Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
tayar da sallar bayan
ya idar ya dubeta tare da nuna mata bathroom yace “kije kiyi alwala kizo muyi sallah"
Bathroom ɗin ta shiga ta ɗauro alwalar gabaɗaya a tsorace take dashi kallon da yake mata yafi
komai tayar mata da hankali hakanan idan ta tuna haduwarsu kwanaki sai taji tsoronta ya ƙaru,
sunyi raka'a huɗu ya dafa kanta yayi mata addu'a ya riƙo hannunta yasa yatsansa a tsakiya
yana shafawa a hankali tanajin wani yar a jikinta yayi ajiyar zuciya ya janyo ledar daya shigo da
ita ya buɗe sai ƙamshi takeyi tana tururi tsire ne da yaji kayan lambu ya ɗauka yakai mata
bakinta ta kawar dakai ya ɗaure fuska yace “banason gardama kinsanni"
Hakanan ta karba sukaci suka sha yasata tayi brush ya fita bai jima ba ya dawo ya miƙa mata
rigar bacci ta karɓa tana juyata yace “kisa ki kwanta" ɗagowa tayi idanunta sun cika da bacci da
hawaye tace “ka taimakeni Daddy Farooq ka mayar dani gda Allah tsoro nakeji" lumshe
idanunsa yayi ya buɗe kawai ya koma jikin window yana kallon ɗaiɗaikun mutanen dake
wuccewa ganin bashi da niyyar yi mata abinda take biɗa ne yasata ta janyo duvet na gadon ta
shimfiɗa a ƙasa ta janyo pillow ranta a tafashe tayi wurgi da rigar ta kwanta a ƙasan yana can
yana kalle²nsa baisan abinda take ba saida ya juyo.
Ganinta a ƙasa ya bashi dariya ya fara rage kayan jikinsa idanunsa na kanta ta dunƙule guri
ɗaya sai juyi takeyi, saida ya rage dagashi sai boxes yaje yayi brush ya ɗauki wani body spay
ya fesa ya kashe hasken ɗakin ya haye gadon ya kwanta yana me karanto addu'ar kwanciya
bacci. Bawai baccin yake ba don ya ƙwallafa ransa akan abinda yasa ya ɗaukota yau shiyasa baccin
ma ya gagareshi, yanajin numfashinta ya sauya ya miƙe ya sauko ya ɗagata cak ya azata a
gadon ta miƙe zumbur yayi saurin mayar da ita ya kwantar ya kwanta a gefenta yana ɗaukar
wayarsa dake ring ganin number Granny yasashi kashe wayar gabaɗaya. Ya janyota jikinsa ta janye tare da kai masa duka abin ya bashi dariya sosai yace “Waike
meye yake damunki ne?" Batayi masa mgn ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya matseta a jikinsa
ta yanda bazata iya motsawa ba taja yaja dole ta sakar masa tanajinsa yana sarrafata yanda
yaga dama bata da mafitar data wucce kuka haka ta rinƙa rera kukan duk da yanaci masa rai Hakanan yaci gaba da tafiyar da ita har ya cimma inda yakeso yaje ta sauke rirriƙeshi tana kuka
me ban tausayi tanayi masa magiya da yaruka kala² turanci Hausa barbanci duka shikam baima
jinta bare ya fahimceta saida ya ƙarar da mgnrta sannan ya fara samun kansa cikin mintinan da
basu wucce 40 ba gabaɗaya ya canza mata halitta ya massheta cikakkiyar mace da wuya da
azaba yasata suma
Saida nutsuwarsa ta dawo jikinsa sannan ya fahimci halin da take ciki ya miƙe da sauri ya nufi
bathroom ya jiƙo towel ya dawo ya rinƙa mammatsa mata
Jikinta ta sauke ajiyar zuciya tana tsiyayar da hawaye a idanunta ya sauke numfashi ya ɗagota
ya haɗata da jikinsa yana shafa bayanta ya kasa yi mata mgn wani tausayinta yana zaga jikinsa
daqyar da rarrashi ba furuci ya samu tayi shiru ya taimaka mata tayi wanka ta dawo ya bata
paracetamol tasha ta kwanta ya rufeta baccin wahala ya ɗauketa.
Shima kwanciya yayi ya zubanta idanu yana kallon yanda take sauke numfashi a wahalce yana
shafa gashin dake kwance saman goshinta da haka bacci ya ɗaukeshi sukayi bacci cikin
nutsuwa da asuba ya tashi ya tasheta jikinta zafi zau haka sukayi sallar ta sake kwanciya
tanajin yanda jikinta yayi tsami duk da gasa jikinta data ƙarayi.
Shima da yayi sallar kwanciya yayi basu tashi ba sai 10:00am ya fita ya samo mata abinda
zataci suka karya ya dubeta da kulawa yace “Zan kaiki gda ko zaki zauna anan sai zuwa anjima
kin ƙarajin ƙarfin jikinki?"
Sunkuyar dakai tayi yayi murmushi yace “Kuma kunyar ta meye?" Batayi masa furuci ba sai
miƙewa da tayi tasa mayafinta ta nufi ƙofa ya miƙe yana kallon tafiyarta yana dariya ƙasan
zuciyarsa da taimakonsa suka fita ta shiga motar yaja suka tafi, suna zuwa kafin ya gama
parking ta buɗe motar ta fice tayi dururu ta faɗa gurin Granny bazata iya shiga cikin gdan ba
kunya takeji batasan aikin banza tayi ba Mama Yabi tana ganinsu.
Tana shiga Granny ta miƙe tace “Naga ta kaina Ni Sa'ade wannan gantalallen yaron yakai ɗan
kuka wato bazai iya bari ki tare ba shine saida ya fafake ki to yadai shiga hankalinsa ya kwanta
ɗan banza zaizo ya sameni, koda yake algunguma kema so kike shiyasa kika badakai"
Itadai bata da lkcn cakaki da Granny ta shige ɗakin ta kwanta
tanajin yanayin baƙo a jikinta da haka bacci ya ƙara ɗauketa batasan sanda ya shigo ya fita ba
sai azahar Granny ta tasheta tare dayi mata sannu yanda take lallaɓa jikinta ba ƙaramin tausayi
ta bawa Granny ba hakanan tayi mata ƴan jiƙe²nsu na tsoffi ta bata tasha sannan ta ɗan samu
ƙarfi ta shiga gdan suka gaisa da Momy tana bin surukar Tata da kallon tuhuma yanayinta kaɗai
ya isa ya nuna wani abu ya faru da ita.
Bata zafafa ba tana kallonta ta shige ɗakin gyatumarta ta ishe mama saman sallaya ta zauna a
kaikaice suka gaisa tace “yau zukuɗun najiki shiru koda yake Granny tace bakida lfy ne meye
yake damunki?" Sunkuyar da kanta tayi ƙasa cike da kunya tayi shiru, sarai Mama tasan dama
bazata iya faɗi mata ba shiyasa itama bata zafafa da tambayar ba taci gaba da lazuminta bayan
ta gama ta miƙe tace “ki ɗauki wancan rubutun kisha maganin sammu ne ɗazu Hassan ya kawo
shi wai Granny ce tasashi ya rinƙa yi miki"
Batayi gardama ba ta karɓa ta sha da bismilla ta ƙara bin katifar Mama haka ta yini a kwance
kamar ruwa abinci ma ta kasa ci sai ruwan zafi kawai da takesha sallah kawai ke tashinta har
Magrib ta tashi daƙyar ta shiga wanka ta fito ɗaure da towel a ƙirjinta.
Ja tayi da baya da sauri daidai lkcn da Mama ke fita daga ɗakin taja ƙofar Aliyu ya miƙe ya
nufota ta janye da sauri yakai hannu ya riƙota jikinta ya fara rawa ta buɗe baki zatayi mgn ya
haɗe bakinsu yana sakar mata wani zazzafan kiss ta rintse idonta tanajin yanda yake tsotsar
bakinta kamar ya samu sweet a sanyaye ya saketa yana mayar da numfashi yace “kinajin
tsoron karna ƙara ne?"
Saurin ɗaga masa kai tayi yaja numfashi yace “idan kika tare a gdana ma haka zakike jin
tsorona?" Ƙasa bashi amsa tayi yayi murmushi ya sanya hannu ya zare mata towel ɗin tare da
matsawa jikin ƙofar ya murɗa mata key.
Itadai Kharime tana tsaye jikinta sai ɓari yakeyi zuciyarta bugawa takeyi da ƙarfi yace “kinga
nifa ba wancan abin zanyi miki ba ko a gidana kike zan ɗaga miki ƙafa ki warke kafin na ƙara
shiga kawai Breast zaki bani nayi wasa dasu kaɗan na ɗan rage zafi" kafin tace komai ya
kamota ya haɗata da jikinsa ya fara shafa mararta zuwa ƙirjinta da salonsa me tsayawa a rai.
Sun jima kafin yaja wata ajiyar zuciya ya saketa yana kallonta cike da ƙauna yace “gsky bazan
jureba Kharimatu zanyiwa Dad mgn su bani ke kafin na ɗauke ki" itadai batada bakin cewa
dashi ƙala ya tashi yace idan kin gama azumin mgnr mayi mgn a waya" zaro kwalin waya yayi
sabuwa dal ya miƙa mata ya sake miƙa mata wata leda yace “Granny tace yau gabaɗaya bakici
abinci ba zan kira na tambayeta idan kinƙi ci zan dawo zan ciyar dake da kaina sannan kema
zaki ciyar dani"
Karɓa yayi sai lkcn ta magantu tace masa “na gde Allah ya ƙara arziƙi" jin addu'ar tata yayi har
cikin ruhinsa yace “na gde ya juya ya buɗe ƙofar ya fita ta aje wayar da ledar ta dauki rigar
baccinta ta sanya ta zura hijjab tayi sallar Isha sannan ta buɗe ledar nama ne gasasshe sai fura
damammiya sai ice cream da tarkacen chocolate cake da sauran kayan ciye²
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ27-28 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Neman guri tayi ta zauna ta zubawa kayan idanu a haka Mama ta shigo ta ishe ta a zaune ta
rafsa uban tagumi tayi murmushi ta zauna tare da dafata ta ɗago firgigit ganin Mama yasata jan
numfashi ta cire hannun Mama tace “Banyi tunanin zaki samu kulawa daga Aliyu irin haka ba
saboda yanayin izzarsa da kwarjininsa da kuma soyayyar da yakeyiwa matarsa Kharimatu shi
namiji da kike ganinsa kamar yaro ƙarami haka yake duk inda yafi samun kulawa nan
hankalinsa yafi karkata na fahimci akwai dalilin auren nan naki da Aliyu ya aureki ne domin
wasu dalilansa koda yake dalilansa suna da ƙarfi matuƙar zai kwatanta adalci, nidai fatana Allah
ya tsaremin ke"
Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannunta ta ɗauki wayar daya kawo mata tana dubawa waya ce
me tsadar gaske ta girgiza kai tana ƙara bin wayar da kallo iyakar tunaninta bata taɓa kawo
ranar da zata riƙe waya me tsadar wannan ba taci naman sosai ita dama masoyiyar kayan
sanyi tasha ice cream ta kwanta itadai Mama binta kawai takeyi da kallo tana mamakin irin
sanyin da ɗiyar tata tayi duk da dama ita ba ma'abociyar hayaniya bace.
Da dare ne wayar tayi ta ring ta janyota ganin sunansa akan sensor yasa gabanta faɗuwa haka
dai tai ƙarfin halin ɗagawa baijata da doguwar mgn ba tambayarta kawai yayi taci abincin tace
eh ya kashe, tun daga wannan ranar ya zamewa Aliyu farilla kullum sai yazo gdan ya ganta
kafin ya fita aiki wataran idan ya dawo ko kuma yace abashi ita zasuje unguwa ran Mama
bayaso saidai bazata iya ce masa a'a ba shida matarsa Granny cema me ƙoƙarin hanawa to
itama dole tanada iyaka musamman da yaje yayi mata daɗin baki ya kasheta da kalamai
shikenan tayi muƙus a gdan ma idan yazo sai ya kira Anam ɗin sashin Granny ya lallaɓeta da
yaudararrun kalamansa ya samu nutsuwa da ita tun tanaƙi har ta saduda.
Satin Salma uku a Niger ta dawo 9ja a lkcn shirye²n bikin yayi nisa sosai don har kayan amarya
ankai sabon gdan daya gina mata komai Abba ne yayi mata tarkacensu ne na barebari kawai
sukayi kayansu duk akaje aka jere a gdan ana jiran sati yazo akai amarya ɗakin mijinta.
Cikin kwanakin da aketa shirye²n shagalin bikin ne kuma ɗif ya ɗauke ƙafarsa a gdan nasu
babu wanda ya kawo wani abu kowa yabar abin a cewa hidima ce tayi masa yawa Anam ce
kawai jikinta yayi sanyi ganin ko waya ya daina kiranta ana saura kwanaki biyu bikin har an fara
shagalin biki ana saura kwana uku bikin suka ɗunguma ita da Mama suka koma Guru acan
zaaje a ɗaukota ranar da zasu tafin ne ta kira shi a waya kira uku bai ɗaga ba sai a na huɗu ya
ɗaga yace ta fito harabar gdan yana jiranta.
Ta zari mayafinta ta fito da zaƙuwa saboda sun kwana biyu basu haɗu ba tun daga nesa ya
kafeta da idanunsa kallon kusan faɗuwa yasata daƙyar ta iso gareshi har zuwa lkcn ita yake
kallo ta tsugunna tace “Ina yini" numfashi ya sauke ya cire hularsa ya shafa sumarsa yace “kina
lfy kinjini shiru amma baki nemeni ba" ƙasa ta sakeyi da kanta cikin kunya tace “nayi tunanin
hidima ce ta ɓoyeka" murmushi yayi yace “daba ita ce bafa?" Nuni yayi mata da ta miƙe ta tashi
tsaye tana wasa da zara²n yatsunta ya kwantar da kansa jikin mota yace “Granny ce tayimin
tsakani dake shiyasa na ƙaurace miki"
Da sauri ta kalleshi ya ɗaga hannunsa ya ɗora daidai goshinsa yace “amma kiyi hƙr nasan
zuciyarki ta ayyana miki wasu abubuwan ko? Am kamar me dame ta ayyana miki nasan dai
tace miki Aliyu ya gujeki ya daina kiranki ya daina zuwa inda kike, bayan haka sai me?" Dariya
tayi da ta bayyana kyawawan Haƙoranta ya zubanta idanu yana murmushi yace “naso ayi
komai anan a gama Abba yace a'a saidai ayi a garinku okey ki kasance cikin aminci kiyimin
tanadin Pure honey da zaki shayar dani a daren angwancina" turo baki tayi tace “meye ma ya
rage bayan komai ka kwashe....." Rufe mata baki yayi yace “Aa bari faɗa ban ɗauki komai ba
kawai rage zafi nayi za dai ɗauka zanci na ƙoshi ranar da su Granny bazaa sanyamin idanu ba.
Juyawa tayi zatabar gurin yayi saurin riƙota ya haɗata da jikinsa yace “Da banida wani uzuri
tare zamu tafi amma babu komai saura ƙiris" haka ya rinƙa yi mata kalami duk ya kashe mata
jiki kafin yace “kinsan me" girgiza masa kai tayi ya matso kusa da ita sosai yace “ina sonki...."
Kwasa tayi da gudu tana waiwayensa tana dariya shima yanayi mata dariya baibar gdan ba
saida yaga tashin motarsu.
Suna ɗagawa juna hannu cike da shauƙin juna har sukayi nisa sannan ya hƙr tunda motarsu ta
tashi yaji gabansa na faɗuwa jikinsa duk ya mutu hakanan ya tsinci kansa cikin kewarta daƙyar
yaja motarsa ya nufi gdanta da yasa aketa shiryawa ya zauna a falon ya zubawa manyan
hotunan su idanu tsayin lkc ya shagala da kallon hotunan daya sanya akayi musu manya ya
kafesu a falon kyawunta sihirtacce ba kowa yake gane tana da kyau ba sai wanda yasan asalin
sirrin kyau shi kansa a farko idan Nazeer yana yaba kyawunta musawa yakeyi sai yanzu ya
gaskata itaɗin kyakkyawace ta kwatance musamman cikin watanni biyun nan daya gyarata da
manya mayuka oily skin nata sai wani ɗaukar idanu sukeyi.
Wayarsa ce ta katse masa tunanin Second wife ya gani a rubuce saman sensor na wayar ya
ɗauka da sauri tare da lumshe idanu ya kara a kunnensa kafin yayi mgn yaji hayaniya ta cika
masa kunne ya miƙe da sauri tare da cewa “Khamilu ina Kharimatun...." A ɗaya ɓangaren akace
“mal ka nutsu mun tsinci wannan wayar ne a cikin wata jaka Allah yasa babu security so muna
dubawa sai mukaga wannan number ansa Zaujhnoor shiyasa muka kiraka....." Katseshi yayi da
cewa naji malam ina matata kardai kacemin hatsari sukayi ida drivern ina Mama?" Wani ne ya
karɓi wayar yace “bazamu tantance komai ba amma dai an ɗaukesu ankasu asibitin Dutse
saboda yafi kusa da inda sukayi accident ɗin so ana buƙatar makusantans......"
Bai gama sauraron wayar ba ya fice da gudu ya shiga mota ya fice a gdan cikin tashin hankali
shidai bazaice ga yanda akayi yaje Dutse ba sai ganinsa yayi a cikin asibitin yana zuwa ya tarar
da Alh Ma'aru a asibitin lkcn suna emergency ana ƙoƙarin ceto rayuwarsu abu da ƙarar kwana
an samu nasarar samun rayuwar kowa amma banda ta Mama Yabi Allah ya karɓi rayuwarta a
wannan hatsari inda Khamilu ya samu karaya huɗu Ita kuwa Anam doguwar suma da Ɓarin
cikin da babu wanda yasan dashi ta samu sai karaya ɗaya a ƙafa.
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ29-30 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
09031307566
Tashin hankali da ɗimuwar da Aliyu ya kasance a ciki ba kaɗan bace daƙyar da rarrashi Abba
yasashi ya nutsu tare da nuna masa hƙr shi ya kama da dauriya saboda Anam a gurinsa kawai
ya rage zata samu nutsuwa idan shi bai nutsu ba taya ita zata nutsu?
Da wannan kalaman ya ɗan samu salamar zuci ya zubawa amaryar tasa ido da take cikin halin
suma sosai yaji takaicin suɓcewar cikin nasa duk da kasancewar baisan sashi ba a ransa yake
raya da yanzu yaransa sun kusa zama huɗu fah rashi biyu sukayi ga rashin surukarsa ga rashin
cikinsa, a haka Su Mal Datti kakan Anam sukazo aka tafi da gawar Mama zuwa Kano don tafi
kusa domin a sutura ta Aliyu baije ba haka ya wanzu a asibitin sai yammaci liss komai ya ɗan
tsagaita sukayi transfer ɗin petiant ɗin zuwa asibitin Mal Aminu Kano aka ɗebe su a Embulance
zuwa Kano Granny ke jinyan Anam cike da tausayi da jin ƙai tana tuna kalaman yarinyar a mafi
yawan lokuta idan anyi zancen mutuwa takance mata.
Granny nidai fatan da nakeyi kada mutuwa ta ɗauke min Mama tabarni nikaɗai ina Gantali a
duniya wlh duk ranar dana buɗi ido naga babu Mamana a gefena tabbas idan nima ajalina bai
rigaya ba to kuwa sai an rinƙa haɗamin da addu'a domin tsaf zan iya zaucewa"
Hawaye ta ɗauke a idanunta yau ga ranar da take tsoron zuwa ta iso babu mama Yabi
mutuniyar kirki da duniya bata ɗaɗsta da ƙasa ba gashi abin yazo mata a daidai lkcn da tafi
buƙatarta fiye da komai, Granny ta Jima tana alhinin wannan rashi kafin ta tashi ta nemi
makwanci ta kwanta haka suka wanzu a asibitin wajen kwana huɗu sannan Anam ta fara
dawowa hayyacinta.
Ta fara buɗe idonta tana me ambaton sunan Allah a hankali ta fara sauke idanunta kan
mutanen dake zagaye da ita ta jima idanunta akan Aliyu da shima ya kafeta da idonsa da suke
cikin farin glass a nutse ta ɗaga hannunta ta miƙa masa ya kama hannun nata ta yunƙura alamu