Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
A wurin Uwais duka wannan mai sauki ne tunda yana samun yadda yake so da Amrah a
shimfida. A wannan fannin kam yana yaba mata, kuma yana samun contentment don haka duk
wani flaws na Amrah kankani ne a idanun sa. Hausawa suka ce, so hana ganin aibi, shi Uwais
bayan son da yake wa Amrah har da kauna yar usli mara algus. Ya kama nan da kwana uku Amrah za ta koma Malaysia, bayan sun shafe watanni ukku
tare suna barzar amarci, don haka Uwais yau duk a dame yake, ya zama upset ya kasa
nutsuwa a ofis. Kusan duk bayan mintuna talatin sai ya kira Amrah a waya don ji yake kamar
kafin ya kima gida zai je ya tarar ta koma Malaysia. Sai yanzu da ya san dadin aure ya fahimci cewa yayi babban kuskure da ya yarda da
yarjejeniyar karatun Amrah, lokacin idanun sa sun rufe da neman aure, bai yi tunani
consequences ba, yanzu kam ya fahimci bai iya rayuwa shikadai na tsayin sati biyu ma ba
watanni hudu ba babu mace, in hakan ta faru akwai babbbar matsala, wadda bai san yaya zai yi
da ita ba..
Duk da kasancewar sa matashi mai jini a jika, mai tashen kuruciya da hatiman banki, Ubangiji
Allah bai dora masa sha'awar zina ba, bai taba fatanta wa kansa ba don haka ya shiga tunanin
mafita ga rayuwar sa. Don ba zai bar Halal ya sabawa Ubangiji don karatun Amrah ba.
Don haka yau da ya taso aiki shine sayi banza sayi hopi duk da yasan Amrah na so na
makulashe da kayan amfani saida ya biya ya sayo mata. Ya san abinda ya tarkowa kansa ba
karami bane amma an ce faduwar gaba asarar namiji, kuma a ganin sa a halin yanzu ai yafi
Alhaji Umar Dikko iko da Amrah. Amrah tun daga kofar falo ta tare shi, ta ci sassanyar kwalliyar ta mai taba ruhin Uwais,
bakaken riga da wando ne a jikin ta samfurin CK, ta makalkale cikin jikin sa kamar zata yi kuka
"Habib-Qalby, yau ka dade baka dawo ba, saura kadan in bi bayanka, ga duhu ya fara shigowa
ka sanni da tsoro". Makale ta yayi a kafadun sa suka karasa bedroom din su yana fadin " i'm
sorry Amrah, na je nemo miki pizza dinnan ne da kike so ta Dominos, na tarar basu bude ba sai
da naje wani wajen mai nisa" ya fada yana bude ledojin da yayo mata sayayyar, sai smiling take
yi gashi duk abubuwan da take so ne. Uwais ya gama sanin Amrah ciki da bai, ta manna masa
kyakkyawar sumba a kunci sannan tace "nagode Habiby, amma tare zamu ci, i'll be chewing it
for you (zan dinga tauna maka)".
Dariya Uwais yayi ya marairaice ido tamkar yaron dake gaban Mamarsa "a hakan kuma da
dukkan zuciyar ki murna kike zaki tafi ki barni ni daya. Anya Amrah ba zamu sake shawara ba?
Nace me zai hana tunda bakiyi nisa da fara karatun nan ba a shekarar farko kike ki hakura, na
nema miki admission a BUK, Ammi na acan take bazaki sha wahalar samun admission ba. A ganina Amrah kasancewar mu tare yafi komai muhimmanci, mu shirya welcoming our
incoming babies...... Amrah i'm sorry na yi alkawarin da na zo ina tantamar yiwuwar sa, i can't
live without a wife Amrah, bansan irin ragaitacciyar rayuwar da zan yi ba. In kin amince Daddy
ba zai ce komai ba tunda rayuwar mu ce mu biyu ba tasu ba.....". 9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Idanun Amrah har wani kanakancewa suka shiga yi sabida bacin
rai, tace "Habiby, ka san abinda kake fada kuwa? BUK? Who? Ni Amran? Amran da na sani
Amrah Umar Dikko? In ma wasa kake tun wuri ka bari kafin Daddy ya ji ka". Ta mike cikin fushi
ba tare da ta dauki komai daga sayayyar da ya yi mata ba ta nufi dakin ta.
Tana shiga daki mahaifin ta ta kira, tana kuka ta gaya masa duk abinda Uwais ya ce. Alh. Umar
Dikko murmushi yayi irin na manya da suka san halin dan adam. Yace.
"Ke ba tantabara sarkin soyayya ba? Duk Yayyen ki wacece tayi aure kafin ta ci karfin karatun
ta sai ke? Kin ga farar fata kin rude kin yarda da dadin bakin sa. Abinda baki sani ba mu maza
duk halin mu daya bama iya rayuwa babu mace. Kafin ya aure ki ba abinda bazai ce ba, amma
yanzu tunda kin zama nama sai yadda yayi dake. Tun farko ma me ya kai ki kula shi har kika bari soyayya ta shiga tsakanin ku kina level 1? Inda
kin bi tsarin dana yi miki tun farko da hakan bata faru ba.
Amma tunda bisa yarjejeniyar nan muka amince aka yi auren ni da iyayen sa to yayi kadan
wallahi. Gobe zan turo direba kawai ki biyo shi ku taho, daga nan Abuja ki wuce Malaysia, in zai
iya auren ya jira ki as promised, in bazai iya ba babu dole fa a rayuwar nan Amrah... your future
is your life, kafin kiyi tunanin farin cikin namiji think of your future, think of yourself first, kafin
kowa ya biyo baya.
Your husband only wants to destroy your future......" Amrah bata iya ta karasa sauraron abinda
Daddyn ta ke fadi akan Uwais ba ta kashe wayar ta. Ta san Uwais yana son ta, kuma son ne
yasa yake son kasancewa da ita, amma is it true that he wants to destroy her future??
Tambayar da bazata iya yiwa Uwais ba, domin yanada kima a idanunta da madaukakiyar
daraja, saidai bazata yarda ta bari ya kassara burin rayuwar ta ba don amfanin kansa.
Yau ma kowa a dakin sa ya kwana. Everyone of them is entitled to his opinion. Uwais ya tafi aiki
a washegari ba tare da Amrah ta bashi karin kumallo ba kuma batare da ya ganta ba.
Wajejen karfe biyu na rana yana fama da ayyuka a kwamfutar ofishinsa sakon Amrah ya shigo
masa.
"On my way to Abuja, daga can zan wuce Malaysia, See you soon... so much Love.
-Amrah.
Al'amarin da ya daurewa Uwais kai, ya kasa koda motsi akan kujerar sa. Bai taba hango
matsala kwatankwacin wannan zata kasance tsakanin sa da Amrah ba. In yayi la'akari da cewa
auren so da kauna suka yi dukkannin su. Amma Amrah har zata iya yanke wannan hukuncin ga
auren sa ba tare da ta ji ko dar ba? Lokaci na farko da ya ji yayi fushi matsananci da Amrah,
fushi kuma ba na wasa ba. Ya sa a ransa zai daure ba zai kara neman ta ba ko a waya har sai
ya ga iya gudun ruwan su ita da mahaifin ta.
Don tsananin bacin rai da ya koma gida sai ya samu kansa da janyo trollies yana hada kayan
sa, gara masa ya koma gidan Ammi da ya zauna gwauro har tsayin wata hudu. Ko ba komai zai
dinga samun abinci. Amma yau da wata ce ta yi masa haka ba Amrah ba, zai hakura da auren
ta ne kawai. Amma Amrah zata ci alfarmomi har guda biyu; alfarmar son da yake mata da kuma
mutuncin dake tsakanin sa da Jabeer.
Ammi na falo tana karatun 'Bulugul Maram' din ta. Sanye da shudiyar laffaya, da butar shayin ta
da tambulan a gefe, sai ganin maigadi tayi yayai sallama yana shigowa da akwatunan Uwais,
yana wucewa da su part din sa.
Ta saki baki tana kallon sa a lokacin da yake shigowa. Fuskar nan tayi jawur, ta nan take gane
fushin Uwais ko bacin ransa tun yana yaro. Bata ce komai ba har ya zo ya samu wuri ya zauna
daga gefen kafafun ta.
"Ammi masa'ul khair"
Tana cigaba da kallon sa ta amsa fuskar ta ba yabo ba fallasa, sannan tace "wadannan
akwatunan fa? Ko balaguro zaka yi?" Ya girgiza kai cikin shanye bacin rai, don ya san Ammi ba
wai tana farin ciki da auren sa da Amrah bane kawai ba yadda zata yi ne kuma tana so ta bashi
hakkin sa, shi yasa ta yarda ya aure ta. Don haka dole ya rufawa Amrah asiri don dorar da
dangantakar su. Yace.
"Babu komai Ammi. Amrah ta koma makaranta ne, sai bayan watannni hudu zata samu hutu,
shiyasa na dawo gida kawai don kadaici zai dame ni, babbar matsala ta abinci".
Ammi cikin mamaki tace "makaranta a ina?" "Limkokwing, Malaysia" Ammi ta rasa abinda zata
ce, daga bisani ta ce "dama ka san tana karatu a wata kasar ka aure ta? Ko kuwa sabon zance
ne?" Uwais ya sunkuyar da kai, sai yanzu yake ganin wautar kansa, sannan yace "eh Ammi" sai
kawai ta gyada kai ta ce "Allah ya bada nasara". Har wata ajiyar zuciya Uwais ya saki don bai zaci Ammi zata gajarta zancen a haka ba. Shi
kuma baya son zancen yayi tsaho har ya kai ga fada mata cewa Amrah ta tafi ne ba tare da
iznin sa ba.
Haj. Safeeyah tace "bari in sa Fahimah ta gyara maka dakin, don tun bayan tafiyar ka babu
wanda yayi amfani da sassan, na san yayi kura sosai, Talatu bata nan na aiketa kasuwa".
Ba tareda ta saurari me zai ce ba tasa murya tana kiran FAHIMAH. Uwais sai ya sunkuyar da
kai, sannan ya ji gaban sa ya fadi, da ya tuna wai itama zaman matar sa take. Zaman shi ta ke
yi. Don shi sam ya manta da ita da existence din ta.
Fahimah ta fito daga kicin dauke da madaidaicin tray data shiryowa kanta abinci zata ci, ta
shigo falon tana amsa kiran Ammi ba tareda ta san Uwais yana nan ba. Dai-dai lokacin da
Uwais ya dago kai. Sexy eyes din sa suka sauka akan Fahimah. Ita kuma bata tsammaci ganin
sa a falon ba, don haka farantin dake hannnun ta da duk abinda ke kai ta saki a kasa ba tareda
ta sani ba.
Idanun Uwais na da matukar tasiri ga mental well-being din ta, ta yadda a duk lokacin da ya
dubeta da su take neman hankalin ta da nutsuwarta ta rasa.
Komai dake kan farantin ya kife, tangaran sun fashe sannan jikin ta ya hau bari. Ammi takaici ya
ishe ta na yadda Fahimah bata iya mallakar kanta a duk lokacin da ta ga Uwais kamar wadda ta
ga mala'ikan daukar rai, tace.
"Yau nake ganin sakarci, sai ki dauko tsintsiya da mopper ki share, ke ba makauniya ba balle
ace tuntube kika yi, kiyi maza ki kwashe kije ki gyara masa sassansa".
Ta juya a sanyaye ta koma kicin don ta dauko tsintsiyar. Uwais mikewa yayi yana sakin dan
karamin tsakin da Ammi bata ji ba. "Zan je wajen Jabeer na dawo Ammi, kafin a gyara dakin".
Ammi tace "Rehlah Sa'eedah" wato a dawo lafiya.
Bayan fitar sa Ammi ta bishi da kallo sannan ta yi murmushi ta maida duban ta ga Fahimah
wadda ke durkushe tana tsaftace wurin data yi messing, ta kasa dagowa har Uwais ya zo ya
wuce ta gaban ta. Ammi a ranta tace "muje zuwa dai, ai sannu - sannu bata hana zuwa ai, sai
dai a dade ba'a je ba". *****
FAHIMAH A DAKIN UWAIS
Wannan ne karo na farko data taba shigowa dakin Uwais a rayuwar ta, da farko kasa tabuka
komai tayi, domin ji tayi gabadaya kuzarin jikin ta ya kare, koda yayi watanni baya dakin
kamshin tsadadden turaren sa 'Maison Francis' bai bar sanyaya dakin ba. Babban hoton sa
window size cikin kayan aikin sa na GT shi yafi daukar hankalin ta domin yayi kyau ba na wasa
ba a cikin hoton. A jikin bed-side wani dan karamin hoton ne cikin frame da ya sha adon zuciya, fuskar sa ce
data Amrah a ciki kamar zasu sumbaci juna. A hankali ta kai hannu ta dauki hoton a tafin
hannun ta tana share kurar jikin sa da gefen gyalenta, tana kallon su da wani irin mixed feelings
da ya fi kama da "kishi mai nukurkusa zuciya". Kishin da bata taba ji akan Amrah ba sai yau,
ganin yadda ta maida Uwais jazur, ga 'yar kiba yayi, tabbacin yana samun gamsashshiyar
soyayyar mace. Mai mace kamar Amrah yaushe zai taba waiwayar ta?
Amma me? Mayaudariyar zuciyar ta sai ta ci gaba da bata hope da courage na cewa wata rana
irin haka na zuwa....ranar da zata ga fuskarta haka gab da ta Uwais, watakila closeness din har
ya fi haka. Duk da haka bata jin kin Amrah a ranta domin ta yaba da yadda ta karbeta a ganin ta
na farko da ita. Ba abunda ke bukatar gyara a dakin sai kura da ko'ina yayi, don haka ta hau karkade komai
tana gogewa tayi shara ta gyara abinda duk ya kamata ta tsaftace, sannan ta wanke masa
toilet wanda yake fari kal shi ko kurar ma bai yi ba fari kal yake tabbacin a baya yana samun
kulawa sosai. Da ta kammala ta feshe dakin da 'air freshner' din 'raspberry' ta shimfida masa sabon bedsheet
mai kauri da Ammi ta bata ta shigo da shi sannan ta juya zata fita.
Kamar wadda aka yiwa umarni sai ta sake juyowa, ta kalli hoton sa dake kafe, sannan ta runtse
idon ta ta juya ta fita.
"Na gama Ammi!"
Ta fadawa Haj. Safeeyah dake zaune tana lazumi, mace ce mai yawan ibadah da bata bari
lokacinta ya wuce a banza. Kai ta gyada mata. Sai Fahimah ta wuce kitchen ta tadda Baba
Talatu don ta taya ta shirya abincin Uwais. Ko dama can tare suke girkin su muddin Fahimah
tana gida. Suna cikin aikin Baba Talatu ta dube ta sosai ta ga kullum kara ramewa take yi. Ta san dole
Fahimah ta kasance cikin damuwa sai dai ta boye hakan a ranta, don bata taba ji ko ganin Aure
irin nata ba. Har yau ta kasa gane manufar Ammi ta hada wannan baudadden aure, ita
Fahimahn tana nan a gefe kusa da uwar sa, shi yana can tare da matar da yake so suna more
kuruciyar su. Anya ko Fahimah bata son Uwais hakan bazai ke damun ta a karkashin zuciya
ba? Koda yake Ammi tace jami'a zata fara, ta san Fahimar su da son karatu, watakil in ta fara
zuwa makarantar zata samu abin debe kewa. Baba Talatu ta nisa ta ce.
"Uwar daki na, daga yau ke kadai zaki dinga dafa abincin ubandaki na, sannan ke zaki dinga kai
masa, gyaran dakin sa da kula da komai nasa a gidannan ya dawo wuyanki domin da ke yafi
dacewa har zuwa lokacin da zai bar gidannan".
Fahimah tayi mata kallon "sannu sarkin kankanba". Sannnan ta ce "shin Baba Talatu meye
gami na da shi din?" Dariya Talatu tayi tace "wai ai naga aikin neman lada ne da neman
aljannah, kiyi don neman dacewa da aljannah ba don komai ba" da sauri Fahimah ta girgiza kai
"ban iya shishshigi ba, kuma bazan fara yanzu ba. Ayyukan neman lada yawa gare su. In ya ga
dama ya bi matar sa. Ni ki daina alaqanta ni da Ya Uwais, don babu komai tsakanin mu bayan
'yan uwantakar musulinci da Ammi ta hada, kuma ita nake fatan ta cigaba da wanzuwa a
tsakanin mu har karshen rayuwa ta.
Baba Talatu ta yi murmushi ta ce "Fahimah har yanzu ke yarinya ce, amma yaya zaki nade
hannu a kirji ki koma gefe ki barwa kishiya miji? Miji fa aka ce Fahimah ba saurayi ba! Ai
kowanne li'irabi kike dashi ki ajiye shi a gefe ki yi hobbasar kwatarwa kanki 'YANCI don tabbatar
da martabarki ta diya mace. Ni ban yarda wai wannan farar tsadar ta fi ki komai ba, mace sunan ta mace, kowacce irin kala
ce ita, bahaushiya, balarabiya, ba'abziniya, bafullatana ke har bayerabiya duk daya muke.
Balle ma Fahimah ke kike ganin kan ki a baya don baki da hasken fata irin ta ubandaki na,
amma bakar mace ai ita ce mace ta alfarma, shi kansa ya san hakan sai don dai wani dalili
nasa na daban amma.....".
Zancen duk ya gundiri Fahimah, tace "Baba Talatu chapter closed, inda aka san darajar ka
acan ne zaka yi rawa a baka kudi, a inda ba'a san darajarka ba kuwa maimakon ka samu kudi,
kana iya karewa da dan banzan duka!".
Uwais da ya je bai samu Jabeer a gida ba sai Murjanatu, ta gaya masa Jabeer yana Abuja,
zurfin ciki irin na Uwais yasa bai tattauna komai akan matsalar sa da Amrah da Aunty
Murjanatu ba duk da ya san kusancin dake tsakanin su. Maimakon ya koma gida sai ya samu
gefen hanya ya gangara ya tsaya, ya kashe motar gabadaya yana kallon wayar sa da kiran
Amrah ke ta shigowa akai-akai ba kakkautawa. Zuciyar soyayyah na azalzalarsa da ya
dauka.....zuciyar maza na hambarewa. Duk son da yake yi wa Amrah dole ta yi abinda zai nuna
mata shi ba irin mazan da mace ke juyawa bane don kawai yana son ta.
Ya fi karfin mintuna ashirin a wurin yana tunanin abinda zai yiwa Amrah ya rama bacin ran data
sanyashi, kin amsa kiranta is not enough. Amma ga mamakin sa ya kasa daukar wani matakin
bayan wannan. Amrah ta riga ta yiwa zuciyar sa illah bai da wani katabus a kanta.
Da kyar ya jawo motar ya dawo gida, bai tadda kowa a falon ba duk sun shige daka, ya wuce
dakin sa kansa tsaye. Wani irin gyara da dakin ya samu da sanyin air fresh da Fahimah ta fesa
su suka yi masa sallama, wadanda suka cakude da rabar iyakwandishan. Sai lokacin ya tuna ya
ji sanda Ammi ke fadin Fahimah ta