Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
Amrah ya daina sa ta a lissafi don ta gaya masa ya daina takura mata da kiran waya, da
jidalallen cikinsa za ta ji mai tsirfar tsiya, ko da karatun da ke gabanta? A lokacin da ta gaya masa hakan, ransa ya yi matukar baci, ba ta ma tsaya ba ta saurari abin
da ya kira ta ya fada mata ba ta fadi hakan, dama ya kira ta su yi sallama ne a kan tafiyarsa
Switzerland. Don haka sai kawai ya sauke wayar daga kunnensa ba tare da ya ce da ita komai
ba. Yasa a ransa ba zai kara kiran ta ba har ya bar kasar Switzerland.
Kwanaki uku da yin hakan ta kira shi at her leisure time, shi kuma ya ki ya dauka. Sai ta turo
text na ban hakuri da kalaman soyayya, ko kula ta bai yi ba, hankalinsa kacokam ya koma kan
wadda ta ke da lokacinsa, wadda ita ko karatun ta ke yi ya kira ta za ta tsaya ta saurare shi, ita
a kan karan kanta Fahimah tana kiransa idan kewarshi ta dame ta, wani abu da Amrah bata iya
ba. Fahimah ta kan kira shi a lokacin da ta tabbata ya bar ofishin su na World bank zuwa
masaukinsa.
A wannan dan tsukin Uwais ya tantance da abu guda, gara ka auri matar da ke matukar sonka,
a kan ka auri wadda ka ke matukar so. Domin ita wadda ka ke matukar so, in ta gane za ta yi ta
wahalar da kai ne.
Ita kuwa wadda ke matukar son ka, ko da daga baya ka zo ka kaunace ta da dukkan zuciyarka,
ita a wurinta ka yi mata favour din ta ke kallonta as fortune. Probably zata yi hakuri da kai akan
komai cikin kowanne hali. A typical example of Fahimah a gare shi.
Sannan duk abin da yake hangowa a Amrah, sai daga baya ya samu kyal-kyal banza ne, farar
fata kam akwai ta da dogon gashi, sannan âyar babban gida ce, âyar manyan 'yan bokon
kasa. Amma a mua'amala ta auratayya ya fi samun nutsuwa da satisfaction daga mara
kyale-kyalen 'yar marainiya wato Fah-himah. Su âyaâyan manyan mutanen sai mulki da iko da kansu. Ba kuma yadda za a yi da su.
Cikin biyu ne ko daya; ko ka yi hakuri da su as they are ka nema wa kanka wata madafar, ko ka
hakura da aurensu ba su da damuwa, domin suna hango wanda ya fi ka a komai. They may
find thousands of you....
Wannan ya taimaka gaya wajen dusasar da tauraruwar Amrah daga zuciyar Uwais, ya dai saka
a ransa ko me za ta yi masa ba zai sake ta ba. Don kuwa yana sonta har gobe. Amma
zuciyarshi na kuna in ya tuna boko ya fi shi muhimmanci a wurin Amrah kuma za ta iya zabar
karatun ta a kan aurensa.
*****
Fahimah, ta ci gaba da zuwa makaranta don bayan sun gama exams ba su samu hutu ba
zarcewa suka yi da sabon zango. Tafiyar Uwais ta samar mata da nutsuwa domin a da kullum
cikin damuwa ta ke da takunkumin Ammi a kansa duk da bata nunawa, wanda ya maida shi
Uwais dinsa na baya mara walwala, mara kula kowa.
Zuwan Fahimah cikin rayuwarsa ya canza da yawa daga cikin odd behaviours dinsa, ya
fara zama jovial har kafin Ammi ta sanya masa get da kebewa da Fahimah.
Ammi da kanta ta fahimci walwalar da Uwais ya shiga a baya na da nasaba da samun hadin
kan Fahimah da ya yi a Sudan, sannan walwalar ta ragu, da ta ce sai ya gama gini, ya kuma
gaya wa Amrah gaskiya, sannan zai sake mallakar Fahimah a matsayin matarsa. Ba ta
regretting decision dinta, domin ta ga yadda Uwais ya maida hankali a kan gininsa da kuma irin
kudin da yake kashe wa ginin ya tabbatar mata Fahimah ta samu kyakkyawan matsugunni a
zuciyar Uwais.
Fahimah Shagari, dalibar tsimi da tanadi, ga ta da uwa farfesar tsumi da tanadi, idan suka dawo
gida babu abin da Ammi ke yi sai koya wa Fahimah economics, assignment, test da statistics
duka Fahimah ba ta da matsalarsu. Da aka yi jarrabawar zango na farko Fahimah 4.50 ta fito da
shi.
A hakan ma sai da Associate Prof. Safeeyyah Shagari ta yi wa Fahimah korafi cewa tunanin
Uwais ta ke, shi ya sa aka kada ita maki 50 daga cikin CGPA din ta, bata tunanin cewa shi yana
can yana kara gina kansa? Zata zauna ta maida kanta baya a kansa.....
Fahimah sai ta yi murmushi kawai, don ita wannan makin ma da ta samu bata zaci za ta same
shi ba. Da gaskiyar Ammi duk abinda ta fada ahaka yake. A kullum sallamarsu da Uwais ta ke
tunawa which was so emotional; ya nuna mata kauna da soyayya mai tsayawa a zuci, mai
kassara diya mace, wadda ta bar ta emotionally disturbed. A haka watanni uku ke gangara musu da ci gaba da nasara a tare da kowannensu. Dukkansu
are goal oriented musamman Amrah is very determined.
Wannan ya sa ta manta da mijin gabadaya, in har ba ta kalli zungureren cikinta bama ba ta tuno
shi, shi ma ya yi banza da ita, don duk wata kulawa da yake so yana samu daga Fahimah cikin
dare ta waya. Maganganun da Uwais ke wa Fahimah a waya na sanya ta a wani hali na
tsananin kewarsa, ta ji ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganshi tare da ita.
Amrah ta shiga edd dinta ana saura sati biyu Uwais ya dawo daga Switzerland, kuma an yi
saâa lokacin suna gab da zana jarrabawa, don haka iyayenta cike da bacin rai suka ce ta
taho Abuja, wata shekarar sai ta zana din. Ko kadan ba sa murna da wannan haihuwa ta Amrah
ba ta cimma komai a rayuwa ba (a cewar Aunty Wasila). âKe dabbar ina ce ki ka yarda ki ka dau ciki a wannan lokacin kamar wadda ba ta je
makaranta ba?
Ba ki san dan contraception na zamani ba? Ai shi ke nan sai ki yi deferring karatun ki zauna
kula da jaririn Uwais, ba ki ganki ba duk kin bi kin tsofe daga aure shekara dayaâ?.
In ji Aunty Wasila ranar da Amrah ta sauka a gidansu da ke Apo.
âHasbunallahu wa niâimal wakilâ?. In ji Jabeer da ke shigowa, âWasila, kina tsoron
Allah kuwa? Kina son gamawa da duniya lafiya? Sunnar Annabin ki ke wa wadannan munanan
maganganun haka? Ni dai wallahi Daddy ya cuce ku, kwata-kwata hanyar da ya nuna muku ta
saba wa addini, da ba a yi auren ba a haife ku? Ko da an haifeku ba aure zaku so hakan? Zina
ta yi ta samu cikin ko kuwa da kike mata wannan titsiyen?
To ahir dinki a kan dan Uwais, don wallahi a kan wannan cikin daga ke har Amran zai iya daure
ku har sai igiya ta yi rara!".
Wasila ta zumbura baki daidai lokacin da Mamansu ta shigo. Ta ce, âAmrah me ki ke so a
dafa miki?â?
Amrah wadda idonta ya cika da hawaye ta ce, âMama ki yi min tsakani da Aunty Wasila,
cewa nake ita âyaâya uku gare ta? Ina ruwanta da cikina da za ta ce min dabba a kansa?
Aure fa nake yi ba zina ba, ban ga dalilin da za a ce za'a bani query don an ganni da ciki baâ?.
Mama ta kyabe baki, ta ce, âmasu aure manya, ke ki ka ga za ki iya, da ma Daddy ya ce
yaron nan ya gama da ke, in ba a yi wasa ba karatun likita sai dai a ga kannenki da shi ban da
keâ?.
Amrah ta fashe da kuka, ta ce, ta fasa haihuwa a gidan kada ta haihu su bi dare su kashe mata
da, ta fuskanci duk ba sa son Uwais ita kuma tana son kayanta.
Mama ta ce, âKi fi ruwa tafiya, muna nan za ki dawo mana in dai namiji ne. Namijin ma irin
wannan kallelen mai idanu a tsakar ka, daga ganinshi womaniser neâ?...â?.
Amrah hannu ta sa ta toshe kunnuwanta, ta rasa me Uwais ya yi musu haka, daga Yaya Jabeer
sai Aunty Murjanatu ke kaunar aurenta, amma a ce har uwar da ta haife ka?!
Womaniser! Kalmar tayi tsauri da yawa a alaqantata da mutum mai daraja da mutumci irin
Uwaiss.
Wannan bakin cikin ya sa washegari ta tattara kayanta sai Kano. Ga shi tana cikin EDD bai
kamata ta yi doguwar tafiya ba, amma da ta haihu a gidansu ta gwammace ta haihu a hanya,
babu mai taba mata Uwais ta kyale.
Ko da Daddy ya dawo Mama ta gaya masa Amrah ta yi fushi ta tafi, ta fasa haihuwa a gabansu
don kawai Wasila ta gaya mata gaskiya, ta kwashe duk yadda aka yi ta gaya masa.
Daddy a take ya dau waya ya kira Amrah, lokacin suna gab da shiga Kano ita da direban gidan
su. Ya ce, âAmrah?â?
Ta ce, âNaâam Daddyâ?.
Ya ce, âkada ki sake in kara ganin kafarki a gidana, in kin haihu kuma babu wanda zai zo ki je
ga ki dangin miji su yi miki komai da uwarki zata yi miki, ga da namiji nan don soyayya ku wuce
Indiaâ?.
Amrah ta bude baki za ta yi bayani, Daddy ya ce, âBana son jin komai, tunda duk abin da
muke hango miki ba kya hangowa, weâre talking of your future which is ruined nowâ¦â?.
Kuka Amrah ta fara tana ba shi hakuri da kyar ya hakura, amma ya ce ba za ta haihu masa a
gida ba. Amrah ta ce,
âNa ji na yarda, amma don Allah ka yi hakuriâ?.
Ya kashe wayar ya rabu da ita.
Jiki a sanyaye ta isa Kano, sai ta rasa ina za ta dosa, ba ta iya zama gidan ba Uwais, don haka
ta ce da direba ya wuce da ita âYankaba.
Ammi da Fahimah na zaune suna karatu a falo, assignment na Fahimah suke solving. Ammi na
nuna mata. Sai sallamar Amrah suka ji ta shigo tinkis-tinkis da tirtsetsen cikinta.
Gaba daya suka hada baki wajen cewa, âMaraba da mutanen Malaysiaâ?.
Talatu ta shigo da jakar kayanta, wadda Maigadi ya shigo da ita. Fahimah ta karba sai ta wuce
da ita nata dakin. Ammi babu sakewa sosai tsakaninta da Amrah don haka gaisawa kawai suka
yi, da tambayar bayan rabo. Fahimah kuwa tuni ta tafi kitchen don hado mata abinci da abin
sha.
Har dare Amrah na zuba idon ganin ta inda Uwais zai bullo su wuce gida, amma shiru ka ke ji
har karfe goma. Fahimah sai hidima ta ke da ita, dauko wannan miko wannan, da ta ga ta fara
hamma daga zaune ta ce,
âAunty Amrah ko za ki shiga daga ciki ki kwanta?â?
Ganin idon Ammi ya sa Amrah ba ta furta damuwarta ta rashin ganin Uwais ba, ta bi shawarar
Fahimah, domin sosai take son kwanciyar, suka yi sai da safe da Ammi, sannan ta bi bayan
Fahimah zuwa dakinta.
Fahimah tuni ta gyara mata gadonta, ta ce ta kwanta a gadon don ta fi jin dadi ita a kan
lallausar bargo da ta shimfida a kasa za ta kwana.
A lokacin ne Amrah ta tambaye ta ko Uwais sai karfe nawa yake shigowa?
Fahimah ta juyo tana kallonta da mamaki, ta kasa cewa komai. Ita ce za ta gaya mata mijinta
bai kasar? Abu wajen watanni biyu? To ba sa waya ne?
A karshe ta ce,
âNa ji Ammi ta ce, yana Switzerlandâ?.
Amrah ta zaro ido cikin kidima, Fahimah ba ta bi ta kanta ba ta ci gaba da shirin kwanciyarta.
Wajen sha biyun dare Amrah tana barci wayar Uwais ta shigo wayar Fahima, kuma wayar tana
kan bedside daidai inda kan Amrah ke kwance. Hasken wayar ne ya dame ta ta dauka don ta
mika wa Fahimah don da alama ta yi barci, amma hoton da ya fito kan fuskar wayar ya sa ta
mamaki hadi da bayyanar lambobin da daga gani ka san na kasar Switzerland ne.
Abu biyu ya sa Amrah jin gara kawai ta amsa wayar nan. Don hankalinta ya kasa tsayawa waje
guda. Dalilin Fahimah na dora hoton Uwais a kan lambarsa, da irin tune din da kiran ke
bayarwa, sannan uwa-uba wane Yaya ne zai kira âyar uwarsa late at night haka? Lokaci ne
na masoya da ma'aurata bana âyan uwa ba. Kawai sai ta amsa wayar ba tare da ta ce komai ba. She just want to confirm it's Uwais ko ta
samu nutsuwa.
Muryar Uwais tar-tar cikin yanayin da ke nuna akwai marital intimacy (sexual bond) ya ce,
âFahhima na kasa barci, wallahi hakuri na ya kare. Jiya saura kadan in maimaita irin laifina
na Sudan, na ji tsoron Allah na ji tsoron fushin ki, musamman da na tuna tsiwar da ki ka yi min
a ranar da tsanar dana gani cikin kwayar idon ki, na ce gara in rufawa kaina asiri in kashe ko
nawa ne in miki ticket da visa ki zo min ko na kwana uku ne don Allah Fah-himah kada ki ce
min a'ah, Iâm missing everything, the luscious and succulent lips, your sweet...â? kalmar
karshe da ya fadi ya sa Amrah gigicewa don ko ni ban iya rubutata, wani karfin gwiwa ya zo
mata.
A nitse ta ce, âBa FAHHIMAH ba ce, AMRAH ceâ¦â?. Sannan ta kashe wayar silently.
Ta koma ta jingina bayanta a jikin gadon. Abin da ta kasa tantancewa shi ne, da ma tuntuni
zaman miji da mata suke yi, ko kuwa farkarsa ce tuntuni suke blackmailing dinta? Ko kuwa
Uwais extra-marital affair yake having da âyar rikon gidansu???
Ko da ta ce Fahimah ta auri Uwais, wallahi duk cikin lalurar yaron ciki ne, saboda a lokacin
burinta kawai Uwais ya daina kusantarta, don ta daina jin qamshin (Maison Francis). Amma
daga baya bayan ta samu ingantacciyar lafiya komawa ta yi tana cewa, âAllah ya sa ban fada
da bakin malaâiku baâ?. âNi Amrah....Amrah Umar Dikko, ni Uwais ya yi wa haka???â?
Hawaye suka soma sintiri a kan fuskarta kafin wani azababben ciwon mara ya zo ya turnike ta.
Salati ta shiga yi tana juyi don ba ta san nakuda ba, amma wannan ciwon da ta ke ji yau ta
tabbata nakuda ce, amma da ta haihu a hannun farkar mijinta gara ta koma Abuja ko da da
rarrafe ne......... 9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Washegari Amrah ta wuce Malaysia, da ma sati biyu za ta yi. Satin
biyu ma cikin lokacin karatunta ne, ta yanke komai ne don ta samu ta gyara tsakaninta da
Uwais, kuma ta samu ta gyara dan kadan ko ba duka ba duk da bai samu wata kulawa a tare
da ita ba saboda lalura iri-iri na cikinta. A daren ranar bayan tashin Amrah daga airport gidan Ammi ya taho. Ammi da Fahimah suna
zaune a falo suna kallon shirin Arewa24 Uwais ya yi sallama, hannayensa duka biyun zube
cikin aljihu. Idanunsa straight a saitin Fahimah wadda daga amsa sallamarshi ta mike. Ta ba su
wuri shi da Amminsa. Ba ta yarda ta kalli Uwais cikin ido ba sabida Ammi, kuma dai ba ta hango
komai a tare da shi sai tsagwaron rigima yau, tunda ya koma gwauronsa kamar da.
Ammi ta amsa mishi, ya zauna suna kara gaisawa, ta ce, âYan Malaysia an tashi kenan?â?
Ya ce, âEh Ammi ta tashi yanzuâ?.
Sannan ya sunkuyar da kai cikin jin nauyin abin da zai fada.
âAmmi na zo ne tafiya da Fahhima, sai ta zauna gidan Amrah kafin a karasa nata ginin.
Ammi kin ce duk ranar da na shirya karbar aurena da Fahimah da hannu bibbiyu ranar ne za ki
ba ni ita.
Yau ga ni da kokon barana Ammi, gwiwa a kasa, ki yi min alfarma ki ba ni Fah-himahâ?.
Haj. Safeeyah ta gyara zamanta tana kallonshi sosai, kamar mai son hango reality na
maganganunsa cikin kwarar idanunsa. Daga bisani ta ce,
âUwais, ka gaya wa matarka cewa kana auren Fahimah?â?
Ya girgiza kai, ya ce, âAâah tukunna Ammi, sabida na ga tana gidan, kuma Amrah ba ta
gama samun karfin jikinta baâ?.
Ammi ta yi wani miskilin murmushi, ta ce, âTo ba da ni za a yi aikin rashin gaskiya ba, kuma
Fahimah ba za ta je gidan matarka da kayanta a ciki da iyayenta suka zuba mata ta yi zaman
aure ba.
Har sai ranar da ka zaunar da ita ka gaya mata cewa tare aka daura aurenta da na Fahimah,
sannan ka kammala wa Fahimah ginin gidanta ita kadai, don ba za su zauna tare ba. Sannan
zan yarda ta tare.
Duk wannan âyar dadin da ka ga suna yi, ina tabbatar maka don Amrah ba ta sani ba ne, da
tuni komai ya rushe. Don haka ka je ka gama da wadannan matsalolin na gabanka kafin ka zo
gabana da neman daukar matarka.
Sannan Uwais, na hana ka shiga dakin Fahimah daga rana irin ta yau, daga lokaci irin na yau,
sai kun koma gidanku, don ni ba tsohuwar banza ba ce, da za ka dinga binta daki a gabanaâ?.
"Yau dai Ammi tsagwaron mugunta ta ke ji!â?.
Uwais ya fada a ransa, gumi na karyo masa ta kowacce kafa mai fitar da gumi a jikin dan
adam. Gini kam ya yi nisa amma bai karasa ba ai. Amrah kuma in ba ta waya ake so ya gaya
mata ba, cikinsa ya zube bai san ta hanyar da Ammi ke so ya je ya gaya matan ba.
Ya shirya a ransa ne sai ta dawo wannan hutun, nan da watanni