MEYA JAMIN COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   1 / 11

1 to 3K   out of 31.7K words

[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?



Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)



1-2


Tsugunne a bayan gdan wata matashiyar budurwa ce yar sha shidda zuwa sha bakwai baƙa me
matsakaicin tsaho da ɓoyayyen kyau take wankin kayan yara na makaranta tanata rawar sanyi
da alamun yanayin hunturun yana kaɗa duk dama Dole ne ya shigeta duba da ko arziƙin rigar
sanyi bata samu ba, wani yaro ne qarami da bazai wucce shekara bakwai ba ya fito daga wata
ƙofa alamu sun nuna itane ƙofar da zata sadaka da asalin gdan.
Hankalinta nakan wankin da takeyi bata ankare sa tahowar yaron ba saiji tayi ya watsa mata
ruwan sanyi a jikinta ta zabura da sauri ta miqe cikin kiɗima take duban yaron idanunta ya kawo
ruwa tace “Farook ni ka watsawa ruwa a wannan sanyin ko?" Murgiɗa mata baki yayi yace “an
watsa miki ɗin talaka almajira kawai Momy tace kizo ki haɗa mana break in kinƙi kuma ta
zaneki"
A sanyaye ta saki aikin da takeyi tana daga rigarta data manne a jikinta ta nufi ƙofar parlourn ta
shiga da sallama babu kowa a parlourn sai Muwaddat da jannat ta dubesu dukkansu babu
wanda ya samu arziƙin ko wankin idanu ta matsa ta dauki Irfan daketa miƙo mata hannu tana
masa murmushi tace “yarinyana ko Pampers baa cire miki ba bari nayi muku wanka sai nabaku
abinci Isiya yakaiku makaranta ko?" Ta Faɗi da sigar tambayar yaran Muwaddat ta zunguro baki
gaba tace “aa nidai Aunty Anam ki bamu abinci tukunna da yunwa muka tashi"




Saukowar masu gdan ne yasata haɗa nutsuwarta ta durƙusa cikin ladabi tace “barka da fitowa
yallabai Hajiya Barka da asuba" baiko kalleta ba yasa kai ya fice a falon Hajiya Salma ce ma ta
harareta tace “kinanan kina sakarcin naki na tsiya zaki makarar min da yara ko duba ko
Pampers baki cirewa jannat ba saboda ke kin zama mara mutunci to ki makarar dasu sai
hankalinki ya kwanta jaka kawai....."
Kalmar ƙarshen ta bugeta sosai ta sunkuyar dakai hakan bai mawa Hajiya Salma ba saida ta
saukenta ƙusa a tsakiyar kanta ta rintse idanu hawaye nabin kuncinta inda sabo zuwa yanzu ya
kamata ace ta saba da izayar gdannan tunda kusan a cikinta ta rayu tun tana shekara biyar
suke tare da mahaifiyarta a wannan gda duk da kasancewar ba'a asalin wannan gidan suke ba
mahaifiyarta tana gdansu Aliyu wato mamallakin gdan tanayima iyayensa aiki lkcn da Aliyu yayi
aure ne matarsa ta matsa tanason yar aiki shine aka kawo ta gdan nasa matsayin yar aikin

gdan yanzu shekara takwas kenan tana aiki a gdan a gabanta duk aka haifi waɗannan yaran
Umar Farooq Muwaddat da jannat amma har yanzu yanci yaqi zuwan mata daga megidan har
matar gdan har yaran gdan babu wanda take samun sauqi ta gurinsa har garama Salma wani
lkcn takan jata suyi hira idan yan mutumcin na kusa.



Ɗaukar yaran tayi suka nufi dakinsu tayi musu wanka tasa musu uniform ta fito ta haɗa musu
break ɗin sukaci Farooq nata barna shida Muwaddat babu wanda ta isa hanawa yanzun uwarsu
tana dawowa su kitsa mata ƙarya da gaskiya ta hau ta zauna ta zage ubanta daya mutu tun
batasan kanta ba ta zage uwarta data qare rayuwarta a bauta don rufa mata asiri sannan idan
bai isar mata ba ta gama ta da dukan mutuwa wannan yasa take takatsantsan da lamarin gdan.
Daƙyar Allah ya taimaketa suka gama ta goya Jannat suka fito ta bawa Isiya lunch box ɗin
yaran suka shiga Mota itakuma ta lulluɓe jannat ta koma ta karasa wankin ta shanya ta shiga ta
fara gyaran gdan ɗakin Aliyu ne kawai bata shiga ba saboda yayi mata ƙwaƙƙwaran kashedi
akan shigar masa ɗaki tun yana gda ko anan ɗinma da Salma taso sakar mata gyaran ɗakin da
ita da Salman yacima mutumci dole tasa ta hqr take gyara masa idan ta dawo daga aikinta.




Tana kammalawa da parlourn ta nufi ɗakinta ta gyara ta kwantar da jannat tayi wanka tasa wata
jemammiyar atamfarta domin Salma ta hanata Sanya kaya masu kyau kullum kaganta cikin
tsumma zaka ishe da hijjab a jikinta batasan dalilin wannan doka ba.
Sai biyu ta shiga kitchen ta manta bata tambayi masu gdan abinda zasu ci ba ta ɗauki wayarta
ta kira number Hajiya Salma saida ta katse ta sake kira sannan ta ɗaga cikin masifa tace “wai
Anam ke wacce irin wawuya ce ina aiki zaki dameni...." Cikin ladabi tace “kiyi hqr Hajiya
mantawa nayi ban tambaye ki abinda za'a girka muku ba....." Da masifa tace dalla Malama
bansani ba ni zaki tambaya bazaki tambayi su Farooq ba to ki girka ubanki....." Qit ta kashe
wayar Anam ta tsaye sororo da waya a hannunta tanajin ciwon yanda Hajiya Salma batajin
nauyin zaginta yanzu daga tambaya sai cin mutumci?
A saluɓe ta nufi kitchen tana tunanin abinda zata girka lumshe manyan idanunta tayi dabara ta
faɗo mata tasan Aliyu yanason tuwon shinkafa miyar taushe aikuwa nandanan ta fita tabawa
driver sautun kayan taushe wanda babu a gdan ta koma ta ɗora tuwonta ta malmaleshi a leda
ta fara tafasa namanta isasshe tasa masa kayan ƙamshi nandanan ta haɗa komanta sannan
taja da baya tayi farfesun naman kaji da yaji Attahiru ta jere musu a dinning ta dauko man
shanu soyayye ta narka takai musu dinning ɗin.




Shige daki ta zauna tana game da rakani kashinta jin motar masu gdanne yasata miƙewa ta fito

tana riqe da hannun jannat sanye da ƙaton hijjab ɗinta caraf bisa tsautsayi idanunta ya fada
cikin na Aliyu tayi saurin janyewa ta rusuna tayi musu Barka da dawowa ya amsa a shaƙe ya
buɗe baki yace “hajiya tace kije can gobe Umaimah zatayi birthday akwai ayyuka acan"
Ajiyar zuciya tayi ko banza ta huta da masifar Salmah ta kwana biyu miƙewa tayi ta koma
ɗakinta ta haɗa kayanta a yar ƙaramar akwatu ta dauko ta fito ta canza kaya tasa mayafi har
sunyi wanka sun dawo dinning ɗin sunacin abinci ta rusuna tace “na shirya zan tafi" dubanta
Salmah tayi tace “kwana uku zakiyi ki dawo" jinjina kai tayi Ta miƙe Aliyu dake satar kallonta
yace “ki jirani a waje ganinan"





Jinjina kai tayi ta fita ta tsaya jikin motar ya ɗauki sama da 30 minutes sannan ya fito fuskarsa a
murtuke ya buɗe motar ya shiga ya zauna ta buɗe gdan baya zata shiga yace “kinsan dake ni
drivern babanki ne shiyasa zaki zauna a baya na tuqaki" bataso ake taɓa mata iyaye yanzun
zuciyarta take karyewa ta juya jiki a mace ta shiga motar ya figa a guje ya fice daga gdan suka
nufi Danladi na Sidi inda family house dinsu Aliyu yake suna zuwa ta buɗe motar ta fice yabi
bayanta da kallo da mugun faduwar gaba ganin yanda take motsa jikinta.
Lumshe idanunsa yayi abin yayi masa dadin gani mamaki ya cikasa yaushe yarinyar ta girma
haka har ta haɗa kayan ruwa haka? Saurin jan tsaki yayi yana kawar da tunanin ya fito a motar
ya nufi cikin gdan a parlourn Ƙasa ya ishe su ita da Mamanta ta kama mata suna morping yana
da hotuna Mama ce taga shigowarsa ta rusuna da girmamawa ta gaisheshi ya amsa kamar
yanda yake amsawa da gadara ya haye sama Anam ta taɓe baki tace “kamar wani namijin
ƙwarai a gda sai yanda akayi dashi" daƙuwa Mama Yabi ta watsa mata tace malafar ubaki ƴar
nema koma mene ai yayi miki rana dalilin zaman gdansa gashinan kema ƴar Sakandire ɗin nan
da yara sukeyi kin samu kinyi ta kuɗi to ubaki zakice da Haidar?"




Bata kuma cewa komai ba Umaimah ta fito da wata ƙawarta tana ganinta tace “yawwa Anam ki
shiga ɗakina ki gyaramin ki shiryamin wardrobe ɗina kayan sun hargitse" amsawa tayi da to
cikin ladabi ta nufi saman tayi sallama Hajiya Muniba tana zaune hakimce a parlourn gaban
Anam ya fadi. Ta rusuna ta gaisheta ta amsa mata a wulaqance tace “lfy" cikin in...Ina tace “Hajiya Umaimah
ce tace nazo na gyara mata ɗakinta" jinjina kai tayi ta nuna mata hanya ta miƙe taci uwar
ɗammara da mayafin ta nufi ɗakin na Umaimah ta soma gyarawa bayan ta gama ta fito har
yanzu suna zaune a parlourn sabanin ɗazu yanzu harda Granny ta ƙwama uban glass tana
ganinta sukayi murmushi a tare tace “ƴar nema jikar na samu kinje kin ɓuya luf abinki Haidar ya
boyeki baku Abuja baku Kano zonan naji fatar ki ko tayi laushi"
Dariya tayi da tasa fararen haƙoranta da suka jeru reras da kyakkyawar wushiyar suka bayyana
dimple ɗinta ya lotsa tace “Granny tawa bari nazo nayi miki tausar Tailand" Alh Ma'aru dake

gefe yayi murmushi yace “Anam ta Granny nifa Ina tunanin Granny zan dawowa dake su Aliyu
sa nemi wata" riƙe baki Granny tayi tace “hooooo Ni Mairamu rufamin asiri da wannan ƴar
ƙaniyar ɗiyar tun tana mitsitsiyarta ma azaba take ganamin balle yanzu dubi yanda take wani
haɓaka kamar amsawa tsiro taki yo dubi iyayen nonuwa da ɗuwaiwaka idan ta zauneni ai saidai
na farka a kabari"



_whattsAp number 09013718241_



*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?



Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)



3-4



Wata baƙar kunya ce ta kama Anam tayi ƙasa da kanta cikin tsananin jin kunya sumsum ta fice
Alh Ma'aru yana mata dariya yana cewa “Anam badai kunya ba Hajiya kin bawa yar dakin naki
kunya" itadai ƙasa ta sauka taci gaba da taya Mama Yabi aikin da takeyi suna gaf da gamawa
Aliyu da Alh Ma'aru suka fito sukayi musu adawo lfy sannan sukaci gaba da ayyukansu basu
suka gama ba sai bayan Magrib Anam ta shige ɗakin Mama Yabi tayi alwala tayi sallah ta miƙe
a katifa Mama Yabi ce ta shigo masu da abinci ta tashi sukaci suna taba hirar su ta ƴa da uwar
suna dariya can Anam ta haɗe rai ta koma kalar tausayi Mama ta dubeta tace tunda kika zo na
fahimci damuwa a yanayinki meye ne yake faruwa?" Ƙwalƙwal tayi da ido tace “Allah mama na
gaji da masifar Hajiya Salma kullum saita zageki ta zagi ubana da banma sanshi ba ga ƴaƴanta
rashin kunya babu kwaɓa kamar ƴaƴan Allah bani musamman Farooq da Muwaddat ji suke
kamar zasu iya cin abinci akaina"



Jinjina kai Mama Yabi tayi ta zubawa ƴartata ido tare da sauke numfashi tace “zuwa yanzu ya
kamata ace kin saba da waɗannan ƙananun abubuwan Anam ya mutum zaiyi da yanda
Ubangiji ya tsara masa rayuwarsa ne saidai ya gode masa kawai in yaƙi kuma ya godewa

azabarsa don Allah ki koyi haƙuri da yanayin rayuwa komai zai wucce insha Allahu watarana sai
kiga labari kike badawa"
Bata da wata sauran kalma data rage da zatayima Mama bayani ta fahimceta dole tasata yin
shiru ta kwanta itadai da Dad zai taimaketa kamar yanda ya furta ya dawo da ita gurin Granny
tabbas da taji daɗi sosai. Bayan sunyi sallar Isha wani aikin suka dauko ita da Mamanta sukeyin
komai cike da kulawa da juna har suka gama wajen 11:30 suka nufi ɗakin Mama suka kwanta
sunata yan hirarrakinsu mama tana faɗa mata so takeyi idan lkcn hutunta yayi zataje Gashua ta
kwana biyu rabonta da gida Yobe shekara huɗu kenan kallonta Anam tayi tace “amma meye zai
hana mu tafi tare Mama nima inason naje naga dangina"



Dafa kanta mama tayi tace “to banda abinki Kharimatu ai zakije ne kinsan yanayin aikina da
naki ba ɗaya bane kedai kije kiyita hqr da halin iyayen gdanki watarana zai zama tarihi kinji"
ɗaga kai tayi ta fara addu'ar kwanciya bacci badon taso hukuncin na Mama ba sai don ba
halinta bane jayayya da mahaifiyarta da wannan bacci ya ɗauke ta da asuba kuwa suka shiga
zarafin aikin abincin birthday duk da cewar an bayar da kwangilar wani amma yanayin yanda
suke d yawan masifa gasu da ɗabbaƙa bidi'a yasa gidan ya cika ke kya dauka bikin aure sukeyi
ko suna Anam Bata samu kantaba sai huɗu da yammaci tun safe dake Allah ya hore mata lfyr
aiki kamar engine tayi wankanta ta ɗauki wata lashinta da Umaimah ta bata tasa riga ce
doguwa saiya kasance sun fito mata da asalin surar ta da ƙuruciyarta abinka da chocolate color
oily skin sai milk ɗin less ɗin yayi mugun haskata tayi kyau na ban mamaki ta fita ta nufi sashin
Granny ta sameta ita da Alh Mahdi wa gurin Alh Ma'aru ta rusuna ta gaida shi ya amsa mata da
sakin fuska Granny tace.



“Ƴar nema kinzo ki tumurmusani ɗin ne?" Dariya tayi tace “haba My Kakus ƴar tsohuwa yaushe
rabonki da tausa irin tawa me daɗi saboda daɗinta fah kikece mata tausar Tailand" kama ƙafarta
tayi tana matsawa a hankali Alh Mahdi ya tashi yace “Hajiya Iya tunda kin samu ƴar hira bari
naje gurin yaran can da suka cika mana gda da kiɗa kamar ƴaƴan yahudawa" Fita yayi Hajiya Iya da Anam sukaci gaba da hirarsu Hajiya Iya na korarta ita kuma ta nace taƙi
tafiya saida tace “zakici kunnen Uwaki bari na kira miki Mala'ikinki Haidar ai yana gdan naga
zuwanshi da iyalinshi ƙila na samu salama kajini da ƴa ƴar kusun uwa tanata murɗemin
yatsa......" Wata ƙara Hajiya Iya ta saki daidai lkcn da Aliyu ya shigo tayi caraf tace “yawwa Haidaruruwa
kaɗamin wannan ja'irar yarinyar gurɗemin yatsu take neman yi" kafin ma ya waiwayo kanta tayi
wuf ta shige ɗakin Hajiya Iya tana cewa “Granny kefa kikace nayi miki shikenan tunda bakiso
bari na gyara miki ɗakinki na jera miki kayanki a wardrobe"


Bata kula da hararar da Aliyun ke watsa mata ba shi yarasa meye tashi batazo ɗaya da yarinyar

ba yanda ta nufi ɗakin tana kaɗa jiki yayi mugun ƙular dashi a haukansa gani yake donshi takeyi
wanda ita batasan ma da hakan ba tunda bata taɓa samun mai faɗi mata ba. Tana jiyo hirarsu
da Granny yau ma kamar kullum Ƙorafi takeyi masa shi yaƙi gaba kullum kaganshi kamar
haɗowar hadari bayada fara'a baya da rahama a fuskarsa inda shi kuma yace “nikam Granny
kinsamin ido da yawa duk duniya kece kike cemin na ragu kona ƙaru ke kuma ba iya yimin
maganin matsala ta zakiyi ba"........
Sunata hirarsu da zolayar juna yanata dariya abinda kullum yake bawa Anam mamaki ko a
gdansa ita zata iya rantsewa bata taɓa ganinsa yana dariya ba kullum fuskarsa kamar ta bijimin
sa amma Indai ya haɗu da Granny yanzu zakijishi yana ɓaɓɓaka dariya, taɓe baki tayi a ranta
tace “miskilin banza da baya iya control na gdansa a fili kuma amsa kiran da Granny take mata
tayi ta fito tana goge fuskarta da tsumma ta rusuna tace “gani Kaka" nuna mata kitchen tayi tace
“wannan kitifaffen ubangidan naki zaki haɗowa abinci yace anan zaici"
Miƙewa tayi ta nufi kitchen ɗin yana latsa wayar hannunsa ta haɗo sinasir da miyarsa da taji
tantaƙwashi da man shanu ta dauko masa lemu me sanyi da ruwa ta jero masa ta nufo inda
yake gabanta na faɗuwa ko a gda bata ƙaunar kai masa abinci saboda baayi masa gwaninta.
Tsugunnawa tayi a gabansa mayafin jikinta ya zame daga kanta dake me yauƙi ne ya sauka
ƙasa bisa rashin saa rigar irin me buɗaɗɗen wuyan nan ce tudun dukiyar fulaninta duk a waje
suke hakan yayi daidai da ɗagowarsa da nufin yi mata masifar daya saba tsautsayi yasa idonsa
ya caki ƙirjinta da batama lura da mayafin ya zame ba ya zubawa wannan abu me matuƙar
ɗaukar hankalinsa a jikin mace idanu kamar wanda ya warke daga ciwon makanta, hakan yayi
daidai da ɗagowarta da nufin neman izinin tashi domin ta gama haɗa masa kawai ta mayar da
idanunta a ƙirjinta taga abinda ya shagala da kallo. Ta kuwa firgita ainun a razane ta wawuro
mayafinta ta rufe jikinta ko ina na jikinta ya ɗauki rawa tasan yau ta shiga uku har shida gaban
shida har tara ma ta shiga.

[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?



Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)


5-6


Cikin kiɗima ta ja da baya ta zube a ƙasa tayi knile down tace “kayima girman Allah da darajar
Hajiya da Alh kayi hqr wlh tallahi bansan ya zame b......" Ɗaganta hannu yayi ya haɗiye
kunyarsa cikin ƙara ji yace “tashi kibani guri mara sanin ciwon kai wato ke nan har kinkai
budurwar da zaki rinƙa tallan jikinki a kwararo toni ko jiki zai burgeni me zanyi da wannan baƙar
fatar taki wawuya dake bagidajiya"
Itadai Anam har tuntuɓe takeyi saboda sauri sukayi kicibis da Granny ta riƙota da sauri tana
cewa “ke marainiyar Allah nutsu kama kanki meye yayi zafi da wannan firgici haka me Haidar

ɗin yayi miki?" Toshe bakinta tayi domin batada kalmar magana ta janye ta kwasa a mugun guje
ta nufi bayan gdan saida ta fakaici ido sannan ta shiga gdan ta shige ɗakin Mama Yabi cikin
Sa'a itanma batanan ta kwanta tana mayar da numfashi tare da yima Allah gdy daya kuɓutar da
ita daga cin duka gurinsa tananan kwance har aka gama birthday ɗin kowa ya watse saida ta
tabbatar da tafiyar Aliyu da Salma sannan ta fito suka shiga gyaran gdan basu gama ba saida
dare ya shiga suka ƙarasa suka kwanta .




Washegari ma aikin ne dasu Hajiya Muniba irin matan nan ne da baayi musu gwaninta komai
kayi baka iyaba su gyara nan tace ba hakaba su gyara nan tace a'a daƙyar Allah ya basu ikon
gamawa itama wannan rana sunji a jikinsu dan ko abinci basu samu damar ci ba sai Magrib
suna cikin cin abincin Umaimah ta shigo ta

1 / 11