MEYA JAMIN COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   8 / 11

21K to 24K   out of 31.7K words


bedroom ɗinta ta zaunar da ita a gefen gado tace “amarya kike sak yau gaki a angonki ina fatan
hannun bazai hana ku sakewa ba?" A mugun kunyace da al'ajabin canjin na Salma tayi ƙasa
da kanta Aliyu dake tsaye yana mamakin yanda matar tasa ta sauko cikin ƙanƙanin lkc yace
“sai abishi a hankali ai kinsanni da tausayi" juyowa tayi ta sakar masa murmushi tace nasan

wannan yanzu meye zakuci a sama muku?"
Agogo ya duba takwas da minti biyar na dare ya ɗago yace “na hutassheki kema kije ki kwanta
ki kulamin da kanki zan fita na samo abinda zamu tari baƙuwar tamu" lumshe idonta tayi tace
“Idan kayi hakan zanji daɗi kaje ka dawo zan tayata hira har ka dawo" jinjina kai yayi ya juya ya
fice ta zauna kusa da Anam tana kallonta tana saƙa abubuwa da yawa a ranta tana murmushin
da ita kaɗai tasan ma'anarsa haka suka zauna jefi² tana yima Anam hira itadai saidai tayi ajiyar
zuciya domin kuwa zuciyar Tata a karye take kukan ne kawai batason tabashi damar zuwa.
Sun jima a zaune Kharimatu har ta farajin bacci sukaji shigowarsa ya buɗe ƙofar ya shigo da
sallamarsa ya aje ledojin ya fara ƙoƙarin cire rigarsa yace “Am My Salmah ki ɗauki leda biyu ki
tafi dashi na gde da kulawa Allah yabarni daku a haka" miƙewa tayi ta ɗauka tayi musu sallama
daƙyar ta haɗiye abinda yake cakar zuciyarta ta shiga ɗakinta ta kulle tayi jifa da ledar hannun
nata ta zube a jikin ƙofar ta ɗora hannunta akanta zata kurma ihu tayi saurin toshe bakinta taja
ɗuwawu ta isa jikin gadon ta haɗe kanta da gadon ta saki kuka.




Zama yayi kusa da Kharimatu ya kamo hannunta da hannunsa yakai bakinsa yayi kissing nata
yaja fasali yace “ya kikeji a zuciyarki game da wannan sauyin da aka samu a gurin Auntynki?"
Ɗago manyan idanunta tayi ta saukesu akansa baisan meye yasa ba baya jure su haɗa ido da
yarinyar mugun kwarjinin takeyi masa hakan yasa ya sauke idonsa yace “kiyi mgn" ajiyar zuciya
tayi ta yunƙura zata miƙe ya janyota ta faɗo jikinsa yakai hannu ya riƙe hannunta me ciwon ya
saita fuskarsa a tata tare da haɗe bakinsu guri ɗaya suka lumshe ido a tare duk da a mugun
tsorace take dashi haka ya rinƙa sarrafata bai ƙyaleta ba saida ya samu nutsuwa da ita sosai ya
shafa saman goshinta yace “kina da baiwa My Kharry Allah yayi miki albarka" itadai kunyarsa
takeji sosai duk da ba wannan ne karo na farko da hakan take faruwa tsakaninsu ba inda sabo
ma kusan ta saba dashi a cikin watannin auren nasu baya bata da sauƙi.
Bayan komai ya nutsa ne sunyi wanka ya buɗe musu abinda ya siyo sukaci dakansa ya rinƙa
bata a baki sukaci sukayi hani'an sannan sukayi brush Suka sake kwanciya, saime cikin dare
kamar wacce aka tsikarawa allura ta zabura ta miƙe cikin wani irin tashin hankali tana furta
“A'uzubillahi minasshaiɗanur rajim Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un" shima tashi yayi a firgice ya
riƙeta da ƙarfi yana kiran sunanta ta ƙanƙameshi jikinta yana wata muguwar tsuma ƙirjinta sai
bugawa yakeyi da ƙarfi.

[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ35-36 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566



Kiran sunanta yayi da ƙarfi yana cewa “Me... Meye ya firgitaki haka meye damuwarki" sake

shigewa tayi jikinsa tanajan ajiyar zuciya ganin yanda ta fice a hayyaci lkc guda yasashi fara
tofa mata ayatul kursiyyu a tsakiyar kanta da addu'o'in neman tsari a hankali yaji zufa yana keto
mata zuwa anjima kuma yaji taja fasali ya nitsa hannunsa cikin sumarta yace “Meye ya tsorataki
haka My Khary?" Numfashi ta sauke ta ɗago ƙwayar idanunta da suke cike da bacci ta sauke
akan fuskarsa ta sake jan fasali ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tace “Wasu irin halittu ne masu
kama da gizo² suka biyoni suka ɗafemin jikina suna cizona kuma duk inda suka cijeni rami
yakeyi shine inata neman taimakonka kawai kayi tafiyarka ka ƙyaleni a tsakiyarsu inata kiranka
kaƙi juyowa"
Shafa bayanta yayi yace sharrin mafarki ne kawai shine kika tashi kina ihu salon ki tashi
mutanen gidan oya koma mu kwanta saida safe" komawa sukayi suka kwanta ta sake sabuwar
addu'a bacci ya ɗauke ta tana maƙale a ƙirjinsa shikam hakanan yaji zuciyarsa taƙi kwanciya da
labarin mafarkinta data bashi koda yaga tayi bacci saida ya sake tofeta da addu'a sannan shima
yayi baccin.




Da asuba ita ta tasheshi yajasu sallah suka sake kwanciya ya maƙaleta batason yanda yake
nuna mata nacinsa saidai bazata iya hanashi haƙƙinsa ba haka suka bawa juna aikin safe suka
sake sabon bacci sai goma sukaji ana taɓa ƙofar ta miƙe da sauri ta faɗa bathroom shine ya
tashi ya buɗe ƙofar yana miƙa Salma ta leƙo ɗakin tans cewa “Ina sister na kaida baka gajiya da
bacci ka makarar da ita koda yake yau Sartuday ku huta abinku"
Lumshe idanunsa yayi yace “Tana bayi yanzun zata fito" yana mata bayani idanunta nakan
gadon da suka turmushe da kuma bra ɗin da take ƙasa wani mashi ya caki ƙirjinta ta haɗiye
wani yawu me ɗaci ta dubeshi tace “ok idan kun shirya ga breakfast can a dinning" jinjina kai
yayi ta juya ta fice ya koma ya ɗebe kayan daidai lkcn data fito a wankan tana goge sumarta ya
zagaya ya rungumeta ta baya yayi kissing wuyanta yace “Morning My Chocolate" murmushi
Kalmar tasata.




Ta janye a jikinsa tace “kayi wanka tukunnan" nufar bathroom ɗin yayi yana cewa “kamata yayi
kiyimin wankan nan ba kibani umarnin yin wankan ba" shiru tayi masa ta buɗe wardrobe ta
ɗauki kayanta wasu sabbin riga da zani na atamfa tasa ta ɗaura ɗankwalin tana sanya ɗan
kunne ya fito ya karɓa ya saka mata ya miƙa mata mai ya kashe mata idanu tare da nuna mata
jikinsa inda sabo ta fara sabawa da sangartarsa ko lkcn da yake ɗaukar ta yakaita hotel idan
yayi wanka miƙe mata yake yace ta shafa masa hakan yasa ta saba ta shafesa tsaf ta ɗauko
masa kayansa data gani a gurin ta taimaka masa yasa ya kamo hannunta suka fito.

Salma na zaune ta zuba uban tagumi a parlourn taji saukowarsu tayi saurin kawar da
damuwarta tana mamakin yanda taga Kharimatun lfy ƙlau nandanan taji wani baƙin ciki ya
cushe mata zuciya wannan wacce irin yarinya ce duk abinda aka shirya mata yake neman
watsawa a banza, ƙwafa tayi a zuciyarta tace “in kinsan wata ai bakisan wata ba zanyi
maganinki bari muga kamun ludayin wannan da akace nasa miki a abincin tukunna" zama
sukayi a dinning ɗin ta gaisheta cikin ladabi ta amsa da murmushin da baikai zuci ba da kanta
ta haɗawa kowa break ɗin Kharimatu ta ɗauki nata a kunyace tayi bismilla takai bakinta
nandanan annurin fuskar Salma ya ɗauke jin tayi bismilla abincin da bata iya ci ba kenan
komanta ya rushe duk kuɗin data kashe sun tashi a banza wannan shegiyar yarinyar dole a
canza taku ƙaramin asiri bazai kaita ƙasa ba saidai tsafi.
Daƙyar Salma ta rinƙa tura abincin bayan sun gama ta tashi ta kwashe kayan Kharimatu ta miƙe
domin ta tayata tace “aa yi zamanki ki huta amarya bata wahala kedai ki kula mana da mijinmu
shine kawai aikinki" kunya ce tasa Kharimatu ƙasa da kanta ya riƙo hannunta yace “kinji abinda
akace miki ko ki kula dani" yanda yayi mgnr yabasu dariya sukayi dariya ya miƙe yace “Zanje na
gaida su Hajiya ku kulamin da kanku" fatan alkhairi sukayi masa Kharimatu ta miƙe ta sake
gyara parlourn suka zauna suna hirarsu sama sama Salma ke janta da hirar nandanan ta saki
jikinta sukayita harkokinsu tare ranar har girki tare sukayi abinsu can yamma aka dawo musu da
yaran gdan da suka tafi hutu gdan kakanninsu yaran suna ganinta suka fara murna ta jasu
jikinta sukayita shirmensu a haka Aliyu ya dawo ya tarar dasu yaransa sai nishaɗi sukeyi da
ganin Uwar goyonsu shima sai yajishi cikin farin ciki ya zauna a cikinsu yana tayasu Salma sai
tsiya takeyi masa wai yamai da kansa yaro.




Basu suka bar parlourn ba sai goma saura na dare Muwaddat tace “Aunty yau ɗakinki zan
kwana" Farooq ma yace “nima acan zan kwana" Aliyu dake zaune ya miƙe yace “Nima Aunty
yau a ɗakinki zan kwana" dariya sukayi Salma tace “aikuwa saidai kai ka hƙr kabarwa yara
Auntynsu" murmushi yayi yace “dake don yara aka halicce ta ba to aikuwa saidai su su hƙr
subarmin so nake na samo musu ƙani da wuri" haɗiye takaicinta tayi ta nufi saman tana cewa
Allah ya taimaka zanyi murna da hakan mukam munyi adabo da haihuwa" ɗaukar Jannat tayi
tace “muje mu kwanta saida safe ko" miƙewa dukansu sukayi suka bita suna murna yau zasu
kwana da Auntynsu. Muryar Aliyu taji a bayanta yace “My Kharry!" Tsayawa tayi ya tako ya
dafata yace “ina jiranki a ɗakina" saida ƙirjinta ya buga tayi ƙarfin halin cewa ok bari na kwantar
dasu"




Jinjina mata kai yayi ta nufi saman yana biye da ita ta buɗe ɗakin yaran ta kwantar dasu tare
dayi musu addu'a bayan tasa musu kayan baccinsu kwanciya tayi a gefen su sunata yi mata
surutu har bacci ya ɗauke su Dukansu.
Shirun Aliyu yaji tayi yawa ya miƙe ya buɗe ƙofar ya nufi ɗakin yaran ya isheta tana bacci

rungume da Jannat ya zubanta ido shauƙin ƙaunarta da sha'awarta suna ɗibansa ya matsa ya
zare Jannat ɗin ya kwantar da ita ya ɗagota gabadayanta ya nufi ɗakinsa da ita ya kwantarta
kamar wata baby yana ƙare mata kallo yaja numfashi ya ɗora bakinsa saman lips ɗinta ta buɗe
idanunta akansa shima ita yake kallo tace “ina yaran?" Dariya tambayar tabashi ya janye yace
“da kina tunanin kinci bulus ne zaki tafi gurin yara kibarni shanye kamar mayafi" miƙa tayi ta
tashi zanne ya zauna a gefenta yace “meye na miƙewar?" Murza idanunta tayi tace “kayan nan
zan cire" janyota jikinsa yayi yace “ki kwanta abinki zan cire miki" hannu yakai bayanta ya zuge
zip ɗin ya zuge na sikelt ɗin ya zare mata ya ɗora bakinsa saman wuyanta yana lasa ta lumshe
idonta tanajin wata muguwar faɗuwar gaba da batasan meye ya sabbabata ba cikin lkc ƙanƙani
kanta yayi wata muguwar sarawa ta sanya hannunta biyu ta riƙe kanta ta saki wata
razannanniyar ƙara data sanya kowa na gdan fitowa...........




Oum Hairan
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ37-38 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566



Ƙoƙarin riƙeta Aliyu yakeyi saidai tafi ƙarfinsa watsoshi tayi ƙasa itama ta zube tana wani irin
abu daya tashi hankalinsa ya matsa ya riƙe ta daidai lkcn da Salmah ta turo ƙofar ta shigo tayi
kansu da sauri tana faɗin subhanallah meye ya sameta?" Kallonta kawai Aliyu yayi yaci gaba da
yima Kharimatu addu'a amma kamar Bama yi yakeyi ba ganin abin bana wasa bane ya tashi ya
fita yana kiran wayar Alh Ma'aru dake dare baiyi nisa ba ya sameshi nan yake faɗa masa
abinda yake faruwa hankalinsa ya tashi matuƙa da kansa ya fita ya ɗauko limamin unguwarsu
suka nufo gdan nasu bayan ya ɗauki Granny yanayin da suka tarar da ita ya basu tsoro liman
ɗin ne ya soma yi mata addu'a ta rinƙa miƙewa tana son ƙwacewa daƙyar Suka samu ta fara
mgn cikin wata irin murya data tsorata kowa dake gurin sukaji ta fashe da kuka tana cewa “mu
ku ƙyalemu bamu muka kawo kanmu ba ita ta taɓomu mu haukatata ko mu sanya mata ciwo
mun kasa yin ko ɗaya sharaɗin zuwanmu bazamu barta ta samu ciki ba amma abin takaicin
saida ciki ya shigeta" wata dariya ta ƙara fashewa da ita data sanya Salma matsawa taci gaba
da soki burutsun surutunta liman nata kwarara mata karatu.




Basu suka samu ta jirge ba sai wajen asuba sannan ta kama bacci liman ya sharce gumi ya
dubi Aliyu yace “ka biyoni gda ka karɓo mata rubutu gdy yayi suka fita suka barta kwance

tanata baccinta suna fita Salma ta sheƙe da dariya ta matsa kusa da gadon tace “yaro man
kaza kin tabka kuskure da kika bari kika shigo gonata zaki gane kurenki mijina gdana sunfi
ƙarfinki sai na mayar dake abar tausayi kuma abar kwatance a duniyar maciya amana" tsaki
taja ta juya ta fice daga ɗakin bai jima sosai ba ya dawo kamar yanda Mal Kabir ya faɗa masa. Haka ya rinƙa shafa mata rubutun a ƙasan mararta zuwa ƙirjinta ta rinƙa sakin ajiyar zuciya bai
jima da gama shafa mata ba ta buɗe idonta ta saukeshi a saman agogo takwas da rabi ta
yunƙura zata miƙe ya ɗagata taja numfashi tare da sauke idanunta akansa yayi mata murmushi
yace “Ya jikin" lumshe idonta tayi kanta har yanzu sarawa yakeyi ta buɗe idonta akansa tace
“Meyesa baka tasheni da asuba ba?" Kawar dakai yayi yace “bakida lfy ne shiyasa" da wannan
ta miƙe ta shiga bathroom tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallah ta shirya cikin wasu riga da
sikert na jeans tayi kyau sosai sauka yayi ƙasa ya ɗauko mata break ya dawo.




Zama sukayi da kansa ya rinƙa bata abincin a baki tun daga wannan rana ya zame mata al'ada
duk dare basa bacci kwana yakeyi akanta sai safiya tayi suke samun nutsuwa tsayin wata guda
sai kuma laulayi ya sawo kai kullum tana kwance kamar ruwa tun ga amai da take fama dashi
babban abinda ya fara bata mamaki da tsoratata a yanayin zaman gdan nasu idan yana gda
Salma zata nuna mata tafi kowa kulawa da ita idan bayanan kuwa ko leƙota batayi haka suke
rayuwa sannu a hankali lkc ya rinƙa tafiya cikin yanada watanni hudu cikin wani dare da bata
mantawa dashi ranar ba ita keda girki ba Salma ce tun yamma takejin yanayin zazzaɓi ajikinta
haka ta gama abinda takeyi a daddafe ta kwanta bacci ya ɗauketa cikin baccin taji wani mugun
huci yana tunkarota ta buɗe idonta da sauri tare da dirowa a gadon daidai lkcn da wata
doguwar halitta ta ƙaraso gabanta batayi aune ba taji an feso mata wani abu me azabar raɗaɗi
a jikinta azabar data ratsa ta itace tasata sakin wata gigitacciyar ƙara ta zube a gurin
kasancewar dakin a kulle yake Tsakanin ɗakinta dana Aliyu akwai tazara baijita ba amma
Salma taji ta basar hakanan tayita juyi tana murƙususun azaba ta daɗe sannan ta samu raɗaɗin
ya ragu tana addu'a sannan ta buɗe idanunta taga wannan mutumin ya ɓace taja ajiyar zuciya
tanabin jikinta da kallo.




Me zata gani wasu irin ƙananun ƙuraje ne gabaɗaya jikinta sai zubar da ruwa sukeyi aikuwa ta
mike a razani tana ƙara bin jikin da kallo tana faɗin “Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un" tsoro ya
sake kamata ta tsigar jikinta tana tashi wasu zafafan hawaye suka zubo mata cikin tashin
hankalin da bata taɓa shigaba tace “Na shiga uku Ni Kharimatu wannan wacce irin masifa ce?"
Ashe wasa farin girki ne cikin lkc ƙanƙani taji kanta da jijiyoyin jikinta sun ɗaure ɗam ta kasa ko
matsa komanta kafin kace meye wannan ta yanke jiki ta faɗi.
Bata farka ba sai a gadon asibiti tana buɗe idonta jikinta ta fara kallo ta rintse idonta cikin
ƙyanƙyami da tashin hankali ta rushe da wani kuka me gunji tace Innanillahi Granny meye
wannan a jikina" Granny da Mom da suke zaune a gefe suka nufota da sauri cikin tsananin

tausayi Granny tace “Sannu Kharimatu ke kuma taki ƙaddarar kenan daga wannan sai wannan
Ni waɗannan ƙuraje don dai sun dage akan ayi maganin asibiti ne nikam nafi tunanin sihiri ne"
Mom ce ta cafe da cewa ashe muna ɗaya dake lamarin yarinyar nan akwai alamun bincike
Hajiya iyakar zamanmu da ita batada jinnu kina gani fah dagayin aurennnan abu yaƙi daɗi
kullum ita kenan ta yanke jiki ta faɗi yanzu kuma ga wata sabuwar masifar ta sako kai kiga fa
jikinta yanda ƙurajen nan suka girma fata me kyau ta zama kamar bayan bishiya sai daddarewa
takeyi"




Jinjina kai Granny tayi tace “Ma'aruf ne yake biyewa yaron nan Ni dama Muniba tun farko banso
zaman Kharimatu da Salma guri ɗaya ba nasan sai an cutar da yarinyar nan" karɓa Mom tayi
da cewa “ai gashinan sun fara gani Hajiya dole idan yarinyar nan ta samu sauƙi ya raba musu
gda ko kuma ya sawwaƙe mata tunda zamansu taren ba dole bane" akan wannan shawarar
suka tsaya.
Tun ranar data farka a asibitin take sanya idon ganin Aliyu shiru babu shi babu labarinsa har
yau gashi kwana uku da farkawarta abinda yake bata mamaki ko a waya bataji yana kiran
Granny ba yau tun safe ta tashi jikinta sai ruwan mugunya yake zubarwa abinda ya tashi
hankalin kowa babu shiri Granny ta Kira Aliyu ta sanar dashi abin mamaki sai cewa yayi da ita
shifa ayi duk abinda ya dace Bama ya gari yana Lagos zai turo musu da kuɗi" jinjina kai
Granny tayi tace “Anya Aliyu yau yarinyar nan watanta guda a asibitin nan tun washegarin ranar
da aka kawota baka ƙara dawowa ba matarka ma batazo ba meye yake faruwa ne haka?"




A kausashe yace “Itama batanan muna tare anan yaran suna gdansu Salma daganan Dubai ma
zamu wucce Salma keda ciki zataje ta huta acan maybe sai yakai 6 months zamu dawo"
murmushi Granny tayi tace “Lallai ne Gadanga kabar yarinya marainiyar

8 / 11