MEYA JAMIN COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   10 / 11

27K to 30K   out of 31.7K words

nasa" dariya Mom tayi tace “Haba Kharimatu
shekara ɗaya yaro kamar ya shekara biyu yaushe zaki yayeshi?" Ƙasa tayi da kanta tana
murmushi tace “Waida yayi wata ashirin ko ya kika gani?" Jinjina kai tayi tace “Hakanma yayi
amma ki cireshi da yayi sha huɗu saboda kinga makaranta zaki koma ga form ɗinki canma Dad
ya siyo miki registration káwai zaiyi miki da ɗan abinda ba'a rasa ba saidai makarantar ba anan
Kano take ba Alkalam University dake Katsina ya sama miki zaman hostel ya ganki shikuma
karatu bazai yiwu da yaro ba"




Miƙewa yayi ya ɗauki wayarsa da key ɗinsa ya fice daga ɗakin babu jimawa daya cikin masu
aikin gdan ya dawo ya dubeta yace “Yallaɓai ke nemanki a waje" ɗagowa tayi suka haɗa ido da
Mom diririce tace “am in kaje ina zuwa" murmushi tayi tace “tashi kije ya ɗauke miki ɗa kinsan
bayason jira zai iya tafiya dashi" Miƙewa tayi ta fito yana tsaye jikin motarsa sarai tagansa ta kawar dakai tayi wuccewarta Jawad
yana ganin ta wucce ya rushe da kuka yana kiran Aunty tanaji Aliyu na ƙwala mata kira taƙi ko
tsayawa bare yasaran zata waiwayo ganin haka yasashi binta da sauri dake itan ba sauri takeyi
ba baisha wuyar cimmata ba yasha gabanta saura ƙiris ta shige jikinsa tayi baya da sauri yaja
numfashi yace “Wai meye ke faruwa ne Kharimatu na zaci idan kowa ya juyamin baya ke zaki
kalleni ta gaba" ɗagowa tayi ta kafesa da manyan idanunta ya janye nasa daga cikin nata sosai
idanunta keyi masa kwarjini baya jurewa kallon ƙwayar idonta baki ta buɗe cikin sanyin
muryarta tace
“Matsa zan wucce" baice mata komai ba kuma bai matsa ba ta canza hanya ya riƙota yace




“Ki fahimceni Kharimatu wlh ba laifina bane bansan matsalar da haɗaku gda ɗaya da Salma
zata haifar kenan ba da wlh bazan haɗaku ba kinaji ba kinsani Baba Na'ibi ne yazo bama na
ƙasar nan lkcn aka buɗe masa gdana ya shiga suka ƙwaƙule binne binnen da akayi a ɗakinki da
ƙofar shiga gdan ko shekaran jiya munyi waya dashi ina faɗa masa matsalata inasonki inason

dawo dake cikin rayuwata amma na kasa takawa naje inda kike idan na kiraki baki ɗagawa
cemin yayi na jirashi minti biyar babu jimawa ya kirani yace naje ɗakina cikin wardrope ɗina ta
tsakiya cikin kayana na birkita sosai akwai wata laya nayi bismilla na ɗauketa na warware na
zuba mata fitsari ko ruwan kwata na ƙona ta wannan itane abinda ya raba tsakanina dake.
Kharimatu
nayi yanda yace ɗin kuma tun ranar na samu relief ya kasance kullum cikin tunaninki nake
Kharimatu ki tambayi Mama Saude cikin kwanaki ukun zuwana Guru biyu tana cemin bakyanan
na tambayeta inda kike taƙi faɗa min na dawo na tambayi Granny ta ci mutuncina Dad har
marina yayi akanki Mom ce kawai take tausayina cikin lamarinki"



Murmushi tayi me ciwo tace “Naji bani hanya na wucce" yanda tayi mgnr yasashi kallonta yace
“Baki yarda ba ko Kharimatu?" Ɗagowa tayi ta kalleshi tayi masa murmushin daya sanyashi
sakin baki yana kallonta tace “Ina tunanin saboda ɗanka daka banzatar ka watsar da rayuwarsa
ya kasance da mutuwarsa da rayuwarsa duk basa cikin abinda ya dameka kake bibiyata ko? Ok
Indai saboda Jawad ne gashinan ka riƙe abinka don Allah ka rabu da rayuwata Aliyu inason
Jawad amma na hƙr nabar maka abinka nasani tunda Allah ya azurtani da cikin haihuwa idan
Ya nufeni da sake aure zan haifi madadinsa....."
Wata tsawa ya buga mata yana huci jikinsa na rawa yace “Ni kike faɗawa zakiyi aure ki haifi
wasu yaran kuma da igiyoyin aurena uku akanki saboda bakida mutumci" bata tsaya
sauraronsa ba ta juya tayi tafiyarta tanaji yana kiranta bata juyo ba saima sauri data ƙara ta
shige sashin Granny ta datso ƙofar ya iso da sauri ganin yanda Jawad ya ƙara rushewa da
kuka.




Granny ce ta fito saboda kukan da ta jiyo Jawad yanayi turus taja ta tsaya ganin Kharimatun
zaune a falon tana share hawaye, matsawa tayi gareta ta dafa kafaɗarta tace “Ina kika baro
Jawad ɗin nake jiyo kukansa?" Ƙasa tayi da idanunta tace “Ya....yana gurin Babansa" bata
kuma ce mata komai ba ta nufi ƙofar ta buɗe ta ishe Aliyu sai rarrashin yaron yakeyi yaƙiyin
shiru.
Yana ganinta ya fara miƙa mata hannu ta dubi Aliyu da duk ya ruɗe duk da darene hasken dake
gurin ya bata damar ganin yanda idanunsa ya kaɗa yayi jawur tayi juyawarta zatayi tafiyarta ya
riƙota yace “kiyiwa Allah kada ku hukuntani da haka kuka yakeyi Granny kuma nono yakesha
idan ita batada hankali ta tafi ta barni dashi aike babbace kinsan daidai" fusge hannunta tayi
tace “Irin hankalinmu ɗaya Aliyu itama tana buƙatar hutu tunda ba ita kaɗai tayi cikin ba hasali
ma kafita ƙarfi lkcn da za'a samu cikinsa domin gashinan ya bayyana kansa duk wanda
yagansa yaganka yasan jininka ne kaje ka haɗashi da ƴan'uwansa"
Zuba mata ido yayi kukan yaron yana masa kuɗa a kunne ya juya zuciyarsa na zafi idanunsa
sai raɗaɗi sukeyi ya isa motarsa ya buɗe ya shiga har lkcn Jawad kuka yakeyi ɗagashi yayi ya

rungumeshi a ƙirjinsa yaron ya ƙanƙameshi yayi luf a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya, so
ƙauna da tausayin ɗan nasa yaji yana ratsa jinin jikinsa yanda yaron yayi luf a ƙirjinsa yasa
hawaye zubo masa wato shima yana buƙatar duminsa, meye yasa ya nesanta kansa dashi?"




*Oum Hairan*
[11/14, 8:41 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ45-46 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566



Kasa tashin motar yayi yaci gaba da jijjiga yaron har saida yaji numfashinsa ya sauya ya
saukeshi yaga ashe yayi bacci yaja fasali ya kwantar dashi a kujera yaja motar ya fice a gdan
zuciyarsa a hassale ya nufi gdansa yayi parking ya fito ya ɗauki Jawad ya kulle motar ya nufi
cikin gdan buɗe ƙofar yayi ya shiga dake shi ɗaya ne a gdan ya kwantar da yaron a gadonsa ya
zauna ya haɗe kai da gwiwa yanajin zuciyarsa na tafashi lkc zuwa lkc yana furzar da iska me
zafi bashi ya kwanta ba sai wajen 1:30am bawai bacci ya kwanta yayi ba tunanin mafitarsa
kawai yakeyi.
Bayan tafiyarsa Granny ta koma ɗakin da Kharimatu take ta dubeta tace “meye yasa kika bari
ya ɗauki yaron nan?" Ɗago idanunta da suka jima da jiƙewa da ruwan hawaye tayi tace
“bansan ya ɗauke shi ba Granny Jawad ya fita wajen parlourn Mom yana wasa anan ya
ɗaukeshi" jinjina kai tayi Hajiya Bushira tace “Yanzu ina Jawad ɗin?" Granny ce tace “cewa nayi
ya tafi da abinsa itama ta huta...." Zaro ido Hajiya Bushira tayi tace “Ya tafi dashi kuma Hajiya
amma kunyi ganganci yanzu idan matar nan da ba ƙaunar Kharimatu take ba ta huce haushinta
akan Jawad fah" Murmushi Granny tayi tace “Nasan Halin Aliyu koda Salma nanan bazai taɓa
yarda ta taɓa masa ɗa ba balle Bama tanan tana gdansu tana jinya tunda ta haihu ta haɗu da
lalura Cancer mahaifa ce ta kamata sai kuma irin ƙurajen da kikayi da cikin Jawad sunanan sun
feso mata sai mugunya take zubarwa sunje asibitin sunyi na gargajiyar ance dasu ƙaiƙayi koma
kan masheƙiya akayi mata ita tayiwa kishiyarta shine Abin ya dawo kanta"




Zuciyar musulmi sai Kharimatu taji tausayin Salma ya ɗarsu a ranta tace Allah sarki Granny na
tausaya mata ciwon nan akwai wahala ubangiji ya bata lfy" taɓe baki Granny tayi tace “karma ta
samu lfyr mugun nufinta ne ya koma mata nifa dama bantaɓa ƙaunar yarinyar nan ba wlh bata
kwanta min ba shima donta zame masa jaraba ne" Itadai Kharimatu tunanin ɗanta kawai takeyi ta kwanta ta juya musu baya sai hawaye take

sharewa tana tunanin yanda zai kwana babu ita daƙyar bacci ɓarawo ya saceta shima bana
daɗi ba da safe ma data tashi duk wani sukuku ta tashi ga nononta ya cika sai damunta yakeyi
basarwa kawai takeyi tana duba agogo lkc zuwa lkc kawai so take taji zuwan Aliyu amma shiru
har la'asar.



Sai bayan Magrib ya shigo gdan yayi parking tana tsaye jikin window ta zuba masa ido tana
ƙare masa kallo cikin hasken daya mamaye gurin sai yanzu take ganin ramar da akace yayi
Granny ta Bata lbrn wata tunda suka dawo Salma ta tafi gdansu yaran nasa a gurinsa suke
shine komansu Salman da kanta tace bazaa ɗorawa iyayenta wahala ba sosai taji tanajin
tausayinsa duk aikin da akace ba naka bane idan aka Barka dashi an jarabci rayuwarka, ganin
ya saɓa Jawad a kafaɗarshi taji kamar taje ta kwace ɗanta tana ganinsu suka shiga sashin
Mom ta zari mayafinta tayi waje itama ta nufi sashin Mom ɗin tana kai kanta zata shiga shikuma
yana fitowa ganintan da yayi yasashi cafkar hannunta da ƙarfin da bata isa ta ƙwace ba ya nufi
motarsa da ita suka tsaya jikin motar ya ja numfashi ya ɗago idanunsa akanta yace “Wlh duk
girman laifina gareki ban cancanci wannan horon ba Wlh Allah ɗaya Kharimatu da rana ɗaya
bantaɓa rabuwa da tunaninki ba don Allah kiyi hƙr ki manta da duk abinda ya faru nayi miki
alƙawarin bazai sake faruwa ba har abada insha Allahu"




Zame hannunta tayi ta juya tabar gurin yabita da kallo yana mamakin kafiyar yarinyar a fili yace
“dama haka kike?" Tambayar kansa yayi bashida amsa haka ya shiga mota ya tafi ta shiga
sashin Mom tana shiga Jawad ya taso da gudu har yana faɗuwa yana fasa baki amma bai fasa
isowa gareta ba ta kalli Mom so take ta ɗaukeshi kunyar Mom ta hanata murmushi Mom tayi
tace “ki ɗauki ɗanki Kharimatu banda shashancinki meye na barinsa ya tafar miki da ɗa" ajiyar
zuciya tayi tasa hannu ta ɗaukesa ta rungumeshi ya ƙanƙameta shima hawaye ya zubo mata
tayi saurin sharewa ta zauna suka gaisa da Mom suka taɓa hirarsu Mom tace mata “Kharimatu
nafi yi miki sha'awar komawa gdan mijinki fiye da zaman nan da kikeyi Aliyu yana sonki
Kharimatu wlh na tabbata bayin kansa bane abubuwan da suka faru da farko naji haushinsa sai
daga baya na fahimci sharrin mace ne yasashi aikata duk abinda ya aikata kiyi hƙr badon Aliyu
ba domin Allah ki komawa Aliyu kinji?"




Tunda Mom ta fara mgnr take matsar idanu harta gama ta zuba mata idanu tanason taji
cewarta, ƙasa tayi da kanta tana wasa da ƙafar Jawad da yaketa ɓaɓɓaka dariyarsa mom ta
sake magantuwa da cewa “bakice komai ba Kharimatu ko bakyason zamanku da Aliyun ne?"
Hawayen ta share tace “Ba haka bane Mom kawai inajin tsoron kada tarihi ya maimaita kansa

Mom banida uwa banida uba banida ɗan'uwa shakiƙi da zanyi magana dashi naji daɗi idan na
rasa gatan miji to rayuwata batada wani amfani domin zanyita da ƙunci ƙuncin da zaike azabtar
da ruhina Wlh Mom Inason mijina Amma inajin tsoron abinda ya faru ya kuma faruwa"
murmushi Mom tayi tace “Indai kinason mijinki to kuwa zaki koma ɗakinki Kharimatu itafa wacce
kike wannan abin akanta ma yanzu ba matarsa bace ita da kanta tace saiya saketa wai asiri
kikeyi mata akansa mukuma bincikenmu ya nuna mana itace tayi abinta ya koma mata itama
mahaifar tata data taɓu taketa zubar da jini ba ciwo ne na Allah da Annabi ba ke akaso ɗorawa
abinta ya dawo kanta amma ta kwarzabi kanta shine fa yayarta ta kirashi Suka ƙare masa
tanadi kinsanshi shikuma babu hƙr aikuwa a ranar ya raba kansa da ita ta rigashi dawowa ma
daga tafiyar da sukayi ashe ita tafi wata biyu a ƙasar nan shine da yaran acan koda suka dawo
ma bai sanar damu basa tare ba sai jiya daya kawomin yaran"




Cike da tsoro tace “Mom basa tare fah kikace" jinjina mata kai tayi alamun tabbatarwa tace
“harma ta kusan gama idda zanyima Alh mgn yayima Granny magana tayi hƙr ta baku dama ku
gina rayuwar ku kinji" Kharimatu dai shiru tayi tana tunano irin mulkin da Salma ta shimfiɗa a
gdannan wai yau batanan lallai rayuwa babu tabbas dole kabita a sannu. Wayarta ce taji tana ring ta zarota ganin sunansa yasata kifa wayar tare da sata a silent yayi
kira yafi nawa taƙi ɗagawa shigowa yayi parlourn ya cika da mamaki ganinta zaune arziƙin ɗaga
wayar tasa ne babu ya jinjina kai kawai ya fice, bata wani damu ba taci gaba da zamanta saida
taji tashin motarsa sannan ta miƙe ta nufi sashin Granny bata gama zama ba Granny tace
“Yanzu mijinki ya fita nikam ya sanyaya min jiki harma nayi karambanin cewa dashi yaje nanda
sati biyu zaki koma gdanki amma da sharaɗin koda zai dawo da matarsa bazai haɗaku gda
guda ba sannan zai barki kiyi karatunki kuma duk ya amince harma yace cikin satinnan zai siya
miki mota".......




*Oum Hairan*
[11/17, 9:16 AM] Oum Hairan&Affan: *MYJ47-48 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta
min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300
ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta
0931307566



Shiru tayi tana tariyo irin abubuwan da suka faru a baya zuciyarta na ayyana mata idan ta koma
fah waɗanda suka fisu zasu iya faruwa ita kanta ta shaida tanason Aliyu saidai tana tsoron
rayuwa da asiri komai addu'arka wataran saiya taɓaka tunda ya taɓa ma'aikin Allah hawaye taji

ya zubo mata Hajiya Bushira ta sanya hannu ta share mata tace “Haba Kharimatu ai da canma
sakaci akayi yanzu kuwa tunda komai ya bayyana ai kije ki rayu gidan mijinki da zuciya ɗaya ki
ƙaddara fah komai ya wuce" jinjina kai Granny tayi tace to mema zai faru ai insha Allahu Salma
tabar Aliyu kenan har abada" Kasa furta komai tayi saidai kawai ajiyar zuciya da take




Shawarwari Hajiya Bushira ta jata ta rinƙa bata duk jikinta ya mutu da dare suka kwanta
washegari da wuri suka shirya tafiya Patiskum ɗin suna tsaka da shiri ya shigo suka gaisa da su
Granny Itako ko kallonsa batayi ba ta miƙe ta shige ɗaki ya jinjina kai ya juya ya fita batare da
yace komai ba Granny ce ta shiga ɗakin ta sameta tace “Mijinki yace “Tare zakuje kukai Hajiya
Bushira ku dawo da sauri ta ɗago idanunta tace “Mu dawo kuma Granny?" Jinjina kai tayi tace
“Eh ki biyosa ku dawo" shiru tayi amma hukuncin yayi mata tsauri sosai batason takura a
rayuwarta.
Fita akayi da kayan akasa a Motar suka fita suka shiga yaja suka tafi yanata jan Jawad da wasa
itadai ta gimtse ko uhm bata cewa sai bin hanya kawai da takeyi da kallo lkc zuwa lkc tana
share hawaye tunda suka taho ya lura da sharar hawayen da takeyi baidai ce mata komai ba
zaman kurame akayi har sukaje Patiskum idan anyi mgn a motar to shida Hajiya Bushira ne ko
kuma yana yima Jawad wasa suna zuwa ta fita a motar ta shiga gda ta shige ɗakinta sai yanzu
ta samu damar yin kuka isasshe ganin rayuwarta takeyi matsayin ƙararrriya wahalar da tasha ta
kasa goge mata Allah ya sani badon girma da mutumcin Iyayen Aliyu a gurinta ba da ko zata
mutu saboda sonshi bazata sake yarda ta zauna zaman aure dashi ba saidai kash sunfi ƙarfin
komai a gurinta dole haka zata zauna dashi tayi hƙr da ƙaddararta




Basu wani jima ba abinci kawai sukaci wajan la"asar yace su fito su tafi Hajiya Bushira dakanta
ta rinƙa shirya mata kayanta tare da bata wasu tarkacen mata masu yawa ta rubuta mata yanda
zatayi amfani da kowanne ya ɗaukesu suka tafi tunda suka taho lkc zuwa lkc yake kallonta Lkcn
da suka shigo Kano ana sallar Isha ya dubeta ya kawar dakai tare da juya kan motarsa zuwa
Nassarawa G.R.A ya nufi wani babban gurin saukar baƙi saida yayi parking ta fahimci inda ya
kawosu gabanta ya faɗi ta ɗago da sauri tace “Ya haka?" Murmushi kawai yayi mata ya fita tana
ƙoƙarin fita ya kulle motar ta zauna ita ɗaya don ya ɗauke ɗansa basu jima ba suka fito ya buɗe
mata motar ta fito fuskarsa babu wasa yace mata "muje" babu musu tabisa suka shiga ya buɗe
dakin daya kama musu ta maƙale a ƙofa ya shiga ya kwantar da Jawad dake bacci ya tako ya
iso gabanta ya riƙo hannunta ya janyota ciki ya kulle ƙofar matsawa tayi daga kusa dashi ya
shafa gemunsa yace “Ina mamakin yanda kike son azabtar dani da wata sabuwar ɗabi'a
Kharimatu kiyi hƙr badon niba domin Allah babu abu ɗaya da nayi miki don raina yanaso
Kharimatu anayin tafi haka ma kuma a dawo a zauna so don Allah ki manta da komai muyi
rayuwa me inganci"

Ɗagowa tayi ta zubansa idanu can ta kautar dakai tace “Naji ka bani dama na tafi gda banason
hotel ɗin nan daka kawoni idan ka matsa zan ƙara yarda a raina har yanzu banida yanci banida
galihun da za'a saurari cewa ta sannan....." Rufe mata baki yayi yace “Ba haka bane Kharimatu
taimakona zakiyi don Allah kada ki gaza nasan keɗin me tausayi ce" tubure masa tayi ta zauna
ta sashi a gaba ta rinƙa kuka iyakar kalamansa saida suka ƙare gashi bazai iya jure kukanta ba
hakan yashi miƙewa ya ɗauki Jawad yace “Shikenan muje Kharimatu" miƙewa tayi da sauri ya
buɗe mata ɗakin ta fice suka shiga wamota yanata huci zuciyarsa nayi masa zafi ya rasa
yaushe Kharimatu ta koyo kafiya da taurin kai.




Yanayin parking bai gama tsayawa ba ta fice

10 / 11