Chapter 10 Reading BAHIYYA complete book BY amina ibrahim HN Novels

BAHIYYA complete book BY amina ibrahim

Author :  amina ibrahim Category :  KDP NOVELS

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 36.2K words

mallaki gidan kansa ya daina haya wanda ni kaina naga dacewar hakan domin ga sayen abinci ga kuWin haya ga lalurar yaro ta ™aru,daga haka sai muka yanke shawara cewa idan na tafi kai musu jariri, zai sayar da gonar guda biyu da ™annen sa ke nomawa sannan a bashi nashi gadon Mahaifin su da ya bari. Tunda muka je kowa yake murnar zuwan mu kamar ko yaushe amma tunda yayi wa su Amadu zancen gona da kuWin sa shikenan zance ya canza. Tun yana can ya so a siyar suka dage da lallai ya kamata ya koma wurin kasuwar sa su kuma idan suka sayar daga baya sai su haWa komai su je da kansu su kai masa, tunda dai abin dole yana da jan lokaci, ni tunda naji sun fara mishi wannan hanya hanyar nace mishi ban yarda da su ba, amma abin ka da Wan uwa yace min ai ba matsala, nayi sallama da iyayena da mahaifiyarsa kamar ko yaushe muka shirya muka dawo gida. Bayan dawowar mu saida akayi rabin shekara babu su Amadu babu dalilin su, tun babanku baya magana har ya fara tuntuSa ta da zancen kai tsaye nace mishi ai saida nicce kada ka yarda dasu tun farko kace ba haka ba, ™arshe muna nan Abu wasa wasa har aka shekare, daga nan ya yanke shawarar sake komawa yaji ina zance ya kwana, to tunda Malam ya sa ranar tafiyar nan ya kwanta wani irin mummunan ciwo wanda idan mutum ya kallesa ba zai sa ran zai ™ara kwana ba, mukayi ta yawon asibiti duk a banza, watarana sai nace mishi Malam ko dai zaka je Nijar Win ne daga can ka nemo magani ko Allah zai sa a dace. Sai ya girgiza kansa yace min shi yanzu ya bar zancen Nijar Win nan sai dai wani lokaci kuma, in faWa muku cikin ikon Allah tunda yace ya janye tafiyar sa muka nemi ciwo muka rasa, abu kamar wasa. Muna nan kuma aka Wauki lokaci ya sake saka ranar tafiya sai ga ciwo ya dawo kamar ba zai yi rai ba, to daga nan sai muka fara tsora ta, da kaina nace malam ka janye tafiyar nan har wani lokaci yace min ai ya bar zancen kuma shi ya ma cire rai da wannan tafiya, shima tun daga nan ciwo"

"ya warke, haka haka tun bamu gasgata ba har muka yarda cewa akwai wani abu a ™asa... "

Cikin tsananin firgice wa da ruWewa nace.

" Mama karki ce min don Baba ya nemi ha™™insa ne Su Baba Amadu suka aikata mishi haka, kina nufin"

asiri suka mai kenan??

Kuka take mai tsuma rai cikin raunatattar murya.

" Bahiyya wannan abun ba Babanku kaWai suka yiwa ba, har da ni, domin shine silar da yasa har yau ban"

"sake komawa tushe na ba, kuma ko yanzu ban isa nace zan tafi ba ni kaina, kuma abin da ya bamu tsoro,"

firgici da ban al'ajabi muka kasa warware shi har Mahaifinku ya bar duniya shine '´an uwana da na

"Mahaifinku har yau babu wanda ya sake neman ina muke yau shekara ashirin da shida kenan rabon mu da gida, a wurin Malam maharazu kawai muke samun labarin su, a ta hannunsa ne Malam ya samu labarin rasuwar mahaifiyarsa, Nima a wurin shi na samu labarin rasuwar iyayena, da sauran Labaran"

dangi na daWi ko akasinsa. 

"Jikina sai Sari yake ina wani irin kuka mai ban tausayi, cikin ruWewa nace."

" Yanzu Mama akan abun duniya, suka rabaku da dangin ku?? Saboda abun duniya Mama! InnaLillahi wa"

"inna ilaihiraji'un! Kai duniya ina zaki damu,'´an uwanka uwa Waya uba Waya sune zasu aikata maka wannan mummunan aika aikar saboda wani ban zan abun duniya wanda dole watarana sai an barsa "

"In banda kuka babu abinda Mama da Nuhaira suke, lallai tabbatas zancen Mama haka yake banga wani"

abun burgewa ba a cikin wannan labarin wanda har na koma ga Allah ba zan manta sa ba. Dafa kafaWarta nayi nace a hankali nace.

" Lallai Mama da ciwo sosai a cikin rayuwar ki, wannan labarin da ban al'ajabi ya ke, Don bare yayi maka"

"abu ba zai zama da ciwo sosai ba kamar Wan uwanka, yanzu ta dalilin laifin babanmu shi ne ya shafe ki kema kika rasa dangin ki ba gaira ba dalili, kiyi ha™uri Mama, Wallahi Allah baya zalunci kuma baya yafe ha™™in wani akan wani, kuma addu'ar wanda aka zalunta bata da wani shamaki tsakanin ta da ubangijin mu, na san cewa kun daWe kuna addu'a akan wannan zaluncin da suka muku kuma muma daga yau zamu Wora, matu™ar bamu da ha™™in su suka yi mana wannan aika aikar to muna addu'a Allah ya bi"

mana ha™™inmu a inda ba su da wani tsimi ba su da dabara

Nuhaira ce tace.

 To Mama shi Yah Ishaq Win kenan ya samu zuwa Nijar Win kafin ya rasu??

GyaWa kanta tayi tace.

" Eh! Tun zuwan da muka yi yana zanen goyo, bamu samu komawa ba har ya rasu "

Ajiyar zuciya na sauke ina ™ara jinjina girman wannan al'amari a raina na sake kallon Mama nace.

" Mama mutanen nan sun aikata kuskure, kuskure babba domin raba iyaye da Wansu baban zunubi ne,"

"saboda tsabar rashin imani Mama suka raba ki da duk dangin ki babu tausayar suyi tunani cewa ke fa mace ce, zuciyar ki ba zata iya jurewa ba "

Daga haka sautin kukan ta ya ™aru sosai da ™yar muka samu ni da Nuhaira muka rarrashe ta ta samu

bawa zuciyar ta magana.

Daga haka kowa ya mi™e ya tafi wurin nasa yayin da zuciyoyinmu suka cika da rauni da damuwa.

"Da dare cikin gabatar da sallar Isha, Ikram ta shigo tana mai ™wala kiran sunana, Nuhaira ce ta tare ta"

"tana tambayarta ya a kayi, Ina ji tace wai Maman su ce take Kirana cewa da Malama. Bayan na idar naje na sanar wa Mama na tafi."

Ina shi ga muka gaisa da Ita na samu wuri na zauna tare da rungume autar Fahaira nace.

"""Gani Malama "

Tattaro nutsuwar ta tayi ta Kalleni da kyau tace.

""" Bahiyya kyaun al™awari cikawa, kuma da ilminki yadda kuka yarjejeniya da Hajiyah Hanifah ya kamata"

"ki cika, ta kira doctor Sam ya kirani tace tana bu™atar zuwa UK ganin likita domin jikin ta ya matsa mata kuma tare take so ku wuce kamar yadda kuka al™awaltama juna "

GyaWa kai nayi cikin gamsuwa da maganar ta nace.

"""Haka ne malama, kyaun al™awari cikawa. Daman can ba mantawa nayi ba, taya zan manta Malama?"

"Matar da ta dalilin ta ne muka tsinci kanmu da sake darawa a rayuwa, ko kaWan bana dana sani, wasu ma da ake Wauka aikatau tun daga garin su zuwa wata uwa duniya na tsawon shekaru suyi ta wahala"

dare da rana ballanta kai da aikin bai taka kara ya karya ba kuma shekara Waya kacal. Kawai dai Mama ta

"nike tunani har yanzu ban iya faWamata ba, kullum cikin zullumi nike  "

Cike da ™warin guiwa tace.

" No kar ki damu in sha Allah zan yi mata bayani kuma zata fahimta da yardar Allah, ke dai abinda nike so"

"da ke shine ki tsaya matsayin ki da Allah ya ajiye ki, ki ki ye yi kanki ki kuma zama mai wadatar zuci da godiya da duk abinda aka miki, ki ri™e ibada Bahiyya, mutanen nan sai a hankali, wasu wallahi ko ibada bata dame su ba, saboda haka kada kije ki samu canjin wuri ki ce zaki canja Wabi'arki "

GyaWa kai na nayi na ce.

"""in sha Allah zaki same ni mai kiyaye. Ro™ona shine kuci gaba da kulamin da Mama da Nuhaira, sannan"

"wannan kuWin ku yanke shawara a tsakanin ku wace kasuwa za'a yi da su, ni bani da ja da hakan, Allah ya yi mana jagora "

Daga haka na mi™e tare da yi mata sai da safe na shige gida.

"Bayan kwana biyu da maganar mu da malama, sai ga mama da kanta ta kirani Waki tace min."

" Bahiyya naji komai daga bakin Malama, ba abinda zance sai dai ince Allah ya kiyaye ki a duk in da kike,"

"amma ba don abun yayi min daWi a rai ba, to amma wani lokacin muna kan so abu ya zama ba alheri ba"

"ne garemu, wani lokacin kuma sai mu™i abu ya zama shine mafi alheri a gare mu. Tace min gobe ne zaku"

tafi

Cikin faWuwar gaba na ce.

 Gobe kuma Mama??

" Eh, tace matar tace ba tada lafiya kuma likitan na ta a can yake "

Cike da Murmushi Nuhaira ta kalle ni tace.

" Aunty Bahiyya kin ji daWin ki ke kam, kina ba™in cikin baki je Nijar ba gashi yau Allah yayi zaki je garin da"

"yaci uban Nijar Win, wani hanin ga Allah bai wa "

Šan guntun murmushi na saki tare da girgiza kai na nace.

" Nuhaira ba zan biye miki ba, domin ke har yanzu tunani bai gama shigar ki, in ba shi taya zaki haWa"

tafiyar zumunci ta jini da wannan tafiyar da babu haWin iya babu na Baba...

Tare numfashi na tayi tace.

" Ni dai ba ruwa na, UK tafi Nijar, kuma dan Allah ki yo min tsaraba Aunty Bahiyya ki sawomin kayan kanti"

"irin riga da wandon nan da naga matar nan ta saka ranar, wallahi ni dai ta burgeni ainun "

Ni dai jinta kawai nike domin can ™asan zuciyata wani abu ni ke ji yana yimin ba daidai ba.

Washe gari ko har ™ofar gida wata haWaWWar mota tazo tayi parking wanda kallo Waya zaka yi mata ka

tabbatar cewa ba daga ™aramin gida ta fito ba. Tsayuwar Motar da zatayi sanadin canja al™iblar tafiya ta

a idon '´an unguwar mu zuwa sayar da jikina domin karuwanci na biyawa Mama na kuWin aikin lalurar ta bayan sun san bamu da wannan kuWin bamu da dalilin su.

"Kuka na ke sosai tare da ri™i™™e Mama tamkar raina zai fita, yayin da Malama da sauran' ´an uwa da"

"masu da zuciya Waya da masu yi don munafurci suka tsaya suna ta bamu baki, suna neman jin tushen"

maganar ina zanje. Wanda har suka ™araci gulmar su suka gama babu wanda yace musu ga inda zani.

Har na shiga motar sai kuma na fito da gudu na zo jikin mama na ™ara fashewa da kuka ina faWin.

" Mama dan Allah dan girman Allah Mama ki tsare shan maganin ki a kan lokaci akan kuma ™a'ida, duk"

"sanda kika ji matsala Nuhaira ta rakaki asibiti mama, kuma ki yimin al™awarin cewa ba zaki sake shiga"

"wata damuwa ba har abada, ko da ace bamu da kowa mu uku Mama mun wadaci kanmu, a haka muna farin ciki sosai, ki kula da Nuhaira Mama.  "

Daga nan kuma na juyo ga Nuhaira na rungume ta nace.

" Ke ™anwata marar jin magana da baccin safen da bana so dan Allah ki kula da kanki sosai, ki kula da"

"Mama kinji ko, nayi miki al™awarin zan saya miki duk abinda kika ce kina so, kamar gobe ne zaku ga na"

"dawo, in sha Allahu "

Daga haka na wuce direct na shige motar ina ta Waga musu hannu tamkar wata ™aramar yarinya har suka

Sacewa gani na.

Bayan mun fito kan Titi malama ta hau ™ara yi min nasiha saboda tare muke ita zata rakani zuwa gidan

Hanifah domin su ™ara tabbatarwa cewa a hannu nagari nike.

"Nan na ro™e ta cewa dan Allah mu fara bi ta gidan Maman Khadijat in ™ara yi mata godiya kafin na tafi,"

sai gashi ko munyi nasarar zuwa gidan amma bata nan kamar yadda masu gadi suka shaida mana. Daga nan drivern ya fito ya juya akalar mota zuwa gidan Hanifah.

"Tun daga farkon unguwar na fara kalle Kalle domin wannan ba kamar sauran unguwanni ba ce, duk"

"yadda nike ganin unguwar su Maman Khadijat da mugun kyau wannan unguwar ta cuna mata, tamkar"

"ba'a Najeriya ka ke ba, Gate ne gasu nan kala kala, idan mun wuce wannan mu kai ga wannan, ga kaki nan kala da kala duk a matsayin masu gadi."

Ban ™ara tsinkewa da al'amarin ba sai da muka shiga cikin tamfatsetsen gidan kacokam na ™ara

tabbatarwa kai na da cewa Lallai yau ni Bahiyya zan shiga wata duniya ta daban.

Kallon malama nayi kamar yadda itama naga take kallo na tare da yimin alama cewa mu fita.

Jiki na take ya hau karkarwa tamkar ana kiWamin mazari ta dalilin tozali da nayi da wasu shirga shirgan

samudawa waWanda babu alamun wasa a tare da su sun ™a™™ame tamkar wasu sandararrun gunku

na................

*OUM AMEER*

*BAHIYYA*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ŠIN KUŠI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA

IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

*BABI NA GOMA SHA UKU*

"........... Wani ™ayataccen falour ne na alfarma akayi mana masauki muka zauna, ni dai ko a nan a darare"

"ni ke zaune, Malama ce ma naga ta saki jiki sai aikin kalle kalle take."

"Jiga jigan hotuna ne kala da kala ita dai Matar gidan kallo daya nayi mata a wani hoton na gane ta, sai dai"

hotunan maza ne biyu na gani ba zance ga mai gidan ba.

Bayan malama ta gama ™are musu kallo ta kalle ni cikin mamaki tace.

 Bahiyyah kin san nan ko gidan waye?

Girgiza kai na kawai nayi alamar ban sani ba.

GyaWa kai tayi tana mai ™ara jinjina girman al'amarin tace.

 Daman farkon tozali na da ita raina ya bani cewa kamar ita sai dai girma da matsayi irin wanda take da

"shi shine ya hana zuciya ta amincewa da cewa ita ce, to ashe ita Win ce. Babbar '´ar kasuwa ce, ita ce mammallakiyar Šan-Ali Decor and Event wanda ake ji da shi a faWin ™asar nan wanda bata jima da sake buWe reshenta a United Arab Emirate ba,Mahaifinta shahararre ne kuma sananne yanzu haka Ambassador ne a ™asar Cairo , mijinta kuma Umar Farooq mai gishiri shima shahararre ne kuma sannan ne a faWin waje da kewaye Bahiyya,shi jika ne Waya tilo ga Madinat shahararriyar mai kamfanin"

Almadinah textile and more da ke da rassa daban daban a faWin ™asar nan da kewaye. 

Ajiyar Zuciya ta sauke sannan ta kalle ni jiki sanyaye tace.

" Ban san wace kalar ™addarar ce ta haWaku ba Bahiyya,Don wannan haWuwar taku da ™addara zan kira ta,"

"na san ba don tana neman komai daga gare ki ba sai dai don tayi niyyar ta taimaka miki kawai because you have nothing to pay her in return, banga abinda zaki bata ba a duniyar nan domin tafi ™arfin ki ta ko ina, in ma masu aiki ta ke nema nasan dole sai masu kwalin karatu mai zurfi don ko a gidan hajiya Rasi'at da bata kai ta ba suma haka tsarin su ya ke. Allah ne kaWai masanin abinda yake zuciyarta akan neman ki da tayi Win nan har na tsawon shekara Waya, abinda zan faWa miki na ™arshe shi ne Bahiyyah ki tsare"

"mutuncin ki komai wuya komai tsanani, ki yi musu biyayya daidai yadda zaki iya. "

GyaWa kaina nayi tare da jinjina girman lamarin a kaina nace.

"""In sha Allah Malama zan kiyaye "

"Zaman mu a nan munfi 2hours, bayan an cika mu da kayan ciye ciye abinci kala da kala muka ci muka"

"™oshi sannan daga baya sai ga wata matashiyar mata da hausarta bata fita sosai ta zo tace mu tashi mu biyo ta. Haka muka yita bin ta mu shiga nan mu wuce nan ko ina gwanin burgewa tamkar duniyar da ba'a mutuwa a cikin ta, sai daga ™arshe muka isa wani parlour na alfarma mai wani sanyi da ™amshin"

rahama mai kwantar da zuciya.

Ko a nan ma sai da muka shafe kusan mintuna talatin sannan sai gata ta iso cikin takun ta na ™asaita da

girma na manyan mata ta samu wuri cikin Waya daga cikinsu cikin lumtsatstsun kujerunta ta hakimce.

Tuni ni da Malama muka shiga mi™a gaisuwa ni kuma a zuciyata ina ta mamakin yadda malama ta wani

baje a ™asa tana faman kwasar gaisuwa yayinda ni na san cewa itace ya kamata ace ta gaidata domin ko

bata haife ta ba saura kiris.

Murmushi tayi sannan ta kalli Malama tace.

 Na gode

Murmushin itama Malama tayi tace.

" Ba komai Hajiya, Daman cewa nayi bari na rakota domin in ™ara tabbatar da cewa a hannu na gari zata"

"faWo, Allah ubangiji ya baki lafiya ya kuma zaunar da ku lafiya "

Murmushi Hanifah ta sake yi hannun ta ri™e da wayar ta tana latsawa ba tare da ta kalle ta ba tace.

 Kar ki damu In sha Allah babu wata damuwa

" To nayi murna da jin haka, ni zan koma sai Allah ya sake haWamu da alheri "

Daga haka Malama ta mi™e nima na yun™ura da nufin mi™ewa tayi saurin dakatar da ni tace in zauna ba

"sai na rakata ba, amma fir na ™i saurarenta Sai da na biyo ta har mota, kaya ne ake ta tula mata ni™i ni™i Wai gashi nan in ji Hajiya, Malama kuma daga gefe sai faman ™ara jaddada min take cewa in bi matar nan sau da ™afa bata da wata matsala, a raina har abin ya soma bani Mamaki ni dai toh kawai nike kira mata har ta shige mota ta wuce. Hawayen da suka silalo min na goge tare da yin sauri na bi bayan matar"

nan da ta Wazu domin ba lallai ne na sake maida kaina wurin ba.

"Wani irin tsoro ne ya dirar min a zuciya ta wanda ban san dalilin hakan ba, ko don yanzu ya rage"

"parlourn daga ni sai ita ne Oho! Tunda na zauna bata sake kallon in da nike ba tamkar Allah bai yi ruwana a wurin ba haka tayi min wanda sam banji daWin hakan ba, ko ba komai atleast ya kamata tace min wani abu don ta nuna tasan cewa ina wurin kai ko kallona tayi ni hakan ya wadatar, amma tayi da ni"

"kashi duk Waya wanda maman Khadijat baya daga cikin halayyar ta, shiyasa ni ke sonta."

"Ba abin da nike sai tubka da warwara ni kaWai a cikin zuciya ta, daga ™arshe na Sige da tunanin Mama da"

"Nuhaira wanda ba san lokacin da Hawaye suka shiga kwaranya daga cikin idanuwa na ba. Bayan na gama hawayena na tsayar da su don kaina, sai na sake Wago kaina da nufin sake kallon wannan ishashshiyar matar sai dai wurin wayam ba kowa ban san lokacin da ma ta tashi tayi tafiyar ta ba, wasu sabbin

10 / 13