Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
dubeta tace “Ya Aliyu yace kije ku tafi gobe Monday
sunada aiki" wani abu ya tokare mata maƙoshi abincin data zuba a bakinta yaƙi haɗiyuwa a
ranta tace “shikenan shi bawa bashi da hutu bashi da ƴanci a rayuwarsa?
Mama ce ta taɓa ta tace “ki tashi karkiyi laifi Haidar ba wuya bane fusatashi" miƙewa tayi sarai
tasan halinsa ko kayanta bata ɗauka ba ta fita yana zaune cikin mota ta nufi motar gabanta na
faɗuwa da kuma matsananciyar kunyarsa ta isa ta buɗe ta shiga bata ko samu arziƙin kallo ba
ya gama wayarsa yatada motar suka tafi har sukaje gdan bai tanka mata ba yana parking ta fita
yabi bayanta da kallo tare da taɓe baki.
Turus taja ta tsaya saboda ganin yanda parlourn yayi kaca² yaran duk sun ɓatashi da gudu
Jannat ta nufota ta ɗauke ta tana juyawa da ita tanayi mata dariya yarinyar ma na dariya daidai
lkcn da Salma ta fito Anam bataji tahowarta ba kawai sukayi karo aikuwa ta angajeta bisa
tsautsayi ta faɗa kan cup ɗin glass ɗin ɗaya fashe a parlourn aikuwa ta fasa ƙara saboda
nitsewar da kwalbar tayi a goshinta jini yayi wata irin tsartuwa ya fallatsa har jikin Aliyu dake
tsaye tun lkcn da Anam keyima Jannat wasa.
Da gudu ya ƙara so kanta ya ɗagota gabaɗaya jini ya wanke mata fuska yace “subhanallahi
Salma bakida hankali ne wasa fa takewa ƴarki shine zaki ture ta har kiji mata ciwo haka kefa
kika dameni naje na ɗaukota yara sun dameki dama abinda kika shirya yi mata kenan?"
Yana mgn yana tare jinin da hannunsa inda ita kuma Anam taketa jijjiga kanta daya ɗaure da
wani mugun ciwo, taɓe baki Salma tayi tace “to ko zaka rama matane Aliyu naga alamun kaji
ciwon kaima a jikinka" kallon Salman yayi rashin lkcn bata amsa yasashi kama hannun Anam
yace “Sannu Kharimatu tashi muje ayi miki dressing na gurin" miƙewa tayi tana layi saboda ba
ƙaramin jini ta zubar ba motar yaja a mugun guje suka fice daga gdan suka nufi wani asibitin
kuɗi a cikin unguwar ta Yankaba tasha wahala kafin su zare kwalbar sukayi dressing gurin
likitan ya dubesa yace “zatayita fama da ciwon kai dole ta rinƙa samun hutu" jinjina kai yayi ya
biya su suka fito har yanzu kuka takeyi bawai na zafin ciwon bane a'a tunawa da tayi cewa da
mahaifinta yana raye qila duk da haka bata rinƙa faruwa da itaba.
Sau ɗaya yace mata sannu har sukaje gda wani abin mamaki Salma Bata gyara gurin da jinin
ya zuba ba balle ta gyara parlourn Suna shiga Anam ta ɗauki tsintsiya zata share parlourn ya
dakatar da ita yace “kije ki kwanta kawai" aje tsintsiyar tayi ta nufi ɗakinta ta kwanta nandanan
kuwa zazzaɓi ya rufeta me zafin gaske a daren taci wahalar zazzaɓin batayi tunanin zatakai
safe ba hakanan dai ta rinƙa addu'o'in da suka sawwaƙa a bakinta har zuwa wayewar gari da
safe da wuri ta tashi domin shirya yaran zuwa makaranta ta kamasu tayi musu wanka tanayi
tana duba breakfast ɗin data ɗora harta gama ta haɗa masu gdan basu sauko ba ta zauna tana
rawar sanyi tana bama yaran abinci zazzaɓi na ƙara ƙarfi sanyin A.C na haɗa ta ita ba abin ta
kasheba matar gdan ta nakasata.
Gama sallamar yaran tayi takaisu ga driver ya tafi makaranta dasu hadda jannat dake itama
ansata juma'a ne bata zuwa ta dawo a wahalce ta rinƙa gyara gdan ta kusa gama parlourn taji
sun sauko ta durƙusa cikin ladabi ta gaishesu Salma ta ɗauke kai sai Aliyu ne yace “ya jikin...."
Kafin ta bashi amsa yaga yanda take rawar sanyi yace “ko zazzaɓi kikeyi ne?" Ɗaga masa kai
tayi ya matsa ya taɓa jikinta yaji zafi zau ya dubi Salma yace “ki ɗauki key na motarki ki tafi zan
Kaita asibiti" wani malolon baƙin ciki ne ya cika zuciyar Salma ta kuwa taso masa da cewa
“haba Aliyu wannan ai wulaƙanci ne akan wannan ƙazamar talakan zakace naje nayi driving
bayan kasan banason......."
Ɗaga mata hannu yayi ya dubi Anam yace “Ɗauko hijjab ɗinki Kharimatu" da sauri ta miƙe
domin shiga ta ɗauko hijjab ɗin jiri ya ɗebeta ji kakeyi tik ta zube a ƙasa ya isa da gudu ya
ɗagota ya fice da ita yasata a mota suka fita suna zuwa aka bata gado tsoron kira yake ya faɗa
yasan masifar Granny Indai tasan dalili to ba Salma ba shi kansa ya kaɗe har ganyensa. Ganin lkc na tafiya gashi yanada taro 9:30am yasashi yin shahadar kiran wayar Mama Yabi ta
ɗaga suka gaisa ya faɗa mata abinda ke faruwa aikam ta ruɗe tace “bansan yaushe Kharimatu
zatayi hankali ba kawai saboda sakarci taje zata illata kanta ganinan"
Ajiyar zuciya yayi ganin ya ɗorata ta ɗoru yaci gaba da zama gurin Anam tare da zubanta ido
yanda take kwance da drip a hannunta baccin wahala ya ɗauketa kanta sanye da hula fuskarta
wasai ga ɗaurin dressing ɗin da akayi mata jiya a hankali ya gangaro zuwa gangar jikinta yana
ƙare mata kallo tunda yake baitaɓa tsayawa ya ƙarewa Anam kallo ba sai Yau Nazeer abokinsa
yana yawan faɗa masa wato Aliyu babyn nan ta gdanka Anam tana matuƙar burgeni ɓoyayyen
kyaunta yana ruɗani bantaɓa gajiya da kallonta ba nikam da zan samu dama zanso abani
wannan yarinya matsayin mata nasan zanji daɗin hakan" taɓe baki yayi ya miƙe yana ƙare mata
kallo yace “kai kasan wani ɓoyayyen kyau Nazeer Ni bayyananne na sani".......
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc
0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
~Paid book~
Oum Hairan
7-8
Kiciɓis sukayi da Mama a ƙofar shiga ɗakin suka gaisa ta shige ciki ta zubawa ƴartata ido cike
da tausayi ƙarasawa tayi gabanta ta riƙo hannunta daidai lkcn data buɗe idonta tace mata
“sannu Kharimatu ashe haka tsautsayi ya faru dake kema kin cika gaugawa ki rinƙa bin
abubuwa a hankali kinji" lumshe idonta tayi tanajin ɗacin abinda ya faru da ita a ranta Aliyu ya
shigo da sallamarsa a ƙasan maqoshi ya ajiye ruwa da magunguna yace da Mama “tunda kinzo
zanje office inada Meeting zuwa tara da rabi" kuɗi ya zaro ya ajiye a gefen gadon tayi masa gdy
ya fice a ɗakin batare dako inda Anam take ya kalla ba.
Bayan fitarsa Mama ta haɗa mata shayi me kauri da madarar daya kawo ta zauna tana bata
tanaci daƙyar abincin ɗaci yakeyi mata a baki hakadai ta rinƙa turawa harta ƙoshi jefi² suke yar
hirarsu da Mama Anam ta kasa jurewa ta faɗawa Mama asalin abinda yaji mata ciwo har ya
haifar mata da zazzaɓin sosai Mama taji babu daɗi amma a fili sai tace “babu komai akwai Allah
da talaka da mai arziƙi duka wanda yayi su son abinsa yakeyi saboda haka komai yayi farko
zaiyi ƙarshe"
Ba haka Anam tasoba domin zuwa lkcn hƙrnta da zama a gdan Salma ya ƙare burinta kawai
barin gdan saidai batada wata hanya ta barin gdan dole saida shahalewar Mama, yini sukayi a
asibitin da yamma Aliyu ya dawo shida Granny tanata zubawa Anam sannu likitan yazo ya
sallameta yayi Hamdala domin bayaso asirinsu ya tonu yafiso ayi a lulluɓe mgnr ɗebe kayan
sukayi suka zuba a mota bayan sun shiga Granny tace “Ali wannan yarinyar gda zata wucce
gurin uwarta idan ta warke ta dawo wannan kasaltacciyar matar taka me shegen son jiki ba
ƙyaleta zatayi ta warke ba"
Bayason jan maganar dole ya amince saboda gudun tujarar Granny suka wucce Ɗan ladi nab
Sidi zuciyar Mama da Anam wasai suna zuwa ya zubesu ya juya ya nufi gdansa. A falon ya
tarar da Salma taci uwar kwalliya ta harɗe tana kallo tanacin donnut ya dubi yaran yagansu da
kayan islamiyya yace “ya haka Salma gobe babu makaranta ne?" Ɗagowa tayi tace “kayan naji
suna tsamin gumi shine nabarsu idan kun dawo waccen yarinyar ta wanke" jinjina kai yayi lallai
Salma batada imani wato wadda aka sallamo a asibiti take tsammanin tayi mata wanki lallai
Granny tanada hangen nesa.
Samansa ya haye yayi wanka ya fito ya zauna a dinning ya buɗe abinci ya faraci baici na kirki
ba ya miƙe ya nufi waje ya zauna a kujerun dake cikin flowers na gdan yana duba jarida
Bai koma cikin gdan ba sai bayan yayi sallah Magrib da isha sannan ya shiga ya nufi saman ya
shiga ɗakinsa ya sake watsa ruwa ya kwanta shiru yana jiran Salma har dare ya tsala yaja tsaki
ya juya lamarin Salma ta fannin kula da shimfiɗarsa yana bashi tsoro kullum ita cikin uzuri take
yau aiki gobe ciwon mara jibi zubar jini idan bataga damaba sai su shafe satittika a haka babu
ruwanta shikuma ga miskilanci Indai bata kawo kanta ba ya daina kiranta.
Wayewar garin ta shirya tsaf tana mita ta shirya yaran suka fice suka tafi aiki sukuma yaran aka
wucce dasu makaranta a mota take tambayarsa wai meye ya hana Anam dawowa? A gajarce
yace “ganin dama" daga haka tayi masa shiru shima yayi mata ya ajeta a ma'aikatarsu ya
wucce Campanynsu.
Kwanakin da Anam tayi tare da Mahaifiyarta abin gwanin daɗi ji takeyi kamar karta koma.
Ranar data cika sati tana ɗakin Granny sunata shirmensu Suka tsinkayo sallamar Aliyu saida
gabanta ya faɗi ya shigo ɗakin idanunsa na kanta hakanan ya riski kansa da wata muguwar
faɗuwar gaba lkcn da ya sauke idanunsa akanta cikin sati gudan da baya ganinta sai yaga
gabaɗaya ta canza masa tayi wani haske fuskarta tayi fiyau da ita, janye gashinta tayi daga
hannun Granny da take daure matashi tana ranƙwashinta tana cewa “ni banda tsiya Allah yayi
miki yalwar suma ki rinƙa neman lalatata da shirme idan tayi fushi ta kaɗe ai naga da uwar da
zakiyawa mijin da kishiyar gwalli"
Turo baki tayi tace “tabdi lallai ma Granny nikam ki dainamin fatan kishiya wlh ko sunan banson
ji" ba Granny ba hatta Aliyu saida ya zare tabarau ɗin idanunsa ya kalleta tayi ƙasa da kai ganin
irin kallon da yakeyi mata yasata jan mayafinta ta fice sumsum har taje bakin ƙofa yace “ki
shirya zamu tafi gdan babu kowa Salma ta tafi Ziyarar aiki Sokoto sai yara"
Amsawa tayi cikin ladabi duk da bataso hakan ba amma ya zatayi ta fice ta nufi cikin ta ishe
Hajiya Muniba a parlour tayi mata sannu da gda ta amsa mata a yatsine ta wucce ta tarar
Mama hatta haɗe mata kayanta dauka kawai tayi tana hawaye ta fita daidai lkcn da yake fitowa
a sashin Granny ya shiga gdan bai jima ba ya fito ya shiga motar itama ta shiga suka wucce.
Yaran sai murna sukeyi ta dawo itakuma tana ƙunci sarai Aliyu ya lura bataso dawowar ba daga
yanayinta baisan dalili ba duk sai yaji ya tsargi kansa da takura mata to amma ya zaiyi zaman
gda daga shi sai yara bazai yiwu ba itakuma Salma yanayin aikinta yana yawan sasu yawo.
Kayanta ta ɗauka ta shige ciki yabita da kallo shi kansa baisan meye yake kallo a jikinta ba
amma tabbas yasani ba tun yau ba wani abu yana burgeshi game da yarinyar a hankali batare
daya sani ba ya kira sunanta taja ta tsaya cikin fargaba tare da juyowa shikansa baisan dalilin
kiran ba yace “am ki dafamin coffee ki kawomin ɗakina" saida taji wani ras da yace ɗakinsa
domin a tarihin zamanta na gdan batajin ta taɓa shiga ɗakinsa yananan bai bata dama ba har
marinta saida yayi akan aikenta ma da Salma takeyi tun lkcn ta daina gigin zuwar masa
ɗaki........
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc
0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
Paid book
Oum Hairan
9-10
Shiga tayi ta aje kayan ta fito ta nufi kitchen yaran suka biyo ta musamman Farooq yana ce
mata “nifa yunwa nake ji daddy indomie kawai ya bamu" jinjina kai tayi ta kunnan kan Gas biyu
ɗaya ta doransa coffee ɗaya ta ɗora abinci ta riga gama dafa masa coffee ɗin ta ɗauka ta nufi
ɗakin nasa ta ƙwanƙwasa yana zaune ya zuba uban tagumi baisan abinda zuciyarsa take shirin
aikatawa ba amma tabbas tana tunzurashi ya aikata wani abu saidai shi kansa yanajin faɗuwar
gaba idan ya tuna abin mai wahalar yuwuwa ne bayan haka ma zuciyarsa kamar ba adala bace
a cikin sati guda tunanin nan ya fara bijiro masa wanda ya ɗarsu domin nemawa yaransa mafita
shin tayaya ma Anam zata amince da wannan shirin nasa? In itan ta amince mahaifiyarta da
mahaifansa zasu yarda? Musamman ma Hajiya Muniba.
Ya jinjina wannan lamari yafi a ƙirga kafin ya ankare da taɓa ƙofar da akeyi yabata izinin
shigowa ta buɗe ta shigo da sallama a bakinta amma kanta a ƙasa yake ta ajiye masa flat ɗin
data jero kofunan ta miƙe zata fita yace “am bakiji ba...." Tsayawa tayi tare da juyowa ta koma ta
tsugunna tace “Na'am" zubanta ido yayi ya kuma kasa cewa da ita komi har saida ta gaji tace
“Abinci na ɗorawa su Farooq zai iya ƙonewa"
Numfashi ya sauke ya bata izinin tashi ta miƙe ta fita ta koma kitchen ɗin ta tace shinkafar data
ɗora ta zuba musu miyar data dumama ta ɗauka suka fito Parlourn tana bawa jannat Muwaddat
da Farooq sunaci yanda yaran sukecin abincin zai tabbatar maka da gaske yunwa sukeji.
Sunci abincin sosai ta gyara gurin ta jasu ɗakinsu ta kwantar dasu bayan tayi musu wanka
itama tayi tayi sallar Magrib da isha da bata samu tayi ba ta kwanta a cikinsu tana rungume da
Jannat tayi musu Addu'a bacci ya ɗaukesu dukkansu.
Fitowa yayi domin duba yaran ya buɗe ɗakin ya shiga tare da kai hannu ya kunna glub gabansa
ya fadi ganinta kwance tsakiyar yaran ya daɗe tsaye yana kallonta luguden zuciyarsa na
ƙaruwa a kallo na zahiri baya hango wani abu dake burgeshi ga Anam Amma ya fahimci
zuciyarsa ta jima da sanya masa wasu alamomi masu neman fassara. Juyawa yayi ya fice zucciyar tasa cike da tunanin ta inda zai fara aikinsa tabbas lkc yayi da ya
kamata ya samawa yarinyar yanci wanda ya farajin ɗarsuwar dacewar sa daga tausayi, ya ɓata
dogon lkc yana tunanin rikicin da yake shirin ɓallowa kansa da Anam Amma zuciyarsa taƙi
karaya a ƙarshe wayarsa ya ɗauka ya turawa abokinsa Nazeer cewar gobe su haɗu a office
yanason su tattauna. Hakance ta faru washegarin kamar yanda Anam ta tashi da wuri haka
shima ya tashi lkcn daya fito tana kitchen tana haɗa abin karin safe tana goye da Jannat da
tayima wanka ta juyo ta ganshi tsaye a ƙofar kitchen ɗin ta sunkuyar da kanta tare da gaisheshi
cikin ladabi ya amsata yace “ina sauri ne" daga kai tayi tare da ɗaukar kayan data gama dasu
takai dinning ta dawo ta gyara kitchen ɗin ta shirya yaran ta miƙawa driver su ya tafi kaisu
makaranta hakan yabata damar sake kwanciya.
*********
Duban juna sukeyi da Nazeer kowa yana sauke numfashi inda Nazeer yake goge zuffa ya ɗago
cikin tsananin mamakin abokin nasa yace “ƴar aikin gdanka kakeji kanaso kuma so na aure? To
ya kuma zakayi da masifaffiyar matarka me baƙin kishin masifa?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya aje biron da yake wasa dashi a hannunsa yace “abinda nakasa
samun amsarsa kenan am ni Ina ganin idan harsu Hajiya sun amince bazai zama matsala ba
asanya rana gajeriys cikin sirri zanyi ƙoƙarin nema mata gida ƙarami nasata a ciki kafin komai
ya daidaita bansan meye yake damun mata ba sun gaza ta ɓangarori da dama na auratayya
amma daga lkcn da namiji yayi niyyar ɗauko musu wacce zata tayasu sai suyi tsalle suce
basusan zancen ba duba dai Nazeer kaga rayuwar gdana nasani duk da cewar Salma Bata
cikin matan da zaayima tambarin ƙazanta Amma fah da taimakon Anam kullum kaje gdannan
Anam Bata tsaye bata zaune itace kula da yara gda da masu gda to inda zata iya ɗaukar
wannan aikin meye yasa bazan gayyato ta tazo ta tayamu rayuwar har abada ba? Am Bama
wannan ba Nazeer duk da cewar Ni bana cikin jinsi na maza masu takura ko yawan buqata
hasali ma ta wannan fannin inada rauni amma fah a hakan duk lkcn dana buƙaci Salma sai ta
kawomin uzuri kuma fah duk da haka cewa takeyi Ni ragone"
Shafa ƙeya Nazeer yayi yace “hakane
saidai kasan tunanin mata ya bambanta da namu sukan a ɓangarensu wannan babban abin
kunya ne zaka aikata tabbas za'ayi surutu Bama iyakar surutu ba harda abinda yafi surutu to
amma dake ka shirya saika fita da qwanjinka idan rabone sai kaga ka dauka"
Miƙewa sukayi tare suka fita sun jima jikin mota suna ƙara tattaunawa sannan sukayi musabaha
suka rabu kowa ya shiga motarsa lkcn da yaje gda bai iske kowa ba a parlour ɗakinsa ya shiga
ya cire kayansa ya watsa ruwa ya sanya jallabiya ya sauko ƙasan ɗakin Anam ya nufa ya
ƙwanƙwasa ta miƙe a gyaran wardrobe ɗin da takeyi ta buɗe yana tsaye da cup a hannunsa ya
zubanta idanunsa masu kama da wanda kejin bacci ta sunkuya cikin nutsuwa tace “barka da
dawowa" lumshe idonsa yayi yanajin muryarta na ratsa sassan jikinsa yace “ina yaran nan?"
Sunkuyar dakai tayi tace “dake juma'a ce Zeeze tazo ta ɗaukesu wai Aunty Salma tace tazo ta
ɗaukesu suyi weekend acan"
Jinjina kai yayi yace “ina buƙatar abinci" yana faɗin haka yayi gaba ta