Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
dama Muniba ashe ita kaÉ—ai kika haifawa Aliyun da take neman kisa akansa?"
Ƙasa Hajiya Muniba tayi da kanta tace halin kishi dai irin na wasu matan da basu da lissafi da
control É—in zuciya akansa in banda haka meye abin tashin hankali akan Kharimatu Ni ganin ma
da nakeyi batakai kishiya ba yarinyar nan....."
“Eh aifa dama Dole kice haka mana tunda ba Abida aka ɗaukarwa ba idan batakai kishiya ba
kisa gyatumin mijinki ya auro......"
Dafe kuncinta tayi da sauri saboda wasu faya fayen maruka da Aliyu ya sauke mata a kuncinta
ta saki ƙara tare da matsawa baya ya nufota cikin muguwar Hassala yayi ball da ita ya rinƙa ƙoli
da ita har wajen asibitin yace “Zan iya ƙyaleki akan duk wani rashin mutumcinki amma ki kiyayi
abu biyu taɓamin iyaye da kuma ƙara gigin taɓa lfyr Kharimatu....." Miƙewa tayi tayi kansa tace
“inkaga dama ka kasheni bazan fasa ƙudirina akanta ba wlh Indai baka saki yarinyar nan ba
saina kasheta" murmushin takaici yayi yace “na roƙeki karki fasa kiyi duk abinda zakiyi abinda
kike baƙin ciki akansa saita jishi a jikinta kuma itama saita haifamin kamar yanda kika haifa
kekam na daÉ—e ina nadamar auren jahilar mace irin ki tabbas aurenki jalabi ne gareni ba alkhairi
ba wawuya mara lissafi to waima ke a haukanki wannan ce zatasa nafasa abinda nayi niyya?
To kuwa ki canza tunani domin na fahimci ko a makaranta ta ƙarshe kike ɗauka shiyasa kike
tunanin barazana zata canzama Aliyu ra'ayi"..........
*_21-22Oum Hairan_*
~Paid book~
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta
0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_
_____________________________
Cije leɓe Salma tayi tana kallonsa ya juya ya shige cikin ward ɗin tare da faɗawa security na
ƙofar kada su kuma barinta ta shigo cikin asibitin aikuwa duk bala'inta basu barta ta kuma
shigar musu ba dole tasata juyawa ta fice a asibitin ta koma gdanta tuburan take hauka duk
wani abu da yake mallakin Anam a gidan saida ta watsoshi waje sannan ta nemi guri ta zauna
ta rushe da wani irin mugun kuka tana lalubar wayarta ta kira number yayarta Amina dake Niger
tana aure ta rushe mata da kuka tace “meye yasa duk abinda na tsana yafi kusanta ta Amina
meye yasa duk cikinku da muka fito ciki É—aya babu wacce mijinta yayi gigin yi mata kishiya saini
kuma ma don tozarci ya rasa dawa zai haÉ—ani saida Æ´ar aikin gdana...."
Wata uwar ashar Amina ta saki tace “kiname kikayi wannan sakacin? Koda yake aike yar daɗi
miji ce tausayinsa kikeji gashinan shi ya fara nuna miki kalar nasa tausayin....." Cikin kuka tace
“wlh bantaɓa tunanin haka daga Aliyu ba Amina ki bani mafita ina cikin tashin hankali yau fah
Aliyu saboda yarinyar nan har tsawa yayi min kuma ya É—aga hannu ya mareni har yana yimin
kashedi akan nace zan kasheta"
Salati Amina tayi tace naga ta kaina Ni Inno ubanwa yace ki nuna masa haukanki bayan kinsan
zaki iya nemawa kanki mafita to kiyi gaggawar saita kalaminki kada kija abinda zaiƙi yarda dake
ke bakiga abinda ya faru ba lkcn da akayi min kishiya banyi hauka ba amma kwananta nawa?
Numfashi Salma ta sauke tace “Abin da ciwo Amy ƴar aikina fah...." Dakatar da ita tayi da cewa
“in kuwa kinaso kici riba kiyi musu kisan mummuƙe to sai kin koyi riƙe kishinki kin jata a jikinki
kin nuna mata so da hakane zaki cimma burinki"
Shiru tayi tana nazarin maganganun Yayar tata to ta Ina zata fara bayan ta riga ta bata rawar ta
da tsalle bayan hakanma da wacce zuciyar zata iya danne kishin Aliyu harma ta É—auki Anam
matsayin da Amy takeso ta É—auke ta?
Miƙewa tayi tana zagaya falon zuciyarta na ayyana mata abubuwa da dama ranar taci kuka
kamar ranta zai fita hakanan tasa aka É—ebe kayan da tayi watsi dasu aka mayar dasu É—akin
Anam ta zauna ta zabga uban tagumi lkc Zuwa lkc tana duba agogo shaiÉ—an yana raya mata
yanzu saboda Anam Aliyu ya manta da ita ko gdan yaƙi dawowa gashi har yamma tayi. Ranar tayi dogon yini ita ɗaya damma Amee na kiranta tana sake bata logar yanda zata ɓullowa
lamarin da dabarun danne kishi har shawara tabata kan karta bari ya raba musu gda akwai
matsala inda ita kuma ta tubure kan cewa itafa batason ma takai ga ya haÉ—asun, daqyar dai ta
samu ta shawo kanta ta yarda da abinda take É—orata akai sukayi sallama tana shirin komawa
sama ya buɗe ƙofar ya shigo ta tsaya suna kallon juna Lumshe idanunsa yayi ya raɓa ta
gefenta zai wucce tace “Don Allah kayi hƙr...." Juyowa yayi da sauri ta rusuna a ƙasa idanunta
na tsiyayar da hawaye tace “Bayan na dawo gda na kira Hajiya nake sanar da ita abinda yake
faruwa shine tayimin nasiha tare da yimin furucin daya kashemin jiki Aliyu ba laifina bane
abinda na aikata É—azu kishin kane da ciwon abinda ka aikatamin amma insha Allahu hakan
bazai ƙara faruwa ba nayi maka alƙawarin zanyi iyakar ƙoƙarina na tsare mutuncinka zan....."
Ɗaga mata hannu yayi ya wucce ɗakinsa yabarta shanye da baki ta miƙe ta nuna ɗakin tare da
yin ƙwafa tace “akalar raƙumi me sauƙin juyawa zakayi bayani ne tunda ka shigo gonata"
shigewa tayi É—akinta ta kwanta tanata tunanin abinda ya dace ta fara yi.
Aliyu kam koda ya shiga É—akinsa duniyar ce tayi masa zafi rikici sukayi sosai da Granny akan
dawowar Anam gdansa ya kafe saita koma gdansa ita kuma ta kafe saidai su tafi da ita badon
ransa yanaso ba haka ya hƙr ya bar su suka tafi da ita fam house nasu saboda Dad yace bazaa
nakasa marainiyar Allah ba tunda ya baro asibitin yake ƙuncin zuciya. Tunaninsa yana ga Anam yanaji kamar yaje ya taho da ita wannan tasa ya kasa saurarar Salma
saboda itace taja masa komai.
Wannan dare kwana yayi yana juyi yanajin Salma ta gama bugun ƙofarta ta gaji ta tafi ta qyale
shi. Da safe da wuri ya tashi yayi wanka ya fice a gdan ko haÉ—uwa basuyi da Salma ba ya nufi
gdansu a É—akin Granny ya ishe Anam tana kwance a gadonta tanata bacci kanta daure da
bandeji ya tsaya a gaban gadon ya zuba mata idanu tana sanyi da jar rigar bacci iya cinya,
ƙirjinta ya zubawa idanu yanajin wani shauƙinta batare daya shirya ba ya durƙushe a gabanta
yakai hannunsa ya shafa fuskarta dake cike da suma sajenta ya kwanta luf kan smile face nata
yankan manyan idanunta sunfi komai ɗaukar hankalinsa musamman ɗan ƙaramin bakinta,
Irin kallon ƙurullar da yakeyi mata shine yasata motsawa tayi miƙa tare da buɗe ido ta miƙe da
sauri tana bin jikinta da kallo tare da jan bargo ta rufe jikin nata miƙewa yayi yana shafa
sumarsa yace “Ya jikin naki?" Cikin sakaliyar muryarta tace “Da sauƙi ya kwanan su Farooq"
numfashi ya sauke yace “basu dawo ba daga gdansu Salma zasu wucce makaranta idan an
tashesu zanje na É—aukosu zan kawosu su duba mamansu"
Sunkuyar dakai tayi ya sunkuyo daidai wuyanta yace “Granny tanason jamin layi dake
Kharimatu na buƙaci ƙara aure ne don ina buƙatarsa Da gaske ina buƙatar kulawarki Please ki
saki jiki da mijinki Aliyunki kinji"
Ƙasa tayi da kanta cikin tsoro da jin nauyin kalamansa tace “Nidai inajin tsoron Aunty Salma
Daddyn Farooq nafika abin faÉ—a akanta domin nice nake yini da ita tun kafin ta fara aiki Allah
inajin tsoron kada naje ta....."
Rufe mata baki yayi yana mata murmushi yace “babu wani abu da zai faru fa hasali ma tayi
nadamar abinda tayi miki jiya har hƙr tazo ta bani"
_Tabbas zuciya tanajin takaici a lkcn da akayi banza da ita kuyi hƙr na jina shiru da kukayi nima
ba haka naso ba duk da komai bai kammala ba yanda nakeso zanyi ƙoƙari idan nayi wannan
yau gobe nayi wancan har zuwa lkcn da abubuwa zasu daidaitarmin insha Allahu kuyi hqr ku
fahimceni musamman yan VIP section daya kamata na rinÆ™a yi muku post kullumí ½í¸“_
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *_MYJ 23-24 Oum Hairan_*
~Paid book~
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta
0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_
_____________________________
Da sauri ta girgiza masa kai tace “Aa Daddyn Farooq nidai hƙrn zakayi shine yafi zame mana
alkhairi wlh idan ka matsa saina koma gdannan zan gudu ne...." Kawar da kansa yayi a kanta
yayi murmushi yace “dama dai baki kasance me taurin kai ba Kharimatu nine nayi miki
alƙawarin babu abinda zai ƙara faruwa makamancin haka zan baki mamaki zan nuna miki na
isa da gdana kuma nine me ikon zartarwa a gdana....."
Bai gama rufe bakinsa ba Granny ta shigo tana cewa “Anji kakaki Sarkin zartarwa kazo ka
cikata da É—ebabben surutunka tana fama da kanta waini Aliyu yaushe ka koyi naci ne?" Kwantar
da kansa yayi a katifar gadon yace “ba naci bane Granny kulawa ce Allah da gaske bansan zan
ƙara son wata mace ba a duniya sai bayan da Kharimatu ta zama mallakina Please Granny kinfi
kowa ikon zartarwa idan kikace eh dole kowa eh zaice ki taimaka ki amince Kharimatu ta zauna
a gdana wlh naji bana sha'awar rabansu muhalli..."
Daƙuwa Granny ta watsa masa tace “Ashe dama yaudarar mu ka shirya zakayi lallai ma
É—annan yaushe ma aka haifeka da zakayimin wayo? Ni Sa'adatu na goyi ubanka amma ace yau
É—an Ma'aru ne zai gwadamin zamani, to ka kiyayeni bana ciki da iskanci Kharimatu ce bani
baka har sai kayi mata gdanta domin Ni ba shashasha bace da zan É—auki marainiyar Allah na
baka ka kaiwa mahaukaciyar matarka ta illatata a banza sullutu babu abinda zaka iya sai ban
baki"
Sanin cewa tunda tayi wannan furucin babu mai canza mata ra'ayi yasa ya saduda ya dafa
cikinsa yace “to shikenan rigimammiyar tsohuwa ku sammin breakfast na karya" harara ta galla
masa tace “ina matarka da zakazo ka cinye mana abinci?" Shafa kansa yayi yana kallon Anam
yace “gata kin ɗauke min ita ai dama itace me bani abinci kuma kin ƙwacemin ita kinga kuwa
hakanan zaki hƙr ki bani na safe na rana dana dare tsohuwa me fashin mata kawai"
Jan maganar yake nema shiyasa Granny ta fice ta rabu dashi ya juya ga Anam da kanta ke
ƙasa tunda suka fara mgnr da Granny ya tashi ya koma kusa da ita ya riƙo hannunta ta janye ya
sake kamowa ta kuma janyewa kawai saiya janyota gabadaya ya haɗata da jikinsa yace “Idan
ya kasance mata zatake gudun mijinta to meye ribar auren Kharimatu?" Bata bashi amsa ba saima ƙoƙarin janyewa da takeyi ya ɗora hannunsa saman kanta data
ɗaure dogon gashinta da baƙin band ya buɗa gurin da akayi mata ɗinkin ya shafa ta rintse
idonta yace “sannu kinga Salma tajamin asara an yankemin gashin nan me tsada" yana mgnr
yana sunsunar wuyanta daidai lokacin Granny ta turo ƙofar ta shigo Kharimatu ta janye a jikinsa
shima ya saketa cike da kunya
Ƙwafa Granny tayi ta aje masa kayan abincin ta kamo hannun Anam tace “muje kisha
maganinki" murmushi yayi kasancewar yasan saboda shine ta janyeta shi abinma dariya yake
bashi shida matarsa a rinƙa kangeta daga gareshi tsohuwar akwai rikici karyawa yayi sannan ya
tafi gurin sabon ginin da yakeyi inda daganan ya wucce gurin aikinsa. Haka rayuwar taci gaba da tafiya Anam na samun sauƙi inda surukanta suke kula da ita sosai
Hajiya Muniba ba ma'abociyar son taga É—an nata namiji tilo cikin damuwa bace wannan tasa
dole ta tursasa zuciyarta son duk abinda yakeso musamman Anam da ta kasance kusan
tarbiyyar su tunda da ita da mahaifiyarta duka a ƙarƙashin kulawar su suka rayu tsayin
shekaru,.
Babban abinda yasa suka mayar da hankalinsu ga Kharimatun shine tun auren Aliyu da Salma
basu taɓa jituwa da mahaifiyarsa ba Salma batada mutunci bata ganin kowa da gashi Indai
akan Aliyu ne har Hajiyansa kishi takeyi da ita.
Satin Mama Yabi biyu a Guru ta dawo lkcn ginin Aliyu yayi nisa sosai dake da masu gidan rana
aikin kawai akeyi ma'aikata har kwana sukeyi a wannan aiki nandanan kuwa saiga gda ya kusa
haɗuwa inda ya kafa ƙahon zuƙa akan daya gama ginin za'ayi biki abashi matarsa inda Granny
it's kuma ta kafe kan saita ƙara murmurewa hakan tasa ya tsiro da wani sabon salon wulaƙanci
baya tashi zuwa gdan sai dare idan yazo baya shiga sashin Granny sai ya daidai ci tara ta gota
daidai lkcn yasan duk inda Granny take ta soma gyagyaÉ—i anan yake samu yaje ya takurawa
Anam da taɓe² itakuma tayi ta tureshi bataso ko kuma ta sanya masa kuka.
Yauma tun Magrib yazo gdan Granny ce ta shigo ta ishe ta a zaune tana karatun hisnul Muslim
ta zauna kusa da ita tace “Wannan ɗan neman ne yazo yake cemin zakuje a gwadaki ɗinkunan
lefenki" da sauri ta É—ago tare da zaro ido tana tuno irin rabuwar da sukayi jiya daya matseta a
mota yanayi mata magiyar tabashi yaci kaɗan" narkar da kai tayi tace “Don Allah Granny kice
masa aa wlh tsoro nakeji" taɓe baki tayi tace “Ni Sa'adatu rufamin asiri da wannan soyayyen
É—an da akayi cikinsa da rana wlh nagaji da fitsarar Gadanga kije mijinki ne ban isa na hanashi
iko dake ba kuma ma yau ta sama ya biyo uwarki yaje ya haÉ—ani da ita itane take faÉ—amin"
Sunkuyar dakai Anam tayi tanaci gaba da gyara ƙumbarta Adama me aikin Granny ta shigo ta
rusuna tace “Anam kije inji maigida Aliyu yana jiranki a mota" kallon Granny tayi gabanta na
faɗuwa Granny ta kawar dakai tace “tashi kuyi kuje ku dawo kada dare ya ƙara nisa" sunkuyar
da kanta tayi tanajin kamar tace bazata ba saidai babu dama. Ganin batada niyyar tashi yasa Granny ɗauko mata mayafinta tace “bancika son gardama ba
batayi miki kyau dake ba ɗabi'arki bace ki tashi yana jiranki" a sanyaye ta miƙe ta sanya
mayafin da takalmi ta fito gabanta na faÉ—uwa. Tunda ta fito ya kafeta da ido ta cikin hasken
daya haske harabar gdan zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yana ƙarfafar ƙudurinsa daidai lkcn da
take isa ga motar ya budewa Yaran yace “oya ku koma gurin Hajiya idan na dawo saimu tafi
gda" da gudu suka shige ciki shikuma ya buɗe mata ƙofar yana ƙarfafar zuciyarsa ta rakuɓa ta
zauna a kunyace da irin kallon ƙurullar da yakeyi mata tace “ina yini" ajiyar zuciya ya sauke me
ƙarfi yaja motar ya fice daga gdan suka nufi Tarauni anan yabada ɗinkunan nata basu wani
daÉ—e ba telan ganinta kawai yayi yace suna iya tafiya.
Ta sauke ajiyar zuciyar da saida ya kalleta tayi ƙasa da kanta yaja motar suka tafi inda ta ɗago
a firgice ganin ya canza hanya maimakon ya nufi Danladi Na Sidi sai taga ya nufi Airport road ta
dubeshi da sauri tace “Daddyn Farooq...." Hannu ya ɗora a bakinsa alamun tayi masa shiru
hakanan dole taja bakin ta tsuke tafiyar na ƙara tsayi tsoronta yana ƙara bayyana tana gani ya
shigar dasu wani babban guri me yalwar haske yayi parking a parking space na gurin suka
bashi pass ya buɗe ya fita bai jima ba ya dawo ya buɗe mata yace “fito muje"
Fitowar ce ta bata ikon ƙarewa gurin kallo a fili tace “Hotel Daddyn Farooq me zanyi a hotel?"
Bai bata amsa ba ya riƙo hannunta yanajin wutar sha'awar da yake fama da ita kusan wata
guda don tunda aka É—aura aurensa da Anam Salma bata sauraronshi shekaran jiya ma ta tafi
Niger yayarta Amee ta haihu janyota yayi ta faÉ—a jikinsa baya ko jin kunyar mutane a haka suka
haura saman ya buÉ—e É—akin suka shiga ya mayar ya rufe tare da É—ago kanta ga mamakinsa
yaga ashe tuni ta ɓalle da kuka.
Janta yayi ya haÉ—ata da bango ya É—ago fuskarta yasa hannunsa É—aya yana share mata
hawayen yace “Allah yana farin ciki da matar da take sanya mijinta cikin farin ciki Kharimatu don
Allah kada ki hanani samun nutsuwa sake Allah feeling É—ina na kwanakin nan dabanne bazan
iya control É—in kaina a yau ba shiyasa na yanke shawarar É—aukoki ki samamin nutsuwa.............
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *_MYJ 25-26 Oum Hairan_*
~Paid book~
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta
0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_
_Ina yan kasuwar mu ta online masu so a tallata musu hajojinku to albishirinku Oum Hairan tayi
muku tsari me sauƙi domin tallata muku hajojinku cikin farashi me sauƙi su bazu a duniya ku
samu customers ɗaga sassa daban² na ƙasar nan dama maƙotan ƙasashe kudai kuyi maza ku
garzayo domin jin ƙarin bayani,_ _MORE IMFO CALL 09031307566 OR CHAT ME FOR WHATTSAP NUMBER 09013718241._
_TABBAS ME TALLA SHIKE DA RIBA SAI MUNJIKU_í ¾í´—
_____________________________
Janyewa tayi a jikinsa ta koma gefe tana girgiza masa kai yayi murmushi ya cire key na ƙofar
ya nufi bayi yayo fitsari ya É—auro alwala har yanzu tana tsaye inda ya barta yana gyara kwalar
rigarsa yace "kinyi sallar Isha?" ÆŠaga masa kai tayi ya shimfiÉ—a sallaya ya