Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   21 / 67

60K to 63K   out of 200.4K words

daukar gyale tace "kai dai tazo man ka gani ko bayan raina ka rike wannan ka huta yace sai dare ya raba zamuje yana cikin daji" "daji kuma amma mutumin arziki ne zaiyi rayuwa a daji"? "Yo Ilyah taya dama wanda yasan me yake zai bar zaman cikin jama'a ya koma daji boka ne fa".

"Boka kuma amma me ye had'i na da boka mezai bani"?.

"Me zai baka kake tambaya? Tab lallai Ilyah bansan asirin da sukai maka ka lalace haka ba har boka kake cewa wai me zai baka"? Zama Ilyah yayi yana jan wani kwano dake rufe ya bud'e ganin shinkafa yasa ya fara ci wani kallo Ramatu ta masa tana cewa "yau nake ganin sakarai sauna Iliyasu anya Habu da Sabi'u basu je gurin yan bori sun kashe maka zuciya ba gaskiya bazan yarda ba saina je gurin boka na naji komai" Ilyah bai sake ce mata 'kala ba haushi ne ya kama Ramatu ta soma balbale shi da masifa amma yai banza Saida ya gama ya mike yana kallon ta yace "karki damu nan da sati biyu zaki bud'e ido kiga surukar ki nima biyun zan aura Bara'atu da Maimuna domin ina matukar kishi da habu har bansan yadda zan kwatanta miki ba" cikin farin ciki Ramatu tace "yauwa d'an albarka haka nake son ji sai yanzu naji zuciya ta tayi sanyi na fasa zuwa gurin bokan yau sai wani lokacin" Ilyah na shirin fita yace "in an jima zansa a kawo miki nama" zaro ido Ramatu tai baki washe tace "kai kai kai kace yau zanyi bacci da mafarki ina jiranka dan albarka" sa kai Ilyah yai ya fita a gidan yayin da yabar Ramatu sai rawa take a d'aki tana shewa.

Alpha tunda ya fara jinyar rasuwar Lami ake fama dashi lafiya ta'ki samuwa saidai yanzun ba kamar da ba ya samu sauki jikinsa ya warware amma har lokacin nutsuwar sa bata dawo ba saidai da sauki tunda yana magana zaune yake a parlon gidan su Naja'atu wanda yanzu zuwa gurin ta na d'ebo masa kewa tsawon lokaci baiyi magana ba dan Naja'atu har ta fidda rai da zaice wani abu sai kuma taji yace.

"Naja'atu wai dan Allah da gaske shikenan Lami ta rasu bazan sake ganin taba har abada taya zan manta da ita"? Sauke ajiyar zuciya Naja'atu tayi tare da dan rufe ido tana tuno rayuwar da sukai a baya cikin son boye hawayen ta tace "Alpha kayi hakuri dan Allah tabbas Lami ta rasu bata duniya ta tafi ta barmu da kewarta babu yadda muka iya sai addu'a abinda ya rage tsakanin mu da ita bansan ta yadda zan fara kwatanta maka yadda na damu da Lami da halin dana shiga a kanta ba Alpha na sani kana tsananin son ta nice mutum ta farko dazan bada sheda akan haka dan Allah kayi hakuri ka dauka rayuwar da kukai a baya kamar mafarki ne" kai Alpha ya jinjina "lallai kowanne lokaci da irin nasa salon dole ya nemi taimako dan tunanin ta na gaf da rusa masa rayuwa Zuciyar sa ta kusa bugawa kallon Naja'atu yai kafin ya mi'ke yana cewa "shikenan Najat na gode zan tafi ki gaida min mama" mi'kewa Najat tayi suna fita tare tayi masa rakiya ya tafi bayan rasuwar Lami tana so ta fad'a masa tana son sa ta kasa kawai tana matukar tausaya masa ne daga haka abu ya zarce kullum idan suna waya tana shawarar fad'a masa ta kasa balle su had'u face to face saidai tana adda'ar Allah yasa shima yaji wani abu a kanta.

Zaune Balarabe yana shan fura yake gefensa Dalah tana tankad'en garin masara d'agowa yayi yana cewa "nikam ina Indo ne har yanzu ban ganta ba tunda na shigo gidan nan"? 'Dan murmushi Dalah tayi tana cewa "ai tun d'azu ta fita nidai tace min gurin Adama zataje kuma ban sani ba ko ta biyo ta wani gun" kallon ta Balarabe yai "amma me nace miki bance ki daina barinta tana fita koda yaushe saboda ina ji da ita bani da wata 'yar ita kadai ce jini na gashi ba wani girma tai ba ina tsoron kada wadannan yan iskan da suke lalata yara cin zalin nasu ya biyo ta kaina" sauke ajiyar zuciya Dalah tayi daidai ta mi'ke zata je gaban murhu tace "insha Allahu malam babu abinda zai same ta" shiru Balarabe yai hankalin sa jin bai kwanta ba mi'kewa yai yana cewa "bari na bi bayanta gaskiya na taho da 'yata" yana fadin haka yai waje da kallo Dalah ta bishi cikin jin dad'in nuna kulawarsa ga 'yar tasu guda tal kamar rai da yake.

Lokacin da yaje gidan Adama tace masa ta bar gidan tun d'azu nan fa yaji ya susuce da sauri cikin azama ya juyo yana kalle kallen inda zai ganta can ya hangota tana cikin yaran anguwa suna wasa karasawa yai yana cewa "Indo na me kike yi anan zo mu tafi gida" d'agowa Indo tayi ganin ubanta yasa da gudu ta mi'ke tana zuwa ta d'afe shi tana cewa "baba" daukarta Balarabe yayi yana cewa "me kika zo yi nan"? Tana washe baki tace "wasa" "wasan kuma har nan? Indo na muje gida kinji" to tace tana rike hannunsa yana tafe tana masa zance suka zo wucewa ta gefen wata mace dake zaune tana sakin 'kosai a wani kofar gida kana ganinta kaga 'yar duniya dan hatta bakinta yayi bakin busa haya'ki taje tayi rayuwa a gurare daban daban tasan harka har ta had'u da wani mutum alhaji me kud'i ya aureta ta haifi yarinyar gud'a d'aya Bahijjah kamar gaske suna zama cikin lumana rana daya ta aika shi lahira ta washe dukiyarsa tayo awon gaba da ita da yake ta haram ce tuni tasa tagaba ta 'kurmushe kamar yadda wuta ke cin audiga ta wajen inda take sana'arta Balarabe ya biyo daidai zai wuce cikin shishshigi ta d'ebi 'kosan a leda tana cewa.

" 'yan mata ga kosai".

"A'a ta gode kibar kayan ki" Balarabe ya fad'a batare daya kalli inda take ba kara matsowa tai tana cewa "haba kai kuwa ba kyau maida hannun kyauta baya dan Allah ka bari ta kar'ba" dakatawa Balarabe yai cikin jin haushin ta da sauri ta mi'kewa Indo ledar tana cewa "ki gaida mamanki" to Indo tace kafin ta sake magana fuuu Balarabe ya bar gurin da kallo ta bishi tana cewa wacce ke zaune kusa da ita.

"Ke Meroh kinsan wannan mutumin? A ina yake"?.

Dariya Meroh tayi tana gyara daurin kwalin kanta ta soke shi a gaban goshi tana cewa "meya faru kike tambaya"?.

Daidai Balarabe yasha kwana ya 'bacewa ganin ta tace "ba komai kawai kallo d'aya nayi masa naji ina son sa" zaro ido waje Meroh tayi "kai 'kawata kin d'ebo da zafi kinsan waye wannan har kikace kina son shi bazai ta'ba aurenki ba".

Jiki a sanyaye tace "meyasa kika ce haka"?.

Kai Meroh ta rausaya "saboda ba mata a gaban sa matar sa daya ce kamar rai sunanta Dalah yana matukar kaunar ta ita da wannan yarinyar da kika gani a hannunsa dan haka gara tun wuri ki saukewa kanki wahala".

Kai ta girgiza tana sake kallon hanyar daya bi tace "Meroh bazan iya ba ina son sa kuma dole saina aure shi ta dad'i kota akasin haka da yardarsa koda 'kinsa da amincewar sa ko da karfin hatsi nidai saina aure shi Meroh kiban shawara tun bayan rasuwar baban Bahijjah ban kara ganin Wanda ya kwanta min a rai ba sai shi yanzu ya zanyi"?.

Ta'be baki Meroh tayi "ya zakiyi kuwa Asabe bayan hakuri kece 'bakuwar zaman garin nan amma mu da bamuje ko'ina ba munsan waye balarabe ba mutum ne mai wargi ba baya daukar raini ki taka a sannu".

Shiru Asabe tai na d'an lokaci tana tunani kafin ta d'ago tana kallon Meroh tace "to amma kawata babu wata hanya da zanbi ya soni ko mu 'kulla mu'amala daga nan na samu kusanci dashi"?.

Zaro ido Meroh tai "ki samu kusanci da wa"? Lallai kam Asabe kice mu tanadi geron waina dan wallahi kinji na rantse miki idan kikai kokarin cusa kanki da masa shishshigi tofa maganar gaskiya wata rana saidai ki jiki a kabari dan balarabe mutum ne mai zafi".

Tsaki Asabe tai tana cewa "duk zafinsa yayi ta banza akwai inda zan kai shi a gama min dashi wanda sai yadda naga dama zan juya shi kamar yadda ake diban ruwa a randa yayin da ake jujjuyata yadda ake so kin gane".

Dariya Meroh tayi "humm Asaballiye tawa na gane mana wato akwai wani abu da kike shirin yi ko akwai wata muguntar da kike son had'awa".

Kai Asabe ta jinjina tana cewa "tabbas Meroh ina son wannan mutumin kuma duk rintsi saina aureshi kota tsiya kota arziki ko yana so ko baya so dan ban ta'ba ganin abu ina so na rasa ba kuma bazan fara akan sa ba a yau din nan basai gobe ba zan fara shiri na domin cika buri na idan naga dama nan da sati sai an daura mana aure dashi" sauke ajiyar zuciya Meroh tayi tana cewa "shikenan 'kawalliye romon gwada mukam 'yan rakiya ne idan abun ya tabbata" "ai ko zai tabbata Meroh ki zuba ido saina baki mamaki kinsan Marka aminiyata ce tasan lungu da sa'kon bokaye ita zan nema" Asabe ta karasa maganar tana sake kallon hanyar da balarabe yabi ha'ki'ka tana kaunar sa bazata cuci kanta ba zata samu mafita ita dai Meroh kallon Asabe kawai take tana tausayawa matarsa domin tasan wace Asabe indai ta 'kwallafa ranta akan balarabe bazata kyale shiba saita samu ta aureshi.

Ganin yadda gabadaya lamarin Ilyah ya cakud'e yasa hankalin Ramatu yai matukar tashi kuma ta kasa gane alhaki ke bin Ilyan na rashin biyayyar da yaiwa Baffah sai kawai ta fara zaton ko Salamatu ce tayi wa Ilyah siddabu dan haka ta dauri niyya ta tafi gurin boka da akai mata kwatance yana cikin wani ba'kin daji abun tsoro tafiya miliyon kasiran kafin ta isko inda yake.

Tsoro ne ya mamaye Ramatu jin wani irin 'kugi da gurnani kamar ta shiga tsakiyar dajin da namun dawa suke rayuwa jikinta ne ya fara rawa jin an daka mata tsawa yasa taci wani uban tuntu'be ji kake kifff tass ta kifa kasa wata tsawar aka kuma sakar mata wanda a wannan karon Ramatu yanke jiki tai tana fad'uwa kasa a sume wata ba'kar mahaukaciyar dariya aka saki saiga wani irin abu me dubu ya dira a gaban Ramatu tare da fara gewaya ta zuwa wani lokaci saiga Ramatu an d'aga ta sama ana jijjiga ta wanda wahala tasa tilas ta farka tana bud'e idonta ganin ta a sama ana majujuwa da ita yasa ta fara ihu tana kururuwa lokaci guda kuma tai tsit ta kame guri daya jin an daina juyata kasa ta le'ko taga shakka babu tayi nesa da 'kasa yanzu ya ita ya zatai tana cikin wannan tunanin taji an fisgota da mugun 'karfi yuuuuu tayo kasa ji kake tim ta daki 'kasa 'kara ta saki tana kiran "wayyo Allah na shikenan na mutu na lalace........................

"Rufa mana baki!!! Me ya kawo ki nan"?.

Jikin Ramatu nata kakkarwa ta mi'ke da sauri tana shirin zubawa a guje aka kuma jawota baya 'kiiiii tasss ta kuma kifawa nan guri ya kaure da kukan jirajirai zuwa wani lokaci kuma aka daina kukan sai dariya tuni Ramatu ta yada kwalin kanta dan gyale da takalmi tuni sun dad'e da fad'uwa.

"Ku kamotaaa ku ri'ko ta yau zamu sha jinin ta ku tatsilo mana ruwan idonta ku zu'ke kwakwalwarta馃槻馃ぃ".

Jin haka yasa Ramatu wage baki cike da tsoro zata kurma ihu aka daka mata tsawa "durkusa anan ki sunkuyar da kanki kasa ki rufe ido idan kikai kuskure zaki hallaka" jiki na 'bari Ramatu ta durkusa tana runtse idonta da 'karfi.

'Dif taji gun yayi shiru kamar babu halitta mai rai daga baya taji iska da guguwa mai karfin bala'i tana kad'awa sai kuma taji saukar abu kusa da ita timmm ga tafiya diff diff anayi jikinta rawa yake sosai zuciyarta na bugawa tana nadama da danasanin zuwan tanan.

"Bud'e idonki kiyi kalloo馃懟".

Da sauri Ramatu ta bud'e idonta ganin wasu kalar ba'ka'ken halittu tai suna yawo jikinsu duk gashi idanuwan su jawur ga babbansu zaune kamar dutse a kafe kato dashi ya gwalalo mata ido ha'koran sa za'ko za'ko.

WASH ALLAH NA GASKIYA FANS NA GAJI 馃槥 TYPING 馃摬 DA WUYA GA AZUMI SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH ZAN DORA MUKU INSHA ALLAHU.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse Jigawa new world new life and new style 馃憣 sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa 馃槣.

MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY

馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮

TYPING 馃摬 {sat, Apr12 11:59AM}

YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

馃拵ME KAMAR SARKI 馃拵





WhatsApp no:+234 8160983083

MRS AL'AMEEN AHMAD CE MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 馃拑.

馃崌 ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU 'YAN UWANA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA馃 FATAN ANYI SALLAH LAFIYA馃崌馃尮.

*****

KAMAR YADDA NA ALKAWARTA CEWA IN ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH DA RAI DA LFY ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI 馃憫 ALLAH YA KAWO MU DAN HAKA KU MATSO MU TAFI TARE DAN YAU ZAMU SHIGA DUNIYAR NISHADI ZAMU KWASHI FARIN CIKI YADDA YA KAMATA 馃槀馃檲馃榿.

Wannan page din naka ne d'an uwa rabi jiki inai maka barka da sallah fatan alkairin Allah ya kai maka duk inda kake kaida ahlinka d'an mutan kanawa.

YUSUF KING__SKEEBOY馃憫馃憫馃帶馃帶 SHATAN RAPPER馃幎馃幎 REAGEA RP RAP DA KUMA HAUSA HIP HOP YAYAN ZAINAB (KALAR CAMERA) 馃摳 DA NA'IM.

馃帳馃幖馃帣锔忦煄ю煄桂煄叼煄葛煄娥煄佛煡侌煄火煄 )(*(*()*)*)( 馃尮 )(*(*()*)*)(

27~AL-BASIR

The all seeing

28~AL-HAKAM

The judge

14~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mutta'kinah.

馃寗 CARICATURE ND WREAK馃寗

Episode 27_28

Kuka Ramatu keyi kamar ranta zai fita cikin wahala da gajiya ga wani masifaffan tsoro daya gama cikata na ganin wannan baka'ken halittun da'kyar take sauke numfashi tayi zaman dirshan a kasa.

"Ku kamotaaa naceeeeh".

Jin abinda wannan mummunan ba'kin dodan ke cewa yasa Ramatu zunbur ta mi'ke a gigice ta fita da gudu a gurin ko waiwaye babu a tunaninta suna binta sai datai nisa sosai ta fita daga dajin kafin ta waigo ganin babu kowa yasa taja burki tana haki ta tsaya tare da goge gumi ta kalli gabas ta kalli yamma har yanzu tana cikin dajin amma tasan duk tsiya ta tsira domin ta baro wajajen wadannan halittun.

Ganin abu tai ya dira gabanta tare dayin girgiza sai taga wannan katon dodon nan muryar shi kamar saukar tsawa yace.

"Hummm saiii yanzunn kika karaso? Barka da zuwa nan ma fadar muceeeeh".

Yana gama fad'in haka taga gurin ya cika da dodannin masu jan ido da gashi ga babban nasu yana mata kallon nama a dafe a kwano hannunsa ya d'aga yana nuna Ramatu sai ji tayi anyi sama da ita suuu zuwa wani lokaci taji tayo kasa taffff sai gata zaune a gaban sa kan wani dutsi na tsafi an kewaye ta tana tsiyayar wuta mai ci sosai a wannan lokacin kasa kuka Ramatu tai ta 'kame guri daya kawai tana jiran mutuwarta.

"Meye ya kawo ki nan, me kika zoyi a gurin muuu? Fad'i muna sauraron ki".

Bakin Ramatu ne ya soma rawa ta kasa magana tsabar tsananin tsoro sai kakkarwa take.

"Kiyi maganaaa mu ba'ai mana shiru anan idan kuma ba haka ba zamuyi farfesun ki"馃榿.

Zaro ido Ramatu tai hawaye na zuba batasan lokacin data d'ora hannu aka ba tana cewa.

"Kuyi hakuri kada ku kashe ni dan Allah.................

Tsawa duk suka daka mata "rufe mana baki kafin mu cinye ki danya yanzun nan fad'i bukatar ki".

Da'kyar Ramatu ta iya saita kanta har lokacin muryarta bai daina rawa ba ta soma magana.

"Dama na kawo 'karar kishiya ta ne tayi wa d'ana Ilyah asiri ya daina sana'a duk kudinsa ya kare baya ta'buka abin arziki shine nace inaso itama yadda bata bari naji dad'i ba kar nata d'an ya jiyar da ita dad'i".

"Mun fahimce ki amma ba itace taiwa d'an ki asiri ba saidai dama mu ba'a neman mu da alkairi zalunci kadai muke sonyi yanzu me kike so ayi mata?.

Dan shiru Ramatu tayi tana tunanin muguntar da zata had'a mata kafin ta d'ago tana cewa.

"Boka so nake ayi mata abinda zaka kamu da jinyar kwanciya wacce har abada bazata 'kara tashi zaune ba dukiyar da take ta'kama d'anta yana dashi ta 'kare a wajen nema mata magani shine abinda nake so".

Dariya duk gurin suka kama sunayin wata wasu irin maganganu.

"Yadda zaki aikin ki bari sai 'kafa ta dauke cikin dare kowa yana barci zaki fito bayan gari da ruwa ki zuba magani a ciki saiki wanka da ruwan a gurin ga wani d'an gatari dashi zaki tonon da zaki binne maganin saiki kira sunan Salamatu sau uku kina kafta gatarin a kasa idan kin gama saiki mi'ke ki koma gida canma kije kiyi haka ki tababata babu wanda ya ganki to zaki nasara shikenan kin gama komai burin ki zai cika amma ki sani idan kika fara aikin mu babu dainawa duk randa wani ya kamaki zaki mutu idan kikai kuskure zaki mutu kuma ba'a mayar mana da aikin mu sannan abinda kika aikatawa wani ko wata rana zai dawo kanki".

Zaro ido Ramatu tai kamar zai fito waje tace "zai dawo kaina a'a boka na fasa na hakura zan canza wani guri...........

Marin da aka kifa mata ne ya hana ta karasa abinda take son cewa har ha'korin ta daya Saida ya fita cikin mamaki taga katon dodan ya dauka ya sashi a bakinsa ji kake karass kass yana taunawa kamar ya samu kwakwa yana ya bud'e bakinsa saiga wata tsuntsuwa ta fito ba'ka wuluk tazo ta sauka a gaban ta tana aje mata wasu abubuwa kafin ta koma wannan ha'korin nata daya fita.

Ihu Ramatu tai wanda hakan ya baiwa ha'korin dama komawa bakinta ya dasu

21 / 67