Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
âDon Allah fita min a nan Uwais, da kai da gallababben turarenkaâ?.
Yau Uwais din tsura ta fada not Habiby ko Habib-Qalby, ya ce, âTo kin sa na dauko âyar
Ammi ko in maida ta ne?â?
Da sauri ta mike tana fadin, âAi ban san tare ku ke ba, ba ka yi min bayani baâ?.
Suka tadda Fahimah a inda ya barta, Amrah da faraâa sosai ta ke mata barka da zuwa, ta
dauki jakar kayanta ta ce, âHabiby ya ya sunanta?â?
Irin kallon da ya yi wa Fahimah ya sa ba shiri ta sunkuyar da kanta. Ya ce, âTambaye ta
mana? Ai tana jinkiâ?.
Murmushi Fahimah ta yi ta dubi Amrah wadda a take ta ji Allah ya dauke mata kishin Amrah da
ke ranta. Ta ce, âSunana Fahimah. Wasu kuma kan ce, Fah-himahâ? (tana nufin Uwais, shi
ne mai kiranta da Fah-himah)â?.
âNi ma Fah-himah zan ce, yafi dadi, Fahhimah please taso mu je in raka ki dakin da na ware
miki tun safe. Ki kwanta ki hutaâ?.
Fahimah ta mike ta bi bayan ta. Uwais ya bi su da kallo admiringly a zuciyarsa kuma yana
taraddadin ranar da gaskiya za ta bayyana ga Amrah, duk sunan da ta kira shi da shi a lokacin
daidai ne. Makaryaci? Mahaâinci, mayaudari ko maciyin amanar soyayyah? Heâs ready to
face and accept all the names in dai a karshe za ta yi hakuri su hada kai su yi rayuwa mai
albarka su ukun.
Amrah will never be enough for him shi ya sani, duk da cewa har gobe ita ce zabin zuciyarsa,
muhallin da kowacce ke da shi a yanzu cikin ransa daban ne da na âyar uwarta; duka yana
son abinsa, kowacce da bigiren da ta cike cikin zuciya, ruhi da gangar jikinsa.
Amma Fahimah na da wani extra matsayin a zuciyarsa wanda ya wuce soyayyahâ? wanda
sexual bond ke karawa tsakanin miji da mata, sama da wannan ita din abin so ce ga
mahaifiyarsa da ba ya hada ta da kowa a duniya sannan ta zama wani babban bangare na
barin jikinsaâ? abin nufi, a ita ne yake samun nutsuwar da duk da namiji ke son samu a diya
mace. Yayin da Amrah har gobe take a matsayin MATAR SO ta likawa a goshi.
Ya yi kokarin ya daidaita matsayin kowacce da na âyar uwarta cikin zuciyarsa a daren yau,
sai ya ga cewa daidaiton bai yiwuwa, domin ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce
da ta shallake tunaninsaâ?....Ashe namiji kan iya son wata a lokaci guda, sama da first love
dinsa???
Amrah na can tana sharar barci ta yi daidai a kan gado ta baro Uwais kamar marayan da ya
rasa uwa don ta roke shi kada ya zo inda ta ke in ba so yake ta amayar da âyan hanjinta ba.
Uwais ya mike tsam yana daure igiyar pajamas din shi cikin ransa yake fadin,
âAna me? Ni ba aminin gwauro ba?"
Dakin Fahimah ya nufa bayan ya leka Amrah ya tabbatar ta yi nisa a barcinta.
Kamar Fahimah ta san haka za ta faru don ta gama gane Uwaisun nasu cikin dan lokaci kalilan,
kunya bata ishe shi ba a wannan fannin kam, zai iya janyo mata abin kunya wajen wadda ta
dauke ta 'yar uwa, don haka tun sanda zata kwanta ta rufe kofarta ta ciki da key ta kuma barshi
a jiki ta yadda ko ya sa nasa ba zai shiga ba. Ya murda kofar sai ya ji ta gam-gam, wato ya ji ta a rufe, sai ya soma kiranta a matukar
tausashe.
âFah-himah, bude min kofar mana, ni ne Uwaisâ?.
Fahimah da ke bisa darduma tana sallolin nafilah don gusar da birbishin kishin da ya cika
zuciyarta ta yi sallama, sannan ta matsa jikin kofar cikin damuwa ta ce,
âWani abu ka ke so Ya Uwais?â?
âKi bude na ce, ko ma me ye sai ki jiâ?.
âGaskiya ba zan bude ba Ya Uwais". Ransa ba karamin baci ya yi ba, kuma yana tsoron ya
daga murya Amrah ta tashi don haka ya sassauta murya ya ce,
âPlease Fahhimahâ? Iâm begging you in the name of Allahâ?...â?.
Muryar Uwais dake raurawa har cikin tsokar zuciyarta, yadda muryar ke raurawa haka zuciyar
ta ke raurawa, weakness na wanda kake so ba karamin rauni bane a gareka, amma ta
gwammace ta tsaya a kan gaskiya da adalci, in ita aka yi wa haka ya ya za ta ji? Amrah ba ta
san da komai a tsakaninsu ba, sai kokarin kyautata mata ta ke da zuciyarta daya. Ta dauketa
kamar kanwar Uwais da ta kawo mata ziyara. Amma sai ta saka mata da dauke Uwais a cikin
dakin ta?
âYaya Uwais ka yi hakuri ba fa zan bude ba. Don ban ga abin da ka ke so a nan baâ?..â?.
Muryarsa wani iri don tsananin bacin rai, ya ce, âFah-himah...., amma saboda takaici sai ya
kasa karasawa, ya juya ya bar wurin. Dakin Amrah ya koma yana fadin yau sai dai turarensa ya
sumar da Amrah in ma suman za ta yi.
Fahimah ba ta san ya suka kare shi da matarsa ba, da asubah Amrah ta hau buga mata kofa,
da Fahimah ta ji muryarta sai ta bude, Amrah ta fado dakin tana ajiyar zuciya, at last she
escaped! Smell din da bata so. Sannan ta zauna a gefen gadon da Fahimah ta tashi, ta ce,
âZan kwanta a nan don Allah, bana son turaren Habiby, shi kuma ya ki fahimtata ya nisance
ni ba da gangan nake yi baâ?".
Ta yi ajiyar zuciya abin tausayi, sannan ta dubi Fahimah cikin rauni "kin huta da ba'a yi miki aure
ba Fahhimah, aure takura ne, nauyi ne, jidali ne wallahi ina da na sanin yinsaâ¦â?.
Fahimah ta ce, âKul! Amrah ki daina fadin haka, domin aure umarnin Ubangiji ne kuma
sunnar Annabi SAW ne. Ya kuma ce wanda ba ya son sunna ta, to ba ya tare da niâ?.
Amrah ta ce, âAstagfirullahâ? wa'a tubu ilaih, amma duk bayanin da zan miki bazaki gane
ba tunda baki da aure, my husband mai yawan takurawa ne, yayin da ni nake tsaa-tsaki,
sannan ina fama da kaina, amma ya kasa daga mun kafa ya bar ni in sarara ko kadan.
Yanzu kam na yarda gara ya kara aure, Fah-himah I so much like you, in da aure tsakanin ki da
Habiby don Allah ki taimake ni ki aure shi... tafiyarmu ni da shi ba za ta yi tsayi ba in aka cigaba
a hakaâ?...don bani da isashshen lokacin sa, yanzu haka na baro komai dake gabana na taho
tun daga Malaysia don in ba shi lokacina amma na kasa faranta masa da komai, tunda na zo
lafiyata ta ki daidaito.
Shi kuma ya kasa daga min kafa, jiya fada muka yi baram-baram ko barcin kirki yau ban iya na
yi baâ¦â?.
Fahimah ta rungumo Amrah a jikinta cikin lallashi, ta ce, âKi yi hakuri Amrah, marriage is not
a bed of roses kuma duk soyayya sai ana samun misunderstandingsâ? amma Yaya Uwais is a
nice person, duk da ba ni da experience a kan aure na san abubuwan da ki ke fama da su
lalurorin karamin ciki ne kawai, da zarar kin samu lafiya ko kusa bazaki so kowa ya rabi
Uwaisun ki ba, balle kiyiwa kan ki fatan ya kara aure, kuma insha Allah zai wuce, da zarar
cikinki ya yi kwariâ?.
Ta yi shiru sannan cikin murmushi, ta ce.
âAmrah ki ke so ko in ce ki ke fatan wata ta auri Uwais? Ba kya tsoron ta kwace miki shi ne?
Ki bar wannan tunanin wahalar ovulation ke damunki, da kin haihu ko kuda ba za ki so ya gifta a
tsakaninku baâ?.
Amrah dai ba ta ce komai ba, amma ta ji dadin maganganun Fahimah, ba ta san sanda ta fada
ba tsabar bata cikin normal hayyacin ta, kuma tana bukatar taimako daga 'yar uwarta mace
koda da shawarar fatar baki ne. Tace.
"Fah-himah I just like you, and i love your simplicity ".
Da sauri fahimah ta girgiza kai tana jin kamar ta bude baki ta gaya mata gaskiya, don ba ta
saba rashin gaskiya a rayuwarta ba sam sai yau. Yau din ma don kada ta shiga hurumin da ba
nata bane. Kamar Uwais ya san me ta ke shirin yi sai kawai ya bude kofar ya shigo dakin babu
zaton su. Ya dau wankansa as usual ya yi shirin ofis cikin bakaken suit, ya dube su ya girgiza kai.
âDaga ganin wannan zaman naku gulmata ake, kin bar ni zan fita ban ci komai baâ?. Ya
fada yana kallon Amrah directly cikin idanunta. Ji ya yi ya kara sonta duk flaws dinta, tunda tana
son Fahimar sa.
Fahimah sai ta zame jiki ta bar musu dakin, kofar da ta ke da tabbacin kitchen ce can ta nufa. A
gurguje ta dama wa Uwais custard ta zuba madara (peak) ta ruwa gwangwani daya, ta soya
plaintain da sauri ta zo ta aje masa a dining. Daidai lokacin suka fito daga dakin nata shi da
Amrah, ya ja kujera ya zauna ya soma tsiyaya vanilla custard din a kofin mug na tangaran.
Fahimah ba ta tsaya tare da su ba, ta koma kitchen din don ta sama wa Amrah wani abu mai
dan gishiri da maggi kuma mai yaji da za ta iya ci kamar yadda ta gaya mata cewa abu mai yaji
da maggi kawai taje iya ci..
Farfesun tarwada ta yi mata, Amrah ta ce ta saka tarugu sosai. Haka ta yi ta shan romon da
cokali tana gumi tana fyace hanci.
Da rana girki na musamman Fahimah ta yi wa Uwais tuwon semo miyan danyen kubewa da yaji
zallar tsokar kaza, ta cire duka kasusuwan ta dagargaza tsokar cikin miyar. Amrah ta ce ba za
ta ci komai ba wanda Fahimah ta dafa don bata marmarin tuwo, sai spicy chicken take so, ta
kira Uwais tace idan ya dawo aiki ya tsaya ya taho mata da ita daga Chicken Republic. Amma Fahimah ba ta kyale ta haka ba, sai da ta yi mata dan wake da manja da yaji, ai kuwa
Amrah ta yi ta zuqulqula tana shi wa Fahimah albarka.
Ita kuma ta zage ta gyare gidan ciki da bai dinsa, dakin Uwais ne kawai ba ta shiga ba.
Da ya dawo ya kawo wa Amrah kazar. Kallo daya ta yi mata ta ji ta ginshe ta. Ta ce, âHabiby,
na ci dan waken Fah-himah na koshi kuma ku nemi mai cin wannanâ?.
Kwanan Fahimah bakwai a gidan gaba daya rayuwar gidan ta yi armashi. Amrah na samun
hutu yadda ya kamata Fahimah na kula da cinta da shanta, tsaftar gidanta har ma da
walwalarta. Wani irin sabo wanda ya fi kama da na âyan uwantaka ya shiga tsakaninsu.
Uwais ya gaya mata Ammi ke rikonta ba âyar aiki ba ce kamar yadda ya gaya mata a baya,
amma ko da wasa bai fada mata Fahimah daga orphanage ta zo hannun Ammi ba. A ganinsa
wannan sirrin Fahimah ne wanda daga shi sai Ammi yakamata su sani, don sama wa Fahimah
cikakkiyar walwala da sukuni a cikin mutane âyan uwanta. Uwais ya yi juriya kwarai, don kuwa bai kara attempting zuwa dakin Fahimah cikin dare ba, ya
yarda da hujjarta na ce wa Amrah deserves respect, a gaban idonta ko a bayan idonta sabida
kyakkyawar zuciyarta da kyautatawar ta..
Sati biyu na cika Fahimah ta soma shirya kayanta don komawa gida, Ammi ta yi waya gobe
insha Allah za ta sauka a Kano.
Amrah har da hawayenta da Fahimah za ta tafi, ta hada mata cosmetics designer din AVON set
guda. Ita da Uwais da Fahiman suka tafi filin jirgi dauko Ammi. Suna ta hira ita da Amrah,
Amrah na fadi mata âI cant' express my kind gratitude, for your being with me, for your kind
assistance Fahhimah, ina ma Ammi za ta bar min ke mu ci gaba da zaman mu tare?â? Uwais ya yi murmushi yana tukin mota zuciyarsa ta masa dadi, ya juya ya ce da Amrah da ke
gefensa,
âIta kuma ta yi ta zama kenan ba za ta je gidan nata mijin ba?â?
Amrah cikin zolaya ta ce, âAi don ta ki ne, amma na ce mijin ma ta zo mu aura tareâ?.
Uwais daga jin haka bai iya kara cewa komai ba, ko kwakkwaran motsi bai kara ba, don
mamakin Amrah ya gama kashe shi. To amma ya ya za ta ji idan ta ji cewa all these while
Fahimah zaman matarsa ta ke yi kamar ta? He is just fooling her? Ko ya ce they are just fooling
her? Daidai lokacin da suka shiga filin jirgin Malam Aminu Kano, tuni su Ammi sun sauka, a reception
suka hango ta. Fahimah da gudu ta runtuma ta rungume Ammi. Yayin da Ammin ke fadin,
âAutar Ammi, na yi kewarku. Da fatan na same ku lafiya?â?
Amrah ta iso tana yi wa Ammi barka da zuwa. Ammi ta kama hannunta tana tambayarta karfin
jikinta. Daga nan suka karasa mota Uwais ya ja suka tafi, amma wannan karon Ammi ce a
gefensa, Amrah da Fahimah suna baya, hira suke sosai. Fahimah na ta bai wa Ammi labarai
har suka zo gida. Baba Talatu ta yi musu girkin tarbar Ammi, Uwais da Amrah ba su jima ba suka wuce, Fahimah
na kokarin kaucewa hada ido da Uwais a duk inda Amrah ta ke, haka yanzu da za su wuce ya
biyo ta har dakinta yana so su yi sallama cikin gigicewa Fahimah ke korarsa.
âKa yi wa Allah Ya Uwais ka tafi, in yaso ka dawo daga baya, I cannot hurt this beautiful
soul!".
Gaba daya ta rude har tana tura shi waje da hannayenta.
Shi abin ma dariya ya ba shi. Ya ce, âZan tafi, amma ki sani kin ci bashi ba dan kadan ba,
next haduwarmu biyan bashi ne, DEAL ne. Amrah kuma na gaji da wasa da hankalinta, don
haka ki kwarara zuciyarki, soon ba da jimawa ba zan gaya mataâ?.
Fahimah ta ci gaba da tura shi, fatanta kawai ya fita a dakin.
Uwais ya shammace ta ya hade bakunansu, kissing her deeply har sai da alâamura suka
soma fin karfin Fahimah. Can cikin tsakar kanta ta jiyo Amrah na fadin.
âHabiby, where are you?â?
Fahimah ta ja baya da karfi, trying hard ta yi pushing Uwais back, amma ta kasa. Wata irin
kyakkyawar runguma ya yi mata yana fadin.
âFahhimah don Allah kada ki bar ni saboda Amrah, don na ga yanzu kin fi sonta a kainaâ?.
Fahimah ta gatsina baki, ta ce, âDa can din sonka nake yi Ya Uwais? Ka yi wa Allah ka
tafiâ?.
Uwais ya ce, âHummm! A bar kaza cikin gashinta, amma Fahimah na san kin dade kina son
mara kirkin Yayan nan naki, dalili na na kara uzzura miki kenan, da kiranki da sunan da zai
dinga bakanta zuciyarki don ki cire ni a ranki don na san duk ranar da Ammi ta gane hakan
sunana angon Fahimah, ina so ko bana soâ? To kana naka Allah na naSa, yau ga ni red - handed a dakin Fahhima cikin tafin hanun ta, ina
begging for shan minti ana ture niâ¦â?.
Anyway bazan gaji da cewa ba kin burge ni, da ko Ammi bata taba sabin zuciyar ki ba. I salute
your courage.
Hannu ta sa ta toshe kunnuwanta tana fadin, âYaya Uwais ka fita ko in yi magana da karfi
Amrah ta san kana nanâ?.
âDa kin hutar da ni, don kullum shirya yadda zan fada mata nake yi kwarin gwiwar na
subucewa, musamman da na gane tana son ki sosai".
Daidai lokacin Amrah ta iso kwanar dakin Fahimah tana kiran sunansa.
Juyawa ya yi ya fita, ya bar Fahimah tana sakin murmushi, in wani ya ce mata Uwais ne
wannan din da gudu za ta karyata ba don raâayal aini abubuwan ke faruwa a gabanta ba.
Lallai shi Allah mai canza alâamura ne zuwa duk yadda ya ga dama, kuma buwayi ne gagara
misali, sannan ba abin da ya fi karfin ikonSa.
Ta kwanta a hankali rigigine bisa gadonta tana tariyo dan abin da ya faru tana ta blushing ita
kadai, amma wani bangare na zuciyarta ya shiga fargaba, fargabar ya ya alâamura za su
kasance when Amrah comes to know the bitter truth din da ba ta sani ba???
******
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ta rasa irin godiyar da za ta yi wa Ubangiji da ya mallaka mata
soyayyar Uwais. Amma duk lokacin da Amrah ta fado mata a rai sai ta ji gabanta ya fadi. Ya
Uwais ya yi babban kuskure da su duka ba ta san ya za su yi da consequence dinsa ba. Ammi
da ma ta ce babu ruwanta, shi da ya boye shi zai warware, wanda ya ja ruwa shi ruwa kan
doka. Ita ba a boye ta yi hukuncinta ba.
A yanzu kam babu tsanar Amrah a ranta don ta yaba da halayenta. Ko mata hudu Uwais zai
kara aure a cewarta ba ta da matsala da su, tunda Fahimah ce uwargida, karatun Amrah a wata
kasa shi kadai yake ci mata rai.
A karshe kuma ta gode wa karatun na Amrah, don da ba don shi ba ba ta san ranar da Allah
zai karkato da hankalin Uwais ga Fahimah ba.
******
Uwais ya sauka a kasar Switzerland lafiya, aka dauke su zuwa masaukin da aka tanadar musu.
Thing are perfect ga hutu ga jin dadi, amma rashin iyalinsa ya sa ba ya jin dadin komai. Ita da
ma