannan nukunukun na canza
kaya a gaba na".
Fahimah ta runtse idanunta a lokacin da Uwais ya fidda rigar jikinta gabadaya ta saman kanta,

ya tsura mata idanu yana tazbihi ga mahaliccinsa. Ya juyo ta round sannan ya rungume ta. He
then began to kiss her passionately, al'amarin da bai tuke a ko'ina ba sai a tsakiyar gadon
barcin su. Hutun da bata samu ba kenan saidai wannan karon bata ji wahalar da tayi tsammani
ba, ya tafiyar da komai gently cikin nutsuwa da soyayya. Ba su suka tafi gidan su Ammi ba sai karfe biyar na yamma.
Ammi girki na musamman ta yi wa Fahimah da kanta, farfesun Zabuwa da ya sha kayan
kamshin larabawan Sudan, sannan kunun kanwa mai yaji da zafin sa, ta sa ta a gaba ta ce sai
ta shanye, kuma yanka daya ba za ta bari ba. Ba su kara ganin Uwais ba sai karfe tara na dare,
don sun je Oumdurman gaida wani kakan Ammi.
Yana shigowa dakin da suke da sallama dauke a bakin sa bayan dawowar su daga
Oumdurman. Fahimah ta kara mannewa ta lafe a jikin Ammi gabanta har lugulgude yake.
Soyayya kam ta ci gidansu, bata marmarin komai yanzu banda isashshen barci, yanzu Uwaisun
kam shi da dodo ba su da maraba a idon Fahimah.
Ammi ta ce, "Har an dawo? Ya ya ku ka baro mutanen Omdourman din?"
"Kowa lafiya Ammi duk suna gaishe ki, na gaji sosai Ammi, Oundurman akwai nisa".
Ammi ta dubi Fahimah da ta bingire a kasa tana barci. Ta ce,
"Ke kuma Fahimah barci haka kamar 'yar goye muna hirar mu yanzun nan?"
Uwais ya yi wani miskilin murmushi don ya san barcin karya ne Fahimah ke yi. Ammi ta soma
bubbuga ta,
"Fahimah-Fahimah, tashi mana ku tafi?"
Fahimah ta tashi tana mutsittsikar ido da turo baki ta ce, "Ammi ni a nan zan kwana, wallahi
Ammi ban iya takawa na gaji".
Uwais ya kanne ido guda a gaban Ammi, ya ce,
"Ba matsala, sai in dauke ki don dai zuwa mota?"
Kunya ta kama su daga ita har Ammin sai da ta yi da-na-sanin karyar ta, ya mike yana fadin,
"Ammi bar abincin nan, mun ci a Oumdurman. Idon na fita kuma, zan sha fresh milk a Fundaq".
Ammi ta ce, "Tashi ku tafi Fahimah kin ji? Kin ga gobe za ku koma gida akwai bukatar ki tattaro
kayan ki da kan ki, kada ya manta miki wani abu.
Amma Fahimah fir ta ki tashi, Ammi so ta ke Yaya Uwais ya karasa kashe ta da ranta, saboda
cikin al'amarinsa babu daga kafa babu tausayi ko jin lallashi. Ammi ta kada ta raya amma
Fahimah ta kafe abinda bata taba yi wa Ammi ba (musu) ta ce ita kam ta zo kenan, Nigeria ma
ba ta komawa sai tare da Ammi. Ya dauko mata abinda zai iya ya bar ragowar.
Tausayi ya sa Ammi ta kyale ta, ta kira Uwais wanda har ya shiga mota ta ce su tafi su bar ta,
ya taho mata da dukkan kayanta. Za ta lallaba ta gobe su koma gida tare. Bai ce komai ba
amma ya hassala, ya ce da Mahdi ya ja motar su tafi.

Cikin daren kuma Ammi ta dauki lokaci tana nusar da Fahimah akan aure, ta ce, "Wannan shi
ne ai auren Fahimah da manufar yin sa. Hakuri da juriya za ki sa a ranki, duk wata mace da ki
ka gani da 'ya'yanta abin sha'awa sai dai ta yi wannan hakurin ta same su.
A hankali za ki saba kin ji ko Fahimah ta? Lada ne babba ki ke samu a wurin Ubangiji wanda zai

miki silar shiga aljannah".
Sosai ta fahimci cewa cikin al'amarin Ammi Safeeyyah babu son kai ko son zuciya, face kauna
zallah ta fisabilillah da ta ke mata, shi ya sa ta ke so mata rayuwa da gudan jininta mafi soyuwa
a gare ta. Fahimah ta kwana addu'ar Allah ya ba ta lafiya, juriya da tsawon ran da za ta ci gaba
da kulawa da bukatar gangar jikin Uwais, da komai nasa, har zuwa ranar da ta daina numfashi.
******
Washegari suka yi sallama da kowa, bayan Ammi ta tsuma 'yarta ta gyare ta tas da gyara irin
nasu na Sudanese din asali. Jirgin karfe tara na safe suka biyo wanda zai sauka a Kano.

A cikin jirgi babu irin korafin da Fahimah ba ta sha daga Uwais ba a kan abin da ta yi masa
jiya, har da cewa,
"Me ki ka dauke ni ne? Wanda bai iya rayuwa sai da ke ko me? Dana kwana nikadai me
kika ga ya same ni? Karewa ma matata da na ke so ta dawo already, don ta bani kulawar da
duk nake bukata. Don Allah Fah-himah ki jika abinki ki shanye".

Fahimah ba ta tanka shi ba, amma ji ta yi gaba daya hankalinta ya tashi. Idan da gaske Amrah
ta dawo ita mene ne makomar rayuwarta?
Shin za ta iya sake barci a duniya ba tare da Uwais a gefenta ba? Ya sanya ta cikin wata
sabuwar rayuwa mai wuyar bari da wuyar mantawa. Ta yarda ashe a can baya So kawai ta ke
masa na fatar baki, yanzu ne ta san tana son Uwais har ruhi da bargon jikinta.
Idan kuwa abin da Ammi ta ce gaskiya ne (physical relationship between husband & wife).
Alamu ne na so, kuma ba ya faruwa sai da soyayya ko yaya ne, to ta yarda Uwais yana sonta
ko da bai furta a fatar bakinsa ba.
Ita kam ai yanzu kalmar kiyayyar Uwais ta daina razana ta, ta daina bakanta mata rai ko da zai
kwana yana fadi akan mumbari ta bakin Ammi, domin kuwa har kakannin I love you Uwais ya
gaya mata ba tare da ya san lokacin da ya fada din ba.
In haka ne ashe ita ma mutum ce, kuma mace mai daraja kamar kowacce mace duk da kalar
fatar tata, ba za ta kara bar wa Amrah miji ita kadai ba.
Da Uwais ya ishe ta da mita da korafinsa da ya ki karewa sai ta tashi tsam ta bar masa wajen,
ta koma can wata empty seat a cikin jirgin ta zauna. Tunda ya ambaci cewa Amrah ta dawo ta ji
ko muryarsa ba ta son ji, kallonsa ma bacin rai yake sanya mata.
Ya so ya bi ta inda ta koma ya ci gaba da damunta da complain don kuwa ba da wasa ba ya
azabtu a jiyan, ya ji haushin abinda tayi masa, yayi hakuri ne sabida Ammi, sai ya hango ta tana
share hawaye, duk kuma sai jikinsa ya yi sanyi, domin ya fahimci ko me Fahimah ta ke wa kuka
ba zai wuce RABUWAR SU ba tunda Amrah ta dawo. To amma shin yana da guts na gaya wa Amrah yana da wani auren, auren ma na wadda ya
taba kira ‘yar aikin gidansu? Ko kuwa shin zai iya jure rayuwa yanzu babu Fahimah?
Tsakanin ita da Amrah wacece ta fi muhimmanci ga rayuwar sa?

Tambayoyi ne da ba shi da amsarsu, kuma bai san amsar tasu ba. Sannan bashi da mai amsa
masa. Har jirgin su ya yi landing a Kano. A nan airport dama ya adana motarsa, ya je inda ya
bada ajiyar ya dauka suka wuto gida.

Baba Talatu ce ta bude kofar falo tana musu sannu da zuwa, ta karbi kayayyakin hannunsu,
Uwais ya wuce bangarensa, ita ma sai ta wuce nata dakin domin ta yi wanka ko ta warware
gajiyar da ke nukurkusarta.

Kafin ta fito Baba Talatu ta shirya musu abinci a dining mai rai da motsi, wanda ta yi musamman
domin tarbar su, sinasir ne da waina da miyar egusi wadda ta ji ganyen alayyahu da naman
rago. Fahimah sai ta samu kanta da zama ta tsantsara kwalliya ta gani ta fada da kyakkyawar
atamfa super Vlisco light blue. Wai aka ce in ba ka yi ba ni wuri, ba za ta kara bari a barta
matsayin ‘yar jiran gida ba.

Uwais ya fito bayan magriba ya canza zuwa kananan kaya, bakar riga ce shirt a jikinsa samfurin
Balanciaga da wando chinose, sumar nan ta sha wanki da arganavita ta kara baki sai sheki ta
ke. Da Fahimah ta daga ido ta dube shi sai da tsigar jikinta gabadaya ta tashi. Da ta tuna duka
wannan kwalliyar ta Amrah ce ba tata ba, sai bacin ran duniya da wani bala’e’en kishi
suka zo suka lullube ta.

Uwais gab da ita ya ja kujera ya zauna, kafadunsu na gugar na juna, sanyin kamshin (Maison
Francis) har cikin ruhinta. Ta lumshe ido sannan ta bude su a kanshi tana kallon sa da idanun
rauni, jin yana take mata yatsun kafa da nashi yatsun. Ya ce,
“Madame, ya ya kin gama shiryawa? Yanzu za mu wuce faâ€?.
Fahima ta zaro sparkling eyes dinta a kanshi cikin rashin fahimta, Uwais ya gyada kai cikin
tabbatar mata.
“Tare za mu tafi Fahimah, gidanki za ki koma!â€?.
Sai ta ji tamkar an yi mata rahma, duk da bata da niyyar bin nasa, at least ya nuna yana son
zama da ita koda bata bishi ba, tamkar ya yaye mata wani nannuyan dutse daga kirjin ta, duk
wata damuwa da wani bacin rai sai ya kau. Ta ji kamar ta rungume Uwais, amma ta kwabi kanta
da ta ja ajinta. Girgiza kai ta yi, “Babu inda za ni Yaya Uwais babu sanin Ammiâ€?.
Uwais ya juyo sosai ya sanya fuskar Fahimah cikin tafukansa biyu, ya sumbaci lebunanta
keenly, skyblue kwalliyartacikin atampa ta yi mishi kyau ba dan kadan ba, ta kara fiddo da
ainahin kalar fatarta mai kyau da ilhamar ta.
Ya ce, “Idan kuma Ammin ta dawo ta ce na barki ke kadai fa?â€?
Da sauri ta ce, “Ba komai, zan zauna, ai ga Baba Talatu ta dawoâ€?.
“Are you sure za ki iya barci?â€?
“Sure, I wouldâ€?.
Sai ga hawaye kuma sun zubo.

Uwais ya sanya babbar dan yatsansa ya lakato hawayen, ya ce,
“Wannan fa na mene ne?â€?
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Uwais ne a gaba, Fahimah na biye da shi a baya suka ratsa ta
tsararrun falullukan Amrah, a falo na karshe ya ce ta zauna don yana kyautata zaton Amrah ta
yi barci.

Amma da ya daga labulen bedroom dinta sai ya same ta tana sallah, wadda bai san ta nafila ce
ko isha ce ba.
Ya zauna a gefen gadonta har ta idar. Tun tana sallar ya fahimci ta kai hannu ta toshe hanci,
tsaki ya yi ya ce,
“Amrah why? Wai a kanki aka fara ciki ne? ko ko naki ne ya fi na kowa tsurfa?â€?
Ta sallame sallarta tana kallonshi cikin haushi, ya je ya dade ya yi dare son ransa kuma ya zo
yana mata zancen wofi, zuciyar mai ciki da ma a kusa ta ke, ta ce,

16 / 20