Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
dan haka yanzu ido ne naku babu abinda ya isa ya 'kwaceta a wurin mu tayi bankwana kenan bazan hana ku binta ba ga hanya nan saidai zaku mutu hhhhhhhhhhh ku taho馃懟馃懝" yana fad'in haka ya 'bace addu'a malam yaci gaba tayi ba fashi da gudu suka sake yin dajin can suka hango Ramatu a wani wuri tana lilo abinda ya basu mamaki babu alamar igiya amma bala'in hillon da take ya 'baci addu'a malamin keyi yana nifar inda take yaje gaf da ita yaga wani ba'kin abu yazo ya shiga jikinta bai fasa ba ya sake matsawa wani irin tattarashi yeji anyi kafin ya ankara an li'kashi da kasa da sauri ya mike bai fasa addu'ar ba gashi gurin sai canza kala yake yana duhu kamar yanayin almuru Ramatu kuwa kamar wacce ake 'kara hilla ta can ta tsaya sai kuma ta dirgo ta sauka ta soma wata kalar tafiya kamar yar maye tana rangaji tayi gaba tayi baya ihuuuu ta zunduma tana rike kanta wanda malam yai amfani da wannan damar zai ri'ko ta aka daukeshi fiiiii kiffff aka watsa shi gefe har rawaninsa Saida ya fad'i yana yai yunkurin tashi da sauri yana sake nufota kafin ya karaso inda take sai gani sukai ta zama ba'ki 'kirim kamar ta 'kone bata da kyan gani daga haka ta zama 'bakin murtukekken haya'ki ta 'bace 'bat馃檴馃槪 shikenan.
Haki malam keyi sosai yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un mutane na amsa masa kowa jiki na bari malam yace "ya kamata mu barnan yanzu yanzu" aguje kowa ya ruga sai gware suke wadanda suka fad'i ana take su a haka suka samu da'kyar suka fita dajin suka koma gida da labarin abinda suka gani gari sai gulmar ake ana Allah wadai da halinta dama itace taiwa Salamatu asiri ya dawo kanta kowa da abinda zaice shikenan fa'kat masifa ta mutu Bara'atu ta huta ba wanda zai fadi abun alkairi a kanta sai na tsiya ga Ilyah bai nuna alamar zaiyi wani zaman makoki ba ko kadan kawai yadan zauna wunin ranar amma shikenan ya basar sai ranar sadakar uku.
Dalah na zaune tana sa'ka mifici na saidawa da take Indo tana kefenta sai bori take mata ta'ki cin abinci wai saita bata kud'i ta sayo irin alewar bahijjah itakuma sisi bata dashi sauri take ta karasa maficin ta bata takai shagon tunda dama mai shagon yana Sara saiya saya ya bata alawar shigowar Balarabe kenan jin yadda take kuka harda shid'ewa ya daka mata tsawa "uban me akai miki zaki damu mutane da koke koke kamar gidan mutuwa"? Yaro ba hankali kuma ka saba mahaifin ka na sake maka da sauri ta tashi tayi gurin sa bataji wannan tsawar dayai mata ba da gudu taje zatai masa oyoyo tana rike shi ya tureta yana wuce ciki kifawa Indo tai tana kuka da sauri Dalah ta mi'ke tana d'ago ta tare da kad'e mata kasar jikinta ta rike mata hannu suka koma bata karasa maficin ba tsabar takaici haka ta bata cike da damuwa tace "kar'bi kije gurin Bintan gidan Habu ai kinsan gidan ko"? Kai Indo ta d'aga tana goge hawayen fuskarta tace "eh na sani" cigaba Dalah tai "maza ki bata kice wai ta baki kud'in zaki sai alewa inji ni sauri" kar'ba Indo tai zata fita Asabe data fito daga d'aki ta riski karshen zancen Dalah bata ankara ba sai jitai an rafka salati a bayanta Asabe na cewa "to sabon salo gemu a kafad'a malam fito kaji wata magana ga Dalah nan ta aiki Indo maula dan a zageka a gari ace 'ya daya ka kasa mata abinda uba yakewa 'yarsa" kamar an hankad'o Balarabe ya fito yana cewa "meya faru" nuna Indo Asabe keyi "kalli man wai mafici ta bata ta wai waye a cikin matan Habubakar tace wai ta bata abinci yanwa take ji mu bamu girka ba tun jiya kaji fa bayan d'azu ta sauke abincin dan kawai tasa a gari a zageka" kumbura sosai Balarabe yai yana huci kamar zai rufe dala da duka "oh yanzu kuma sharrin da zaki min kenan daga kin bar wannan saiki koma wannan kinje gari kin yad'a wai banai miki sutura duk kayan da kike sawa kece kike dinka abinki na shareki ban nuna miki fushina ba shine kuma yanzu zaki fara tura ta maular abinci bayan ban rageku da komai ba ke wallahi Dalah kina da ba'kin hali indai baki canza ba zan dauki mataki a kanki" juyawa kan Indo yai yana fisge maficin "kema dan ubanki bani nan shekiya munafika tun baki girma ba uwarki zata koya miki halin tsiya halin karya gwafar ubanki zakici wallahi" ya karasa maganar yana ralla mata maficin aka sannan ya jefashi a wuta ya kone dur'kusawa Indo tai a gun tana kukan azaba Dan yajin dukan har 'kwa'kwalwata nuna Dalah yai da yatsa wacce take tsaye hawaye fal idonta yace "ke kuma daga yau sai yau kinyi na farko kinyi na 'karshe kada tsautsayi yasa na kara jin kin tura gidan uban kowa maula biyar bana tauye muku hakkinku wallahi tallahi idan kika sake makamancin haka saimu kwashi dambun tsiya dake sakarya bagidajiyar mata kawai" yana fadin haka yai waje yana maganganu dariya Asabe tai tana kallon yadda Indo keta mulmula gurin daya rad'a mata maficin tace.
"Hummm ubanku zakuci daga ke har tsogalgalar uwar taki zakusan wace Asabe dan wallahi sunana kawai kuke ji wannan somin ta'bi ne ban nuna muku komai ba yanzu aka fara wasan za'a kwashi yan kallo nan gaba kuma ki jira ki gani" d'aki itama ta shige tabar Dalah tsaye kamar bishiya dukawa tai tana d'ago Indo suka koma kan tabarma ta goge mata hawaye cikin danne damuwar ta dason farantawa Indon tace "kinga kiyi shiru ki daina kuka indai akan alewa ne zan sayo miki" cike da yarinta Indo tace "baba ne zai taho min da ita"? Kallon ta Dalah tai da sauri jin furucin datai Allah sarki cikin tausayawa wato dai babu abinda ya canza harta manta da abinda yai mata yanzu amma saboda ta kwantar mata da hankali tace "eh shine zai taho miki da ita kinga d'auki abincin kici zai kawo miki" da murna fal ranta ta dauka ta fara ci Dalah ta zuba mata ido kawai ta fad'a kogin tunani.
A ta'kaice bayan wani d'an dogon matsakaicin lokaci Bara'atu ta haihu yan biyu maza Hassan da Hussain haihuwar su day wata sha biyar ta sake haihuwar mace aka saka mata Nafisa Maimuna itama ta haihu mace sunan yarinyar salmah ta sake mace da namiji amma akwai gaf sosai tsakanin su da shekaru.
Haka a bangaren Habu ma A'i ta haihu mace sunan yarinyar Jamila tsakani shekara biyu da Binta itama ta haihu mace Habu yasa sunan mahaifiyarsa Hauwa (Amatullah) watan Amatu goma sha daya Saude ma ta sake haihuwar mace Aisha daga nan nefa rayuwa ta soma bun'kasa ahli yayi yawa saidai babu wani kyakkyawan zumunci tsakanin su da Ilyah baya sauraron su ko kadan kamar baisan da zaman suba abun ya damu Habu dan haka ya samu Sabi'u sukaje gurin malam Zayyanu aminin Baffah tare da zayyane masa komai akan ya kira Ilyah ya masa nasiha amma da Ilyah yazo bayan ya gama sauraron dalilin kiran bud'ar bakinsa cewa yai shifa kar a takura masa baida wasu yan uwa bayan matansa da 'ya'yansa da kuma dukiyar sa wannan abinda ya fad'a ya matukar 'kona musu rai babu irin shan kan da wa'azi wanda malam Zayyanu baiyi masa ba amma karshe mikewa yai ba magana ya karkad'e musu 'kura yai gaba duk binsa sukai da kallo ransu a 'bace musamman habu da yake jin kamar ya she'ka aguje ya sha'ke masa wuya hakuri da magana mai dad'i malam Zayyanu ya ri'ka musu da nuna musu cewa zai dawo kan hanya zai shiryu kuma suma suna yi masa fatan hakan kafin lokaci ya'kure masa.
Bayan d'agowar yaransu sun kasance babu makaranta ta zamani basu santa ba basayi saida aka zowa mai gari da takarda daga 'karamar hukumar da take mulkarsu dan haka tun jami'an basu tafi ba mai gari yasa aka tara magidanta na garin suyi musu bayani yadda zasu gane karshe bayan su tafi mai gari yasa akai shela nan fa gari ya dauka harda masu zagi wai za'a toshe musu hanyar samun kud'i haka kawai za'a 'kir'kiro makaranta wai ita boko wasu suna ce wallahi yaransu bazasuyi ba kaf 'kauyen baifi mutum biyar ne suka yarda da abinda ba'kin suka zo dashi ba ba'a garin 'karamar hukumar tai makarantar ba a wani babban kauye ne kusa dasu saidai garin nada girma sosai amma dai 'kauye ne bayan an kammala a gari tsirarun mutane ne suka shigar da yaransu wannan makaranta wadanda basu amince ba sunfi yawa suna yi musu kallon wawaye ganin babu yara sosai a makarantar ga malamai 'kwararru yasa suka kai kukan su cewa babu d'alibai wakili ya sake turowa aka sake yin shela ana bi gida gida ana daukar sunan yara da basu uniform da littafai da jaka da sandals kyauta ga motar yan makaranta school bus 馃殞 wacce zata ri'ka fitowa dasu tana kawo su idan an tashi driver ya mayar dasu amma duk da haka a banza wannan baiyi aiki ba dan wasu iyayen har 'boye 'ya'yansu suke dan a 'bangaren Ilyah ma cewa yai Allah ya sauwake makarantar 'karyace da yaudara kila nan gaba su sace yara su gudu babu wanda zaiyi a yayansa kadan ne a garin ke zuwa amma habu dai babu wanda aka bari cikin yaransa kowa na zuwa shi baya jiran motar daukar d'aliban ma a tasa yake d'iban su yakai yawan zuwa da yake har tasa malaman sukai sabo dashi suka sanshi sosai sune silar da aka dawo kiransa da malam Habu yan gari na masa isgili wai kodai yana cusa kaine dan su d'auke shi koyarwa.
A wannan garin kuma da akwai wani mahauci ana kiransa 'kwalisa yara suka samasa sunan sakamakon idan yaje rafi yayi wanka duk sai jikinsa yai farin ta'bo da farar kasa kuma idan ya dawo gari saiya ri'ka tafiya irin ta yan gayu yana doro yara suna tsokanarsa kullum idan d'aliban sun tashi shi kuma nan ne gurin zaman sa wata ranar har kwana yake kuma gashi a lokacin sanyi ne yana kwance da dare sanyi ya dameshi ya kasa barci sai juyi yake yana ma'kyar'kyata tashi yai akwai wani guri ta bayan makarantar da aka jibge kara da yawa kawai yaje abinka da mahaukaci ba hankali ya dauko ashana a aljihunshi ya kunnawa karan wuta dan ya samu yaji d'umi tun wutar tana ci kad'an kadan hartai karfi yadda shima ta dameshi gashi dare yayi babu mutane jin zafi a jikinsa yasa shi matsawa daga gurin yana dariya yace "ina yara kuzo muyi 'kwalisa na kunna haske kun ganshi yana yawa kuzo muyi 'kwalisa na iya had'a haske" ya karasa maganar yana rawa da tafi shi kadai sai shirmensa yake yayin da wuta taci gaba da tsiri har farfatsi take haka ta fara kama makarantar nan ga gidajen garin kusan duk dangan kara yafi yawa ga iska da ake mai karfi watsuwar da wutar take yasa ta fara kama ko'ina gidanjen kusa da gurin farkawar wani mutum ganin hasken daya sa'ba hankali yasa ya fito da sauri daga d'aki zaro ido yai yana raraka wani uban ihu.
"Subahanallahi innalillahi wayyo Allah jama'a ku tashi wuta ta kama shikenan tamu ta 'kare" da gudu yayo waje yana kara zunduma wani ihun "ihuuuuh jama'a ku tashi gobara ta kama kara dan Allah ku farka" nan da nan mutane suka fara tittid'owa suna fitowa gari ya rud'e da salati kowa ya rasa inda zaisa kansa sai ruwa suke de'bowa suna watsawa amma kamar basa zubawa sai kara tsiri take kamar zata ta'bo sama ruwan gidaje ruwan rafi ruwan rijiyoyi haka suka ri'ka kwararawa da'kyar suka samu wutar ta mutu bayan tayi musu mummunan ta'adi duk ta kone gidajen dake makotaka da gurin babu abinda ya tsira sai mutanen gidan da yan kayan da suka samu nasarar fitowa dashi.
Washe gari haka gurin ya zama ba'ki'kirim bayan makarantar ma da rufin ta duk ya 'kone jama'a ta taru an cika guri sai kallo ake babu wanda yasan ya akai wutar ta tashi dole suna bukatar taimako amma basa da wani tsayayye a garin me shige musu gaba haka suka dauki tsawon lokaci suna fama shan wahala musamman wadanda gidajen su ya'kone makaranta ma haka suka cigaba da karatun ba'a gyara ba yau da gobe tafi karfi wasa ganin zasu shiga tsaka mai wuya domin akwai kayan amfanin gonakin su da suka 'boye a cikin karan gashi ya kone sun dawo fama da 'karancin abinci yasa liman din garin sukai hadu sukai shawara aka za'bi manya a garin suka kai kokensu karamar hukuma cewa ga abinda ya same su suna neman tallafi daga can aka d'ebo wakilai domin suzo su gani harda 'yan jarida aka zo suka danyi tambayoyi daya wutar ta tashi sannan sukai wa gurin video da makarantar sannan bayan su koma suka fad'i dukkan abinda suka gani lallai mutanen garin na bukatar taimako ba karamin 'barna wutar tayi musu ba, dole aka dakata dayin makaranta harsai an gyara kafin aci gaba domin gyaran zaici kud'i sosai ga 'konewa gidajen mutane.
Kamar yadda 'yan jaridar nan suka dauki video suna zuwa suka yad'a shi a gidajen television da radio mai martaba yana zaune yana ganin labaran hankalin sa ya tashi wannan abun ya faru amma bai sani ba taya zai zauna lafiya indai irin wannan abubuwan suna faruwa ransa ya 'baci sosai don gani yake maybe sakacin Governor ne domin ai duk tsiya yasan da garin tunda a campaign yaje ya musu za'kin baki gari ko gida daya ne indai lokacin campaign ne ana zuwa dan haka yasan da garin amma ace harsu shafe tsahon watanni takwas da gobarar babu wanda ya tallafa musu abar ta batun makaranta amma magidanta fa wadanda gidajen su ya 'kone a ina suke kwana? A layi ko kwa a ina? 'Daga waya yai fuskarsa babu alamar walwala ko wasa yana bada umarnin lallai yau d'in nan yana son ya gana da gwamna, yadda ya bada umarni haka ne ta faru da dare misalin goma suka samu ganawa mai martaba da Governor ya nuna 'bacin ransa sosai yayi fad'a gwamna ya nuna masa cewa ba laifin sa bane shima bai sani ba wakilan 'kananan hukumomi ne basa aikinsu yadda ya kamata dan haka mai martaba yace lallai gobe ko shi bazai samu damar zuwa ba ya tura wakili zaisa 'kaninsa Alhussain su tafi tare a kai musu tallafi na kud'i sutura da kayan abinci amsa masa gwamna yai sukai sallama tare da alkawarin zai tura wakilin sa gobe suje garin tare.
MRS AL-AMEEN AHMAD CE馃槝.
See u next time, nagode masoya we will meet again 馃馃.
Sai Allah ubangiji mai duka mai yau da gobe jallo mafi girma ya kaimu gobe da rai da nisan kwana 馃槦inai wa dukkan masoyana barka da wuni da fatan alkairi 馃挀馃挄馃挒.
YUSRAH MUSA ABUBAKAR 馃尮馃馃憣 MAI TAMBARIN YMA DUTSE NEW WORLD 馃審 NEW LIFE 馃寣 ANDA NEW STYLE 馃憣 SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DAD'I YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA馃彏锔忦煆烇笍馃椈.
See馃憖 u next morning 馃.
Mrs Al'ameen Ahmad ce 馃槝
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
TYPING 馃摬 Thus, Jun5/6/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR 馃尮馃.
馃拵Me kamar sarki 馃拵
WhatsApp no:234 905 527 3614.
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 馃拑馃拑馃拑.
馃棧锔忦煑o笍馃棧锔忦煑o笍馃棧锔廔na kake d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka ka cancanti jinjina 馃巼馃帀 ina maka barka da wannan lokaci fatan alkairin Allah yakai maka duk inda kake Amin 馃憦馃憦.
馃挄SALEEM MUSA ABUBAKAR 馃尮鉁岋笍.
Sulaiman Ibrahim Usman
Usman Ibrahim Usman
Abubakar Musa Abubakar
Ibrahim Musa Abubakar
Fatima Musa Abubakar
Husnah Ibrahim Usman.
KU TAHO MASOYAN 'KWARAI馃ぃ馃ぉ馃槣.
MARUBUCIYA馃摎馃挾馃憞
鉁嶏笍 Yarima Abdul-maleek
鉁嶏笍 Rayuwa biyu
鉁嶏笍 Safreeyyah
鉁嶏笍'Dan millionaire
鉁嶏笍Minah-Umer
鉁嶏笍Dama kece
鉁嶏笍 Royalty
鉁嶏笍 Husnah ko Badiyat
鉁嶏笍 Zuciyar Aliyu
鉁嶏笍 Haskena Sauban
鉁嶏笍A gidan talaka
鉁嶏笍Kowacce 'kwarya
鉁嶏笍Me kamar sarki.
35~As-shakur馃挄
The grateful
36~Al-Aliyu
The Sublime 馃挄
17~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shakirnah .
馃寗ULCERATION ND ASTONISHED馃寗
Episode 35&36
Washe gari Aisha da Jamila ba lafiya anyi cinye cinyen kayan mai'ko bayamma ta tashi Asma'u kuma bata nan sunyi tafiya ita da Saude sai sati mai zuwa zasu dawo iya Amatu yanzu malam Habu yake kaiwa makaranta dan haka baya kaita a mota saboda ita kad'ai ce mashin d'in haya yake hawa ya rakata kullum yauma kamar yadda ya saba yana zaune a kofar d'akinsa yana jiran ta ganin shiru bata fito ga lokaci yana dad'a 'kurewa kuma dama yau sun makara rana ta d'ago sosai kila ma period d'aya ta wuce d'an 'kwalla mata kira yai.
"Binta wai ina maman nawa ne bata fito ba? lokaci fa yana kara ja karta makara a dake mun ita bazan ji dad'i ba".
Fitowa Binta tai da cooler 'karamar irin ta basket d'in yan makaranta bayanta Amatu sanye da uniform lokacin shekararta shida d'an zuba mata ido malam Habu yai kafin ya sauke numfashi yana cewa "ubangiji Allah ya d'aukaki rayuwar ki mamana ina fatan ki zama wani abu nan gaba wanda bani ko Binta ba al-umma da yawa su 'karu dake" murmushi Binta tai cikin jin dad'i tace "insha Allahu addu'ar ka zata kar'bu amma irin wannan kallon haka da kake mata kamar akwai abinda kake tunani domin na riski lokuta da dama idan kuna tare da ita sai naga ka zuba mata ido meyasa"? Rike hannun Amatu yai yana kar'bar cooler breakfast d'inta ya mi'ke zasu tafi yana cewa "eh dalili shine idan ina kallonta zuciya ta tana samun nutsuwa da kwanciyar hankali shiyasa koda yaushe nake addu'ar Allah ya bata nisan kwana lallai soyayyar wannan yarinyar a cikin rai da jini na take yawo Binta ina son yarana kuma dukkan su daya suke a gurina amma fa maganar gaskiya nafi sonta" ya karasa maganar yana sake rike hannun nata dakyau yana sake jin sanyi yana ratsa shi 'yar dariya Binta tai cikin tsokana tace "soyayya tasa ka manta