FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 20

15K to 18K   out of 59.2K words

mara asali? Kamar matan Sudan da na Najeriya sun kare?
Uwais ji ya yi kamar Kawunsa ya yayyafa masa ruwa a kan wutar da ke tiriri a kirjinsa, ya ce,
Kawu na saya maka tiket, don Allah ka zo a yi ta ta kare. Kai kadai ne last hope dina Kawu, don
Allah ka taimaka min ka gaya wa Ammi ta aura min mata hudu a rana daya in dai da Amrah a
ciki, amma ta cire wannan yarinyar a cikin su zan iya hadiyar zuciya na mutu. Da sauri Kawu Shuraim ya ce, Zan zo cikin satin nan insha Allahu, abin bai kai haka ba, ka
kwantar da hankalinka.

Ammi ba ta san me suke kullawa shi da Kawunsa ba. Yanzu ta fara maida walwalarta tana
harkokinta cikin gida, amma ta cire Uwais daga shirginta, musamman da ta lura shi ma ya dauki
gaba da ita. Damuwarta yanzu a kan Fahima ne, wadda ke ta faman ramewa babu gaira babu
dalili, kuma ba ta son cin abinci. Ga jarrabawarsu ta barin sakandire na tunkaro su. Wajen karfe goma na dare, Ammi har ta yi barci ta farka, so ta ke ta binciki halin da Fahima ke
ciki a daren nan. Ta sauko daga gadon ta a hankali ta daura laffayarta kamar wadda za ta
unguwa, sannan ta nufi dakin Fahimah.
Tun daga bakin kofa ta ke jiyo shesshekar kukan Fahimah ta karasa da sauri ta murda kofar ta
shiga. Ta kifa kai a kan filo ta dunkule jikinta sai kuka ta ke. Sai jin muryar Ammi ta yi a kanta.
Fahimah! Yau sai kin gaya min abin da yake damunki. Wani ke yi miki abin da ba ki so cikin
gidan nan ko kuwa kin gaji da zama da ni ne?
Fahimah ta dago a hankali cikin tsananin faduwar gaba, ba ta taba tsammanin Ammi a wannan
lokacin ba, she will never shed tears a gaban Ammi, don haka tashin hankalinta a yanzu shi ne
ganin kukanta da Ammi ta yi fiye da damuwar da ta ke ciki.
Hajiya Safeeyyah ta zauna a gefen gadon ta ce, Fahima ta ba ki da wanda ya fi ni duk fadin
duniyar nan, don haka daure ki gaya min ko mene ne damuwarki, na yi miki alkawarin sai inda

karfina ya kare wajen sama miki farin ciki, don ke amana ce a hannuna fiye da wannan yaron,
kuma amanar ce tsakanina da ke, ki gaya min ko mene ne Fahimah ta.
Fahima ta riga ta kudire a zuciyarta sai dai ciwon son Uwais ya yi ajalinta, amma ba za ta taba
furta hakan ga kowa ba balle mahaifiya a gare shi. Idan ta tursasa shi ya aure ta to ta kai shi
ina? Mutum gashinan kamar malaikan daukar rai wane dadi mace za ta ji a aurensa? Macen
ma wadda ya fi tsana fiye da kowa a duniya? Don haka ta soma tunanin abin da za ta fada wa Ammi ba tare da ta sanya mata kokonto ba.
Abubuwa da yawa na damunta, not only UWAIS SHAGARI. Tana son sanin asalinta, tana son
sanin su waye suka yi sanadin zuwanta duniya. Ammi ba ta son tambayar nan ko kankani,
amma yau dole da ita za ta bi ta kare kanta da mutuncinta a idanun Ammi Safiyyah. Ammi, babu ciwo mafi muni ga dan Adam irin a ce ba ya da asali, bai san su waye suka haife
shi ba, bai san shi dan sunnah ne ko shege ba. Ammi ko ba ki fada ba na dade da ganewa,
orphanage da muke zuwa shi ne gidanmu, shi ne asali da tushe na, a can ki ka dauko ni.
Ta karasa cikin wani irin kuka da ya keta har cikin zuciyar Hajiya Safiyyah.
A yau ita kanta Ammi ta rasa da kalaman da za ta lallashi Fahimah, ta fahimci irin ciwon da ta
ke ji a ranta, kuma ba ta isa ta warkar mata da shi ba. Kama ta ta yi ta rungume a jikinta ta ce,
Fahima, in kin yarda ni ma UWA ce, sannan kokarina ya kai na kowacce UWA, to ki dubi Allah
ki cire wannan damuwar daga ranki. Im your mother, father and Uwais is your brother. Ki sani
babu wanda rayuwa ta ke cikakka a gare shi, babu kuma wanda Ubangiji ba ya jarraba in one
way or the other.
Mumini an sanshi da karbar kaddarar Ubangiji da kasancewa cikin godiyarsa ala kulli halin.
Wannan damuwar da ki ka sanya kanki babu abin da za ta janyo sai nakasu ga lafiyar zuciya da
kwakwalwar ki.
Insha Allah wata mai kamawa za mu je Umrah mu yi ibada mu nemi kusanci da Ubangiji, za ki
samu sukunin zuciyarki insha Allahu.

Haka Ammi ta yi ta lallashin Fahimah, da kalamai masu dadi da nuna kauna har sai da ta sanya
murmushi a kan fatar bakinta.

******
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kafin muryarsan nan mai tada tsigogin jikinta ta biyo baya. A yau
har wani kauri ta kara mai nuna ya zama cikakken mutum. Wanda ya gama mallakar duk abinda
da Da namiji ke bukata a rayuwar sa. Ta juya a hankali ta dube su da fararen idanunta suna
shigowa, hannun su cikin na juna sun yi balain dacewa da juna, kyau na bugun kyau. Ko
hasidin iza hassada ya kalle su sai ya yaba su a ransa. Wani abu wai perfect match. Da gaske
KISHI gaskiya ne a tare da kowacce diya mace, kuma Fahimah ta ji shi a kirjinta har fiye da
misali, yau ga ta ga matar Uwais! Wadda ta dade tana kimanta zuwan ranar haduwar su da
juna, amma murmushin da Amrah ta yi mata da innocence looks dinta sun sanya Fahimah
mayar mata da martanin murmushinta. Ta kuma amsa sallamarta. Sannan ta maida kai ga
abinda take yi bata kara kallon su ba.
Uwais kamar ya fashe don bakin ciki don bai so Amrah ta ganta ba shiyasa ya kawo ta da safe,
lokacin da ya tabbata tana barci. Bayan sun wuce falon zuwa falo na gaba Amrah ta juya tana
kallonsa da sigar da ta ke kallonsa, wadda ta bambanta da yadda ta ke kallon kowa, ta ce,

Ina ku ka samo kyakkyawar budurwa haka? Ba ka taba gaya min kana da sister ba. Cikin
harshen Turanci ta yi maganar.
Fahimah daga inda ta ke tsaye tana jiyo shi yana bai wa matarshi amsa da cewa, Mai aikin
Ammi ce.
Suka wuce turakar Ammi, Amrah na waiwayonta tana ta mata murmushi, sai ta samu kanta da
kasa maida mata martani sakamakon zuciyarta ta yi bakikkirin da jin amsar da Uwais ya bayar a
kanta. Daga bisani ta yi murmushi mai ciwo, cikin ranta ta ce, ban da abun ki Fahimah, don
Uwais ya ce ke yar aikin gidansu ce ai ya kara miki matsayi, tunda bai ce da matarsa tsinto ki
suka yi a gidan marayu ba. Maganar a ce ita matarsa ce ma ba ta taso ba.
Ta ci gaba da daukar aure a tsakaninsu a matsayin shifcin gizo, zai fi mata sauki; wato irin
almarar nan mai zuwa ta wuce wa dan adam yadda kowacce almara ke zuwa ta wuce, haka
aurenta da Uwais zai zo ya wuce ba tare da ya zama actual reality ba.
A hankali ta zame jiki daga wurin zuwa dakinta tana cewa cikin ranta, ina ma ita ce Amrah?
Watakila da ita ce ke da kyan da Amrah ke da shi da Uwais ya so ta. Ta yi maza ta kwabi
zuciyarta a kan hakan.
Shes proud of her own beauty no matter what, watakila ko da ta fi duk matan duniya kyau
asalinta ma kadai ya isa ya sa Uwais ya kyamace ta. Don haka Fahimah ta soma kallon aurenta
da Uwais a matsayin dabaibayi rather than defensive kamar yadda Ammi Safeeyah ke kallonsa.
Anya kuwa tunani da tsinkayen Ammi a kansu daidai ne? Ta yi ta zama da igiyar auren Uwais a
kanta kenan don kawai a kira ta matarsa? Anya auren bai zame mata dabaibayi ba ya hana ta
yancinta na yammatanci? Ko da ta ke yar gidan marayu in da Ammi ta yi hakuri ba za ta rasa
me sonta a duniya ba, ko ta auri orphan dan uwanta a gidan marayun, soyayyar da zuciyarta ke
yi wa Uwais da ma mai zaman kanta ce. Da Ammi ta yi hakuri ba ta yi amfani da karfin ikonta na
uwa ba wajen ganin Uwais ya aure ta ba, da sannu za ta iya overcoming dinta (rinjayarta).
Haka ta yi ta saka da warwara ita kadai a daki tanajuyejuye akan gado, idan ta ce ta yi watsi da
alamarin Uwais, idan tsautsayi ya gifta suka hadu ko yaya ne, tofa dole sai zuciyarta ta motsa.
Daga nan ta gane cewa soyayyar gaskiya abu ce da zuciya ba za ta iya kaucewa ba. Saidai ayi
mata pretending. Amma daga yau da Uwais ya gaya wa matarsa ita yar aikin gidansu ce, daga
yau za ta soma yaki da duk wata soyayyar UWAIS daga zuciyarta, ko da kuwa da karfin
addu'ah ne.

******
Amrah ba ta samu wata special reception daga Ammi ba, daga gaisuwa shi ke nan, ta ce,
In ce ko ba matsala?
Amrah ta ce, Babu Ammi.
To Allah ya yi muku albarka.
Daga haka ta shiga wata hidimar a daki. Ta dai fahimci Amrah za a zauna lafiya da ita daga
dukkan alamu, bata da kwaramniya kuma bata da girman kai ba kamar sauran yayan masu kudi
irinta ba, shes very simple a cikin muamalarta da kowa.

Tunda suka dauko hanyar komawa gida, Amrah ke zubo wa Uwais tambayoyi duk kuma a kan
Fahimah, shi kuwa komai ta tambaya cewa yake bai sani ba. Yadda ta ga yarinyar shi ma haka
ya ganta a gidan.

Amma wallahi Habib-Qalby ba ta yi kama da yan aiki ba. Zubinta irin na matan kasar Sirreleone
irin kalar fatarta nake burin ina ma in samu. I hate so much brightness. Ga dasashin cikin bakin
ta irin wanda nake shaawa, da a ce ni mazauniya ce da na roki Ammi ta bar min ita, I just like
the girl. Uwais dai sai "umh" yake cewa, yana ci gaba da tukin motarsa cikin nutsuwa har suka isa gida.

Sun yi shirin kwanciya ya shigo dakin Amrah da zummar yin wani abu, sai ya ganta tana kora
magani a bakinta. Da sauri ya idasa shigowa dakin zuwa gabanta.
Lafiya Amrah? Ba ki da lafiya ne?
Ta ce, No, lafiyata kalau. Contraceptive pills ne nake hadiya sabida su aka min recommending
kan cewa sun fi rashin illah ga wanda bai taba haihuwa ba.
Tunda Uwais ya hadu da Amrah daga dating (soyayya) zuwa aurensu ba su taba samun sabani
ba, bai taba jin haushinta a ransa ko miskala zarratin ba. Amma yau ya ce,
Amrah!
Cikin kakkausar murya.
Zan amince da komai, karatu a Malaysia, amma ban da a dinga zubar min da kwayayen
haihuwata. Ban sani ba ko iya su Allah ya yi nufin ba ni a duniya.
Amrah ta dube shi tana kankance idanu, Habib-Qalby, me ka ke nufi ne? Ina MBBS student in
haihu yanzu? Kwata-kwata nawa nake? Ko shekaru ashirin ban rufa ba, ni karatuna ya fi min
komai muhimmanci, wallahi...
Uwais ya yi mata wani irin kallo, ya ce, Har da ni Amrah?
Ai da abuna ka gan ni ka aure ni, ban ga dalilin da zai kai ni haihuwa yanzu ba.
Uwais ya yi sake da baki yana kallonta. Rana ta farko da ya soma tunanin anya nan gaba zai
iya tankwara Amrah? Yayi sake tun farko. Anya bai yi kuskure ba da ya nuna wa Amrah
matsananciyar soyayya a fili? Juyawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, zuciyarsa na tafarfasa.
Ba abin da yake so a duniya irin haihuwa, kasancewar shi daya tal! Allah ya bai wa
mahaifiyarsa. Yayan da yake burin haifa su yake fatan su zamo masa yan uwa. Ashe Amrah
rariya ta ke kora su.
Don haka kwanaki biyu da suka biyo baya ya dauke wa Amrah wuta, amarci da soyayya sun
tsaya, wanda hakan ya jefa Amrah a damuwa. Amma abinda yake so da ita ba mai yiwuwa ba
ne. Ya za ta yi da Da alhalin tana karatu a wata uwa duniya?
Sai yanzu ya fahimci cewa, ashe dai duk son da yake wa Amrah har gobe yana nan a
Uwaisunsa. Murmushinsa duk ya tsaya, haka yawan sakewar da yake wa Amrah.
Damuwar da Amrah ta shiga ba ta misaltuwa, musamman da yake Uwais ya koyar da ita wata
irin soyayya mai wuyar bari, yanzu ya dawo ya koma tamkar ba shi ba, ita kuma ba za ta iya bin
raayinsa ba.
Aunty Murjanatu ta kira domin neman shawara tana kuka, Uwais have changed completely,
haihuwa yake so Aunty Murja, ni kuma ban shirya ba. Ya kasa fahimtata, akalla ina bukatar
shekaru biyar nan gaba kafin na amince na fara haihuwa.
Murja ta ce, Amrah in kina son kwanciyar hankali a gidan aurenki ki bi abin da mijinki ke so, tun
ba ki yi sanadin da dimbin soyayyar da yake miki za ta ragu ba. Komai na Allah ne, ke ba ki isa
ki tsarawa kanki rayuwa ba sai abin da Ubangiji ya tsara miki, haihuwa ba ta hana komai sai ki
dauki Nanny.

Da haka Murjanatu ta samu ta rarrashi Amrah ta kuma tabbatar mata a daren yau za ta je ta bai
wa Uwais hakuri.
Shiri na musamman Amrah ta yi zuwa dakin Uwais cikin wasu tausasan nighties. Uwais na
loosing tie din wuyansa bayan ya dawo aiki bai ji motsin shigowar Amrah ba, sai ji ya yi ta
rungume shi ta baya, kamshin sassanyan turarenta Yves Saint Laurent da sulbin hannunta su
suka gaya masa ita ce. Ya lumshe ido yana tuno wahalar da ya sha a kwanakin nan da ya hora
kansa da rashin Amrah.
Zai iya cewa shi ne horo mafi muni da ya taba karba a rayuwar sa bayan horon auren Fahimah
wanda sanadin auren Amrah ya ja masa, amma ya fiye masa a kan ya biye wa abin da Amrah
ke so. Ko Ammi ta ji za ta kara tsanarta ne a kara lika masa wannan abun aman (Fahima). Shi
kuwa da wani abu makamancin auratayya ya shiga tsakaninsa da Fahimah gara ya koma mace
(ya yi losing manhood dinsa).
Im sorry Habeeb-Qalby, something like this will not happen again I surrender.
Murmushi ya yi, ya janyo ta ta dawo gabansa, wani irin kissing dinta ya shiga yi, passionately,
ya ce, Amrah in ki ka ba ni Da, kin gama min komai a rayuwa, ni ko ba za ki shayar da shi ba ki
haifa ki ba ni abina, zan bai wa Ammi na ta kula min da shi.
Amma in ki ka ce sai kin zama likita za ki haihu Amrah ai zuwa lokacin na soma furfura ina
neman abokin tafiya masallaci ne. Zan taya ki raino ke har nakudar in ba ki so na yarda ki yi
epidural. Ni dai burina in haihu da ke Amrah ko sau daya ne a rayuwa sabida son da nake miki.
Yatsunta ta kai ta toshe masa baki, Na amince Habib-Qalby, Im now ready to conceive, kuma
tare za mu raini dan mu ko yarmu insha Allahu, zan raba lokacina biyu in ba ku rabi, ka taya ni
addua Allah ya ba ni kafadar dauka...
Da sauri Uwais ya ce, Lah yukallifullahu nafsan illa wusaha. Maana, Allah ba ya dora wa wata
rai face abin da za ta iya. Ke mace ce Amrah, kuma mace da aure da haihuwa a ka santa, don
ita jaruma ce fiye da namiji, boko shi ne last priority hidimar aure tana kan gaba da komai.
Amrah don ita ce hanyar shiga aljannah. Daga haka Uwais ya canza akalar hirar zuwa mafi aala a gare shi. Sumbutarta yake kusfa-kusfa
kamar zai hadiye ta.
Ya yi kewar Amrah a kwanaki uku kacal yadda biro ya yi kadan ya bayyana, haka ita ma sai da
ta ji idanunta sun cika da hawaye don tausayin Uwais, domin ta lura ba karamin azabtar da shi
ta yi ba. Addua ta ke, Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran da za ta ci gaba da kulawa da bukatar
gangar jikin Uwais da lafiyar haifa masa yaya, ta yarda Uwais mai sonta ne, mai kuma matukar
kaunarta wanda ya bambanta da sauran maza a halayya da dabi'a wajen nuna wa matansu
soyayya a fili, abinda maza da yawa basa iyawa a wannan zamanin sabida girman kai.
Alhaji Umar Dikko ya raini yayansa ne da tarbiyya ta ilmin boko zallah don haka ya;yan gidansu
duka sun fi fifita boko a kan komai. Abin da Uwais ya lura da shi ke nan da ya sa yake ta yi wa
Amrah uzuri a bisa sababbn dabiun da yake ta gani a tare da ita, wadanda suka sabawa nashi
upbringing din. Alal misali, Amrah ba ta canza daga irin shigarta ta baya ba, wadda ta ke yi kafin
aure ta dan kankanin gyale, hira da abokan karatunta maza, ta waya duk sanda take so, girki
ma kuma ba kullum ta ke yi ba yanzu, in kuma ta yin, to sau daya a rana, sannan kuma very
simple wanda ta tabbatar ba zai wuce mata minti goma ba, haka Uwais yake hakuri da
abubuwa da dama bayan wadannan wadanda yake ganin sun sha bamban da na gidan da ya
fito.

Su ma yan boko ne, amma ba masu dabiun nasara ba. Uwarsa is an Associate Professor.
Amrah ko a ina ta ke za ta iya bude lemo ta sha a tsaye haka yanayin dressing dinta ba ka iya
bambance shi da na budurwa mara aure. Wani abun ko ya gyara mata in bai yi daidai da raayin
gidansu ba, ba za ta yi ba.

6 / 20