SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah

Author :  FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 19

15K to 18K   out of 54.2K words

beyi magana ba shi kuwa seda ya mula kana ya ware dara daran
blue eyes nashi zuro kafan sa na dama ya fara yi seda ya mula kana ya zuro da ɗayan
ma duk sojojin dake wurin sara masa suka yi harda Mash kana suka yi kasa da kansu
rufe motan Mash yayi kana suka rufa masa baya a bakin hole da suke yin taron na
manyan shugabanin su suka tsaya yayin da shi kuma ya shige hole ɗin bakinsa ɗauke
da excuse can kasan makoshi sauran sojojin kuwa tsaya wa suka yi harda Mash ga
wurin a cike da sojoji da alama wani babban taro suke yi yanda kowa ya halarci
wajen,
Tunda ya shiga wajen kamshin turaren sa ne ya fara kaiwa mutanen gurin hari yana
kuma yi musu sallama duk dagowa suka yi suna kallon sa su biyar ne a gurin se shi
daya shigo yanzu suka zama su shida, shikuwa tunda ya shiga be ɗaga kai ya kalli
kowa ba ya karasa gurin kawai yayi kafun ya zauna seda ya sara musu gaba ɗayan su
kana ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun gurin be damu da cewa akwai wa'inda
yafisu matsayi ba abunda yake gaban sa kawai yake yi wayan sa ya ɗauka ya fara
aikin dannawa tun daga sara musu da yayi be ƙara wani abun ba banda wayan sa da
yake dannawa gyaran murya babban cikin su yayi kana ya fara magana kamar haka ''
tun karfe 10 muka shirya wannan taro Amma se yanzu gurin 11 kake zuwa yanzu de
lokaci ya ƙure mana banda lokacin jin korafin ka Amma idan mun tashi daga taron nan
kasa meni a Office''
duk wannan magana da yayi cikin harshen turanci yayi shi gyaɗa kai kawai Sheed yayi
bece komai ba dan yasan dashi yake kansa a ƙasa Amma yabar danna wayan da yake yi
sauran mutanen gurin ma duk shiru suka yi dukkan su ba musulmai bane shi ɗaya ne
musulmi a cikin su hakan kuma be dame shiba baya shiga shirgin da bana saba ogan su
ne wato THE GENERAL OF THE ARMY tsoho ne ya ɗan manyan ta kaɗan ze kai kusan 50 to
52 years magana ya fara cikin harshen Turanci kaman haka,
''ba komai ne ya tara mu anan ba face karin matsayi da nakeso na yiwa wani daga
cikin ku kuma ba komai yasa hakan ba se jajircewan sa akan aikin sa kuma ba kowa
bane wanna face RASHEED'U'DEEN DAULA'' ya kai ƙarshen maganar sa yana zubawa
mutanen gurin ido sabida yaga yanayin reacting ɗin su,da wani irin sauri duk suka
ɗago kansu zuwa ga ogan nasu suna kallon sa wasu daga cikin su fiskan su a murtuƙe
wasu kuma annuri ne kwance akan fuskan su shi kuwa gogan ko gezau beyi ba kai ko
alamun ma yaji maganan da ake yi be nuna ba, be jira jin abunda zasu ce ba ya ci-
gaba da magana '' Rasheed'u'deen Daula'' ya kira sunan shi se a sannan ne ya ɗago
kansa yana kallon ogan nasu nan ma bece komai ba nisawa yayi kana ya ɗaura da faɗin
''Sabida yanayin jajircewan ka akan aikin ka da kwazon ka da kuma yanda kake aiki
da ƙwaƙwalwa wajen gudanar da duk wani binciken ka yasa nake me farin cikin sanar
da kai cewa daga yau kaine sabon MG MEJOR GENERAL ''
Mikewa Sheed yayi ya juya gare sa ya sara masa kana cikin wani irin Voice me daɗi a
kuma dake camly ya furta ''yes sir'' daga haka be kara cewa komai ba kuma be zauna
ba yana tsaye a kamen da yake gyaɗa masa kai ogan nasu yayi kana yace ya zauna se
sannan ya zauna be kuma ƙara cewa komai ba kallon sauran jama'an hole ɗin ogan yayi
kana yace ''akwai me magana ko karin bayani'' ya tambaya yana kallon su mutum ɗaya
daga cikin sune ya ɗaga hannu kana yace'' inada magana ranka shi daɗe'' gyaɗa masa
kai yayi kana yace ''zaka iya yin maganar ka''
mikewa tsaye yayi babba ne shima ya ɗan tasa kaɗan a shekaru baze wuce 40 years ba
magana ya fara kamar haka ''Sir Amma ni agani na kaman hakan be dace ba sabida
yanayin Aikin sa kasan de yace shi ƙasar sa yake so yayi wa aiki toh akan wani
dalili kuma zaka bashi wannan wannan muƙamin shida ma ya kusa komawa kasar su kuma
ƙabilan sa daban hakan maa ai baze taɓa yiwuwa ba''
ya ƙarasa maganan a ɗan hasale da alama abun ya ɓata masa rai sosai ko kallon shi
Sheed beyi ba dama kuma already yasan hakan zata faru ogan nasu ne ya kalle shi
kana shima ya fara magana kamar haka ''cancanta da naga yayi ne yasa na bashi
wannan matsayin duk da sanin cewa ya kusa barin ƙasar kuma yana da burin sa na
ganin ya temaki Ƙasar sa yayi musu aiki tuƙuru kaman yanda ze yi aiki a Kasar sa
haka zeyi a wannan ƙasar ma kuma wannan muradi nasa shiya ƙara nuna min shiɗin yana
kishin ƙasar sa kuma ze tallafa musu ko ya koma ƙasar sa inaso kasani LG yanada
ikkon yin duk wani abun da yaga dama a wannan ƙasar wannan dama ce nabasa''
ya kai ƙarshen maganan sa ciki nuna tabbacin abunda yake faɗa tsaye LG yayi yana
kallon ogan nasu duk takaici ya lulluɓe sa yanzu kenan wanda ya kasance ba ɗan ƙasa
ba shi za'a bawa muƙami babba har MG kuma ma religion nasu ba ɗaya ba kai ina da
sakel yana can ya tafi duniyar tunani yaji ogan nasu yana cewa ''akwai wani mai
magana kuma ko babu dan sauri nake yi akwai abunda yake gaba na yanzu'' kar ku
manta duk Wannan magana da suke yi da harshen turanci suke yin sa komawa LG yayi ya
zauna yana ta saƙa da warwara a cikin zuciyan sa duk shiru sauran suka yi dan basu
da bakin magana yanda suka ga LG yayi magana Amma ba wani abu masu jin haushi nayi
miƙewa the general of the army yayi wato ogan nasu kana ya umarce su da duk su fito
a gabatar da Sheed a matsayin Mejor General a gaban duka sojojin duk mikewa suka yi
suka mara masa baya
Sheed ne ƙarshen fita komai nasa cike da izza yake yinsa suna fita gaba ɗaya
rundunan sojojin suka fara sara musu wajen da aka tanada dan manyan mutane suka
tsaya ogan nasu ne ya fara magana duk sun ƙame wuri ɗaya gaba ɗaya hankulan su sun
maida shi kan ogan nasu sanar da su ƙarin matsayin da Sheed ya samu yayi kana ya
umurci Rasheed ɗin daya zo yayi jawabi akan karin matsayin da aka basa beyi musu ba
kuwa haka ya karaso wurin ya fara magana cikin nutsuwa kaf gurin shiru ya kara
ɗauka daddaɗan kuma sassanyar Muryar sa ne kawai ke tashi cikin nutsuwa yayi godiya
da karin matsayin da ya samu kana ya ɗau alkawarin yin aiki tuƙuru don kare kasar
ya karasa maganan sa da in sha Allah duk gurin tafi suka ɗauka raf raf raf a tare
kana suka fara rera taken kasar nasu duk sun kara nutsuwa ko motsi basu yi seda
suka gama wucewa ogan su yayi wasu daga cikin sojojin suna mara masa baya haka
shima MG Sheed ya mara masa baya sabida idan baku manta ba kafun su fara taron nasu
ya umurce shi da idan sungama yana son ganin sa haka suka wuce koda suka karasa
Office na oga nasu a bakin kofan sauran sojojin suka tsaya shi kuma MG shigewa yayi
bakin shi ɗauke da excuse can kasan makoshi tsaya wa yayi ya sara masa kana ya ƙame
a tsayen da yake gurin zama ya nuna masa seda ya kara sara masa kana ya zauna
kallon sa the general of the army SOLOMON JOSHUA yayi kana yace ''Yaushe kake so ka
koma ƙasar ka'' ya tambaye shi tare da kawar da zancen ɓata musu lokaci da yayi
ɗazu dama kawai yayi magana ne dan kar sauran suga be ɗau mataki akan hakan ba Amma
shi kansa wannan bawan Allah yana masa mugun kwarjini, numfashi MG Sheed yaja kana
ya fara magana cikin tsantsan natsuwa da kuma girmama na gaba da shi cikin harshen
Turanci yace '' nan da 1 month in sha Allah sabida akwai ɗan abunda nakeso na kara
sa kafin na koma'' gyaɗa kai yayi kana yace '' abunda yasa na baka Wannan muƙamin
ba komai bane se yanda naga kake da ƙokari duk da nasan zaka koma ƙasar ka Amma
zakana zuwa sannan idan wani aiki ya taso zan iya kiran ka sannan kuma ina so yanda
zaka yi aiki tuƙuru wa ƙasar ka nan ma kayi hakan'' haka de yaci gaba da masa
bayani da kuma shawarwari kana yace zeyi magana da his Excellency wato shugaban
kasa nasu akan ƙarin girman da yaba shi shikuwa ba abunda yake yi in banda gyaɗa
kai kurum sun yi magana sosai kana ya miƙe tareda kara sara masa kafin ya nemi
izinin tafiya shi kansa ogan nasu ma tafiya zeyi dan dama taron ƙarin girman ne ya
kawo sa Amma be cika zuwa ba tare suka fito kaman ɗa da Uba gasu duka farare tass
seda ya rakashi har motan sa ya buɗe masa ya shiga kana shima ya juya wuce wa yayi
can inda suka yi packing dan shima ba abunda ze tsaya yi wucewa gida kawai zeyi
seda ya kusa isa wurin motocin sauran sojojin suka farga da shi wasu daga cikin su
sun taya shi murna sosai wasu kuma ko kallon inda yake ma basu yi ba irin su LG
DANIEL da mu karaban sa da suke tsaye da alama suna tattaunawa ne a tsaka nin su
Mash ne yayi maza ya karasa inda MG Sheed yake a tsaye da su GENERAL da BRIADERL
GENERAL suma suna ɗaya daga cikin wa'inda aka gabatar da taron tare da su sabida
matsayin su suma yanada girma suna taya shi murna tsaya wa yayi daga gefe bece
komai ba har suka gama kana duk suka wuce shima de wucewan yayi da sauri Mash ya
buɗe masa marfin mota ya shiga kana ya rufe zagaya wa yayi ya buɗe marfin gaba ya
shiga ya kalli BYRON da yake sanye shima da kayan sojojin shine yake zaune a
mazaunin driver kana yace ''lets go'' tada motan yayi suka fita daga wajen sauran
sojojin da suka taho dasu suna mara musu baya haka suka ɗauki hanyar gida

*________________________________*

💋ABUJA💋

❤️(AYRA)❤️

SE MUN HAƊU GOBE IDAN ME DUKA YA KAIMU COMMENTS LIKE AND SHARE FISABILILLAH
GARGAƊI!!!
Ban yarda wani ko wata su karan tamin book a YouTube ko wani guri ba tare da
izini na ba kuma kar wanda ya haɗa min document a bar min kayana yanda na rubuta
shi da kaina na haɗa document ɗina da kaina sannan banyarda wani ko wata su juya
min littafi ta kowani irin siga ba idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar
mutum zebimin hakki na!!!!!!!!
Don neman karin bayani zaku iya nema na ta wannan number 09060413321

🌹MHIZZ TEEMAH🌹CE TAKU HAR KULLUM🥰
🔥THE BEGINNING 🔥

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵
GARGAƊI!!!!!!!
*Ban yarda ba, ban amince wata ko wani suyi amfani da wani sashe daga cikin
littafina ba ta kowace siga,ban yarda a karanta min shi a YouTube ba, ko a haɗa min
document duk wacce tayi hakan ko yayi hakan koda Allah nabar mutum se ya bi min
hakki na!!!!*

Free page 14_15

💋ABUJA 💋
❤️(AYRA)❤️
Ayra na fita daga ɗakin Anty tayi wani irin juyi kaman guguwa sega ta akan gado gif
kaman an wullata,Ayra kuwa tayi matuƙar razana da ganin wannan abun ba kaɗan ba ta
ruɗe tana fita daga ɗakin wani irin rawa jikin ta keyi tsaya wa tayi a inda take
zama tama kasa zaman sabida abunda ta gani yafi ƙarfin Brain ɗin ta jikin ta har wa
lokacin rawa yake yi rasa abunda zatayi tayi tama rasa wani irin tunani zata yi dan
duk yanda kuke tunani to ya wuce nan ta razana sosai,
Indo ne ta fito daga ɗakin ta da idan ta gama aikin da zata yi bata ƙara fitowa
Amma yanzu sabida Ayra ta fito dan ta duba ta taga me take yi ko ta tafi ganin ta a
tsaye jikin ta se rawa yake yi yasa ta kara sa gurin da take dan ita duk a tunanin
ta Anty dukan Ayra tayi kama hanun ta tayi hakan yasa Ayra kara razana tana shirin
sakin ƙara sabida kwata kwata tunanin ta baya jikin ta hankalin ta ma gaba daya
yayi nisan zango sake ta tayi tana ambaton sunan ta jin an ambaci sunan ta ne yasa
ta dawo hayyacin ta ai cikin sauri ta faɗa jikin Indo ta ƙanƙame ta sosai hawaye na
gangaro mata itama indo bubbuga bayan ta ta fara yi a hankali kana ta zaunar da ita
a gurin duk da ta dawo daidai Amma jikin ta be bar karkarwa ba shiru indo tayi tana
nazarin ta kana ta fara tambayan ta meya faru shiru Ayra tayi tana tunano abunda ta
kalla a ɗakin Anty cikin sauri ta runtse idon ta da mugun ƙarfi tana girgiza kanta
da kyar ta tsaya nan ma seda Indo ta riƙe hannun ta shiru tayi batace komai ba
ganin hakan se Indo ma bata ƙara tambayan ta meya faru ba ta miƙe ta wuce ɗakin ta
a cikin ranta haka kawai taji cewa da akwai matsala Amma ta share kawai dan a ganin
ta bawai dan tafara temaka wa Ayra ze zama na duk abunda ya faru seta sani ba
wannan duk ba shirgin ta bane Anty kuwa yanda ta kifu akan bed ɗin bata kara
motsawa ba kanta a kife haka tayi ta sauƙe ajiyan numfashi kamar wacce tayi tsere
da doki can kuma setayi shiru kamar me bacci seda ta nitsu tukkuna ta miƙe idonta
sun kaɗa sunyi jawur fiskan ta ya sauya wayan ta kawai ta ɗauka kana ta fito falon
ko kallon inda Ayra take bata yi ba
Ayra ganin Anty se ta fara ƴan kame kame tama rasa abunyi gaba ɗaya seta takure
guri ɗaya ita duk a tunanin ta Anty zata ɗauki mata ki a kanta ne ko zata dake ta
duk se tabi tayi wani iri shigewa cikin falon Anty tayi ta zauna kan kujeran da ta
tashi tafara aikin danna waya saƙo ta gani na yaron Mama me suna Abdul ya turo mata
saƙo akan ranan Monday zasu dawo tasa Ayra ta gyara musu ɗakunan su ai tana ganin
haka wani irin farin ciki ne ya mamaye ta duk da ranta a ɓace yake Amma taji daɗi
Ayra kuwa da duk tabi ta takure guri ɗaya ta ƙanƙame jikin ta kanta a ƙasa baiwar
Allah batasan me yake shirin faruwa da ita ba dan wallahi dawowan yayyen ta ba
ƙaramin barazana bane a gare ta, ba abunda Anty ta mata se cewa ma da tayi ta tashi
tabar mata ɗaki ba karamin mamaki jin abinda Anty tace tayi ba haka ta mike sum sum
tabar ɗakin
direct part ɗinsu ta wuce yau duniya sabo zata samu tayi abubuwan dake gabanta
tunda bata samu zuwa makaranta ba lokacin sha biyu ya wuce tana shiga ɗakin gyara
shi tayi tass ta wanke toilet tayi wanka kana ta fito karatu ta fara yi seda taji
kiran sallah sanna ta tashi tayi ta roki Allah sosai haka ta koma bed nata ta cigba
da karatun bata ko san inasu Eshall suke ba ko sunje makaranta ko basu je ba
karatun ta kawai take yi har seda taji ta gaji sannan ta kwanta gurin daga nan
bacci yayi gaba da ita
Marwa da Eshall yau ma basu je school ba Eshall ta tafi gidan su kawar ta Christer
ƴar class nasu ne ita ma sunan ta Joseca ita ce best friend ɗin ta har rashin
Sallah da batayi ma duk Joseca ce take zuga ta sabida ita dama ba religion nata
bane a takaice de maraban Eshall da arna suna ne kawai dan tana saka farce da gashi
kai duk wani abunda arna suke yi duk tana yi church ne kawai bata zuwa shima kuma
tana son zuwa kawai de tana tsoron Dad ɗin ta ne shiyasa badan ze hana taba se dan
kawai tasan baze ji daɗin hakan ba dama kuma bawani Addini suke da shiba tunda haka
suka taso suka ga iyayen su ko iyayen nasu ma basa musu magana akan rashin sallan
su ko kuma akan wani abun da suke yi ita Marwa kam ma ba'a magana dan ba ƙaramar
yar duniya bace duk makaran ta ya kara lalata su ga kuma haɗuwar da suka yi da wasu
ƙabilun hakan ya kara wargaza musu rayuwa kuma iyayen su basu bibiyan rayuwan su
waya ma ba ƙaramin ƙara lalata su yayi ba Marwa yanzu haka ma fita sukayi ita da
kawayen ta maza da mata sun tafi yawon su (hmm Allah ya shiryar mana da yaran mu a
wannan zamani da muke ciki wasu iyayen basa bibiyan halin da yaran su suke ciki da
haka ne kuma yara suke yin duk a bunda suka ga dama a nasu ganin ba abunda za'a
musu a gida daga haka kuma se su faɗa wani mummunan abun Allah ya tsare mana ƴaƴan
mu daga mummunan abubuwa suma iyaye ya kamata ku ringa bibiyan halin da yaran ku
suke ciki Please)
*::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::*
🌹DUKKU🌹
Haka suka ci-gaba da riƙe baiwar Allah nan kullum ba suƙi kullum Sadiq yana zuw
yayi mata karatu betaba gwada duba ta ba daga yaje karatu kawai yake mata duk
karatun da ze mata bata ko motsi ko ihun da take yi ma yanzu ta dena shi idan za'a
bata maganin ludayi haka ba abinda take Yi shiru haka zasu gama bata duk abinda
zasu mata yanzu ta dena ihu ko motsi ma ta dena kwata kwata tun abun

6 / 19