Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
sun nuna masa tashi takeson yi ya ta rintse idanunta tanajin azaba da zugi a hannun nata daya
karye ta saki wata yar siririyar ƙara data sanyashi kallonta ta buɗe idonta da hawaye ke ƙoƙarin
gangarowa a hankali cikin muryar tausayi yace mata “Sannu" daga masa kai tayi tana kallon
Granny da taketa matsar hawaye a kasalce tace “Granny meye ya kawo mu nan ina Mama...."
Ƙasa taga Granny tayi da kanta yayinda Aliyu ya fice daga ɗakin da sauri, dukkansu tabisu da
kallon rashin fahimta tanabin hannunta da kallo ta zuro ƙafafunta ƙasa ta tashi tsaye tana layi ta
nufi Granny ta Kama hannunta tace “Idan zan iya tuna wani abu kamar hatsari mukayi ko
Granny please ki faɗa min ina Mama inje inganta ince dai ita bataji ciwo ba?" Rungumeta
Granny tayi da Muryar kuka tace “kiyi hƙr Kharimatu duk abinda da Ubangiji ya zartas akan
bawa shine daidai tabbas mutuwa batada daɗi musamman ta iyaye Kharimatu muna tayaki
alhinin rashin salihar mahaifiyarki Ubangiji yasa lahirarta tafi duniyarta...."
Tun kafin Granny ta ida rufe bakinta sabuwar tashin hankali tayi wankan tsarki ta samu gurbi a
ilahirin sassan jikin Anam ta rinƙa kallon Granny kanta na juyawa tana ganin abubuwa hurhuɗu
kafin kace meye wannan ta sake zubewa a ƙasa luuuuuu.
Daidai lkcn da Aliyu da likitan suke shigowa suka nufota a guje Aliyu ya tallafota yana kiran
sunanta amma ina babu alamun zatayi motsi, ɗagowa yayi ya dubi Granny yace “Fada mata
kikayi ko?" Share hawayenta tayi tace “To Gadanga meye amfanin ɓoye mata abinda dole zata
sani?" Shiru yayi cike da jin takaicin abinda Granny ta aikata ya ɗagata ya ɗorata a gadon ya
kwantar da ita likitan yayi yan aikace²nsa ya fita daidai lkcn da Momy ta shigo asibitin suka
gaisa da Granny ta tambayeta me jiki ta bata lbrn farkawar ta Hajiya Muniba ta jinjina kai tace
“Insha Allahu zata tashi rashin Mahaifiya da ciwo saidai Allah ya bamu ikon yi musu addu'a"
A ranar Anam Bata sake farkawa ba sai kashegari ta tashi lkcn Aliyu bainan sai Granny kaɗai
shassheƙar kukanta ne ya ankarar da Granny ta farka ta isa gareta tanayi mata sannu ta ɗago
tace “Yanzu shikenan Mama ta tafi ta barni? Shikenan bazan ƙara ganinta ba bazan kuma jin
kalamanta ba Granny ta tafi kenan?" Kama hannunta Granny tayi tace “Haka Allah ya tsara sai hƙr da abinda baka isa ka canza ba
Kharimatu kedai kiyita addu'a kuma kiyima mijinki biyayya likitan da ya karɓi Habiba kafin ta
rasu yace second 2 kafin rasuwar ta sunanki da mijinki take ambato tana barin wasiccin kada a
fasa kaiki gdan mijinki tare da faɗawa likitan ya faɗawa Aliyu ya riƙe ki amana ke har rubuta duk
abinda ta faɗa likitan yayi sannan ya sanya mata kalmar shahada tayi ta cika"
Kwantar da kanta tayi jikin Granny tanata kukanta me ban tausayi a haka Abba da Aliyu suazo
suka ishesu Abba yace “Assha Kharimatu meye na kukan hƙr ai ya zama dole agun duk wanda
irin haka ta sameshi" zama Aliyu yayi kusa da ita ya kamota ta dawo jikinsa ya rinƙa shafa
bayanta yana raɗa mata “Sorry Please!" Salma dake tsaye kamar gunki ta haɗiyi takaici iya
takaici tayi kamar ta juya saidai kuma ta tuna kalaman Yaya Ameey dole ta haɗiye kishinta ta
matsa tace da Kharimatu Sannu ya jiki" a hankali ta ɗago suka dubi juna ta janye a jikin Aliyu
cike da kunya da tausayin kai tace “Da....da...sauƙi" taɓe baki Salma tayi ta harari gefen da
surukarta take tace “Allah ya ƙaro afuwa ya jiƙan Mama" duk ɗakin saida suka amsa da Amin
banda Granny da Hajiya Muniba da kusan itace Ummul aba'isin zuwan Salma dubiyar har gda
taje ta sameta tayi mata tatas tare da nuna mawa Aliyu gangancin da yakeson yayi na rusa
gdansa daga tushe wannan tasa yace “Indai batazo ta duba Kharimatu ba to karya dawo ya
tarar da ita.
Tana gama dubiyar da batakai zuci ba ta juya zata fita Aliyu ya kirata ta tsaya yace “Ina zaki?" A
gajarce tace “Gda" murmushin takaici yayi yace jirani mu tafi" batada zaɓi haka ta dawo ta
zauna Hajiya Muniba ta haɗa abinci tabawa Aliyu ya karɓa ya tusa Kharimatu a gaba yana bata
da farko ƙinci tayi saida ya rinƙa amfani da hikimomi sannan ta karɓa tana haɗiyarsa kamar
magani yanata lallaɓata abinda ya ƙara tunzura zuciyar Salma ta cije leɓe a ranta tana kissima
da aikinta yayi yanda sukaso da tuni ba zancen Kharimatu akeyi ba babban baƙin cikinta da
akace mata wai Kharimatu har ɓarin cikin Aliyu tayi to waima yaushe har Aliyun ya zaga har
yayi mata cikin? Lallai namiji ɗan babansa ita lissafin ta ma bata yake tun kafin auren yayi mata
cikin.
Yini tayi a asibitin tana ƙuncin rai tana haɗiyar takaici tana ganin yanda mijin da yakeyiwa kishi
irin na a mutu ko ayi rai yanata lallaɓa wata macen a gabanta bata ƙara ƙuluwa ba sai lkcn da
ɗakin ya rage sai su uku can ƙasa taji muryarsa yana cewa da Anam “Meyesa kika ɓoyemin
kinada cikina a jikinki har saida ya fita nasan dashi?" Itadai batace komai ba yaja dogon
gashinta yace “koda yake kema ba lallai kinsan dashi ba Khary nayi baƙin cikin zubewar cikin
nan amma babu komai Insha Allahu da wuri zan sake baki wani ai kinaso ko?"
Idanunta ta sauke kan Salma data sunkuyar da kanta tana danna waya shima ta kalleshi yayi
mata murmushi yace “yeah so nake ki ƙarajin sauƙi komai zaiyi saiti" Bazata iya jurewa
kalamansa ba hakan yasata miƙewa ta saɓi jakarta tace “ƴaƴana sun kusa dawowa daga school
mal zan wucce" miƙewa yayi yana kissing hannun Kharimatu yace “Zan shigo anjima ki kulamin
da kanki"
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ31-32 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Wani Mugun kallo da Salma ta watsawa Kharimatu saida hanjin cikinta ya kaɗa tayi saurin
sunkuyar da kanta inda ita kuma ta fice daga ɗakin ya lura kowanensu da saƙo a zuciyarsa so
bayason ɓatawa kansa lkc akan abinda bashi da muhimmanci hakan yasa ya rufawa Salma
baya tana tsaye jikin motar sai girgizar bala'i takeyi ya kalleta ya watsar ya shiga yayima motar
key ganin alamun zai iya tafiya yabarta yasata shiga ta rufo ƙofar da ƙarfi ya kalleta ya watsar
ya ja motar ya bar harabar asibitin.
Sunyi nisa sosai taji bazata iya haɗiye abinda kecin zuciyarta ba tace “Me yasa kakeson zubar
da ƙimarka da darajarka gurin yarinyar nan ne Aliyu kai ko kunya bakaji jibi yanda kake wani
zaƙewa tana jisgaka....."
Kallonta yayi da gefen ido yace “kunya? Zubar da ƙima?" Kuma a matata ta sunnah waɗannan
kalaman suka samu gurbi? Hmmm!" Daga haka yaja bakinsa yayi shiru itama ta tsuke nata
bakin badon ta rasa abin cewa ba sai don batason kalamanta suyi yawan da zai fahimci tuban
muzuru tayi masa.
Har suka isa gida babu wanda ya sakewa kowa mgn sun jima a wannan yanayin shiyasa abin
bai wani dsmunsa ya haye sama ya fara ayyukan dake gabansa bayan ya kammala ya fito
ɗaure da towel tana zaune a parlourn ta rafsa tagumi ya matsa gabanta ya sanya hannu ya cire
mata tagumin tayi firgigit kamar wacce ta tashi a bacci ta dubeshi yayi mata murmushinsa me
sanyata ƙara jin kishinsa yace “Meye yaja kike sanya kanki cikin damuwa ne akan abinda
ubangiji ya hukunta Salma kinsan ita ƙaddara tana zuwarwa mutum ne batare da ya shirya
mata ba abin buƙatar kawai ka zama mumini na ƙwarai wajen karɓar ta a duk yanayin data faɗo
maka mi kyau ko akasinta, bare a aurena da Kharimatu banga abinda zaisa ki damu ba
kinsanta kinsan wacece ita batada matsala kusan kece kika raineta so meye damuwarki?"
Ajiye zuciya tayi ta janye kuncinta daga hannunsa ta miƙe ta nufi kitchen yabi bayanta da kallo
ya rasa wanne irin mugun kishi ke addabar zuciyar Salma da har yake neman taɓa muhibbar
aurenta"
Taɓe baki yayi ya miƙe ya koma ɗakinsa ya dauki doguwar riga yasa ya
fito da key na mota a hannunsa tana tsaye jikin window taji bude ƙofar tasa ta juya ta zubansa
ido wani tuƙuki nayi mata zillo a zuciya tunda ta tsaya tunanin ta inda zata ɓullowá wannan
baƙon lamari daya faɗo rayuwarta takeyi. batare data shiryawa furuci ba ya kufce mata tace
“Aliyu...." Tsayawa yayi yana gyara kwalar rigarsa tace “Ina zaka?" Cikin dakiya ya juyo ya
dubeta ya ɗan saki mata fuska yace “zanje nagano jikin Kharimatu ne" ganin yanda yanayin
fuskarta ya sauya yasan mgnr ta daketa batare da yayi zaton cewarta ba yaji tace “Ina buƙatar
lkcnka inason muyi wata mgn dakai idan ka dawo ka gaisheta kace nace inayi mata sannu" ta
faɗa a ƙarshen furucin nata tana aro murmushin yake tanayi masa. Bin ta yakeyi da kallon
mamaki da sallamawa yace “Ok ba daɗewa zanyi ba"
Yana faɗin haka yasakai ya fice ta taune leɓe cike da ƙunar zuciya ta zauna daɓar bisa kujerar
tana lalubar number Ameey ta ɗaga tana cewa “sarkin ƙorafi yau da wanne akazo?"
Tattara numfashinta tayi ta ajiyeshi waje guda tace “Idan naci gaba da bin shawararki zuciyata
bugawa zatayi Yaya Amina mijina ya wucce tunaninki akan yarinyar nan nifa na fara zargin
basubar ƙasa haka ba sunbi ta ƙarƙashinta wajen siye zuciyarsa yau da bakiga yanda ya rinƙa
yi mata a gabana ba ko kunyar ganin idona baiji halan Malamin nan bai fara aikin bane har
yanzu?"
Murmushi Ameey tayi tace “Kin cika gajen hƙr ke yanzu zakice baki fara ganin tasirin aikinmu ba
kina gani fah Mal cewa yayi muddin uwar Kishiyarki na raye duk wani sihiri da za'ayi mata bazai
yi tasiri ba nice na koma nace masa a kawar da uwar gashi har anyi an gama yanzu kuma nasa
akeyin aiki akan ya haɗeku guri guda ta yanda zamufi samun damar aiwatar da abubuwa"
Girgiza kai tayi tace “Nifa bangano alkhairi a zamana gda ɗaya da wannan yarinyar ba zuciyata
bazata ɗauka ba" “Aikuwa dole ki ɗauka muddin kinason kiyi nasara" cewar Ameey taci gaba da
cewa “idan kika lallaɓashi tare da nuna masa amaryarsa tana buƙatar kulawa da tattali duba da
rashin Mahaifiya da tayi da kuma lalurar dake tattare da ita kisan dai yanda zakiyi da salo da
hikima ya amince ya haɗaku idan ya amince da hadekun ki sanar dani zan sanar da Mal ka iya
zai turo baƙaƙen aljanu suyi biso a ɗakin nata muddin wannan abun yana ɗakinta ita da zama
lfy har abada zasuyita bata kashi har sai ta gudu da ƙafafunta idan kuwa bata gudu ba to tabbas
zasu kasheta kamar yanda suka yiwa Zuhrah Kishiyar Janah ƙawata kedai ki zuba ido kiyi kallo
kuma ki koyi kirsar ɓoye kishinki ga mijinki gareta domin muddin kika ɓata takun aiki zai lalace"
Daɗi matuƙa Salma taji da mugun tanadin da Yayar tata take shiryawa kishiyar Tata hakan
yasata wani tsallen murna tace “Shiyasa nake matuƙar ƙaunarki My sis ki daɗe kiyi ƙarko Indai
dake bamayin kukan baƙin ciki amma fah dole mu iya taku kinsan Hajiya kullum wai wata
nasiha takemin wai naji tsoron Allah koda tsoronta nakeji" dariya suka sheƙe da ita Ameey tace
“Manta da tsohuwar nan ita kullum bata ganewa aini nuna mata nake nafi Shaikh Sudais tsoron
Allah"
Dariya suka kumayi tare da sallama ta aje wayar ta miƙe ta nufi kitchen ya ɗauko juice da cake
ta dawo ta zauna tanaci tana latsa wayar zuciyace ta raya mata ta fara aikinta tun yanzu hakan
ya bata ƙwarin gwiwar kiran wayar Aliyu ya daga tace “Baby ya jikin Sis?" Kallon Anam yayi
yace “Tanajin sauƙi kinganta tanata shagwaɓa bacci ma takeji" [11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ33-34 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566
Haɗiye abinda ke damun zuciyarta tayi ta harari gefe tace “Uhm madalla ka gaisheta aje wayar
tayi shima ya aje suna kallon juna yace “ki daina zama da yunwa banason zama da yunwa
Khary" lumshe idonta tayi ta buɗe yace “Ok bazaki daina ɗinba kenan" ƙasa tayi da kanta tana
wasa da hannunta ya riƙo zara²n yatsunta da sukasha lalle ya lumshe idonsa yace “lallai nan
yayimin kyau" ɗagowa sukayi tare ya zuba idanunsa cikin nata yace “likita yace gobe zai
sallameki kinji sauƙi am idan an sallameki gdanki zan kaiki" da sauri ta dubeshi ya ɗaga mata
gira yace “hakan ya kamata zaman nan naki a gda bazai yiwu ba gara kije gdanki kema ki samu
ladan aure kamar kowacce mace"
Girgiza masa kai tayi ya sanya hannu ya ɗago fuskarta yace “idan kika koma gdanki zakifi
samun nutsuwa" bata iya jayayya ba hakan yasata yi masa shiru yayi murmushi yace “shiyasa
nakesonki" ya ɓata lkc a asibitin kafin sukayi sallama da Granny ya tafi tunda yaje gda Salma ta
kawo masa abinci ta zauna kusa dashi tana wasa da yatsunsa yana cin abincin suna hirarsu
tana dariyar yaƙe saida taja hankalinsa sosai sannan ta ɗago ta dubeshi tace “My Haidar!"
Dubanta yayi tare da tattara hankalinsa waje guda yace “yadai My Salmah
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tace “Da zakayimin wannan alfarmar da zanji daɗi sosai Aliyu nayi
alƙawarin duk wani abu da kake tsoro bazai faru ba don Allah ka amince dani" aje cokalin yayi
ya zubanta ido tare da cewa “Wanne Alfarma kenan?" Sosa kanta tayi tace “Kada ka raba mana
gda da Kharimatu saboda yarannan kaga Ni ina zuwa aiki kuma ina yawan tafiye² idan tana
gdan zasu zauna tare tunda dama sun saba rainonta ne kuma kaga nan yafi kusa da
makarantarsu fiye da can inda kake gini bayan haka kaima sauƙin ka ne komai katashi siye
ɗaya zaka siya na amfanin gda memakon idan ka rabamu da komai saika nemi biyu sannan
inason mu samu kusanci kamar yanda Hajiyata da Hajiya ƙarama suke inason mu zama abu
ɗaya ta yanda zakayi alfahari damu, Amma fah kada ka canza min fassara iyakar gskyta kenan"
Tana mgnr tana cigaba da wasa da yatsunsa.
Zubanta idanu yayi a hankali yakai hannu ya ɗago fuskarta ta lumshe idanunta tare da shigewa
jikinsa shikuma ya matseta cike da so yace “Meye ya canzamin ke kikayi laushi haka ne My
Salmah naga a farko kin ɗauki abin da zafi yanzun kuma kin sauka da wuri" murmushin bakada
wayo tayi masa tace “tausayin Kharimatu ne ya fara canzamin tunani sai kuma nasihar Hajiyata
Aliyu na gane abinda kake nufi kaine ka cancanci riƙe maraicin Kharimatu shiyasa naji a raina
zan taimaka maka na tayaka riƙon amanar nan musamman da akace Mahaifiyarta kafin ta rasu
ta damƙa maka ita amana"
Sosai Aliyu yaji daɗin kalaman matarsa nan take yayi mata alƙawarin haɗa su gda ɗaya da
Kharimatu suka tashi sukaje suka kwanta washegari tun safe yasa aka gyara masa daya
bangaren na gdan dake dama gdan nasa yanada girma akwai ɓangare ɗaki biyu manya da
parlour da toilet a kowanne ɗaki sai kitchen ƙarami batare da ya sanar da kowa abinda suka
shirya ba yasa aka ɗebo kayanta da aka shirya a sabon gdan aka dawo dasu nan masu shirya
gidaje suka baje fasahar su wajen tsara mata sashin duk da cewar kayan sun yima ɓangaren
yawa haka aka shiryasu aka zuba mata wasu a store da yake Alh Ma'aru ya narka mata kuɗi
sosai a wancan gdan.
Kwana uku ta ƙara aka sallameta a asibiti da farko sunso tafiya da ita gda suci gaba da kula da
ita saidai basu samu wannan damar daga mijinta ba yayi kicin²n ya matse lamba kan saidai
abashi matarsa shi ya gaji da wannan galantoyin hakanan da Granny ta fusata tace “ga matarka
nan idan ka tafi da ita kasa mata mai da yaji ka cinye ƙarewar so sakarai kawai" Baiji haushi ba ta fice driver ya ɗauketa shima ya haɗa musu kayansu sai gda tunda suka taho
take hawaye har sukazo ƙofar get na gdan yayi horn ta ɗago gabanta yayi muguwar faɗuwa
ganin gdan da ya kawota ta dubeshi cikin kaɗuwa tace “Daddyn Farooq gdan Aunty Salma ka
kawoni fah" shafa sumarsa yayi ya ɗaga mata gira yace “Gdan Aliyu dai ko Kharimatu tunda
Salma batazo dashi a gara ba" numfashi ta sauke yana matsowa jikinta tace “Amma ai ba anan
zan zauna ba kace dasu Granny" murmushi ya sake yi mata ya tallafi kuncinta ya ɗora bakinsa
saman nata ya lashi lips ɗin ta da harshensa ya ɗago yace “Zanfi samun nutsuwa idan kuna a
guri ɗaya kada ki tashi hankalinki bazaki samu matsala da Salma ba ta sauko sosai kinji My
Khary"
Ƙasa tayi da kanta cikin zullumi zuciyarta na bugawa da ƙarfi taji ya buɗe motar ya fito ya buɗe
mata ta zuro ƙafafunta cikin fargaba yayi gaba tana binsa a baya kamar mara gaskiya ya buɗe
falon suka shiga da sallamarsa Salma dake zaune ta miƙe Kharimatu tayi saurin raɓewa a
jikinsa domin mugun tsoron Salma takeji abinda yaja sukayi dariya su biyun Aliyu ya shafa
bayan Kharimatu yace “My Salma kin tsoratamin mata da yawa" dariya tayi tace “Double sorry
Ƙanwata ki daina jin tsorona babu abinda zanyi miki kinji" hannu tasa ta janyeta a jikinsa ta
kama hannunta tana mata murmushi suka haura saman.
Ta buɗe mata ƙofar shiga sashin ta yana biye dasu a baya saida ta shigar da ita har cikin