Chapter 5 Reading BAHIYYA complete book BY amina ibrahim HN Novels

BAHIYYA complete book BY amina ibrahim

Author :  amina ibrahim Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 36.2K words

Baba Maharazu a waya shine sanadiyyar da Malama ta shiga gaba gaba aka

yiwa Nuhaira komai har uniform har komai ya kama kuWi dubu saba'in da huWu termly kuma Dubu ashirin da biyu. Ss1 to Ss3.

"Malama ta kasance ma™ociyar mu ce tunda muka dawo nan garin Kaduna Road suka haWu da Mama, da"

"ita da mijinta duk malaman makaranta ne suna da yara huWu, bariki ba kamar gida ba ne namiji zai bar matarsa ita ma ta fita ta nema domin su taru su rufawa juna asiri matu™ar zata iya, hakan yasa Malama bayan aikin koyarwa ta shiga hulWa da mutane daban daban tana kai kayan mata cikin gari da kuma sauran State tana kuma da shago ™ofar gidanta. Ta iya kanta sosai shiyasa duk yadda kake tana iya zama"

da kai tana kuma da kirki irin nata.

Sanadiyyar komawar Nuhaira school yasa aiki ya taru ya min yawa ni da Mama in kuma na fita cikin gari

ita kaWai tayi ta wahala shiyasa na nema mata almajiri mai taimaka mata.

Yauma haka nayi ta bada kayan miya idan an kawo ni™a kuma in tashi in yi domin Mama ta Wan fita

"unguwa, ™arfe uku nayi na yamma na shirya na fita islamiyya nabarwa Sharifu almajiri sauran aikin kafin Nuhaira ta dawo daga school domin sai uku da rabi suke tasowa kafin ta iso gida kuma huWu tayi shiyasa take zuwa islamiyya yanzu a makare."

Ko da muka shigo gida ana kiran sallar magrib ganin banga mama a waje ba na shiga Waki na tadda ta

kwance a du™un™une da sauri muka isa gareta ni da Nuhaira muna rige rigen tambayarta mike damun

"ta,ko iya Waga kanta ba tayi hakan yasa hankalinmu ya tashi sosai na cakumota da ™arfi nace."

 Mama mi ne ne? Mi ya same ki?

Sai tin zuciyar ta ta shiga nuna min da hannu alamar nan ne yake mata zafi. Cikin ruWewar kuka nace.

" InnaLillahi! Wannan ciwon zuciyar ya matsa miki Mama. Tashi ki daure mu tafi chemist, yau da ke zan"

tafi domin ya duba ki Nuhaira Wauko mata hijabi da mukulli mu tafi

Da sauri Nuhaira tayi yanda nace muka rufe gidan a hankali muka lallaSa da ita wanda ko a chemist Win

kasa zaunawa tayi sai da na zauna ta kwanta a jiki na. Tambaya ta mutumin yayi mike damunta.

Kai tsaye na share hawayena na ce.

" Ta daWe tana complain cewa ™irjinta yana ciwo, to duk lokacin da abin ya tasar mata sai inzo in sayi"

"mata magani ko nan ko kuma wani wuri in bata tasha, to yau dai bama nan ko da muka dawo kuma mun cimmata a haka "

Nidai ganin nayi ya Wauko wani abu ya Waura mata a hannun ta sannan ya saka wani a kunne bayan ya

gama. Ya kalle ni yace min hawan jini ne da ita kuma ya hau sosai fiye da ™ima.

Cikin tsantsar mamaki ni da Nuhaira muka haWa baki wurin kiran.

 Hawan Jini likita?

Cikin kuka na sake cewa.

" Hawan jini ta yaya? Wane irin hawa jini dan Allah, muna zaune lafiya "

Mutumin yace.

" While, ba abin mamaki ba ne ai, musamman idan akwai wata damuwa tare da ita tana yawan tunani da"

"rashin samun ishashshen bacci, amma... "

Sai ya juya ya hahhaWo magunguna ya bani na kusan dubu goma sha Waya.

"A nan ya buWe ya bata maganin, sannan yace"

" idan akwai abinda yake saka ta damuwa kuyi ™o™ari ku Wauke mata hankali a kai, ta ri™a samun bacci"

"yadda ya kamata tana cin abinci mai kyau, in sha Allah zata ji sau™i "

"Daga haka na cewa Nuhaira taje gida ta Wauko masa kuWin shi, bayan ta dawo muka koma gida, kafin"

shiga bacci har mun samu taji sau™i domin har ta tashi tayi Sallah taci abinci.

Washe gari bayan mun gama sallar Asuba muka je muka gaishe ta nayi sauri na haWa mana break fast

Nuhaira ta shirya ta fita makaranta ni kuma na kai mata abin karin nata Waki bayan ta Wanci ba yawa na bata magani kamar yadda likita yace.

Bayan na kwashe kayan na dawo na zauna cikin tausasa murya na kalle ta nace.

 Mama miye yake damunki haka? Mi kike tunani da har ya sa miki hawan jini nan take? Dan Allah Mama

ki gayamin

Girgiza kanta tayi tace.

" Ni dai ban san ina da wata damuwa ba Bahiyya, gaskiya ban sani ba.  "

Cikin rashin gamsuwa da maganar ta nace.

" A'a Mama, dan Allah ki gayamin minene damuwar ki,irin wannan ciwon ba zai kama mutum ba muddin"

ba damuwa ce a ransa ba.

 Ni kam bani da wata damuwa Bahiyya

Juyin duniyar nan nayi amma Mama ta kafe tace min babu abinda yake damunta dole na hak'ura na

™yale ta ina faWin.

" To tunda kince ba abinda yake damunki, dan Allah ki kwantar da hankalinki idan ma akwai wani abinda"

"ba zaki iya gayamin ba kiyi ha™uri ki cire sa a ranki, bana so mu koma wurin likitin bayan kwana biyu ya aunaki yace min ga wata damuwa, idan wani abu ya sameki Mama ban san ya zamuyi ba. Kece ™warin guiwar mu, kece kaWai muke da, ke kika zama bangon jinginar mu idan wani abu ya sameki ban san in da zamu shiga ba. Mama ke ce fa kullum kike min faWa akan in dai na damuwa, in zama mai tawakkali, yau kuma ace kece wai hawan jini ya kama, mi kika nema kika rasa? Idan ma mutuwar Baba ce ya kamata"

ace kin saba kamar yadda kike faWamin Mama...

Hawayen da suka gangaro min na share tare da Mi™ewa tsaye na fita waje jin sallamar yaro ya shigo

gidan namu.

Mama kuwa mirginawa tayi ta kwanta akan pillow wasu hawaye masu zafi na bin gefen kuncin ta. Ha™i™a

"mutuwar Jafaru ta nakasa mata zuciya ta yadda ma bata yi tsammani ba. Idan tace tana samun wadataccen bacci tsawon shekarar nan tayi ™arya, babu abinda take tunani sai mijinta da kuma rayuwar marayun '´a' ´an ta mata guda biyu, waWannan mutanen da suka kashe mijinta sunyi mata illar da har ta kwanta damanta ba zata warke ba. Domin shine jigonta shiya kawo ta wannan ™asar ta Nigeria ba tare da tasan wani mutum na daban ba bayan shi. Gashi har ya koma ga Allah ™asar ta sa ta gagare shi komawa akan wani dalilin banza na son zuciya irin na mutanen yau. Har baro garin Gusau tayi ko zata samu sau™i ta manta da rayuwar su ta baya amma abin ya ci tura. To kuma yanzu ga ™arin wata matsalar ta kunno kai tunda likitan ya faWa mata tana da hawan jini damuwar ta da fargabar ta suka ™aru,"

damuwa ta ™ara baibaye ta fiye da ta baya.

Ita tsoron ta kullum idan ta mutu a wane halin rayuwar 'ya' ´an ta za su kasance? Sannan idan suka isa

aure wa zai aure su idan akaji cewar ba su da dangin uwa babu na uba suka Wai ne su uku suke rayuwar su.

"Bayan kwana biyu kamar yadda likitan yace, na shirya na cewa mama ta shirya mu koma wurin"

"mai chemist kamar yadda yace, ™in amincewa tayi ta kafe kai da fata tace min taji sau™i ba sai mun koma ba. ˜arshe ma faWa ta rufe ni da shi wai duk laifi na ne, daman su mutanen nan matu™ar kana ziyartar su to kullum cikin kira maka matsala suke, da ace na siyo mata maganin ta tun ranar tasha da yanzu kowa"

"na nan hankalin sa kwance, to ita babu in da za ta je ta warke."

"Dole na na kama kaina na ja baki na nayi shiru na ™yale ta, amma Ina kula da ita sosai duk wani motsin ta"

"yana kan idona, sai dai daga baya na gano tabbas Mama bata samun bacci kamar yadda likita yace, akai akai idan na farka naje Wakin ta zaune nike samun ta kan sallayah."

Tun daga wannan lokacin na bata shawara ta ri™a sai ta lokaci idan ma tashin zatayi na dare to ta ta shi

amma ta rage Waukar dogon lokaci.

"Haka mukaci gaba da rayuwa, Mama ta samu sau™i sosai a gaban idanunmu kamar yadda take nuna"

"mana idan abin ya tasar mata sai ta tafi can wani chemist ta sayi magani ta dawo gida ta Soye tana sha don kar mu gani hankalin mu ya tashi. Nuhaira taci gaba da karatun ta, nima ina yawon lalle na da yanzu"

na ™ara yawan customers.

*************

Hanifah

Ko bayan rabuwar su da Farooq sai da ta sake share wata biyu da sati biyu a Dubai sannan ta wuce

Egypt ta sake yin sati biyun ta masu kyau sannan ta dawo.

Duk iya yanda Farooq ya Wauki fushi da ita kasa daurewa yayi dole ya dawo kiranta a waya yana jin

"muryarta amma bai taSa tambayar ta cewa ina take ba, mi take yi ko yaushe zata dawo. Iyaka suyi wayar"

su idan sun ™are su kashe. Sau biyu tafiya tana kama shi zuwa Dubai bai taSa attempting na cewa ya je

wurinta ba. Ya ™yale ta har lokacin da ta ga dama ta dawo don kan ta.

Ko da ta iso ma baya ™asar yana Saudiyya tare da Madinat sun je aikin Umrah sai da tayi kwana huWu da

dawowa sannan ya dawo.

"Tare da Madinah suka shigo gidan, tunda yayi rashin lafiyar nan ta zo bata koma Kaduna ba. Cikin murna"

tazo ta tare shi tana faWin.

 Welcome

Kamar wanda yake mafarki haka yayi hugging Win ta back yace.

 Am i dreaming?

Dariya tayi tace.

 No! Not at all. Is your Hanifah

˜ara ri™e ta yayi gam a jikin shi yana faWin.

 Welcome back home my love

 Thank you

Ganin Madinah yasa tayi saurin janye jikin ta taje gareta with soft smile on her face ta bata side hug tace.

 Welcome Grand Ma

Cikin Kalaman hikima Madinah tace.

 Thank you Hanifah. Da fatan an dawo lafiya

Hanifah tace

 Lafiya lau Grand Ma

Madinah tace

 Ya kasuwa? Ya familyn ki? Da fatan komai lafiya?

Hanifah tace

" Everything is fine, my family are doing good "

 That's nice to hear.

"Madinah tace tare da kama hanyar zuwa masaukinta,luggage Win ta da suke hannun shi da kanshi ya"

"wuce har Wakin ya kai mata, daman tun a mota da suka sauka ya hana kowa Waukar kayan yace aikin shi ne saboda haka shi zai kwashe kayan."

Yana fitowa ya zarce Wakin shi ya je yayi wanka ya shirya itama Hanifah da sauri taje ta sake yin wanka ta

"shirya cikin riga da wando da suka amshi fatar ta sukayi raWau, sai wata hular net da ta saka ta naWe kanta da ita tayi matu™ar kyau. Daman kuma kafin ta shiga ciki sai da ta saka Nafisat cook Winta cewa ta shiryawa Farooq table kafin su fito."

Ta riga shi fitowa hakan yasa ta wuce Wakin shi direct ta sa meshi ya gama shiryawa yana tsaye jikin

"window yana kallon waje, hannayensa soke a cikin trouser pocket Win shi."

"A hankali taje ta rungume shi ta baya tare da Wora kanta a bayan shi tayi lamo, dukkan su babu wanda"

yacewa kowa komai tsawon lokaci suna a haka. Sai daga baya ta ja numfashi a hankali sannan cikin pleading tone tace.

" I'm sorry. I'm very sorry for what I did. I know that I hurt you, but what ever it is you are.  "

Da sauri ya birkito ta ya rufe bakin ta da nasa yayi kissing Winta passionately sannan ya janye ya kalle ta

cikin shau™i yace.

 karki damu ni komai ya riga da ya wuce a wurina Hanifah

Murmushi tayi tace.

 Thank you. Muje kaci abinci Nafisat ta gama shirya table

"Ba musu ya bi ta suka je suka zauna zaman cin abinci, yana cikin ci ya ji an kira sallahr magrib a"

"masallacin gidan sa, da sauri ya mi™e yace."

" Hanifah an kira sallah, ya kamata ace na bar cin abincin nan har in dawo daga isha "

Kallon shi tayi tace.

 To kabari ka ™arasa mana tunda ka fara

Hanyar waje ya nufa yana faWin.

" No, Idan na dawo after isha prayer sai ki sa a sama min wani abin "

"Daga haka ya wuce ya barta. Zaman sa tare da Madinat wannan karon ya sa shi ya Wan canza sosai,"

domin a lokutan baya Sallah a jam'i bata wani dame shi ba musamman idan yana gida. Amma yanzu ya dage sosai har asubahi yana fita.

"Sai bayan ya dawo ya wuce Wakin Madinah direct ya cimma bata nan, ba kayan ta, Wayar ta ya kira kai"

"tsaye tace mishi gata a Kaduna. Abin yayi matu™ar bashi mamaki kamar wadda ake kora, ya rasa ya ta Wauki Hanifah a rayuwar ta ko dai surukar ta ce iyaka kenan."

"Ko da ya shigo bata nan, dining Win ya wuce ya ci abinci sannan ya shige ciki. Kwantawa yayi yay lamo"

"yana tunani. Shi yanzu ya gama yankewa ba zai sake matsawa Hanifah ba akan bu™atarsa ba domin Sacin rai ne kawai zai yi ta addabar sa, shiyasa yanzu ya yankewa kansa yin azumi domin ya ri™a samun sau™i."

"Yana nan yaji an murWa handle Win ™ofar a hankali, ko bai duba ba yasan wacece ta shigo."

Kwantawa tayi akan ™irjinshi ta sa™ala hannayenta cikin wuyan shi. A hankali taji sautin Muryar sa yana

faWin

" Hanifah time yayi da ya kamata ace munyi settling mun samu yara, duk wannan maganar taki a baya ba"

tunani ba ne

Cikin fargaba da tashin hankali tace.

 What! Haba Farooq yanzu duk tsawon lokacin nan da muka Wauka ba ma tare da abinda zaka tare ni

kenan? Bayan kasan cewa abinda ba zai yi yu ba ne. 

" Zai yi yu mana Hanifah,I'm fertile you are fertile too, to minene ba zai yi yu ba a nan? "

 Farooq No!

 Hanifah abinda nike so kenan

"Mi™ewa tayi without thinking twice kawai ta bar mishi Wakin, abinda ba zai taSa ma yiyu wa ba kenan. To"

"Farooq Wai ko dai ya fara shaye shaye ne? Kawai kuma sai tayi tsaki domin babu abinda ya faWo mata a rai sai Grand Ma Madinah da Mahid, ta sani sarai duk sune manyan munafukai da suke so su sanya mata ido a rayuwar gidanta. Ba ta taSa jin ta tsani Madinah ba a rayuwar ta ba sai yau."

"˜arshe kwanciyar ta tayi abinta tayi baccin ta ta ™yale shi bata sake komawa kan shi ba, domin ta gama"

"yankewa a ranta komai zai faru ba zata amince da wannan shirmen nasa ba, iyakaci dai ya gama fushi da ya huce zai dawo, ballantana ma tasan Farooq ba ya iya fushi da ita."

"Washe gari ko da ta fito har ya fice daga gidan ko break fast Bai yi ba, nan ya bar mata kayanta yayi"

tafiyar sa.

Wanda hakan ba ™aramin shayar da ita mamaki yayi ba.

"Waya ta Wauka tayi ta kashin wayar sa amma ya™i Wagawa, ˜arshe sai ga text ya turo mata kamar haka."

 Ki amsamin bu™ata ta kawai Hanifah

Ajiye wayar tayi tare da zaunawa tayi break fast Win ta sannan ta shirya ta fita.

*OUM AMEER*

*BAHIYYA*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMEER)*

*BAHIYYA NOVEL ŠIN KUŠI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA

IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA BAKWAI*

BAHIYYA

Yau ma da wani irin matsanancin faWuwar gaba na farka sakamakon mummunan mafarkin da nayi a

"daren jiya,wanda har yafi wanda na saba yi a kullum muni. A sukuku na fito Waki bayan na gama sallah"

"tamkar kazar da ™wai ya fashewa a ciki, Wakin mama na shiga na gaidata sannan na fito waje na zauna na"

buga tagumi ina karanta wasi™ar jaki. Ganin wankin hula na nema ya kai ni dare ga tarin ayyukana a gaba

na yasa ni yun™urawa da nufin mi™ewa sai kwatsam Malama tayo Sallama ta shigo.

Cike da mamaki na amsa mata sallamar ta domin duk da cewa ban duba agogo ba nasan cewa iyaka

™arfe shida ne yanzu na safe.

Da sauri tace min.

 Bahiyya ina mamanku? Yi maza ki shirya mu tafi Maman Khadijat ta kira ni yanzu tace dan Allah ki zo

tafiya biki ta kama ta garin su ki zo kiyi mata lalle zuwa ™arfe biyu zata wuce.

Nima mi™ewa nayi cikin sauri nace.

 Mama tana ciki bari naje to na shirya

Bayan sun gaisa da Mama tayi mata bayani na shiga Waki na Wanawa Nuhaira duka a cinya saboda

"takaicin baccin da take kwantawa bayan asuba, duk da cewa tasan tana zuwa school amma akan mugun bacci kullum sai ta sake kwanciya bayan sallar Asuba."

Firgigit ta mi™e cike da mita tace.

 Haba Aunty Bahiyya!

Cikin jin haushi nace.

"""Dan Allah ta shi kije ki nema abinda zaku karya ni fita zanyi, kada kiyi latti "

Mi™ewa tayi tare da yin gunguni ta zo ta wuce nima naje na yiwa Mama Sallama muka tafi.

"Ina jin daWin zuwa gidan Maman Khadijat masu kuWi ne na gaske amma babu ruwanta, ta iya sakin jiki da"

"kowa, bata da wula™anci, hakama 'yar ta Khadijat da ta ke ji da ita, Allah ya haWa jinin mu da ita sosai, bata ma wani jin Hausa sosai ni kuma ba wani dogon turanci nike ji ba, haka zamu zauna in tsantsara"

"mata kalar kitson da suka nuna min in yi mata lalle tayi ta santi, tana ce min Aunty Bahiyya Thank you."

Hakama yayanta Ahmad da zaran ya ganni muna haWa ido zai sakar min murmushi yace. Aunty Bahiyya

hi! Mamar take gayamin cewa kullum idan suna fira ta sai yayi ta ce mata ina da kyau sosai ina burgeshi. Shiyasa ni ke jin daWin zuwa gidan domin ba su da matsala.

*************

HANIFAH

"Duk iya ™o™arin ta tayi akan cewa taga ta shawo kan Farooq amma abu ya faskara, zata iya cewa tunda"

"take da shi wani abu makamancin haka bai taSa shiga tsakanin su ba, duk yadda zasu samu ™ololuwar misunderstanding bai taSa Wagawa daga wurin ba sai ya tabbata ya shawo kanta komai ya wuce. Baya fushi da ita kai zata iya cewa ma basu taSa samun makamancinyar wannan matsalar ba, domin zata iya"

bugun gaba ta tsaya ko a gaban waye tayi alfahari da mijinta tace yafi na kowa kaf a faWin duniya.

"Amma yau Farooq ne yake gudun ta, ko da zata farka ta wayi gari ya wuce abinshi ko da zata dawo daga"

office kuma bai dawo wa gidan ba sai cikin dare ya ke shigowa koda zai shigo tayi bacci.

Ranar da ta ritsa shi kuma sai ya wayance mata yace aiki ne

5 / 13