Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
ba yace "ok muje part d'in Mamin" kai Aunty Fadilaty ta d'aga tana mi'kewa suka fita tare suna tafe suna hira dan sosai Asad ke son matar jinin su ya matukar had'uwa 'kanwar Mami ce ita kuma a Riyadh take aure yaranta uku mace daya ZARAH sai maza biyu.
Yasha mamaki ganinsu da yawa harda wadanda ya dad'e basu had'u ba ga larabawan 'yan mata suna rawa a gefe sun kuna wa'kar "ana ahibbu ya habibi" cikin nishad'i ganinsa yasa suka tsaya d'aya bayan d'aya ya kallesu su hud'u ne Hajir Yusriyyah Muyassara da Fujirat 'ya'yan Aunty Futuha da Aunty Aleemah sai kuma Aunty Naizarah lallai bai kyauta ba ya dad'e basu had'u ba yaushe har yaran nan suka girma haka kallon su yai suna gaidashi yace.
"Wato ku yaran nan duk abinda yazo ranku shi kuke yi ko meye abin burgewa a rawa musamman ma ke Hajir kin fi kowa kodai mawa'ki zaki aura"?.
Rufe fuska Hajir tai tana cewa "Allah a'a ni ba mawa'ki bane saurayi na ustaz ne馃ぃ kuma ka tambayi Aunty Fadilah ai ta sanshi kwanan baya munje gidanta dashi".
Kallon Fadilah Asad yai da alamar tambaya yace "wai haka ne Aunty Fadilaty"?.
Kai aunty Fadilah ta d'aga tana dariya tace "ba haka bane bakaga a yadda yaje gaida niba kamar ya taso daga filin kwallo".
Zaro ido Hajir tai "kai Aunty Fadilah Allah yanzu zakisa yace na rabu dashi dama wancan zuwan dayai na ma saida yace na rabu da Zayad kuma wallahi Adeel mutumin karki ne".
"Ri'ke baki Aunty Fadilah tai cikin 'yar tsokana tace "tofa Hajir babban lamari wato Adeel harya sace zuciyarki kamar haka a gabanmu kike yabonsa ah lallai kam shiyasa duk abinda yarinyar nan Zarah tai nake cewa zuwa min ziyarar da kike ne a gurin ki ta koya idan ta kama rawa da malgwad'a kamar tarwad'a abin har mamaki yake bani"
Dariya sauran suke yayin da Hajir ta fara bubbuga kafa kamar zatai kuka dan tasan maybe Asad ya sake mata iyaka da wannan Adeel din kallonta yai kamar bazai magana ba sai kuma yace "Hajir idan kin tabbata da gaske kike abinda kika fad'a zan zo Bahrain zanyi bincike a kansa".
Da sauri Hajir tace "eh Allah na yarda kuma basai ka bari na sani ba ka min bazata ta gidan Aunty Fadilah ko gidan Ummi Hadiyyah"
"Ai ba shawararki nake nema ba can you be quiet馃か ita Muyassara bata dashi"? Ya tambaya yana kallon yadda ta zaro ido jin abin yazo kanta Caraf Hajir tace "tana dashi sunan sa Nurul-qalbih" juyawa Asad yai yana kallonta kamar mai nazari sai kuma yace "da gaske sunansa kenan ko kuma kece kikasa masa hasken zuciya"?.
Hajir kamar ita ake tambaya da sauri ta sake cewa "itace tasa masa hasken zuciyarta" rufe baki baki Muyassara tai jin 'karyar da Hajir d'in ta shirga mata tace "Allah ba nice nasa masa ba sunansa kenan" tafi Hajir tai "aiko ba sunansa kenan badan kar yace kema zaiyi bincike a kansa ne kika gigice harda komawa kalar tausayi kamar zaki kuka" harararta muyassara tai "oh to ko kukan zanyi" rausaya kai Hajir tai "oho waya sani"
"Kai kumin shiru haka bana son jin komai zan zo Bahrain din ai duk ba tsira zakuyi ba".
Shiru sukai suna kallon sa daidai ya kar'bi jaririn dake hannun Aunty Naizarah yace "wannan yaron kine dama kinyi aure"?
Kaita d'aga "Eh kusan shekara biyu ma ai kasan rabuwarmu dakai tun a rasuwar Abu Samir bamu sake had'uwa ba" kai ya jinjina daidai Ajeeb ya shigo yana waya gud'ar da su Aunty Fadilah da Aunty Aleemah suka sakar masa ne yasa Ajeeb sauke wayar da sauri yana toshe kunnensa yace.
"Kai auntis wannan ai sai kusa mutum jinsa ya d'auke na tsawon da'ki'ku irin wannan 'kara kamar ina ramin gyare duk gud'ar ta miye"?.
"Oh really zakace bakasan ta meye ba"?.
Zama Ajeeb yai kusa da Asad yana cewa "yes but I've comfirmed it bansan komai ba 馃槤 na miye"?.
Dariya Aleemah tai tana cewa "eh gud'ar taya ka murna ce kasan dole muyi maka gud'a gobe iwar haka ka zama ango Ajeeb kabar sahun tuzurai irin su o'o馃ぉ".
Murmushi Ajeeb yai yana kallon Asad daya hade gira jin abinda tace Ajeeb da 'yar fara'a a fuskarsa yace "uhmmm Aunty Aleemah kenan aurena mai ganinsa saiya shirya surprise ne".
"To surprise ya wuce gobe kasha manyan kaya kuje mighty Alhussain ya kar'bo maka alkawarin ri'ke 'yar mutane cikin kima ai tayi dace baka da fad'a ba kamar Asad ba shikam matarsa Allah yasa mai ha'kuri ce idan kuma itama mai zafi ce irinsa hummm zakusha rabiyar fad'a" kai Ajeeb ya jinjina yana cewa "tabbas kinyi gaskiya Asad kamar kububuwa haka yake a tafashe zafi wane yaji in kinji ana soja marmari daga nesa shifa Asad tuwon 'kaya ne miyar allura baisan wargi ba" dariya tai "hhhh lallai kam naga alama amma duk da haka ai ya.............................
Katse musu magana Aunty Fadilah tai daidai ta fito daga bedroom din Mami ta 'karaso gurin da murmushi fal fuskarta tana cewa "Asad muga hannunka" 'Dagowa yai daga wasan da yakewa yaron hannunsa yace "miye a hannun nawa"? "Babu kaidai mu gani man" bai bata ba kawai ya tsaya ya zuba mata ido tamke gira tai tana cewa "Asad wannan kallon naka ai sai kasa mutum ya 'kwaru please bring me your hand鉁" mi'ko mata yai yaga dai me zatai masa babu zato yaji ta shafa masa abu a hannu sai tashin 'kamshi yake bud'e idonsa yai akan abun yana cewa.
"Subahanallahi Aunty Fadilaty meye wannan kika shafa min" ya karasa maganar yana jin zuciyarsa na tashi kamar zaiyi amai dariya tai tana sakin gud'a tace "wannan lalle ne na shafa maka".
Had'e rai yayi "lalle? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un meye had'i na dashi kuma amfanin me yake"? "Amfanin dole a shafa maka tunda zaka zama ango".
Kai ango kuma sake had'e fuska yai "wanne irin ango? Ajeeb dai zakiwa haka ba niba kawai kin 'bata min jiki".
'Dan zaro ido Aunty Fadilah tai "oh sorry haka ne mantawa nai but tun d'azu Ajeeb aka shafa masa nasa, kodan ai ba matsala tunda kai Hussainin ango ne ko" shiru yai yana kallon Ajeeb wanda yake dariya wata uwar harara ya sakar masa wato silarsa yasa an bata masa jiki sannan tsabar iskaci yake masa dariya mi'kewa yai yana kallon Fadilah yace.
"Good night Aunty Fadilaty".
"Mu kwana lafiya Asad" ta fad'a da fara'a ajewa Naizarah jaririnta yai yana fita shima Ajeeb bai jima ba ya musu sallama yabi bayansa a bedroom ya samu Asad yana tsaye jikin window daga shi sai 3Quarter da singlet fara iskar waje mai sanyi na shigowa ta windon tana kad'a gashin kansa dake she'ki jin motsi a bayansa yasa ya juyo suna had'a ido da Ajeeb ya sake d'aure fuska yana cewa.
"Wato dan wulakanci Ajeeb gashi nan kasa a dalilinka jikina sai warin lalle yake".
Shima Ajeeb din hade rai yai yana d'auke kai ya karasa bakin gado ya zauna ya kalli yadda lallen ya 'bata masa farar rigar jikinsa yace "da nai maka me? Dama nace Aunty Fadilah ta shafa maka lalle ne uban yan sharri".
"Eh ai silar Kane kaita nufo dashi kasa ta ya'ba min ni meye hadina dashi nine ango ko kai fad'a min"?.
Kallon sa sosai Ajeeb yai sai kuma yasa dariya yana cewa "dama yau ba muyi ba tun safe na lura dakai kana takala ta fad'a ina share ka domin ni ango ne bazan biyewa tuzuru irinka ba shiyasa yanzu daga laifin daba nawa ba kake neman d'ora min dan ni akazo shafawa ya sameka a tunani na ai duk daya ne Asad babu bambanci tsakani na dakai kaine muke uwa daya uban daya dukkan yarda ta Asad tana gareka na amince dakai fiye da yadda kake tunani banida wani wanda ya kaika balle har na kalleshi naji dad'i a raina inai maka wani irin so wanda baki bazai iya musaltashi ba kuma zanci gaba da sonka matukar raina indai ina numfashi,.
'Dan dakatawa yai tare dayin shiru yana kallon Asad sai kuma ya ri'ko hannun sa batare da ya sake cewa komai ba suka zauna a bakin gado hannunsa na cikin nasa ya ri'ke sosai yaci gaba.
"Asad dan Allah komai zai faru gobe karka tada hankalinka ka d'auka cewa kaddara ce kuma kada kayi ba'kin ciki nasara tana tare dakai duk da zakaga abubuwa sa'banin fahimtar ka a matsayina na d'an uwanka ina gargad'in ka cewa kabi gaskiya Asad ka tsaya akan daidai dan Allah Asad gobe karka tada husuma a gidan nan ina fata zakayi min wannan alfarmar"? Ajeeb ya karasa maganar da serious face yana kallon Asad wanda shima shi yake kallo duk jikinsa ya saki da maganganun Ajeeb d'in saiya samu kansa cikin fargaba da shiga tunani iri iri meya faru meyasa Ajeeb yace masa haka a irin wannan lokacin shidai ya a iya sanin sa tunda suke dashi bai ta'ba fad'a masa magana irin haka ba sai yau meyasa? Katse masa tunani Ajeeb yai.
"Asad baka ce komai ba please 馃棧锔弒ay something 锔".
Kasa cewa komai Asad yai sai kallon Ajeeb da yake yana sake jujjuya maganar daya gama fad'a yanzu ya kasa gane me Ajeeb ke nufi ina ya dosa to meya kawo wadannan maganganun? Girgiza shi Ajeeb yai yana cewa "Asad are u ok? Kana lafiya kuwa"?.
Kai ya d'aga masa da'kyar yace "eh" kallon sa sosai Ajeeb yake yace "to amma ina ta magana kayi shiru kamar kurma meyasa naga ka canza yanayi daga yaune fa na final zaman karshe a bedroom tare ni dakai da sunan kwana saidai dan nishad'i shikenan gobe iwar haka bazaka ganni ba koda kud'i inacan kana nan".
Tabdijan wai tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Asad ji yayi hankalin sa ya 'kara mugun tashi fiye da da hajijiya na d'ibansa kansa har ciwo yake ya d'au zafi sosai yake kallon Ajeeb da shikam harkar gabansa kawai yake kamar dai bai fad'i komai ba ganin zai sake magana yasa Asad cewa.
"Please Ajeeb maganar ta isa haka dan Allah na fahimce ka kayi shiru basai ka sake cewa komai ba" murmushi Ajeeb yai "shikenan Asad ni kwanciya ma zanyi na shiga kwana duk jikina ciwo yake good night" yana fadin haka ya haye gado tare da jan bargo Asad na zaune yai shiru cikin dagulewar lissafi ya kasa gane inda maganganun Ajeeb suka dosa balle ya fahimci abinda yake nufi saidai ya jira zuwa asuba idan sun dawo daga masallaci ya sake tambayarsa maybe lokacin ya sake dawowa cikin nutsuwar shi dan gani yake kamar baya cikin hayyacinsa yake masa magana d'azu, jin saukar numfashinsa yasa shi kallonsa har bacci ya d'auke shi fuskarsa ya zubawa ido ya kasa daukewa haka kawai ya gaza bambance wanne irin yanayi ya shiga meke damunsa haka ya 'bata lokaci a zaune yana tunane tunane iri iri har kusan karfe uku na dare ya kasa runtsawa karshe sai mi'kewa yai yayo alwala yazo ya fara nafilfilu bayan ya idarma zama yai yaci gaba dayi a gurin har akai kiran farko akai assalatu sannan ya tashi Ajeeb yayo alwala suka wuce masallaci bayan an idar tare suka dawo idanuwan Asad sunyi ja sakamakon rashin barcin da baiyi ba saboda baya son yawan tambaya yasa suna dawowa ya fad'a gado wanda Ajeeb ya kwanta a kusa dashi yana ja musu bedsheet.
Har gari ya waye sosai rana ta fito Ajeeb ya tashi haryai wanka amma Asad baya ko motsi bai tashe shiba bayan ya shirya ya fita zuwa 'bangaren mai martaba da gurin Mami dan ya gaishe dasu.
Kusan sha biyu na rana shiru Asad bai farka ba dawowar Ajeeb yazo yana d'an babbuga filon dayai matashin kai dashi yana kiran sunansa da'kyar Asad ya bud'e idonsa yayi ja ya kalli Ajeeb daya dafa kafarsa daya akan bed din daya tana kasan carpet da murya barci yace "lafiya meya faru"? Zama Ajeeb yai yana aje masa jakan dake hannunsa yace "lafiya kawai naga karfe sha biyu tayi kuma baka tashi ba kamar ka manta yau daurin aurena dana Ameer shiyasa na tashe ka" Asad baice komai ba yake shirin komawa ya kwanta cikin magiya Ajeeb yace.
"Please karka koma dan Allah"馃憦.
Dafe kai Asad yai jin har lokacin bai daina masa ciwo ba kuma rashin barcin da bai samu yayi da dare bane yasa gashi Ajeeb ya hana shi komawa yasan duk abinda zai fad'a masa yanzu bazai fahimce ba.
"Asad ka tashi man dan Allah yaufa ranar d'an uwanka Ajeeb ce ya kamata ka tashi ka taya ni d'iban nishad'i yau zanyi mata" Ajeeb ya karasa maganar yana murmushi kallon sa Asad yai kamar zaice wani abu ganin ya bud'a baki Ajeeb ya girgiza kai yana cewa "ga kaya nan wanda zaka sa idan zamuje wajen daurin auren ankon mune duka su Ameer da Annur duk iri d'aya ne baza'a bambance angon ba a cikin mu musamman nida kai tunda fuskan mu iri d'aya ka shirya a hankali akwai sauran lokaci sai 'karfe uku da rabi zamu tafi" kai Asad ya d'aga baiyi magana ba yayin da Ajeeb ya juya yana fita komawa Asad yai yana sake sabuwar kwanciya tare da sake jan bargo ya rufe idonsa dan gaskiya indai bai rama barcin nan ba tofa bazai iya samun nutsuwa ba a yau balle har yaje wani d'aurin aure.
'Karfe biyu daidai Ajeeb yazo ya matsa masa lamba dole ba yadda ya iya haka ya ha'kura ya tashi gashi ko breakfast bai ba amma wannan ba shine a gabansaba ba shine matsalar saba wanka kawai yayi ya shirya cikin manyan kayan hausawa shakwara da jamfa ga hula wai wai wai tabdijan sai kun ganshi FANS馃ぁ subahanallahi akwai dirarriyar halitta mai kyau anan abun baya fad'uwa fitowa yai sai nad'e babbar rigar yake ya wurga tanan ya jawota nan ya rasa yadda zaiyi yana shigowa falon Mami Aunty Fadilah ta kama dariya tana kallon sa cikin tsokana tace.
"Asad ya haka? Innalillahi ji yadda kake tu'kuikuye kayan zasuyi squeezing tun daga nan dan Allah kalli yadda ka wani soke hula a gaban goshi baka saba sawa bane ko kuma duk cikin style d'in ne馃槀"?.
Had'e rai yai yana d'an karkata kallonsa gurin Mami dake kallon sa itama tana murmushi tace "Asad kayi kyau sosai haka Fadilatinka ke nufi taga maradar kyau ta yaba" rufe baki Fadilah tai tana dariya tace "waye yaga madarar kyan? Uhm uhm nikam ban yaba ba jira nake ango Ajeeb ya shigo na saki gud'ar ban girma nai masa kirari yau ai bata Asad ake ba ana batun masu aure wayake sako tuzurai 馃槀" dariya Mami tai tana cewa "ayya saurin me kike lokaci ne shima wata rana zaiyi".
Shigowa Ajeeb yai shima ya d'au wankan ala tsine uwar me 'karya馃檳 sai tashin 'kamshi yake fuskarsa da wadataccen murmushi ai kamar yadda Fadilah ta fad'a zazzafar gud'a ta sakar masa a satin kunne tana masa wata daddad'ar wa'kar ango cikin harshen larabci sauran suna tafi da salon wa'kar suna amsa mata Mami tace.
"Fadilah irin wannan bege haka"? Dariya aunty Fadilah tai tana nuna Ajeeb tace "ai dole mu kod'a ango mu yabeshi dan tuzurai suji haushi馃ぃ ko suma sa dage suyi" had'e rai Asad yai dan yasan dashi take kamar bazai tanka ba sai kuma yace "Aunty Fadilaty kin ganni nan ni Asad babu aure yanzu a tsarina bana tunani aikina kad'ai na sani kuma koda ma ace zanyi auren gaskiya ba kwana kusa ba me nisan kwana ne zai gani don sai nayi ritaya馃檴" zaro ido Fadilaty tai "sai kayi ritaya kuma Asad subahanallahi gaskiya bamu amince ba sannan ai ka zama tsoro wazai aure ka"?.
"Mai sona"馃檯 duk tsufa na ko na zama kwallafiya ne".
"Tabd'i wacce budurwar ce zata yarda ta aureka ka zama kwallafiya ka fara gigi".
"No aini ba irin wannan tsufan zanyi ba".
"Oh da gaske taya ka sani"? "Na sani mana alamar 'karfi"? Ya fad'a yana kallon ta rufe baki Fadilah tai tana dariya tace "tana ga mai 'kiba ai shikenan Allah yaja kwanan mu zuwa lokacin bikin tsofaffi ko ba haka ba" shiru Asad yai Ajeeb da suke tattaunawa da Mami daidai sun gama ya juyo yana cewa "Asad muje ko lokaci yayi" yana rufe baki kiran mai martaba ya shigo wayarsa da sauri ya d'aga cikin ladabi yace "hello Abba kayi hakuri gamu nan" sauke wayar yai yana kallon Asad yace "mu tafi Mami auntis mun tafi ku mana addu'ar dawowa lafiya".
"Ok Ajeeb sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya sanya alkhairi" Amin yace suna fita daga part d'in Mami gabadaya gidan fal yake ya cika dam ta ko'ina da mutane manyan ba'ki masu mu'kami su hud'un duka mota daya suka shiga sakamakon Shaukiyyah da Ameer su na gida ne dukka sai aka bari a d'aura a guri d'aya idan anje na Ajeeb d'in.
Alhamdulillah Malam Habu ma yasha kwalliyar tsadaddiyar shaddarsa mai kyau sosai lokacin da suka je har an d'aura auren Aisha da Safwan sai su ake jira a d'aura na Amatun suna zuwa babu 6ata lokaci aka fara abubuwa da addu'o'i an d'aura auren Aliyu Alhassan Aliyudeen akan sadaki wanda ake neman albarkar aure uhmm Allah yayi Shaukiyyah Alhussain Aliyudeen yau buri ya cika itama an d'aura musu aure da Aliyu Alhassan Aliyudeen (Ameer) akan sadaki kai tsaya da wancan.
Bayan an kammala komai mai martaba suka gaisa da Malam Habu yayi masa godiya cikin mutuntawa sannan su Ajeeb suka shiga cikin gidansu Amatu gaisuwar iyaye kowa kallonsu yake su hud'u kaya iri d'aya biyu kama d'aya biyu ma kama d'aya 'ya'yan sarkin gari guda.
Sai bayan karfe biyar suka koma gida Asad yayi mugun gajiya ko part din Mami bai samu ya koma gurin su Aunty Fadilah ba suna parking ya wuce part d'insa bai tsaya huta ba ya shiga toilet yai wanka ya d'auro alwala domin lokaci kad'an ya rage a kira sallah saida ya shirya ya wuce masallaci da akai sallar magriba ma bai fita masallacin ba saida akai isha