Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
jada niba balle ita" cikin zuga Mudi yace "to ai mutumi na kaine kayi sake taya zaka bari yar wannan yarinyar ta ri'ka kallon cikin idonka tana zazzaga maka rashin mutunci baka falleta da mari ba wanda saita ga wuta ba wallahi kada ka hakura ka dau fansar wannan abun da tayi maka" "fad'a batawa Mudi ai dole na sanyata bakin ciki kamar yadda ta sanya ni dole na rama cin fuskar da tai min kuma ta hanyar da kowa bazai ji dad'i ba muje kawai Mudi yau saina kora sosai kaina yadau zafi" wucewa sukai Mudi na sake zugashi da bashi shawarar yadda zaiyi.
Zaman Lami haka babu islamiya yana damunta tana son shiga tana tsoron masifar Ramatu ta kasa fad'awa Baffah gashi tun ranar da aka kawo ro'kon arzikin ta Ramatu ta sake bud'e mata wutar talla kamar jaka wai saita tara kud'in da zata sai mata kayan d'aki Baffah yayi fad'an har ya gaji ya 'kyale.
Lami na zaune a kofar d'aki tayi tagumi Baffah daya shigo cikin rashin jin dad'in ganin ta a haka yace "Lami lafiya meya faru"? Hawaye ne ya zubo mata tana kallon shi tace "dan Allah Baffah na rokeka ka sani a makaranta ko ta islamiya ce nima nayi karatu" sauke ajiyar zuciya yai yana rike hannunta yace "karki damu kinji share hawayen ki insha Allahu gobe da kaina zan raka ki har islamiya gurin malam Haruna yasa sunan ki cikin d'alibai ki fara zuwa daga baya saina dinka miki inifon tunda kinga Alpha din yace a 'kara masa lokaci bai 'karasa gini ba saiki fara islamiyar kafin lokacin ina haka kike so"? Kaita d'aga tana murmushi cikin jin dad'i tace "shima yace min zanci gaba da karatu na bayan bikin nagode Baffah Allah ya saka da alkairi" "Amin karki damu" Baffah na barin gurin Lami da murnarta ta tashi itama tana shiga daki tace.
"Babah gobe Baffah yace zai kaini islamiya" Ramatu dake daurin gyada soyayyiya sai tumurmusa take jin abinda Lami tace yasa zatai magana ta 'kwaru tari ta ri'ka jerawa har shid'ewa da'kyar tace "kawo min ruwa" fita Lami tai ta debo mata bayan tasha tana numfashi tace "Kika ce gobe Baffah zai kaiki islamiya? Heeeeh lallai kam yau ake yinta to bari kiji wallahi baki isa ki makaranta ba abinda na yanke kenan wacce kika je ki kai a wudil din ma ba'a son raina bane talle zaki min kowa na neman kud'i ni kuma saboda da mutuwar zuciya gaki nan rid'ad'a ina kallon ki saidai kici kisha kije makaranta? Tab garama kisawa kanki salama babu wata makaranta da zakiyi idan ba haka ba lokacin aurenki saidai a kaiki daki hororo ba kaya".
Cikin kuka Lami tace "dan Allah babah ki barni nayi wallahi ina son makarant.................duka Ramatu ta kawo mata tana cewa "ubanki yahau baro馃檴 ina magana kina musa min bazaki makarantar ba talle zaki kuma na fad'a zaki tashi ki dauka ki fita ko saina miki shege dukan da zaki kasa tashi shima malam din ina nan daidai dashi" mi'kewa Lami tai tana kuka ta dau farantin gyad'a ta bita Ramatu data bita da kallo tace "kuma saura kije ki zauna a guri daya idan kika dawo min da saura saikin gane" Lami dai bata sake tofa koda alif ba ta fice ta nufi matallata.
Bata fara ciniki da wuri ba sai jikin magriba kasuwa ta bud'e bayan sallar isha Lami ta baro dandali ta sayar gyad'ar tas sai farantin kawai a hannun ta jin taku ana bin bayanta yasa da sauri ta waiga ganin mutum yasa tace.
"Waye"? Shiru ba amsa a tsorace tasa gudu wanda shima ya rufa mata baya ga duhu ga matsatstsan layi tuntu'be tayi da dutse ta fad'i 'kara ta saki daidai ya iso waje da sauri ya toshe mata baki tare da kinkimar ta ya shiga wani kango da ita.
A tsautsayi ya daka mata tsawar cewa ta masa shiru cikin mamaki Lami tace "Tanko kaine me nai maka ka sake ni" kallon ta yayi "oh kin gane ni ashe aiko saina tabbatar ban barki kin kai labari ba yau babu me cetar ki a hannu na yadda kika haramta min auren ki shima wancan mayen da kika wulakanta ni akan sa saina tabbatar bazai same ki ba".
Cikin karfin hali Lami tace "Tanko wulakancin ya isa haka ka sake ni kuma wallahi bazan yarda ba gobe saina kai kararka gurin me gari" dariya yayi "ki kai karata gun wanne me garin? Basai na barki da rai ba balle ki kai labarin" jin abinda yace yasa ta fasa kara tana kai masa duka ta ko'ina shi kuma yana 'ba'bbaka dariya kamar zararre.
Ramatu na zaune lokaci zuwa lokaci ta kalli hanyar kofar shigowa ganin shiru babu alamar ta yasa ta mi'ke tana daukar hijab tace "a'a ni kalau kuwa Lami yau bata dawo ba bata irin wannan daren a dandali bari muga" fita tai ganin yar ma'kotansu abasiyya ta taho yasa Ramatu cewa "ina kika baro lami ko tana can"? Kai abasiyya ta girgiza "a'a ta ma riga ni tahowa saidai in a wani gun ta tsaya" jin haka yasa Ramatu wucewa ta nufi dandalin tana zuwa layin taga farantin da kud'i a baje a gurin salati tayi tana tattare kud'in tare da daukar farantin cikin mamaki ta kalli gabas ta kalli yamma babu alamar kowa da sauri ta fito a layin kamar zata kifa ta koma gida hankali tashe tan kururuwa azo a cece ina Lami tai nan gari ya hargitse aka d'ebo fitilu ana haska ko'ina tace ga inda taga farantin gurin suka je suka fara haskawa har cikin kangon gidan aiko sai gata kwance sharkaf bata motsi jikin ta harda jini da alama fayde akai mata innalillahi wa inna ilaihi raji'un guri ya kaure da salati Ramatu dake waje jiki na rawa tace "meya faru an ganta ne"?..........
Tana rufe baki taga Sabi'u da Habu sun fito dauke da ita ihu ta saki tana cewa "na shiga uku na lalace yau ranar tonon asiri tazo Lami wanne d'an diban albarkar wanda bazai gama da duniya lafiya bane ya miki wannan aika la'ilaha illallahu kaito na dama banga wannan rana ba wannan wanne irin masifa ne da bala'i" hakuri su Salamatu ke bata duk da kowa jikin sa rawa yake aka nufo gida wasu na cewa a kaita asibiti wasu na cewa bata da rai.
Kwantar da ita akai Baffah dake durkushe gabanta yana kallon fuskarta abubuwa da na masa yawo cikin kwakwalwa musamman maganar da sukai na zai kaita makaranta gobe ashe yarinyar nan burin ta nason ganin tayi karatu ta samu ilimi bazai cika ba hawaye ne masu zafi ke zuma daga idon Baffah wanda suke sauka saman goshinta gida kam ya cika da jama'a ya kaure da koke koke mi'kewa Baffah yai da'kyar yabar gurin yayin da masu wankan gawa suka dauketa domin mata sutura bayan su kammala akace ba damar kaita dare yayi saida safe haka tai kwanan keso.
Washe gari da wuri bayan anyi sallar asuba aka mi'kata makwancinta kafin suka dawo zaman makoki da sauran mutane da ba'ki lokacin da aka dawowa da Ramatu zanin da aka lullu'bi Lami dashi nan sabon kuka ya tashi da bori har rirri'keta ake ana dankwafarta da lallahi da bata hakurin cewa addu'a zatai mata ba kuka ba.
Tashin hankali wanda ba'a sa masa rana lokacin da su Musbahu suka labarin karyatawa sukai saida suka zo suka gani da idanuwan su Musbahu yayi kuka ya kara kamar mace balle mama da Naja'atu alpha kuwa tunda ya suma bai farfad'o ba sai a gadon asibiti ya ganshi kwance daure da ledar ruwa hannu yasa ya fisge yana tashi zaune tare da saukowa daga gadon yayo waje likita daya taho d'akin zai sake duba shi ganinsa ya fita sai layi yake yace "a'a ina zaka je baka samu lafiya ba please yalla'bai mu koma ka kwanta" ko sauraron sa alpha baiyi ba yai gaba da sauri likitan yabi bayan shi yana masa magiya.
"Dan Allah ka saurare ni ka dawo ciki na duba ka".
Tamkar da gunki likita ke magana haka Alpha yai banza dashi yaci gaba da tafiya batare da ya kalli kowa ba kasa nutsuwa doctor yai domin yasan waye alpha d'an babban mutum ne duk abinda ya same shi yanzu shi za'a tuhuma bai daina binsa ba har suka fito harabar hospital din anan ya hango mom din Alpha da sauri yaje yana cewa "hajiya dan Allah ki taimaka kiyi masa magana ko zai tsaya", kallon Alpha daya nufi hanyar fita a gate din hospital tayi tare da girgiza kai tace "karka damu doctor zan dawo dashi" tana fadin haka tabi bayansa itama da sauri taga inda ya nufa domin basu taho tare da abbansa ba.
Tsaye ta same shi jikin wani karfe ya kifa kanshi yayi shiru tsayawa tai a bayansa tare da sauke ajiyar zuciya tace "Alpha" bai juyo ba kuma bai amsa ba 'kara matsawa tayi kusa dashi tana dafa shi tace "Alpha me ya faru"? Har lokacin shiru baiyi magana ba juyo dashi tayi tana rike hannunsa cikin lallashi ta soma tafiya dashi tana cewa "haba alpha kaifa musulunci ne ka dau kaddara komai yai zafi maganinsa Allah na sani Lami rayuwar kace kuma kana kaunarta amma wanda ya halicce ta ya fika sonta shiyasa ya kar'bi kayarsa kayi adduar ta samu rahma da haske a kabarinta shine yanzu abinda take bukata kuma kaunar daya rage ka nuna mata kenan kaji", Alpha tari dabai kama shiba baiyi ba ganin haka yasa dole ta 'kyale shi tasan baya cikin hankalin sa doctor na tsaye yaga sun shigo d'an sauke numfashi yayi yana cewa "kiyi hakuri hajiya nayi kokarin dakatar dashi bai saurare ni ba" kai ta girgiza "a'a babu komai doctor nasani muje ka mayar dashi ya kamata ya samu hutu na d'an lokaci" "to shikenan hajiya" doctor ya fad'a yana bud'e kofa ya shiga suka bi bayanshi.
Anyi sadakar uku ba'ki wasu suka fara tafiya saura kadan suma bayan bakwai suka dauri niyya suka koma garuruwan su domin Baffah mai jama'a ne sosai.
Zaune Sabi'u da Habu suke a gaban Baffah suna masa 'korafin abinda akaiwa Lami wanda basu san waye ba Habu ne ya fara magana.
"Yanzu Baffah shikenan haka zamu zuba ido baza ayi binciken wanda ya aikatawa Lami wannan rashin imanin ba gaskiya baza mu yarda ba sai mun kai rahoto gurin 'yan sanda a zo garin nan a tsananta bincike duk wanda yake da hannu sai an hukunta shi".
Tarar numfashinsa Sabi'u yayi "eh 'kwarai Habu wallahi baza mu yarda sai an bi mana kadin wanda yai sanadin yarinyar nan taya za'ai mata haka mu 'kyale kamar wacce bata da gata dole mu tashi musan abin yi amma me kace Baffah"?.
Shiru yai duk damuwa ta addabe shi ya rasa inda zaisa kansa yaji dad'i yana matukar takaicin rashin yarinyar nan yayi kuka ya 'kara harya gode Allah mutuwa lokaci in yazo ba jira amma Ramatu ta cuceshi bazai ta'ba yafe mata ba a rayuwa................................
Tunanin sane ya katse jin Sabi'u na cewa "Baffah baka ce komai ba"?.
'Dagowa Baffah yayi yana kallon dukkan su biyun cikin nazari ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "Sabi'u Habubakar Allah yai muku albarka ya albarkaci rayuwar ku da zuriyar ku na amince da abinda kuka ce kuma na yarda ku dauki mataki akan koma waye ya cutar da Lami kuyi bincike ni na amsa muku da yardata Allah ya taimake ku ya tona asirin wanda yai mata haka yasa bazai gama da duniya lafiya ba".
Da sauri Habu yace "Amin Baffah daga yau yanzu idan muka fita zamu fara aikin mu Baffah ka taya mu da addu'a mu samu nasara matukar aka samu wanda yai mata wannan rashin imanin shima a take zamu kashe shi dan wallahi bai isa mu rabu dashi yaci bulus ba".
"Kwarai Habu kayi gaskiya tashi muje yanzu ma kuwa" Sabi'u ya fad'a yana mi'kewa tarar zancen nasu Baffah yai "a'a Habubakar karku kuje kuyi abinda za'ai dana sani dan Allah ku bi a sannu kunji"? "To shikenan Baffah zamu kula Yaya Sabi'u zo muje" fita sukai Baffah daya bisu da kallo hawaye na zuba a idonsa yana farin ciki da samun su matsayin 'ya'yansa.
Gidan da suka d'aukata sukaje dube dube suka fara amma dai basu ga wata alama ba jingina jikin bango Habu yai yana cewa "tsaya yaya Sabi'u nifa na kasa fahimta musamman yanzu da muka zo nan".
D'agowa Sabi'u yai "kamar ya ban gane ba"?.
Kallon daidai inda suka ganta kwance Habu yai yana cewa "ka duba man lokacin akwai alamomi sakamakon muna rud'e ya hana na tsaya amma wanda yai hakan yabar alamar wani abu kai baka gani ba"?.
Shiru Sabi'u yai yana tunani zuwa wani lokaci yace "amma kai a ganinka waye zai iya yi mata haka a garin nan da kewayen mu waye shi".
Rufe ido Habu yai ya kasa cewa komai abubuwa yake tunawa suna masa yawo a kunne ya riski zancen da Lami tayi da su Tanko lokacin zai fito harya tsaya ya saurari wani abu kamar inda Tanko ke cewa saiya sa tayi kuka da idonta tayi nadama.
Da sauri ya bud'e idon yana kallon Sabi'u yace "yaya Sabi'u tabbas akwai wani abu ina zargin mutum daya wallahi shine kuma ko kaffara bazan ba shi ya aikata mata haka" "waye habu wa kake tunani a ina yake yanzu muje"?.
Kallon Sabi'u Habu yai yana d'an d'aga kansa sama alamar tunani a hankali yace "Tanko ne yaya Sabi'u tabbas shine ba kowa ba" zaro ido Sabi'u yayi yana 'kure Habu da kallo yace "Tanko kuma? Habu Tanko dai da na sani d'an gidan malam Balah saurayin ta? Meyasa kake zargin sa"?.
Ri'ke hannunsa Habu yai yana cewa "kwarai shi nake zargi kasan wani abu na ta'ba jin suna hira da ita shida abokinsa Mudi akan saita rabu da yaron nan Alpha ta aureshi saboda ta'ki amincewa ta shiga gida basu san ina la'be ba suke cewa zatai nadama da dana sani a rayuwar ta dan haka dole nace sune".
"Habu ka tabbata kaji haka"?.
"Eh yaya Sabi'u wallahi da kunne na naji lokacin da suke wannan maganar da ace bishiyar kofar gidan mu tana magana zata bada sheda".
Kai Sabi'u ya jinjina "shikenan Baffah yace kada muyi abinda za'ai dana sani amma ba baza mu 'kyale ba yanzu muje mu same su" fita sukai kai tsaye dandali suka nufa sukai sa'a suna majalisar su harda Ilyah tsayawa daga gefe Sabi'u yai yana cewa "je kayo mana magana dasu" kai Habu ya d'aga yana karasawa yai musu sallama tare da baiwa kowa hannu suka gaisa yana kallon Tanko yace "kadan zo zamuyi magana yanzu" dafa 'kirji Tanko yai idonsa kamar zai fito waje yace "ni"? Wata uwar harara Habu ya sakar masa yana cewa "a'a ba kaiba ni" saroro Tanko yai jikin sa na 'bari yana kallon habu wanda takaici ya gama cika shi cikin tsawa yace "dallacan kana bata min lokaci zaka taso ko saina figoka"?.
A zabure Tanko ya mi'ke tun kafin ya d'ebi takalmi Habu ya jashi kiiiiii suka je gurin Sabi'u sannan ya dawo yana cewa Mudi "malam saura kai kake 'kwalalo min ido" shima jiki a sanyaye ya mi'ke suka fita ganin sun fara tafiya yasa Mudi cewa "ina zamu je"?.
"Ka biyo mu man zaka gani ai" ya fad'a yana sake tisa 'keyar sa gaba har suke cikin kangon gidan nan juyowa Sabi'u yayi yana nuna musu gurin yace "Tanko wanne irin rashin imanin ne haka me Lami tayi maka zakai mata fayd'e gashi ka zama silar mutuwarta"?.
A wannan lokacin tsabar firgici Tanko har saida ya 'kwaru muryarsa a sha'ke da'kyar yace "ni kuma amma Allah ya isa na sharri zaku min ina ruwa na da ita me tamin zanyi mata haka aiko bazan yarda ba saina kai ku gurin me gari".
A fusace Habu ya sha'ki wuyan rigar Tanko yana naushin sa yace "sharri ma kace zamuyi maka tsinanne asararre wallahi yau saika amsa laifinka ko kaima ka ba'kunci lahira ka gano abinda ake gani" ya karasa maganar yana sake dam'ke wuyan Tanko wanda idonsa suka fito waje.
Ganin Habu na neman yi masa illa yasa Sabi'u cewa "ka sake shi Habu kada kaji masa ciwon da zamu zo shari'a ta kada mu" saida habu ya gwara kan Tanko da bango yaga ya fad'i baya motsi sannan ya rabu dashi yana huci ya maida kallon sa kan Mudi da yake rarraba ido alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsa 'kiri 'kiri.
Kamar wanda zai fad'a masa ya kashe shi haka habu yai kansa gadan gadan yana cewa "kai kuma munafiki zaka fad'i gaskiya ko kaima saina tura ka suman kamar abokin naka? FA'DI MANA" yai maganar a tsawace.
Jikin Mudi na rawa yace "dan Allah Habu ka tsaya ni bansan komai ba".
Wani kallo yai masa na baka da hankali amma zan koya maka kafin yace "kace bakasan komai ba ko? Haka kace ko? Lallai yau saina bambance maka abinda ake kira da jaki sha duka" warto shi yai tare da d'uma shi da 'kasa yabi ya take ya hau jibgarsa da dukkan karfi sa ihu Mudi keyi yana neman agaji Sabi'u na tsaye da yake baida zafin rai kamar Habu amma bazai hana shi dukan nasu harsai sun amsa cewa eh.
Jin da Mudi yai idan ya sake za'ai bashi yasa cikin wahala da numfashi da'kyar yace "dan Allah Habu ka tsaya zan fad'a maka gaskiya wallahi zan fad'i gaskiya karka kashe ni zaka 'balla min 'kafa" jin haka yasa da gudu Sabi'u yaje yana 'bam'bare Habu daga ruwan cikin Mudi yai dauke shi yai gefe dashi.
Yana cewa "tsaya haka Habu yanzu zaiyi bayani" huci Habu keyi yana kallon Tanko dake kwance sharkaf kamar matacce a hasale yaje ya wanka masa wani irin gigitaccen mari me karfi sai ga Tanko ya mi'ke tsaye a firgice yana neman hanyar guduwa dam'ko shi Habu yai yana maka shi da 'kasa yace.
"Gidan uban wa zakaje"? Idan kaga na barka ka fita anan