Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 67

72K to 75K   out of 200.4K words

d'akin Bara'atu ta soma bukawa da karfi tana cewa "ke tsinanniya bunjinjimar asara fito ai ba barci kika dawo yiba zaki bud'e ko saina karya murfin kofar na shigo da kaina na fito dake na miki dukan tsiya yar fatararru" cikin takaici Bara'atu ta bud'e kofa tana kallon Ramatu dake tsaye zatai magana Ilyah ya fito daga d'akin maimuna cikin rashin jin dad'i yace.

"Wai dan Allah babah me yasa kike haka ne da asubar farin nan me zatai miki kika zo kina buga mata kofa duk makota na jinki".

Kansa ta koma "dambun ubanka zatai min asararre waini Ilyah kodai bankad'add'iyar matar nan asiri tai maka ban sani ba babu dama nayi magana saika mayar min bakaso a fad'i laifinta nuna Bara'atu tai da yatsa amma Allah ya tsinewa uwarki kandiya dan komai silarta ne itace ma'kasudin komai bari gari ya gama wayewa wallahi ko bari su karya cikin dad'in rai bazan ba sainaje na 'kaddamar musu bala'i iri iri dama ai tasan hadina da ita ta iya d'ebo ba'kin ido tazo a gantsara mata abinci taci zakuci gwafar ubanku ne daga ke har tsigalgalar uwar taki".

"Dan Allah babah kiyi shiru wannan fa zubar da girma ne" Ilyah yai maganar ransa a 'bace.

"Kai zanci malafar ubanka idan bakai min shiru ba so'ko'kon banza sakalin asara wanda kare ya lashewa zuciya kayi asara tunda harka za'bi matarka akan ni da nake uwarka".

Had'e rai Ilyah yai "ni bance miki na zabeta akanki ba fad'ar kice kawai daga naga kinyi ba daidai ba nayi magana gaskiya abinda kike bakya kyautawa wannan fa ba neman girma bane".

Caraf Ramatu tace "dama nace maka ina neman girma ne? Karta girmama nin mana taga yadda zanci 'kashin ubanta tasan karon mu da ita ai abin baya mata dad'i" Ilyah bai sake magana ba ya kalli Bara'atu yana cewa "koma d'aki ki kwanta" da sauri Bara'atu ta shige cike da tsoro ta rufo kofa hararar sa Ramatu tai "humm Ilyasu kayi asara wallahi kaji jiki da ina da wani d'an bazan zauna a gidanka ba saidai ka nemi wata uwar badai niba" shikam tari da bai kama shiba bai sake ce mata uffan ba ya juya shima yana komawa d'akin amaryarsa yayin da Ramatu taci gaba da balbali a tsakar gida ita kadai taja kujera ta zauna sai zazzaga fad'a take bakinta har kumba yake ta'ki yin shiru duk ta dami jama'ar anguwa sai Allah wadai suke har akai assalatu aka shiga masallaci bata tashi ba balle tai alwala da sallah saida gari yai haske sannan tayi niyyar yi.

Habu ne zaune yayi tagumi gaban Salamatu dake kwance sharkaf kamar gawa Sabi'u na gefensa sunyi shiru babu mai cewa uffan shigowa d'akin Rakiya tai da sallama cikin sanyin jiki tace "ya jikin nata"? Kai Sabi'u ya d'aga "da sauki Rakiya" zama tai ta wajen 'kafafun Salamatun tana cewa "amma me gida tunda likitoci sunce ba ciwon asibiti bane mezai hana muyi na gargajiya kaga ciwon gaba yake 'kara yi kuma kalli wani abun tsoro yadda jikinta yake 'kai'kashewa kalli yadda fuskarta ta koma kallonta kamar bana mutane ba" ta karasa maganar tana fashewa da kuka.

Kallon Sabi'u Habu yai cike da damuwa yace "yaya Sabi'u gaskiya wannan ciwon na babah ba 'kalau ba abun da tsoro tunda kaji likita yace a dawo gida ayi na gargajiya lallai akwai abun dubawa ga kuma kullum sai anyi mata 'karin ruwa amma yan awanni ace sun tsotse wanne irin abu ne wannan kodai mayu ne"? Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai ganin yadda bakinta ke kakkarwa ya kalli Habu yana cewa "nima tunanin dake raina kenan saidai bamu tabbatar ba na samu malam Zayyanu jiya akan batun yace yasan wani mutum mai maganin hausa duk abinda ya shige duhu indai anje wurinsa insha Allahu ana samun waraka dama jira nake alhaji Hamidu ya dawo daga saudiyya kud'ina da yake gurinsa ya bani sai mu tafi" gyara zama Habu yai yana cewa "ba matsala yaya Sabi'u indai maganar kud'i ba damuwa mudai lafiyar ta muke bukata bari naje gida na dawo saimu tafi tunda kaga yanzu na iya motar dana sayo ba haya nake bada itaba sai muje" mikewa Sabi'u yai shima yana cewa "to bari naje gurin malam Zayyanun yamin kwatancen garin kafin ka dawo" Rakiya ya kalla "ki jirani a gurinta ina zuwa" to tace yayin da suka fito tare Sabi'u yai gurin da zai sami malam Zayyanu Habu kuma yai gida.

Zaune ya sami Saude da amayarsa A'i dan Binta kam tana gida wanka ganinsa da damuwa yasa Saude cewa "lafiya meya faru naganka haka"? 'Dan tsayawa yai yana kallon Asma'u dake zaune gaban A'i tana mata kitso yace "eh lafiya babah zamu kai gurin magani wani gari yanzu" "subahanallahi sake tashi jikin yai"? Wucewa habu yai zuwa d'akinsa yana cewa "ai dama baya sauka kullum a tashe yake" shiru sukai cike da jimami harya fito Saude tace "bari muje mu gano ta A'i bar kitson nan sai mun dawo" mikewa suka kowa na dauko hijab suka fita motar na waje yace su shiga tunda shine zai jasu shiga sukai duk inda ya gifta da ido ake bin motar masu hassada nayi masu tayashi murna nayi saidai yan ba'kin ciki sunfi yawa a sanda sukaje al'ajabine ya kamasu ganin yadda kumfa ke fita a bakinta sai mummurd'ewa take tana surutai duk zaro ido sukai jiki na rawa musamman A'i da sauri tai baya Dan akwaita da tsoro cicci'bota habu da Sabi'u sukai suna fita da ita wajen motar da'kyar suka tan'kwasata suka sata a cikin kafin suka shiga habu na baarwa Saude sakon yadda zasuyi amfani da kayan abinci kafin suka dau hanya.

Dalah na zaune Balarabe ya shigo da kaya cikin leda a hannunsa ya aje mata ba magana d'agowa tayi a damuwance tana kallon sa kamar hawaye zai zubo mata dan tasan ba kalau ba yanzu gabadaya ya canza ya zama wani iri tace "wannan meye a ciki"? Bai kalleta ba yace ki bud'e ki gani mana ba kina da ido ba"? Bud'ewa Dalah tai ganin kayane yasa tace "na maye"? Kai tsaye Balarabe yace "na fad'ar kishiya ne kin gane aure zanyi Asabe zan aura dan haka duk wani shirginki da kika san yana wancan d'akin ki tattare zan gyara" sauke zazzafan numfashi Dalah tai tana cewa "shikenan Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin inda gaske kike" ya fad'a yana Mi'kewa zai fita sai kuma ya tsaya tare da cewa "nayi gidan Asabe kada ki dafa abinci dani" kafin Dalah tai magana Indo tace "baba ka taho min da biskin" "da uban biskin zan taho miki dashi tsohuwarki ta baki kud'i kije shagon Habu ki sayo ni bani da kud'i" yana fad'in haka yai waje yabar Dalah tana sharar 'kwalla Innalillahi wa inna ilaihi raji'un tun ba'aje ko'ina ba Balarabe ya fara canzawa ina ga yayi auren kenan.

Tafiyar su habu da kwana biyu Rakiya ta haihu gashi ba waya a tsakani balle ta fad'a sai wata tsohuwa ce daga ma'koftansu take kula da ita da jaririn mutane nata zuwa barka ranar suna itace ta za'ba masa tunda Sabi'un bayanan cikin dabbobin da yake kiwo aka yanka mata raguna biyu Binta ma tazo bikin sunan saboda tayi wata biyu jira take Habu ya dawo daga tafiya ta dawo d'akin ta gashi dama Bashir ya bar gida ya tafi dutse karatu sai lokaci lokaci yake d'an zuwa gida su gaisa yana can yayi gidansa da matarsa harda d'an sa Ahmad.

Suna zaune anata hira irin wacce akeyi idan an had"u a gidan biki Dalah da shigo da atamfar biki a hannunta suna gaisawa ta shiga d'akin Rakiya domin 'kawarta ce sosai tun suna yara sakamakon zafi yasa Dalah ta fito waje tana zama cikin mutane a 'kar'kashin bishiyar badalar dake tsakiyar gidan yafendo ce ta kalleta tana cewa "sannu 'yarnan kinji Allah ya miki tsari da sharrin wannan muguwar mace Asabe da mijinki yake kokarin aura" zaro ido waje Hajjah tai "ke wacce Asaben amma dai ba Asabe ta bayan layin muba matar da tai zaman logus ko lagwas (Lagos) yake na manta sunan garin ai itace zai aura"? Kai yafendo ta d'aga "eh itafa" har 'kwaruwa Hajjah take waje tafa hannu da cewa "Innalillahi amma gaskiya Balarabe baiyi zabin mace ta gari ba na taya ki ba'kin ciki Dalah Allah ya tsare ki daga sharrin ta dan wannan matar kwalba ma haka ta ganta" "aike dai kawai bari dan ko wancan mijin nata ma ba mutuwar Allah yai ba kashe shi tai haka mutane suke cewa dama saboda dukiyar sa ta aure shi* "oh ni kinji irin abun ko? Kuna zamanku lafiya zai yayo muku bala'i ke dashi" ita dai shiru tai kawai tana sauraron su yayin da suke tsinka mata zuciya da maganganunsu amma ya zatai bayan ha'kuri da addu'ar Allah ya tsare ta da tarkon Asaben.

Batun su habu kam sunje gurin me magani mutumin ya matukar 'kwarewa a iya cire aljanu komai taurinsu amma me abun ya bashi mamaki babu aljanu jikin Salamatu kuma ba mayu bane yayi iya bakin kokarin sa amma baiga komai ba dan haka shawara ya basu cewa kawai saidai ai mata sauka ko Allah zaisa a dace damuwa da tashin hankali baisa sun iya ce masa 'kala ba sai shine ya fahimci suna wani hali na d'imuwa ya taimaka musu amma dai labarin yana nan yadda yake babu sauki ko sasssuci a jikin Salamatu sunfi wata yana abu d'aya karshe yace sunyi hakuri su koma gida su sake jarrabawa zuwa gurin wani malamin ko zasu dace shikam ya gaza haka suka tattaro suka dawo gida jiki a sanyaye mutane sai zuwa dubota ake harda masu kuka ganin yadda ta koma kamar ba mutum ba ta wani rame halittarta ta canza.

Wata biyar tsakani Salamatu tabar duniya馃槬 wanda kowa yana mata fatan mutuwa ta zama hutu gareta madadin wuyar da take sha lokacin da Ramatu taji mutuwar cewa tai "uhm kace yau Salamatu da shan duka a kabari馃檴" to waiwaye ance adon tafiya ne amma fa ta tuna me wadannan halittun suka ce mata koba dad'e koba jima abinda tai zai dawo kanta nanfa tashin hankali ya same ta ta ri'ka gurza kuka a gidan mutuwar nan kowa yayi zaton akan Salamatun ne ashe ita abinda ke damunta dabam ko gida data koma 'kin cin abinci tai har dare saida Ilyah ya shigo Bara'atu take fad'a masa ya shiga d'aki ya ganta zaune tayi tagumi mamaki ne ya kama shi yaushe rabo yaga Ramatu a haka ai harya manta zama yai yana sake kallon ta da karantar meke damun ta yace.

"Babah lafiya me akai miki"? Jin tashin murya yasa a gigice Ramatu ta tashi a guje tana fad'awa saman katifa tare da jan bargo ta lullu'ba muryarta na rawa tace "na shiga uku na lalace wayyo Allah na dan Allah kuyi hakuri wallahi ba a son raina bane dama fa nace muku na ha'kura kune kuka 'ki wallahi ba ruwana nidai ku 'kyaleni".

Tsananin mamaki ne ya kama Ilyah wannan kuma lafiya maganganun me take haka kamar ta samu ta'bi yaye mayafin data lullu'ba yayi yana cewa "babah nine fa me kikeyi ne haka"? Jin tashin muryar Ilyah yasa ta bud'e ido tana kallon sa tare da sauke ajiyar zuciya tace "Ilyah kaine aina dauka wadannan tsinannun ne" da alamar tambaya yace "su waye tsinannu"? Dan shi ya dauka da Bara'atu da Maimuna take sai kuma yaji tace "wasu tambad'add"un halittu ne saida nace musu bana so na ha'kura amma suka 'ki" Ilyah jiyai hankalin sa ya sake tashi gashi ta kuma lumar dashi ya kasa gane inda ta dosa........................

Tunanin sane ya katse jin ta fasa ihu tana cewa "gasu nan sun shigo ka gansu nan da yawa idanuwan su yayi ja kallona suke wayyo Allah zasu kama ni zasu tafi dani" habawa a guje Ilyah yai tsalle ya shige bayan murfin kofar d'akin cike da tsoro daidai su Bara'atu sunzo ganin yadda Ramatu take 'barin kwanuka duk ta hargitsa d'akin yasa mamaki suma ya kamasu saidai da yake sun san rigimammiya ce zata aikata fiye da haka ma yasa suka tsaya kawai suna kallon ta sai susa take tana yagar gashin kanta ganin takalmin Ilyah a kofar d'aki yasa Bara'atu cewa.

"Kana ciki ne"?.

Jin anyi magana yasa Ilyah kallon Ramatu idanuwan ta sun sauya kala a tsorace ya sand'a zai fice yuuuu tayo kansa tana cewa "ina kuma zaka je bazaka tsaya muyi wasa ba zonan taho muyi rawa" ganin ta kawo masa rifka yasa yai wani irin ihu tare da dira tsalle sai gashi a waje da mugun 'karfi ya zuba a guje ya fad'a d'aki yana banko kofa kaiii suma aguje suka shige d'ayan d'akin yayin da Ramatu ta d'auki ta'barya tana dukan kofar kamar me karfin doki "dan uwarku bazaku bud'e min kofa ba matsiya wato dodo kuka mayar dani tsinannu wallahi gobe sai Ilyah ya sake ku sai kun bar gidan bankad'add'u 'ya'yan talakawa" dukan kofar take da karfi suna jinta kowa jiki na 'bari haka ta kwana tana abu daya har asuba sannan ta koma d'akinta ta sheme ta kama barci babu wanda ya iya fitowa a cikin su duk da sunji shiru an rasa me wannan jarumtar saida suka ji shirun har yayi yawa sannan suka bud'e kofa suna le'ke ganin dai bata nan yasa suka fito suna 'kwan'kwasawa Ilyah shiru yai yana jinsu yay kamar ya mutu馃ぃ saida sukai magana ya tabbatar sune sannan ya bud'e shima ya fito yana zazzara ido ya had'a gumi shir'bim sauke ajiyar zuciya yai yana kallon kofar d'akin ta yayi 'kasa da murya yana cewa "ina take"? suma kallon kofar d'akin sukai Maimuna tace "kila tana ciki" tura ta Ilyah yai "jeki gano馃槀" tirjewa Maimuna tai tana had'e rai tace "ba kaine namiji ba kaine ya kamata ka gano" shiru yai alamar bazai iya ba sai kuma ya kalli Bara'atu "ko ke zaki gano mana"馃ぃ? Itama baya taja tana cewa "a'a wallahi bazan iya ba ni dama jinin mu bai had'u ba bari ma kagani sallah zanje nayi gashi har rana ta fito muna kulle kamar wanda mukai lefi" tana barin gurin itama Maimuna tabi bayanta dole tasa Ilyah tafiya a hankali yana d'auke sau yaje ta window ya le'ka ta tana kwance tana sharara bacci dur'kusawa yai ya dauki takalmi shima ya tafi sallah daga nan ya zarce gidan malam Zayyanu ya masa bayani tunda dama shine wakilin Baffah".

Balarabe ya auri Asabe ta tare abinta cike da murna dan tana sonshi sai zuba masa soyayya take irin ta 'yan bariki Dalah kam ta zama abar tausayawa gashi yanzu hatta Indo bai damu da ita sosai ba ada baya so yaji tayi kuka ko yaga hawayen ta amma yanzu ko zatai kukan jini yana ji bazai kula ba a yadda ake ciki ko mutuwa Indo zatai a yanzu kila bazai nuna damuwa ba yafi son agolarsa bahijjah yar gidan Asabe akan Indo yakan sayo mata komai jiki na rawa ya bata ya dauketa suje yawo amma banda Indo saidai tace ya mata haka a da馃槩.

Hummm duk nisan jifa zai dawo kasa inda jirgin sama yaje wata rana za'a cewa kunkuru barka da zuwa kuma duk nisan turin da za'ai wa lilo zaije ya dawo inda yake馃憣 Ramatu dai an haukace gara Salamatu dan ita yanzu inta faki ido ta fito sai bola kuma bakinta baya shiru tana fad'a-fad'e da zage zaga dama hali a jikin rai maganganu iri iri wanda ba'a san dasu ba sai fad'a take haka duk sunan mutumin daya zo bakinta a 'kauyen inta fara ambatonsa tana tsine masa tana 'kwal'kwale masa albarka saita wuni batai shiru ba kullum idan an rasa ta dama ansan inda za'a sameta saidai a tsinto ta kan bola tana ta tsintar ledodi tana daurewa a jikinta tana surutai kala kala wanda babu wanda yasan me take cewa wanne irin yare ne sudai yan 'kauyen basu ta'ba ji ba saifa a bakinta gajiya Ilyah yai ga kud'i yanzu yana ta bun'kasa amma jinya sai cinyewa take dan haka ya yanke shawara ya dauko wani malami cewa yazo ya ganta yana zuwa da fara aiki Ramatu tahau ihu iri iri da kururuwa yana yayyafa mata ruwan addu'a sai burgima take tana tsalle ta tumu a kasa timm ta tashi ta daki bango tai girgiza har katanga saida ta ture ta zube mutane kwa sun cika gidan kamar anyi busa sai gulma ake babu wanda ya ankara har malam kawai sai gani akai ta zuba da gudu tana yage yage a guje Ilyah da malam suka bi bayanta yan gari ma d'uuuu suka bisu aguje dan ganin 'kwa'kwaf daji Ramatu ta ri'ka linkuwa suna bita ga wata ba'kar iska me duhu data taso ta lullu'besu da guguwa a cikinta da 'kura duk 'kasa ta cika musu ido amma basu daina binta ba kwatsam sukaga kogi a gaban su ruwan har kumfa yake yana murd'ewa da ambaliya amma Ramatu takai take gudu kamar tana bin normal hanya tsayawa sukai suna haki ganin zata bace musu malam yace "ba ruwa bane sharrin miyagun makiya shed'anu ne muje cikin azama suka fara bi ta kan ruwa aiko sai sukaji kasa kawai suke takawa ashe rufa ido ne suna shiga wani ba'kin daji sukaga abu jimmmn ya fad'o gaban su wani shirgegen dodo jikinsa duk gashi ga jan ido turus mutane sukai wasu suka yanke jiki a gurin suka fad'i a sume wasu suka juya da aguje dariya dodan yai wanda tasa bishiyoyi ganyensu ya fara kad'ewa ya zuba muryarsa kamar saukar tsawa yace.

"Me kuke nema anan waccan tamu ce ku juya inda kuna son ranka Wanda kuma yake son muyi fate fatansa to yazo" malam na haki cike da gajiya yace "waye kai" hhhhhhhhhhh!!! Dariya ta hauka da tashin hankali dodon keyi yace "baka sanni ba kawai kalleni a haka saidai zaku wahalar da kanku domin ta zama tamu aiki tasa mukaiwa kishiyar ta har muka zu'ke mata jini ta mutu kuma dama mun fad'a mata aikin zai dawo kanta ta duk daran dad'ewa ta amince

25 / 67