Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 67

51K to 54K   out of 200.4K words

to saidai ka fad'a min amsar tambayar danai maka meyasa kaiwa Lami fayd'e"? Zaka fad'a ko saina fasa ma kai"?.

Ganin ya cakumo shi yana dunkule hannunsa zai kai masa naushi yasa jikin Tanko na rawa bakinsa na jini yace "zan fad'a dan Allah kamin hakuri wallahi zan fad'a maka gaskiya".

Sakin sa Habu yai yana kallon Sabi'u yace "kasan Allah yaya Sabi'u bazan 'kyale su fita nan cikin hayyacin su ba indai basu fad'i gaskiya ba saina dau fansar abinda sukai mata kamar yadda kai ka fad'a a kofar gidan mu dan na jika" ya karasa maganar yana kallon Tanko dake ta goge jinin da ya 'bata masa fuska.

'Durkusawa gaban sa Habu yai yana sha'kar wuyan rigarsa 'kara Tanko yana cewa "Habu zaka yanka min wuya dan Allah ka sake ni zan fad'a maka".

Habu bai sake shiba saidai ya sassauta ri'kon da yai masa fuskarsa a d'aure tamau yace "ina jinka".

Jikin Tanko na 'barin tsoro bakinsa na rawa ya fara magana "dan Allah Habu kuyi hakuri ku yafe min na aikata muku kuskure tabbas nine naiwa Lami fayd'e ranar amma dan girman Allah ku dube ni da idanun rahma ku yafe min"..........................

Takaici ne ya rufe Sabi'u yana kallon Tanko yace "kenan zargin mu ya tabbata kaine silar mutuwarta me tai maka zaka dau alhakin ta"?.

Muryar Tanko na rawa yace "babu abinda tai min kawai naji haushi ne saboda tace min bazata aure ni ba na makara shine abun ya 'kona min na tare ta a ranar na mata fayd'e ba da niyyar kasheta na mata haka ba wallahi da nasan zaka mutu bazan yi mata ba kawai ganin ta gane ni yasa na kasa barinta dan karta tona min asiri har saida naji bata motsi ku gafarce n.....................

Bai karasa ba Habu ya d'auke shi da mari yana hankad'a shi ya mi'ke ransa a 'bace ya goge hawayen fuskarsa yana kallon Sabi'u yace "wallahi tallahi bazamu yarda ba yaya sai munkai 'kararsu gaban hukuma dole ne a yanke musu hukuncin daya dace dasu".

Kai Sabi'u ya jinjina yana cewa "muje" fita sukai daga gidan yayin da Mudi ya tashi a guje yana zuwa gurin Tanko dake kwance yana numfashi ya d'ago shi yana mikar dashi tsaye yace "sannu abokina gaskiya habu ya cika 'kasurgumin mugu kaga yadda duk ya sauya ma kamanni Allah ne yai da sauran kwanan ka a gaba da yanzu ya kashe ka" shidai Tanko shiru yai ya kasa magana cikin azaba da'kyar yake jan kafa suka fita daga gidan.

Bayan fitar su Habu kai tsaye gida suka nufa a kofar gidan suka samu Baffah zaune yayi ba'ki dan haka basuyi masa magana bayan sun gaisa suka wuce zuwa ciki suna jiransa ba'a dad'e ba shima ya shigo tare da zama kan wani 'karamin dutsi dake kafe a wajen kofar d'akinsa yana kallon yadda yanayin ya sauya yasan ba kalau ba akwai matsala.

"Sabi'u Habubakar me ya faru nagan ku haka ko kun samu wani bayani ne".

Kai Sabi'u ya d'aga "eh Baffah samu ma na ha'ki'ka Habu ya baka labari".

Maida kallon kan Habu Baffah yai yana cewa "Habubakar meya faru ne na ganku cikin fushi musamman ma kai"?.

Zazzafan numfashi Habu ya sauke yana cewa "wallahi Baffah baza mu yarda ba sai munje kotu wai tsabar zalunci ashe wannan tsinannan ne Tanko ya mata fayd'en bamu sani ba gashi yanzu da yaji wahala ya fad'a da bakinsa harda dan kada takai labari yasa bai 'kyale taba saida ta daina motsi".

Runtse ido Baffah yai jin abinda Habu ke cewa basu ankara ba sai ganin hawaye sukai sharr yana zuba a idanun Baffah tabdijan tashin hankali wanda ba'a sa masa rana hawaye fa suke ganin a idanun Baffah a zabure cikin tsananin fushi habu ya mi'ke yana cewa "wallahi bazan kyale Tanko ba Baffah saina kashe shi tunda yai silar zubar hawaye a idonka abunda ban ta'ba gani tare dakai ba a rayuwa ta sai yau" juyawa yai zai fita muryar Baffah da alamun kuka yace.

"Habubakar dawo kada ka koma gurin su na barwa Allah shine ya halicce mu sannan shike da iko damu zai sakawa Lami bazai kyale shiba Tanko ya cuce bazan ta'ba yafe masa ba har ranar komawa ta ga ubangiji" ya karasa maganar kukan nasa na sake fitowa.

'Durkusawa gaban sa Habu yai yana kifa kanshi a jikin Baffah kawai shima ya fara kuka wanda Sabi'u da sauri ya rungume su shima yana zubda hawaye suna wannan hali sukaji sallama yaro.

"Wai Baffah yana nan yazo inji Isubu me gari yana nemansa".

'Dagowa Baffah yayi yana kallon yaron cikin ajiyar zuciya yace "kace masa gani nan ina zuwa" yaro na fita Baffah ya mi'ke yana daukar buta ya wanke fuskarsa.

Ran Habu a 'bace yace "wato 'kara suka kai gurin me gari? Aiko yau saina tabbatar basuyi kwanan gida ba wallahi saina d'ebo musu hukuma muje Baffah.

Baffah bai iya magana ba kawai yayi gaba ne suka bishi a baya har gaban me gari suka samu guri dam ya cika da jama'a ma'kil ana ta hayaniya sallama Baffah yai yana zama cikin mutunci suka gaisa da kowa.

Kallon sa me gari yai "Baffah kasan dalilin kiranka?.

Kai Baffah ya girgiza "a'a ina fata lafiya"?.

Cigaba me gari yai "eh lafiya ba lafiya malam Balah ne ya kawo 'kararka cewa Habu da Sabi'u sun daki d'ansa Tanko harda rauni sukayi masa ga sun zubar masa da ha'kora guda biyu haka ne"?.

Kallon su Sabi'u Baffah yai ganin basu musa ba yace "gasu nan me gari ka tambaye su ni ban sani ba".

Kafin me gari yai magana Balah yace "a 'kwarai ka turo suwa adamu dukan mutuwa sannan kace wai baka san komai ba wallahi bazan yarda ba sai munyi shari'a dakai" gun me gari ya juya yana cigaba "me gari nifa ba cewa nai a tambaye shiba kuma ba sasanto naso ba idan bazaka iya ba zan kai gaba a bimin kadin dukan da sukai masa".

Shiru Baffah yai yana kallon Balah cikin mamaki wato d'ansa ya aikata wannan mummunan zunubin amma tsabar tsaurin ido har ya samu bakin magana.

Hayaniyar da suka kaure tsakanin Habu da Balah ne ya dawo da Baffah daga tunanin da yake yana cewa "Habubakar kayi shiru wannan ba zancen ka bane"

Shiru yai Balah dake binsa da kallo yace "kai mara kunya ba dakai nake yi ba da ubanka nake magana ba hurumin ka bane" a harzu'ke Habu zai magana Baffah ya dakatar dashi, mi'kewa Habu yai yana fita a wajen Sabi'u yaso binsa amma ya 'kyale domin yana son jin rainin wayon da Tanko yaje ya shiryawa Balah suna zaune mutane na kallo sai shari'a ake bugawa Tanko na rantsuwar bashi yaiwa Lami fayd'e ba kawai sai jin jiniyar mota sukai tazo tayi parking a gurin Habu ya fito fuska a had'e.

Kowa zaro ido waje yai suna bisa da kallo kai tsaye yaje ya cakumo Tanko yana fito dashi wani d'an sanda dake tsaye yace.

"Barshi aikin mune" yana kallon Tanko yace "your under arrest 馃檴 malam munzo kamen ka" ya karasa maganar yana d'ago ankwa, zaro ido Tanko yai jikin sa na kakkarwa Balah daya taso da gudu ya ce.

"Wallahi yalla'bai bazan bari ka tafi min da yaro ko'ina ba bayan sharri akai masa".

Wani kallo d'an sandan yai masa wanda yasa Balah matsawa da sauri ya koma gefe yana gani suka sa Tanko a mota shida Mudi habu da Sabi'u suka shiga mota tabar gurin da sharad'in kada wanda ya biyo a yau sai gobe.

Zage zage Balah keyi ko gaban sa baya gani ya tafi gida takalmansa a hannu yana shiga ya soma kwalla kira "Delu ke Delu kina ina fito ga ba'kar rana tazo mana yau bankad'a ta same mu".

Da sauri ta fito daga d'aki tana cewa "malam lafiya ya na ganka haka ina Tankon".

Zama Balah yai akan tabarma yana cewa "Tanko yau kwanan bayan kanta zaiyi d'an iskan yaron nan ne Habubakar ya d'ebo masa 'yan sanda sun tafi dashi da abokinsa d'an gidan marigayi malam Ya'u suna can".

'Dora hannu Delu tai aka "mun shiga uku wai me ya had'a sune"?.

"Yo me ya had'a su sharri sukai masa da yake basu gaji arziki ba".

"Sharri kuma malam wani abu ne ya faru"?.

"Eh wai yarinyar nan Lami data rasu cewa saboda anyi mata fayd'e kuma shi saurayin tane duk garin suka rasa wanda zasu la'kabawa sai shi wai shine ya mata".

Ido waje Delu "innalillahi sharrin da zasuyi masa kenan aiko wallahi basu isa ba baza mu yarda".

'Kwafa Balah yai "taya kuwa zamu yarda jira nake gari ya waye ai na tafi gurin yan sandan ayita ta 'kare duk wanda yakai 'kararka aiya gama tozarta ka".

"Amma gaskiya Baffah baisan halacci ba duk irin son da Adamu ya nunawa Lami bai gani ba shine yasa 'ya'yansa su dake shi bayan hakan ma bai ishe Shiba harda d'ebo masa 'yan sanda" Delu ta fad'a tana yin hanyar kofar lungun matar Tanko dan ta sanar mata haka Balah ya zauna shi kadai sai masifa yake duk wanda zai wuce yana jinsa.

Bayan sun koma gida Baffah da fad'a ya kama Habu "haba Habubakar meyasa kayi haka tsakani da kunya ka d'ebo masa 'yan sanda da ka kyale kawai ni zan iya hakura Allah ya saka mata".

Kafin Habu yai magana Sabi'u yace "wallahi Baffah habu yayi daidai gara daya d'ebo musu dan koda ace abinda muke dashi zai 'kare matukar za'a hukunta shi to zanyi komai".

Gyara zama Habu yai yana cewa "to ai Baffah idan ba hakan akayi musu ba zasu sake marmarin yiwa wata yarinyar anan gaba ba sun san tsakani da kunyar su suka aikata mata rashin d'a'a bayan haka taya munsan shine zamu kyale shi aida bamu yafewa kaimu ba abinda muke bukata Baffah ka taya mu da addu'a Allah ya bamu sa'a idan mun shiga kotu".

Babu yadda Baffah ya iya haka ya bisu da addu'a kamar yadda suka ce yana musu fatan alkairi duk inda ka shiga a garin kuwa gulmar ake cewa ashe Tanko ne yaiwa Lami fayd'e shiyasa Habu ya d'ebo masa'yan sanda sai tsine masa ake saboda kowa yasan zai aikata halinsa ne.

Abun da ya baiwa su Habu mamaki a kotu 'kememe Tanko ya'ki kar'ban laifin da ake zargin sa yace baisan zancen ba sharri sukai masa iya 'kulewa ya 'kular da Habu ji yake badan a gaban alkali suke ba babu abinda zai hana sha'ke wuyan Tanko harsai yaga ya daina motsi ya mutu daya rabu dashi".

Anyi gwagwarmaya ansha matukar wahala saida akai da gaske sannan Tanko ya amshi laifin sa azaba tasa yai bayani aka sake tambayarsa da jiddadawa shine ya mata fayd'e shine ya mata fayd'e ya zamo silar mutuwarta ya kuwa amsa eh shine da taimakon abokinsa Mudi dan haka aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari shekara ashirin da biyar Mudi shekara biyar tab a take Balah ya yanke jiki ya fad'i a sume saboda d'imuwa da tashin hankalin abinda yaji Tankon ya fad'a mugayen halaye marasa kyau wanda bai sani ba a gurin ya suma hawan jinin sa ya tashi sai asibiti aka kaishi haka su Habu suka dawo gida ransu fari tas ko yanzu sun cika burin su tunda an yanke masa hukunci mafi tsauri.

Satin Balah uku a asibiti ya rasu Tanko bai sani ba domin yana can kuma gurin da yake mafi tsananin horo ba'a zuwa koda a shekara sau d'aya ne balle yasa rai zaiga 'yan gida haka kullum yake fama da aikin wahala da horo me tsanani.

Lokacin da suka koma gida a kofar d'akin Ramatu sukaga Ilyah zaune ya karkace sai yanka loma yake kamar wanda yai shekara baici ba zama sukai Baffah na cewa "kai Ilyasu idan ka gama ina son magana dakai" bai d'ago balle yasan mutum ke masa magana duk da yasan irin kokarin da su Habu sukai akan case din Lami amma yai banza daya gama ma yana wanke hannu yai hanyar kofar gida da nufin ficewa tab kamar wanda ya watsawa Habu ruwan wuta haka ya mi'ke zunbur yana shan gaban ransa a had'e yace.

"Wai meye haka kakeyi Baffah nefa ke maka magana".

Kallon kallo suka fara kafin Ilyah ya kuma gegewa zai wuce fisgoshi Habu yai yana hankad'a shi sai gashi guruf ya kifa a gaban Baffah a fusace Ilyah ya juyo yana kallon Habu dake tsaye bayansa yace.

"Ni ka hankad'a haka? Habu aiko wallahi sai kayi Dana sani".

Wata uwar harara me zafi Habu yasakar masa yana cewa "wannan shine fad'arka sau ba adadi na saba jin haka a bakinka amma banga ranar da zata zo nayi nadama ba a rayuwa ta domin sani zan gama da duniya lafiya bani da bakin iyaye a jikina".

Cikin 'kunan rai Ilyah yace "kuma waye me bakin iyayen".

"Ina wani bayan kai, ko nayi karya"?.

Kafin Ilyah yai magana Baffah ya katse su "ku dakata magana nace zamuyi ba fad'a ba wannan shashancin bai kamata ba zauna habu" zama yai suna aikawa juna harara Baffah ya soma magana.

"Iliyasu nasan kasani cewa ga abinda yan uwanka suke na fafutikar gano wanda yai silar Lami har Allah ya basu sa'a asirin su ya tonu amma baka ta'ba zuwa ka tambaye mu me muke ciki ba gashi kaji an yanke musu hukunci duk da haka bakai hankalin da zaka tare ni da wata magana ba meyasa"?.

Tashi Ilyah yai yana karkad'e jikinsa yace "to Baffah ina ruwana me kuwa zance muku dama ni na sasu wannan matsalar suce gani sukai zasu iya Lami dai ta riga ta mutu ba dawowa zatai ba gashi kunzo kunata bata zaman ku da 'yan gari nikam babu abinda yai min zafi kada ku sake sani cikin safgarku".

Yana kaiwa nan yai waje shiru Baffah yai Sabi'u daya dafe kai yace "kayi hakuri Baffah dan Allah ka daina sa damuwar Ilyah a zuciyarka kada wata rana ya d'ora maka hawan jini".

"Umh to mezance Sabi'u Ilyasu ya fita daban a cikin 'ya'yana saidai Allah ya shirye shi" Amin Sabi'u yace Habu kam ba'kin ciki da takaici sun hana shi magana kawai mi'kewa yai ya shige d'aki ya kwanta barsu a waje suna ci gaba da tattaunawa.



Tun Baffah yana 'boye musu jinyar dake damunshi har tazo ta bayyana hankalinsu yayi matukar tashi cikin gangarawa suka daukeshi zuwa asibiti kamar bazai rai suna isa aka tura su emergency saboda ganin halin da yake ciki.

Haka suka wuni likitoci na kansa abun har tsoro ya basu sai bayan sallar magriba babban likita ya kira su zuwa office din sa bayan sun zauna ya fara yi musu bayani.

"Nayi mamaki lokacin da nake duba mahaifin ku yana da zaratan samari kamar taya kuka bari har jinya taci 'karfinsa baku kawo shi asibiti ba yanzu dai mun samu an ceto rayuwar sa insha Allahu zai samu lafiya amma dan Allah nan gaba ko ya kuka ga wata 'yar matsala ku taho asibiti".

Sauke ajiyar zuciya sukai cikin jin dad'i sukaiwa likita godiya anan suka kwana iya Salamatu ce ta biyosu ta kawo musu abinci amma banda Ramatu da Ilyah sai dare sosai ta tafi washe gari ma da wuri tayo abun karyawa tazo kasa hakuri Habu yace.

"Waini dan Allah su Ilyah basu san Baffah baida lafiya ko wulakancin nasu ne dan su nuna basu maida shi komai ba".

Cikin yanayin damuwa Salamatu tace "sun sani bansan me yasa basu zoba".

"Ai gaskiya mutanen nan lamarin su da gyara saidai Allah ya ganar dasu".

Mi'kewa Habu yai yana cewa "bari naje gidan" da sauri yasa takalmansa yana ficewa daga asibitin ya tari mashin har kofar gida cewa yai jiransa yanzu zai fito su koma.

Yana shiga yaga Ilyah gaban murhu yana babbakar kan rago wato dai shi wannan rai da rai yana cikin cin nama kamar jikan sarkin mayu karasawa yai yana cewa.

"Ilyah ka kyauta kenan"?.

Da sauri Ilyah ya juyo ganin Habu tsaye yasa batare dayai magana ba ya maida hankalin sa kan aikinsa dan yasan kwanan zance bazai wuce akan jinyar Baffah bane indai haka ne kuwa ko a jikinsa.

Ganin yai banza dashi yaci gaba "dakai fa nake Ilyah yanzu tsakani da Allah kayi daidai kenan Baffah mahaifin kane amma baida lafiya kana gani muka tafi bakace zaka bimu ba gashi da gari ya waye kaga bamu dawo ba mezai hana ka kaje kaga halin da yake ciki ko baza ka zauna ba sai kayi burus".

Idan dutsi ko bishiya na magana to Ilyah ma yayi kamar ba mutum haka ya dauke kai yaci gaba da aikinsa mamaki ne ya kama Habu kawai ya sake baki ya tsaya kallon iya gudun ruwan ilyah, harya gama ya 'bare kan babu wanda ya sake magana saida ya mi'ke zaije ya wanke yace.

"Kai fa Habubakar babu inda zanje garama kabar 'batawa kanka lokaci kaje ka tafi dan babu inda zanje kuma banga wanda ya isa yasa nayi abinda banyi niyya ba dama Baffan wani abu yake ban dazan damu da jinyarsa yaje can ya 'karata馃檰馃槺馃槰".

Wucewa yai yana zuba ruwa ya fara wankewa a fusace Habu yaje yai bol da kwanan da Ilyah yake wanke kan ganin hakan ma bai huce ba dauka yai yana tumurmusa shi a kasa karshe ya jefa shi a cikin kwata kafin ya juyo yana cewa.

"badai akan wannan tsinannan kan bane gashi na jefa a kwata sai naga ta tsiya".

Da gudu Ilyah yazo ya kama Habu da kokawa nan fad'a ya kaure jin hayaniya yasa Ramatu fitowa tana cewa.

"Meye hakan Ilyasu ina kan ragon yake"?.

Ran Ilyah daya gama 'baci bai kalli Ramatu ba yace "gashi can wannan mitsiyacin ya jefa a kwata".

Zaro ido Ramatu tai tana kallon gurin tace "kwata? Aikam ganin yadda yai dumu dumu yasa Ramatu fasa 'karar takaici tana cewa "wayyo Allah na amma wallahi Habubakar anyi mugun mutum wato saboda ba'kin ciki shine ka jefa mana nama a cikin kwata aiko saika biya".

Kallonta Habu yai batare daya amsa mata wancan fad'an da

18 / 67