Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
wai dan Allah miyasa baza ka ri'ka hutawa ba"?.
Isham ya fad'a cikin muryar barci yana kallon sa batare da Asad ya juyo ba yace "kayi barcinka Isham yau ranar dabam take nafi ko yaushe d'aukar zafi kawai ka kyale".
"Ok shikenan Asad Allah ya taimaka" ya fad'a yana komawa ya kwanta.
Asad bai sake magana ba ya juya kan abinda yake shiru Isham yai yana kallonsa gaskiya Asad ya damu yana matukar bu'katar hutu saidai yasan bazai ta'ba hutawa ba harsai yaga ya samu wannan yarinya.................................
Katse masa tunani Asad yai ta hanyar mi'kewa dayai yana kallon laptop da tsananin mamaki yace.
"WHAT"?.
Zabura Isham yai yana tashi zaune shima dai yaga abinda ya tada hankalin Asad d'in da sauri ya wullar da bargon ya diro kasan carpet tare da 'kure laptop d'in da ido yace.
"Asad me nake gani wannan abinda kake nema ne ai ya fara samuwa gashi bayanai ya fita yar Nigeria ce ita kuma cikin masarautar ku fa innalillahi amma wacece Asad wa kake tunanin zata kasance nasan dai ba'a cikin bayi bane a ina take ko a cikin sisters d'inka ne"?.
Shiru Asad yai ya zubawa laptop d'in ido cike da tsananin mamaki d'agowa Isham yai ganin abinda yake kallo yasa yace.
"Asad say something mana kayi magana did something scare you"?.
Kai Asad ya girgiza masa baice komai ba har lokacin sai zama dayai yana yin copy d'in bayanan nan saida ya gama sannan ya d'ago yana kallon Isham yace.
"Isham zanje gida yanzu".馃槼
Zaro ido Isham yai yana kallon sa kafin ya kalli agogo yana cewa "Asad gida kuma a yanzu haba dai qarfe biyu fa da mintuna ka bari gari ya waye"?.
Kai Asad ya girgiza "no Isham I cannot a yau zan tafi bazan jira gari ya waye min anan ba tashi ka kaini airport".
Mi'kewa Isham yai yana cewa "ok Buddy muje" rufe laptop d'in Asad yai yana d'aukar wayarsa suka fita a wannan tsohon daren Isham yad'au mota yakai Asad airport sannan ya dawo gida shima bai iya komawa barci saboda taya Asad d'in murna ganin abin nemansa ya fara samuwa.
*** 馃憫PALACE馃憫 ***
__________________________
________Mami tana zaune a parlonta ita kad'ai da safe tana waya da Aunty Fadilaty da murmushi a fuskarta ganin an bud'o kofa yasa ta mayar da hankalinta kan kofar Asad ne yashigo yana tsayawa bai karaso ba ya qame daga nesa fuskarsa ba walwala ya sanya hannuwansa a cikin aljahun wandonshi ya tsume ya kame guri d'aya sauke waya Mami tai tana kallon sa cike da tsananin mamakin yaushe ya dawo ko jiya da dare ya shigo tofa ai ta d'auka sai yayi shekaru baizo gida ba saboda abinda Ajeeb yayi masa d'an murmushi Mami tai tana cewa.
"Asad lafiya dai miya faru ya ka tsaya anan ko wani abu ne? ka shigo man yaushe ka dawo"?.
Qarasowa yai yana mata sallama ya zauna tare da gaida ita amsawa tai tana sake qare masa kallo lallai ba qalau ba yanayinsa ya nuna kamar akwai damuwa,.
Da kulawa irin ta uwa da d'anta ta sake ri'ko hannun sa tana cewa "Asad lafiya ina nufin kana cikin walwala naga kamar naga akwai abinda ke damunka haka ne"?.
'Dan rufe ido yai yana sauke wani irin numfashi a ransa yana tunanin taya zai fara fad'awa Mami abinda ya kawo shi zatai masa kallon kamar duk da bai nuna kulawarsa ba saida ya tashi buqatarsa ta kawoshi..................
"Asad wai lafiyar ka qalau kuwa"?.
Kai ya d'aga a hankali muryarshi ba kamar kullum ba da alamar akwai matsala yace "Mami ina son kimin magana wannan yarinyar"馃槼.
Tsananin mamaki ne qarara ya bayyana a fuskar Mami har tana sake qureshi da kallo tace "Asad kaine ko kuwa Ajeeb ne"?馃.
Ta karasa maganar tana sake bud'e idonta akansa tunda bayan kama da suke da juna muryarsu ma d'aya ne maybe ko Ajeeb ne ya tsume irin yanayin Asad d'in yazo tsokanar ta dan yaga mai zatai tana son tabbatarwa Asad ne ba Ajeeb ba amma ta kasa yarda cewa shine yake magana akan Amatun domin tasan babu abinda zai kawo Asad gida yanzu daga tafiya wata hud'u kawai saidai in larura amma sai tace bari ta gwada wani abu dan ta gane waye ne a ciki tace.
"Asad lafiya kake nemanta"?.
Murya can qasa yace "eh kimin magana da ita ki tambaye ta tana amfani da laptop ne"?.
Kai Mami ta girgiza tana cewa "Asad meyasa ka fiya jin kaine? kai mezai hana kaje ka sameta ka tambaye ta sai nice zanyi maka jagora"?.
"Eh Mami akwai dalilin da yasa na biyo ta wajenki ki fahimta".
"Ok shikenan na fahimta saboda kana jin kunya kar ace ka'ki kar'bar auren yanzu kuma ka dawo ta ra'bi zaka amsa"馃き"?.
Kaiya girgiza da sauri har yana zabura yace "noo Mami ba haka bane ba nazo dan wata manufa bane har gobe Ina nan akan bakana yarinyar nan ba matata bace kawai akwai wasu abubuwa da nake son na tambaye ta shiyasa nake so nabi ta gurinki ki had'a ni da ita bana son ayi min wani kallo dabam".
Kai Mami ta jinjina tana "Me zaka tambaye ta"?.
"Magana ce tsakanin mu dan Allah Mami kimin wannan duk burina yana a haka a abun dake wajenta idan itance amma saida taimakon ki".
"Asad maganar gaskiya indai ba kar'barta kayi matsayin matarka ba had'uwar ku bata wani da amfani baka da abinda zakace mata dan haka bazaka ta'ba ganin taba Asad na gaji da wannan karka mayar damu qananan mutane kawai ka rubuta mata sallamarta馃槪".
Shiru Asad yai nad'an wani lokaci har Mami ta cire ran zai sake mata magana sai kuma taga kalleta yana cewa "Mami ni bani da ala'ka da wannan aikin Ajeeb ne domin ba matata bace mine tsakanin mu dazan bata sallama indai zaman jirana take zata iya tafiya gidansu yanzu bazan ta'ba waiwaye ko kallonta da sunan wife d'ina ba please Mami try to understand dan Allah馃檹.
Sosai Mami ke kalloshi jikinta yayi mugun sanyi ta rasa me yasa Asad yake a murd'e indai ba shine yay ra'ayin abu ba tofa akwai gagarumar matsala......,...
"Mami baki ce komai ba"?.
"Humm to Asad mizance ka karya min duk wani qarfin gwiwar da nake dashi akan kamar nan gaba zaka yarda ka sauko ka kar'bi yarinyar nan amma sai naga sa'banin yadda nake zato da fatan kasancewa? Shikenan Asad ka kyauta saidai ka sani gaskiyar lamari bazan iya maka abinda kake soba kayi da kanka"馃檮 mi'kewa tai zata bar gurin Asad da yaji zuciyarsa ta tsinke yace.
"Mami ina zakije please ki saurare ni ina da babbar hujja akan 'kin kar'bar auren danai babu wanda zai amincewa uziri na idan baki saurare niba keda Abba"?.
"A'a Asad baka da wata hujja akan wannan bazan maka uziri ba kawai ka rufe min baki ka mayar da hankali ka tsaya kayi tunani idan kayi haka ka juya dason bijirewa abun ba d'an uwanka Ajeeb dayaga ya isa dakai ko mai nasara ba hatta mahaifan yarinyar nan baza suji dad'i ba domin ba'a auri 'yarsu dan a wulakanta musu ita ba kuma kai naga alamar yunkurin ka kenan tun farko rashin sani yaja komai da nasan dakai ne za'ai auren dama Ajeeb ba yana komai dan kansa bane toda zan dakatar dashi karya soma kawai ya aureta zaifi wa kowa kwanciyar hankali to mai faruwa ta riga ta faru bansan akai Ajeeb kewa ba wallahi da ba'a kawo wannan matakin da muke kai yanzu ba kodan yanzun ma bata 'baci ba Asad ka saketa a mayar da auren nan kan Ajeeb馃槻 zanfi samun nutsuwa a kanka domin dama yarinya dashi tai soyayya ba dakai ba dashi ta sake dashi ta saba ta sanshi da fara'a sannan ya nuna mata kulawa wacce ta dace amma zan sake baka lokaci kaje Kayi nazari馃 domin kana buqatar hutu sannan ka daina yin allurar nan akai akai karka ja 'kwa'kwalwarka ta samu matsala ka karasa burkicewa a haka ma ya lafiyar kura馃悊 balle tayi hauka Asad kaje ka sake sabon nazari a nutse duk abinda zuciyarka ta yanke maka zuwa gobe da safe kazo ka sanar dani ina jira" tana fad'in haka ta bud'e kofar bedroom ta shige.
Idon Asad na kallon qasan kyakkyawan blue & white carpet d'in dake zagaye da parlon yayi shiru shiba tunani yake ba kuma ba maganar zuci yake ba ya dad'e a gurin a zaune ko motsi baiyi ba daga baya ya mi'ke yana takawa ya nufi wata kofa dake palon ya shiga shiru babu motsin komai tamkar dai ba halitta a part d'in tsaye yayi yana tunani a ransa "to me zaice mata ta Ina zai fara tambayarta meyasa ma ya shigo nan d'in? Yana cikin zancen zuci yaji an bud'o kofa d'agowa yai yana kallon kofar akan fuskarta ya fara sauke idanuwansa ta fito tana waya ta d'au wankan riga da skirt masu kyau ta kashe d'auri batama lura dashi a palon ba saida ta zauna tana jawo qaramin table na glass dake gabanta ta bud'e laptop馃捇馃攲 tana kunnata kawai ta fara aiki bayan ta aje wayar..
Zuba mata ido yai sosai yana nazari wato Ajeeb wannan ce yarinyar daya za'ba masa da ita aka d'aura musu aure? hummm tabd'ijan lallai ma zasu warware kayansu Dan baiga ta yadda zai kar'bi wannan auren ba domin baiyi niyya yanzu ba bazasu 'bata masa tsari na cewa dayai babu batun aure a gunsa kwana kusa basai yayi retire ya daina aiki kwatsam rana d'aya Ajeeb ya masa haka? Dun'kule hannu yai yana naushin iska kafin ya furzar da wani zazzafan numfashi daga bakinsa ransa a mugun 'bace lokaci guda yaji yanayin sa na sauyawa gashin jikinsa na mimmi'kewa allurar sa na neman tashi 馃檴 jiki na tsumewa idonsa yayi ja sake qare mata kallo yai a karo na ba adadi bad temper (zafin zuciya) nashi na sake hawa da qarfi ya soma takawa inda take zaune itakam har lokacin bata lura dashi ba馃槻.
TOFA FANS ME KUKE TUNANIN ZAI FARU ANAN馃? YAU GA ASAD&AMATU A RANAR HAD'UWAR SU TA FARKO BAYAN LOKACI ME TSAWO..
AFUWAN馃檱馃徏鈥嶁檧锔 KU GAFARCE NI ZANYI WATA MAGANA ANAN DUK DA TUN FARKO BAN FAD'A BA DAMA NACE ZANTAYIN SA FREE SAI YAJE KARSHE BADAN WULAKANCI BA SAI DAN NA FARANTA MUKU.
DAGA NAN ZAN TSAYA DA YIN POSTING KUYI AFUWA.
LITTAFIN ME KAMAR S脛RK脤 COMPLETE DOCUMENT D'INSA NA KUD'I NE KUYI HAKURI ABISA RASHIN SANAR MUKU DA BANYI BA TUN FARKO BA NAYI HAKA NE DAN BATA RAN D'AYA DAGA CIKIN MASOYA BA A'A KUNSAN D'AN ADAM AJIZI NE.
WANDA YA SHIRYA BIYA YAYI MIN MAGANA 馃憞
234 8160983083.
A TURA MASA IDAN MUTUM YASAN BAI BIYA BA DAN ALLAH KADA YA KARASA KARANTA MIN BOOK DOMIN HAKKI NANE MALLAKA TANE BASIRA TACE GUMI NANE KUMA NACE A BIYA TYPING AKWAI WAHALA SHIYASA NACE A BADA IHSANI KUNGA NIMA NASAI
MAGANIN GAJIYA馃槂
HARMA NACI TSIRE馃構
SANNAN NA SAKE SABUWAR IPHONE 13 TAYI MUKU SABON BOOK D'INA 馃挀TAJUDDEEN ARYAM馃挀 INSHA ALLAHU KWANAN NAN ZA'A FARA SHI.
WANDA YA SHIRYA KAR'BA NAIRA DUBU D'AYA NE.
#1k
Acc no: 2410673902
Acc name: Yusrah Musa
Zenith bank馃彟.
Shedar biya tanan WhatsApp no nawa idan ka saka sai kayi secreenshot ka turo min domin wallahi wani tun ina book two ya biya nasa one ke d'in kuma yayi secreenshot d'in ya turo min.
Please Ina kara maimaitawa dan girman Allah duk wanka bai biya ba kada ya karasa karantawa domin hakki nane gumina ne d'an uwa ka tuna hakkin wani ka tuna ranar tsaiwa gaban ubangiji domin hakkin wani a gurin Allah SWT abune mai girma.馃憘馃憘.
馃摫234 816 098 3083
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Mrs 脛l'盲m毛毛帽 脛hm盲d 莽毛.
NAGODE SOSAI MASOYA
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels