Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
Allah cikin lalura ka
ɗauki matarka kunbar gari kuma har kana sanar da cewa zaku wucce Dubai to ita ame kabarta
da nata cikin?"
Tsaki yayi yace “Ke wlh Granny da son takurawa kike naga gashinan kuna kula da ita" bazata
iya jure lamarin ba wannan tasa ta kashe wayarta takai dubanta ga Kharimatu da takejin duk
abinda yake faruwa tace “Inason ganinsa Granny kice yazo don Allah" hawayen tausayinta
Granny ta share tace “zaizo Kharimatu wani aikine na gaggawa ya taso masa ya tafi Lagos
amma kina ransa kiyi hƙr kinji kiyi fatan Allah ya baki lfyrki kawai"
Komawa tayi ta kwanta tana share hawaye kewar mahaifiyarta tana sake bijirowa zuciyarta
sosai tayi kuka Granny nata aikin rarrashinta cikin kukan tace “Ba damuwata yazo ba Granny
damuwata shine son sanin yanda ya karɓi amanar da Mahaifiyata ta bar masa, meyesa ta
amince na zauna da Aliyu tun kafin na amince dashi? Meyesa ta zaɓamin shi tace naje na
zauna dashi harma take bani wasiyyar na zauna dashi iyakar wuya bayan shi tun yanzu ya fara
juyamin baya Granny tunda na farka kwana uku kenan banga Daddyn Farooq ba kuma yanzu
naji kina faɗa cewar tunda aka kawoni asibitin nan washegari bai ƙara zuwa ba"
Sharce gumi Granny tayi ta kamo hannun Kharimatu da taketa zubar da hawaye tace “kinga
Kharimatu inason ki cire komai a ranki don Allah ki manta da komai kinga cikinki ya tsufa
watanni bakwai bakya buƙatar hayaniya ga kuma lalurar nan da take damunki don Allah ki
daina sa Aliyu a ranki Kharimatu ba haka akabar Aliyu ba kinsani wannan lamari yana buƙatar
addu'a me tsanani"
Jan zuciya tayi tace “Yanzu a haka zanta zama kenan?" Murmushi Granny tayi tace “Aa
bazakiyita zama a haka ba yanzu abinma dake akwai zaki koma gabanmu ne aci aci gaba da
magani har Allah ya baki lfyrki"
Zuciyarta na suya haka ta hƙr tabar mgnr ta koma ta kwanta kwana takwas ta ƙara a asibitin
suka sallameta domin suma sun fahimci ciwon nata bana asibiti bane dole tasa aka nemi
maganin Hausa tare da yin waya Guru aka sanar dasu halin da ake ciki Baba Na'ibi wane a
gurin babanta shine ya niƙo gari ya taho Kano ya kawo mata magani cikin ikon Allah Suna fara
amfani da maganin sauƙi yayita samuwa sati guda bata rufa ba wannan ƙanzo²n da fatarta tayi
duk ya ɓare asalin fatarta ta dawo Baba Na'ibi yana kallonta yayi murmushi yace “komai zai
wucce da yardar Allah"
*Oum Hairan*
[11/10, 8:59 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ39-40 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Kwanaki har watanni sukayita wuccewa babu Aliyu babu Salma Kharimatu tanata rainon cikinta
har ya isa haihuwa ranar wata asabar da yamma ta shiga bayi tana tsugunnawa taga wani jini
me yauƙi ya zubo mata ta miƙe da sauri ta fita ta kira Granny dake a sashinta take zaune. Tana
gani ta gane meye ke faruwa tayi murmushi tace “Abin yazo Kharimatu haihuwa ce" gabanta ya
faɗi tace “Granny tun jiya marata take ciwo fah" kama hannunta tayi tace “kije ki zauna bari
nayiwa Mal Hassan mgn yayi miki rubutu idan haihuwar ce ciwon zai tashi ayi a wucce gurin
idan ba ita bace kuma zaiyi sauƙi"
Zaunar da ita tayi ta shiga ɗaki bata jima ba ta fito ta tarar da ita ta riƙe ciki ta cije leɓe tana
ƙoƙarin zamewa daga kujerar kamota tayi ta saukar da ita ƙasa tanayi mata sannu itadai
kallonta kawai takeyi tana karɓar azaba babu jimawa Mal Hassan ya aiko da rubutun Granny ta
bata tasha tace ta kwanta, kwanciya tayi bacci ya ɗauketa cikin baccin taji azabar ciwon ta ƙaru
ta zabura ta miƙe da sauri tana faɗin Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un Granny bayana marata
ƙirjina wayyoh wayyoh Granny shikenan na mutu na ƙare...." Rufe mata baki tayi tace “ke ar
sakarya ki rinƙa salati" fita Granny tayi tayima driven gdan mgn tazo ta ɗauko mata hijjab ɗinta
tasa mata daidai lkcn Mom ta fito itama suka nufi asibiti suna zuwa aka shiga da ita labour
room.
Bata wani ɓata lkc ba Ubangiji ya yassare mata ta haifo sankacecen ɗanta namiji kyakkyawa
kamannin sa na mahaifinsa ne sak sumarsa da bakinsa sune kawai nata, ana gyara yaron aka
sallamesu suka tafi gda sunata murna kamar ba'a taɓayi musu haihuwa ba.
Waya sukayi Guru ƙanwar Mama Yabi tazo ita da Granny suka rinƙa kula da ita abinda ya dami
zuciyarta tun ranar data haihu take kiran wayar Aliyu bata shiga shikuma bai kirata ba zuciyarta
na faɗa mata to ko baisan ta haihu bane?" Wannan abu sosai ya damu ranta ranar da ɗanta ya
kwana biyar suna zaune take tambayar Granny Daddyn Farooq kuwa yasan ta haihu?"
Shiru Granny tayi tsayin lkc fuskarta ta sauya daga fara'a zuwa damuwa hakan ya tashi
hankalin Kharimatu idanunta ya kawo ruwa tace “kiyi hƙr Granny bansan tambayar zata ɓata
ranki haka ba insha Allahu bazan ƙara ba" riƙo hannunta Granny tayi ta share ƴar ƙwallar data
zubo mata tace “ba tambayarki ce ta bata raina ba Kharimatu yanda kika damu da yaron nan
Aliyu shi bai damu dake ba don Allah duk hukuncin dana yanke kada kiyimin gardama nasan
kinason mijinki nima inasonki dashi zanyi ne don ƙwatar miki yancin ki"
Kallon ƙanwar Mama Yabi Granny tayi tace Saude idan anyi suna zaki tafi da Kharimatu Guru ta
zauna acan duk abinda kuke buƙata zan rinƙa turo muku" amsawa Gwaggo Saude tayi da to
sukaci gaba da tattaunawarsu itadai jinsu kawai takeyi tana kallon ɗan nata tana share
hawayen tausayinsu daga ita harshi Yaro kyakkyawa ya shigo rayuwar cikin yanayi mara daɗi rabonta da sanya mahaifinsa a
idanunta tun cikinsa yanada wata biyu wannan wacce irin ƙaddara ce
Kwana nawa tayi na farin ciki da mijinta meye yasa ya gujeta ya daina bibiyarta.
Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Ma'aruf akayi suna na mamaki kwanaki uku da sunan
suka ɗauki hanyar Guru tunda ta koma Guru cikin danginta hankalinta ya kwanta damuwarta ta
ragu gata ga ɗanta yanashan gata gurin yan'uwan mamansa Baba Na'ibi ne ya rinƙa kula da ita
da duk wani motsinta kullum cikin yi mata rubutu da kawo mata magungunan tsari yake domin
ya fahimci bayan rabata da mijin da akayi rayuwarta ma ake farauta don dai kawai tanada ƙarfin
addu'a ne kuma ƙaddararta me ƙarfi ce.
Kullum zasuyi waya da Granny zataji abinda ke faruwa Mom ma tana kiranta taji lfyr jikanta duk
watan duniya Abba yana tura mata kuɗi sosai shi a burinsa ma ta koma makaranta so ya
fahimci Aliyu yanzu bashida ra'ayin karatun mace hakan yasa ya tattara yabar batun karatun.
Watansu takwas a Dubai suka dawo lkcn Salma ta haifi yarta mace yarinyar tazo batada lfy
ƙarshe ma ta mutu sosai sukaji mutuwar yarinyar tunda suka dawo zuciyarsa ta koma masa
gurin Kharimatu musamman daya buɗe ɗakinta yaga batanan alama ma ta nuna itama ta daɗe
rabonta da gdan. Guri ya samu ya zauna daɓar zuciyarsa na bugawa da ƙarfi sai yanzu yake tuna a yanayin daya
tafi ya barta da ƙaramin ciki wata uku gashi kusan watansa tara bayanan tsoro ne ya kamashi
ya miƙe yace.
“To me hakan yake nufi Kharimatu nasan yanzu ta jima da haihuwa tun wata huɗu baya, me
yasa ba'a faɗa masa ba? To kodai itama mutuwa abinda ta haifa yayi?" Da wannan tunanin ya
lalubi numberta ya dannan kiran lkcn tana islamiyyar dake gaban gdan nasu tana koyar da
matan aure taji wayar tata tana ring ta zura hannu cikin doguwar rigar atamfar tata me aljihu ta
zaro wayar tana kissing Jawad dake hannunta ta ɗora idanunta akan wayar da sauri cikin
faɗuwar gaba tace “Aliyu Daddyn Farooq...." Wasu hawaye taji sun silalo mata ta kara wayar a
kunnenta tare da yin sallama yaja wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske yace “Kharimatu kina
inane Ina ɗana ko ƴata nasan zuwa yanzun kin haihu ko me kika haifamin?" Kallon ɗaliban nata
tayi da suma suke kallonta kuka me ƙarfi ya kwace mata cikin tashin hankali ya fara kiran kinga
Kharimatu kada ki ɗaga hankalinki faɗamin inda kike bari nazo ko kina gdansu Granny
ganinan....."
*Oum Hairan*
[11/11, 7:50 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ41-42 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Ƙit ta kashe wayarta ta juya ta fice daga ajin gabaɗaya ma ji tayi zaman makarantar yayi mata
ƙunci wannan tasata barin makarantar ta shiga gda tana shiga Mama Saude ta tareta da cewa
“meye kuma yake faruwa Kharimatu" bata iya bata amsa ba ta shige ɗaki ta kwantar da Jawad
itama ta kwanta tanaci gaba da rera kukanta tanajin wayar nata ring taƙi ɗagawa.
Mama Saude ce ta ɗauki wayar ganin sunan dake jiki yasata jan tsaki tace “Aikin banza akan
wannan sakaran mijin naki kike kuka to kiran me yake miki me zakiyi masa?" Ƙasa tayi da kanta
tace “nima bansani ba ina makaranta ya kirani" tsaki ta kuma ja tace “Ki daina ɗaga wayarsa
kwata² ki nuna masa kema kinada gata" Kallonta tayi cikin yanayi na damuwa ta buɗe baki zatayi mgn sai kuma ta fasa har lkcn kiran
wayarta yakeyi taƙ ɗagawa ƙarshe ma Mama Saude ta kashe wayar ranar hakanan ta yini
sukuku babu ƙwari sai dare ta buɗe wayarta saƙonnninsa suka rinƙa shigowa ba ƙaƙƙautawa
bata bata hankalinta wajen buɗewa ba ta gogesu taci gaba da harkokinta washegari da sassafe
Mama Saude tace ta shirya zasuje Patiskum taso tayi gardama ganin Mama Saude ta dage
yasata hƙr suka shirya suka bar Guru Gidan wata yayar Su Mama Yabi ne da Mama Saude a
Patiskum.
Bayan sun huta ne Mama Saude take bawa Hajiya Bushira labarin abinda ke faruwa
jinjina kai Hajiya Bushira tayi ta dubi Kharimatu tace “Kakar mijinki ta kawo shawara dole a cikin
ido ake tsawurya duk da lamarinku akwai shiga tsakani amma shima yayi sakacin da sai an
nuna masa kurensa zai gane yayi sakaci kiyi hƙr ki zauna anan har zuwa lkcn da tsohuwar nan
zata buƙaci ki koma sonki takeyi shiyasa take miki gata" itadai batace komai ba domin ba gurin
da zata ce ɗin bane tun farkonta tanajin tsoron masifar Hajiya Bushira shiyasa babu shaƙuwa
tsakaninsu saboda bata zuwa gurinta
Da yamma Mama Saude ta tafi ta barsu sukaci gaba da zama a gdan Hajiya Bushira suna
samun kulawa Hajiya Bushira akwai son yara ta kame Jawad ta goye kamar dama sun saba
Itako hutawarta kawai takeyi tun tana ƙirga kwanaki harta koma ƙirga satittika tafi² har watanni
biyar tama hƙr ta fawwalawa Allah ta cireshi a ranta yaronta yanata girma yana neman shekara
mahaifinsa baitaɓa ganinsa ba.
Wata rana suka shirya domin zuwa duba Zahra ƙanwar Aliyu data haihu akayi mata aiki ita da
Hajiya Bushira tunda suka shigo Kano gabanta ke faɗuwa suna zuwa gdan aka taresu da
murna Umaimah ta ɗauke Jawad ta fice dashi sunata mamakin girman yaron da kamarsa da
ubansa duk cikin yaran gdan babu me kama dashi kamar Jawad suna harabar gdan tanayi
masa lilo motar Aliyu ta shigo tun daga nesa ya zubawa yaron idanu gabansa na faɗuwa dake
tare take da sauran yaran suka fito idanunsa akan Jawad da keta dariya.
Yayi kamar ya wucce zuciyarsa taƙi aminta ya koma ya tsaya yana kallon yaron Umaimah ta
ɗebeshi ta watsar dake dama ita ba jituwa sukeyi ba.
Bai damu da kallon da tayi masa ba yakai hannu zai ɗauki yaron daidai lkcn da Kharimatu ta fito
daga parlourn tagansu tsaye yana ƙoƙarin ɗaukar mata yaro ta ɗaga murya da karfi tace “Karki
bashi ɗana Umaimah!" Ba shiba hatta ita Umaiman saida ta juya bata damu da yanda ya kafeta
da ido ba ta ƙarasa ta karɓi ɗanta a hannun Umaimah ta juya ta nufi sashin Granny.
Shikam Aliyu mutuwar tsaye yayi yana mamakin yanda yaron ya girma da irin muguwar
canzawar da Kharimatunsa tayi cikin lkcn daya ɗauka baiganta ba
Zama yayi a kan lilon ya kora yaran ciki yana tunanin to waishi me yaja masa wannan masifar
ne yana son Kharimatu Amma ya yasa gane meye yasa ya kasa kataɓus don ganin ta dawo
garesa gashi har ɗan su ya girma baitaɓa sanyashi a idanunsa ba wannan abin kunya da yawa
yake shikam baiga laifinta ba data hanashi taɓa mata ɗa shi kansa yanajin kunyar kansa idan
ya tuna yanada wani ɗan daya kasa basa haƙƙinsa na ɗa kamar sauran ƴaƴansa.
Miƙewa yayi jiki a mace cikin rashin laka ya shiga sashin Granny suna zaune sun baje a
parlourn sunata hirarsu da dariya Jawad nata haɗawa Granny shirgi tana masa tsiya babu
wanda yasan dashi a tsaye saida Kharimatu ta ɗago idanunta ya faɗa cikin nasa tayi saurin
kawar da kai tare da janyo Jawad ta matseshi a jikinta tasa masa nono yaron ya kama yana
dukan jikinta ta lumshe idonta tare da miƙewa zatabar gurin ya kira sunanta da sauri.
Sai lkcn Hajiya Bushira da Granny sukasan wainar da ake toyawa aikuwa Granny ta miƙe da
sauri tace “Kai gantalalle lfy?" Sosai kalmar Granny ta dakeshi batajin kunyar aibatashi akan
lamarin Kharimatu, cikin sanyi jiki yace “Am dama inason mgn da itane" harara ta zabga masa
tace “wa kakeson mgn da ita Kharimatun? Kasanta ne meye alaƙarka da ita zaka ɓacemin da
gani ko sai naci mutuncinka"
Tsayawa yayi zaiyi mata magiya ta ɗaga hannu ta ɗauke shi da mari tace “Aliyu bakaiba ko
ubanka Ma'aruf bai isa nabashi umarni yaƙi biba Kharimatu ta dawo gdannan inasonta a kusa
dani ba makaranta ma xansa Ma'aruf ya siya mata mota ta koma...." Da sauri yace
“Makaranta kuma Granny da izinin wa?" Murmushi tayi tace “ai batada nauyin kowa a kanta
aure ne nice dama nayi uwa nai makarɓiya Yabi Allah ya jiƙsnta ta ɗauki marainiyar Allah ta
baka dama saida Zahra tacemin Auren sha'awa kayi da Kharimatu naƙi yarda gashinan kuwa a
hankali komai ya bayyana daka samu biyan buƙatarka saika banzatar da ita to mu munaso
kuma Allah yanason kayarsa daga ita har Jawad ka cire su a lissafin ahalinka Kharimatu ta rayu
a gdannan iya rayuwata idan na mutu ta koma danginta na haramta maka ita Aliyu har abada
zan kira iyayenka su shaida"..........
*Oum Hairan*
[11/13, 12:33 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ43-44 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Wani abu yaji ya caki ƙirjinsa ya ɗago da sauri yace “Haba Granny meye yasa kike wannan
mgnr wlh tallahi ban auri Kharimatu domin cutar da itaba ke shaida ce inason Kharimatu Ni
kaina bansan meye yasa na watsar da lamuranta ba" ƙasa yayi ya durƙushe yace “Granny
kiyiwa girman Allah ki janye wannan furucin kinsani ina buƙatar iyalina a jikina Tunda Salma ta
haihu batada lfy kina gani sai me aiki na ɗauka saboda yar....."
Ɗaga masa hannu tayi ta juya tace “Ka iya tafiya wannan kaita shafa ɗannan ba damuwar
Hadizatu bace" kiranta ya rinƙayi taƙi sauraronsa ƙarshe ma ta shige ɗakin da Kharimatu take
zaune.
Kanta na ƙasa tana kallon yanda Jawad ya kafeta da ido tana share hawaye lkc zuwa lkc a
baya ta hƙr ta cire Aliyu a ranta meyasa yanzu data ganshi abubuwa suke neman jsgule mata
meye yasa ko taga laifinsa wani sashi na zuciyarta yake wsnkesa da gaske ne kalamansa shi
kansa baisan meye yasa yayi mata haka ba to amma meye yasa ya haɗa harda ɗanta shima an
rabashi dashi kenan?
Lumshe idonta tayi Granny na kallonta itama Hajiya Bushira kallonta takeyi cike da tausayi
itakam ƴartata tana bata tausayi abubuwa sunyi mata yawa ga maraici ga rashin miji damuwa
dole ta samu matsuguni a rayuwarta.
Muryar Granny ta tsinkayo tana cewa kada ki sake ki sawa kanki damuwa akan Aliyu Kharimatu
inada tabbacin Allah zaiyi miki sauyi mafi alkhairi tabbas Allah baya wulaƙanta marayansa da
yardar Allah duk wanda yake da hannu wajen rabaki da mijinki shima sai Ubangiji ya hanashi jin
daɗin tasa rayuwar" kuka ne ya ƙwace mata ta riƙo hannun Granny tace “Wlh inason cireshi a
raina na kasa Granny ki tayani da addu'a" shafa kanta tayi tace “mijinki na fari uban ɗanki ai
bazai taɓa ciruwa a ranki ba saidai ki koyi dakiya da shariya Kharimatu naji daɗin abinda kikayi
masa ko banza ya fahimci kinsan ciwon kanki kema kuma zuciyace a jikinki"
Sunata hirarsu da Granny da Hajiya Bushira itadai kawai kallonsu takeyi tana jan zuciya sai
Magrib suka tashi sukayi sallah ta kama hannun Jawad suka fito suka nufi cikin gdan yanata yi
mata gwarancinsa tana biye masa. Da sallama suka shiga Mom na parlourn tana ganinsu tayi
murmushi tana satar kallon Aliyu dake kwance tun ɗazu tunaninta ma bacci yakeyi sai yanzun
da taga ya buɗe idonsa akan Kharimatun tace “Au dama ba bacci kakeba kanaji ana sallah"
Tashi yayi zaune yana kallon Jawad da ya saki Maman tashi ya nufi kakarsa da tafiyarsa da
batayi ƙwari ba tararsa Mom tayi ta ɗagashi ta cafe tace “Wato girmanka Jawad yana bani
mamaki saikace ana buga maka iska" murmushi Kharimatu tayi tace “Haka kowa yake cewa
yayi saurin girma nikam bana ganin girman