MEYA JAMIN COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   11 / 11

30K to 31.7K   out of 31.7K words

daga motar yabita da kallo tare da murmushi ya
fita yabi bayanta suka gaisa da Granny tayi musu Barka da dawowa sannan yayi musu sallama
ya tafi.
Yana fita ta faɗa wanka ta haye gado ta kwanta sukaci gaba da hirarsu da Granny har bacci ya
ɗauke su. Cikin kwanakin da suka rage mata na komawarta gdan mijinta tasha gyara ba kaɗan
ba tare da karɓar mata magungunan tsarin jiki takanas Babanta Mal Wada Na'ibi yazo ya sake
kawo mata magungunan tsarin jiki ta kuwa duƙufa yi takeyi sosai yanda ta bashi amanna ko
magungunan matan bata basu haka ba,
Yanda Aliyu keta rawar ƙafa yana bata mamaki kuɗi yake kashe mata bana wasa ba duk abinda
Granny ta kirashi tace kawo miƙawa yakeyi ranar juma'a ta kama zata tare itadai yinin ranar
yinsa tayi jikinta duk babu ƙwari da magrib yazo gdan tana kwance a ɗaki Dad ya Kira wayarta
ta ɗaga suka gaisa da ladabi yace taje yanason ganinta.



Tashi tayi ta yafa mayafinta ta fito ta nufi sashin Mom tana falon suka gaisa ta shiga ciki
gabanta ya faɗi ganin Aliyun zaune a parlourn ta nemi guri ta zauna suka ƙara gaisawa da Dad
yayi gyaran murya yayi musu nasiha me shiga jiki dukkansu saida jikinsu yayi sanyi yayi musu
fatan alkhairi yace “idan ƙura ta lafa Aliyu nasa a canza mata admission daga Alƙalam zuwa
B.U.K so amma samu angama registration da komai fara zuwa ne kawai nata am ga motar
dana siya mata can a rufe d tampol a waje Kharimatu sai a mayar da hankali ayi karatu don
Allah kada asa wasa"
Jinjina kai tayi tace “Insha Allahu Dad na gde ubangiji ya ƙara girma da Arziƙi Allah ya rabaka
da Granny lfy" amsawa sukayi da Amin suka tashi suka tafi ya buɗe mata mota sai wani baje
baki yakeyi yaja suka tafi saida sukaje gdan ta gane ashe sabon gdan daya gina zaisata farkon

aurensu ne da ba'a bari yasata ba taja numfashi yayi parking suka shiga ciki suna shiga ya ajiye
Jawad ya janyota jikinsa ya rungumeta ya sauke ajiyar zuciya yace “Allah shine mafi soyuwa
daa godewa Allah na gde maka daka sake dawomin da Kharimatu na cikin rayuwa ta"



Yanda ya rinƙa lallabata ya tabbatar mata yau saidai ƙwacen Ubangiji ne zai fitar da ita aikuwa
hakance ta faru bayan sunci sunsha komai ya lafa suka shiga domin kwanciya ta kwantar da
Jawad ta cire kayanta tasa na bacci ta haye gado ta ja bargo tare da rungumeta ɗanta yana
kallonta baice mata ƙala ba yaci gaba da danne²nsa a system ɗinsa bayan ya gama ne ya tashi
ya shiga bayi yayi wanka ya ɗauro alwala ya dawo ya haura gadon ya janye Jawad yamai dashi
gadonsa ya shige gurin daya ɗauke yaron ya fara shafa fuskarta zuwa ƙirjinta tana jinsa ta
shareshi kamar bataji ya rinƙa sarrafata yana wasa da ita dole saida ya kamata a hannu
wannan dare Aliyu ya kwashi gara itakuma taci wuya lkcn da zaiyi release yanda ya ƙanƙameta
kamar zai tsaga jikinta ya shiga sun jima a haka sannan ya janye jikinsa ya koma gefe.
Dole ce tasa ta saki jikinta dashi suka ɗora rayuwarsu fiye ma data baya satinta uku da dawowa
gdan ta kama zazzaɓi me zafin gaske duk dauriyarta saida suka dangana da asibiti aka
bincikata sosai suka tabbatar musu shigar ciki ke gareta wata runguma da Aliyu yayi mata saida
ya bata tsoro ta ƙanƙameshi yayi kissing nata yace “Wlh ranar da muka fara haɗuwa cikin nan
ya shiga Kharimatu naji yanayina dama ya bani hakan zata iya faruwa ubangiji ya raya mana ya
inganta"




*Oum Hairan*
[11/17, 10:33 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ49-50 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566


Lumshe idanunta tayi yajata ya zaunar da ita likitan ya rubuta mata magunguna ya fita ya siyo
ya dawo suka tafi kwanaki kaɗan komanta na makaranta ya kammala da farko Aliyu so yayi ya
hana wai sai ta haihu Dad yace kada ya soma yabarta tayi karatunta dole haka ya barta amma
ya hanata jan mota saidai ya kaita idan lkcn tashinta yayi yaje ya ɗaukota cikin watannin koma
ya saitu ta sanyashi ya ɗebo mata yaran duka ta haɗasu su huɗu a gabanta ta riƙe dama dake
sun saba da ita basu wani samu matsala da ita ba sukaci gaba da rayuwarsu kamar baya.
Sannu² lkc yayita shuɗewa har ubangiji ya nufeta da haihuwar yaranta biyu duka maza aikam
yaran sunga gata bayan suna da sati ɗaya da safe suna falon suna hirarsu dake ranar ta kama
asabar ce Aliyu yana gda yaran ma dukkan sunan knowking na ƙofa akayi ta miƙe ta buɗe
gabanta ya yanke ya faɗi cikin firgici tace “Aunty Salma!" Dukka har yaran suka ɗago suna

kallon me shigowar ta ƙara so a duke kamar tsohuwa ta zube a tsakiyar falon.




Wani wari ya dumame gurin yaran suka tashi da sauri suka gudu Farooq yana cewa “Aunty mu
mun gudu bamason ganin dodon nan Jawad zo mu gudu Aunty ki bani twins mu tafi sama
dasu" hawaye Salma ta share cikin kuka tace “Me yajamin banda nadama nayi jayayya da
hukuncin ubangiji Yaya Ameey ta ɗorani a muguwar hanya gashi nice na kwana ciki inason
mijina tasani na rabu dashi na rabu da ƴaƴana Kharimatu duk akanki baƙin kishina yajamin na
nayi muku asiri akan idan kun tafi hanyar zuwa Guru lkcn bikinku kuyi hatsari ku mu dake
ƙaddararki bata mutuwa bace kika tsallake saidai haƙƙin ran mahaifiyarki daya rataya akaina
babu wanda yasan wannan haka nayi amfani da damar na yaudari mijinki ya amince zai
haɗamu gda ɗaya da nasa aka turo manyan shedanu da zasu illataki daƙyar suka samu damar
shafsrki suka zuba miki firgici wannan bai isaba nasa aka turo miki lalura sannan nasa a kashe
ɗan cikinki bansan ya akayi ba duk abubuwan dana ƙulla suka dawo kaina na juyar da hankalin
mijinki na janyeshi munbar ƙasar a lkcn da bakida lfy ashe kaina nayiwa memakon ɗan cikinki
ya mutu tawa ce ta mutu nasa a lalata miki mahaifa kiyita zubar da jini idan kin samu ciki kiyita
ɓarinsa ashe kaina zata juyo shekara biyu kenan bantaɓa hutawa da zubar jini ba kullum cikin
ƙaramin jini ake.
Gashi waɗannan ƙurajen dana sa a turo miki sun dawo jikina kullum cikin ɗoyi nake da zubar da
mugunya gashi duk me maganin da naje gurinsa cemin yake kin samu kariya daga Ubangiji
babu kuma wanda zai bani maganin ciwon nan nawa sai Babanki Mal Wada Na'ibi jiya mukaje
gurinsa yace sharaɗin shine nazo na sanar dake nice nayi miki komai idan kika yafemin zai bani
magani idan baki yafeba kuma saidai na zauna da ciwo na don Allah na roƙeki ki yafemin
Kharimatu ina cikin mawuyacin hali....."




Ta karashe mgnr da wani kuka me gunji Tsaki Aliyu yayi ya miƙe yace da Kharimatu ta tashi
tabar gurin kallonsa tayi da idanunta da itama suketa zubar da ruwa tace “Duk da inajin ciwon
kasancewarta silar gushewar rayuwar Mahaifiyata bangona Yaya Aliyu bazan kasa yafe mata
ba kodon arziƙin su Farooq da Muwaddat da Jannat kije Allah ya baki lfy Ni na yafe miki haƙƙin
rai kuma banida ikon yafeshi tsakaninki da ubangijinki ne" miƙewa tayi tabar gurin da sauri don
Allah ya sani batason ganin Salma.
Duk da halin da Salma take ciki miƙewa tayi tana ƙwafa a ranta tana cewa zakuyi bayani ne
kudai jira naje na samu wancan tsohon banzan ya bani magani na warke wanda zanyi muku
gaba ma sai yafi wannan saikin haukace kin fita tsirara mota ta takeki tunda kika zamo silar
rabuwata da mijina sannan kika rabani da ƴaƴana"

Daƙyar Aliyu ya rarrashi Kharimatu ta manta da komai sati biyu tsakani suka samu kira daga
gun Mom take sanar dasu sunji lbrn mutuwar Salma kuwa sosai Kharimatu ta shiga cikin tashin
hankali tace wlh batasani ba nan Mom tace mata ai sunje Guru sun dawo ambata magani taji
sauƙi suka ɗauki hanyar Maiduguri gurin wani sabon bokansu so kafin sujene sukayi hatsari
mutum biyu ne suka fita ciki harda ƙawar Salma wacce tayi mata jagora zuwa gurin bokan"
Mutuwar ta bugesu sosai Kharimatu taji tausayin su Farooq ƙaunarsu ta ƙara shiga ranta duk da
Aliyu yaso hanata zuwa ta'aziyyar tace masa yayi hƙr yabarta suje da yaran hakanan ya
ƙyalesu suka tafi harshi sukayi ta'aziyyar suka dawo, Kharimatu ta sake ɗaukar ɗambar riƙe
yaran sukaci gaba da rayuwarsu kai zaka zacima duka ita ta haifa cikin ikon Allah bata yaye
twins ba ta kuma haihuwar ƴa mace taci sunan Mahaifiyarta Ruƙayyatu sukece mata Amnah
bayan shekara biyu ta ƙara haihuwar namiji shikenan haihuwar ta tsaya dake ita dama ahlinsu
ba masu haihuwar da yawa bane.



Ta gama karatunta a fannin Business and Administration dake Allah yayita da son ƙamshi
hakanan takeyin turaruka matan lay-out ɗin nasu suna siya ganin hakan batare data sani ba
Aliyu ya siya mata wani babban shago ya zuba mata kayan kwalliya tare da kayan gyaran gashi
da kuma ɓangaren boutique da turaruka humra kulacca turarukan wuta da kuma turaruka ƴan
waje cikin lkc ƙanƙani Ubangiji ya sawa Kharry Boutique and cosmetic albarka ya haɓaka ko ina
zancen sa akeyi a yankin arear tasu haka ta kuma buɗe wani shima ya samu karɓuwa ga
ƴaƴanta biyar dana mijinta uku yaransu takwas ta haɗa ta riƙe rayuwa tayi daɗi tayi riba albarka
ta sauka ta wanzu a wannan zuri'a




_Tammat bi hamdullah_



_Alhmdllh gdy ta tabbata ga Ubangijin talikai daya bani ikon kammala wannan littafi a yau ɗin
nan ina roƙon Allah daidanmu ya karɓa akasinta ya share ubangiji yasa ya amfanar_




Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!

Insha Allahu sabon littafi na me suna BAƘIN RUHI zai fara zuwar muku 20/11/2021

*Oum Hairan*

11 / 11