SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah

Author :  FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category :  KDP NOVELS

Chapter   12 / 19

33K to 36K   out of 54.2K words

ƙarƙashi tsaron sa, zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun ya buɗe wasu
Files nan ya fara binciken sa sannan ya aika Mash ya ƙira masa Ajeeb dan ya datse
masa wasu layuka tunda shima harkan abubuwan da ya karanta kenan ya karanci
computer sosai shima Sheed ɗin ya iya harkan computer sosai dan yana wahala ka samu
soja da be iya aiki da computer ba sabida duka is under there work inde har soja ya
kai soja toh ya iya wa'inna abubuwa na farko shine computer se kuma aikin likitan
ci yana wahala a samu babban soja be iya ba, idan sun fita wani aiki wani acikin su
ya samu rauni barin ma idan a cikin daji ne toh su da kansu zasu yi treating nasa
suna tafiya be da duk wasu abubuwa da zasu buƙata sabida ko inta kwana,so yanzu ma
abunda yasa yace a ƙira masa Ajeeb kawai yana so suyi saurin gama abun ne idan ya
zama na Ajeeb yana yi shima yana yi zasu gama da wuri, befi minti uku da fita ba se
gashi ya dawo yana gaba Ajeeb na biye dashi a baya yana mamakin wai wannan gurin a
cikin gidan yake dan shide tunda yake be taɓa sanin da wanna gurin ba, Sheed yana
aikin sa duk da yaji shigo wan nasu be ɗago ya kalle suba seda ya ƙarasa abunda ya
fara kana ya ɗago ya kalli Ajeeb da wa'inna rikitattun idanun nasa cikin sauri
Ajeeb yayi ƙasa da nasa dan baze iya haɗa ido da yayan nasa ido cikin ido ba dan
kwayar idon sa yana masa kaifi wajen haɗuwa kujeran gefen sa ya nuna masa hakan
yasa ya zauna wani paper ya miƙa masa na numbers ɗin waya guda biyu yace ya duba
masa location ɗin wurin karɓa yayi ya gyaɗa masa kai sannan ya buɗe wani computer
da yake ta gefe nan ya shiga binciken number inda shi kuma Deen yana kallon yanda
yake aikin yayi shiru kaman ance ya kalli computer gefen hagun sa inda anan ya samu
number su yaga kuma suna waya sosai dan basa minti talatin basuyi waya ba, yana
kallon computer yaga yazu ma haka waya suke yi cikin sauri ya karɓi computer hanun
Ajeeb wanda yake duba daga ina number take kuma yanzu me take yi,dan shi gani yake
kaman ba aiki Ajeeb yake yiba yana karba ya fara datsan layin nasu Amma se yaga
duka layi kansu baza a iya datsan saba sun rufe yanda ba wanda ze iya datsan layin
koma wa baya yayi yana jinjina kansa hakan ya ƙara tabbatar masa ba ƙananan
terrorist bane jinjina kai kawai ya ƙara yi ya miƙe yayi hanyar fita daga gurin
suna rufa masa baya shide Ajeeb har yanzu be dena mamakin wannan abun ba yana kuma
jinjina wa Deen ɗin dan ba karamin ƙwaƙwalwa yake dashi ba.

🌹ABUJA🌹

Yau ya kama Monday a yau ne su Abdull zasu dawo wato yayyin su Marwa a kuma yau ne
zasu fara Exams ɗin su
COMMENTS
LIke SHARE
🌹Mhizz teemah🌹


💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba

Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


Page 26_27

Yau ya kama Monday a yau ne su Abdull zasu dawo wato yayyin Marwa a kuma yau
ne zasu fara Exams ɗin su, tun da asuba da Ayrah ta tashi tayi Sallah ta wuce part
ɗin Anty gyra tayi sosai kaman yanda ta saba tas sede gyaran yau na daban yake
komai tass ta gyara shi tabi Anty ɗakin ta nan ma ta gyara shi da yake jiya ta
gyara so ba wani datti yayi ba Indo ma tun da ta tashi aiki take yi kaman sarki aka
ce yana zuwa kitchen ɗin nan tas ta gyara shi Sannan ta fara aikin girkin da zata
yi tana rage wasu abubuwan, Ayrah bayan ta gama da part ɗin Anty ta wuce na Mama
tana bacci harwa lokacin bata tashi ba haka Ayrah ta gyara ko ina tana mamakin
yanda bata ga ana wani shirye shirye a part ɗin Mama ba kaman ba yaranta ne zasu
dawo ba kuma ga Mama baccin tama take yi me aikin ta ma bata fito ba hakan ya bata
mamaki sosai sede bata nuna a fili ba tsaf ta gama ta wuce ɗakunan biyun da ta
gyara jiya nan ta buɗe su ta ƙara musu gyara ko ina kamshi yake tashi kaf seda ta
gyara ɗakunan ta ƙara rufe su sannan ta wuce da key ɗin fannin Anty nan Anty ta ce
suje part ɗin Dad haka nan ma suka je bata ga dad a falon ba haka tayi gyaran tas
in taƙaice muku Ayrah yau ma ba ƙaramin aikatuwa tayi ba dan seda ta gyrah kaf part
part na gidan gaba ɗaya banda na ukun wanda yake a tsakiya shine kawai bata gyrah
ba, seda ta gama gyara part ɗin Dad se gashi ya fito ta tsugunna har ƙasa ta gaishe
sa Amma ko kallon ta beyi ba haka ta ƙaraci tsugunon ta ta miƙe tana kallon agogon
bango 7:45 ta gani da sauri ta wuce part ɗin su ganin ta kusa latti kuma bata ci
abinci ba gashi wani irin bala'e'en yunwa take ji kuma Exams zata rubuta ai baza ta
iya rubuta wa bama inde har bata ci abinci ba,tana shiga ta fito da uniform nata
wasu daban ba wanda ta wanke ba ta ajiye su kan bed nata kana ta wuce toilet ɗin ta
kwaso kayan da ta wanke gaba ɗaya ta ninke su na Marwa tasa mata a drawer ta nata
ma tasa a nata drawer babu kowa a ɗakin su Marwa da Eshall basu nan wanka ta shiga
ƴar shap shap ta saka kayan ta tin a cikin toilet ɗin ta fito kaman yanda ta saba
ta mayar da kayan da ta tuɓe lokacin kusan 7:52 sauri sauri de ta saka Socks nata
ta rataya jakan ta yau bata ma san ko munib ya tashi ba dan bata tashe shiba tsabar
yanda abubuwa suka mata yawa yasa ta manta har ta fita a ɗakin su Eshall basu dawo
ba part ɗin Anty ta shiga se ganin munib tayi cikin shiri yana cin abinci da sauri
ta ƙarasa cikin ɗakin ita ma ta zauna kusa da munib ganin Anty bata nan tare suka
ci abinci tas suka cinye sa munib yana ce mata meyesa yau bata tashe saba,bata ma
basa amsa ba se ji suka yi Bus nasu yazo haka tamiƙ tana riƙe da hanun sa ɗayan
hanun kuma lunch box nasa suka fita ba ƙaramin kyau suka yiba yanda suke tafiya a
taren kaman adda da ƙani hakan ba ƙaramin matching yayi ba har Bus ɗin nasu suka
shiga suka zauna nan ma guri ɗaya zaman ta bada jima wa ba sega su Marwa da Eshall
ma sun shigo tayi mamakin ganin su a ranta tana cewa kenan dama zasu je toh a ina
suka shirya? Kode seda na fita ne suka shiga suka shirya?, kawar da zancen tayi dan
ganin bame bata amsan tambayoyin nata har suka isa ba wanda ya ƙara magana duk fita
suka yi lokacin wajen 8:10 zasu shiga Exams ɗin by 8:30 so suna da sauran 20mns da
zasu ƙara maimaita karatun su kowanen su class nasu ya wuce yayin da itama ta wuce
nasu class ɗin

A bangaren Ruma washe gari Monday cikin shirin ta ta fito falo direct gurin dining
ta nufa inda taga Mom na zaune da alama ita ma fitowan ta kenan kujeran kusa da ita
taja ta zauna tace ''good morning Mom'' shafa kanta Mom tayi kana tace ''kin tashi
lfy auta na'' gyaɗa mata kai tayi haɗe da turo baki jin Mom tace mata auta se ta
ƙara shagwaɓewa mutmushi kawai Mom tayi ta girgiza kanta kana ta fara saving nasu
suna ci suna hira seda ta gama kana tace

''Mom ina Abba zan tafi kinga yau zamu fara Exams'' ''masha Allah, Allah ya bada
sa'a auta na yasa ku fara a sa'a'' Mom ta faɗa ita ma tana miƙewa kana ta cigaba da
cewa ''Abban ki be shigo ba'' lunch box ɗin ta ta ɗauka kana tace ''toh shikenan
Mom idan ya shigo kice masa na tafi kuma kice yamin addu'a in cinye Exams ɗin
kinji'' ta faɗa tana langwaɓar da kai, gyaɗa mata kai Mom tayi tazo har bakin ƙofan
falon kana ta shafa kan autar nata sannan tace ''Allah ya tsare min gaba da bayan
ki ya bada sa'an jarabawa Allah ya bada sa'a'' Ameen ta amsa kana ta fita tana mata
bye ita kuwa Mom juyawa tayi ta koma falo a ranta tana lissafa saura kwana nawa su
Ammar su dawo, ita kuwa Ruma ta samu driver na jiranta shiga motan kawai tayi suka
cilla hanci motan waje suka nufi makaranta lokacin 8:00 tana ta Allah yasa su Ayrah
da Ashfat sunje,koda ta shiga class nasu Ashfat kawai ta kalla haka suka gaggaisa
Ruma na tambayan ta ya mami wato mamar Ashfat ɗin kenan nan de suka fara karatun
papers da zasu yi yau suna cikin haka se ga Ayrah ma sunyi farin ciki sosai da
zuwan ta dama suna ta tunani kar tazo late se gashi ta zo nan suka ɗaura karatun su
tare gwanin ban sha'awa sunyi group nasu su uku suna karatun su basu shiga harkan
kowa a cikin class ɗin har time na shiga Exams nasu yayi haka aka zo seda aka canza
wa kowa wajen zaman sa inda aka kai Ruma can baya ita kuma Ashfat tana tsakiya
Ayrah kuma gaba haka de aka gwamutsa sauran ƴan class ɗin ma sannan aka raba musu
paper tunda aka bawa Ayrah nata paper bata ƙara ɗagowa ba ta duka abunta ta fara
rubutu bata ko kalli kowa ba har ta aka fara summiting yayin da ita ma ta ƙara duba
nata sannan ta tashi tayi summit nasa ta fita a class ɗin bakin dakalin ajin nasu
ta zauna ta ciro ɗayan littafin ta ta fara dubawa tana zaune a gurin har su Ashfat
suka fito suka zauna abunsu suka ta karatu,kowani paper suna yin 1hr 30mins ne zasu
yi break na 1hr by 12:30 zasu koma gida kullum paper biyu zasu nayi haka suka yi
karatun su sosai suka yi duk wani abun da zasu yi sanna suka shiga last paper su,

A gida kuwa se gyare gyare da shirye-shirye dawowan manyan yayu ake Mama de tana
ɗakin ta ba abunda tayi sede kuma yau bata fita ba tana de kwance ne bata damu da
wai yau ƴaƴan ta zasu dawo ba kwata kwata ma kaman bata san da dawowan nasu ba Anty
ne de take ta rawan ƙafa tun safe Indo take fama da aiki girki kala kala ake yi
sabida su ɗakin Anty fess ba dirty Dad ma yana gida be fita ba, wajen ƙarfe 11 dad
ya tura driver Airport na Abuja yaje ya ɗauko su yaso zuwa ɗauko su da kansa Amma
Anty ta hana sa hakan yasa ya aika driver, wajen minti talatin get man ya buɗe musu
get sakamakon hon da driver yayi suka shigo cikin gidan har second get suka wuce a
dede part ɗin Anty ya tsaya duk su Anty da dad suna tsaye a gurin,fitowa driver
yayi ya buɗe marfin gefen hagu fitowa wanda aka buɗe wa yayi kyakkyawan saurayi
ne,fari baida wani tsayi sosai kuma ba guntu bane sanye yake da three-quarter da T-
shirt ruwan toka yakai ƙasa da gwiwa sa da ka ganshi kaga tantirin ɗan Air fiskan
shi ba halamun rahama tana nan a daƙile ya haɗu askin kanshi irin na gayu wanda
ake aske gefe da gefe abar iya tsakiyan kai da gashi bakin sa baƙi da alama yana
shan wani abun a shekaru baze wuce 29 ba kafan sa na sanye da Gucci hanun sa kuma
na sanye da wata siririyar chain irin na maza ƴan Air dayan gefen aka buɗe the same
wani saurayi ne kyakyawa dede gorgodo ya fito fari baida tsayi sosai yana sanye da
T-shirt baƙi da jeans fari daga ka gansu kaga ƴan uwa kuma jini ɗaya,da sauri su
dad suka ƙarasa kusa dasu sukayi musayar runguma gabaɗayan su kana suka wuce ɗakin
Anty driver ya kai musu da kayan su bakin part ɗin Anty ya wuce ya juya da motan
packing space ya faka ta, zama suka yi sunɗan taba hira kaɗan inda duk Abdull yafi
maida hankali kan hiran da suke shi kuwa Fa'iz wayan sa kawai yake danna wa tun ɗan
gagaisawa da suka yi be ƙara cewa komai ba suna cikin hiran yaushe gamo inda Anty
take tambayan su ya American Abdull ya amsa da lafiya yanzu sun gama karatun su
dake karatu ne ya kaisu shi Abdull kasuwan ci ya karanta dan shi yake ra'ayi kuma
mahaifinsa ɗan kasuwan ne, miƙewa duk suka yi bayan taɓa hiran da suka yi duk suka
wuce part ɗinsu domin su yi wanka su huta suka yi musu sallama sannan suka fita
miƙewa Anty tayi tace da dad ya tashi su kai musu kayan su haka kuwa suka rufa musu
baya da kayan nasu kowannen su aka kaimasa ɗakin sa sannan suka juya suka barsu dan
su samu su huta Anty da dad suka wuce part ɗin sa su kuma duk wanka suka yi
kwanciya Abdull yayi dan ya matuƙar gaji Fa'iz kuwa jakan kayan sa ya buɗe inda ya
fara ciccire komai yana wurgarwa neman abu kawai yake seda ya cire komai na jakan
ya ɗauki computer sa da wani hard coverd book zama yayi ya buɗe computer ya fara
aikin sa yana yi yana rubutu a cikin hard book nasa acikin su ba wanda ya nemi
Mama, a ɓangaren Ayrah kuwa bayan sun fito daga last paper su na yau wurin 12:30
aka tashe su Ayrah tabi Bus dan komawa gida yayin da Ashfat da Ruma dake ɗaukan su
ake zuwa yi suka tsaya bayan sunyi sallama da Ayrah kusan a tare aka zo ɗaukan su
kawai se Ruma ta shige motan gidan su Ashfat ɗin tace wa driver ta idan ya koma
yace tawuce gidan su Ashfat nan ya gyaɗa mata kai suka wuce Ashfat se daɗi take ji
dama sun jima basu je gidan juna ba kuma ƴan uwa ne,bakin wani get driver yayi hon
me gadi ya buɗe masa babban gida ne ya haɗu ba laifi bangare biyu ne a gidan, yana
parking suka fito da gudu Ashfat tayi part nasu ta shiga ko daman yin sallama bata
samu ba ta fara kwala wa Mami ƙira se dariya take yi baki yaƙi rufuwa wai tana son
faɗa mata Ruma tazo, ''Mamiiiii Mamiiii wai kina inane'' ta ƙara faɗa da ƙarfi
lokacin har Ruma ta shigo Mami dake kitchen tana girki jin yanda tilon ƴar tata
take ta kwala mata ƙira yasa ta fitowa da sauri ita duk a tunanin tama wani abune,
ganin Ashfat se murmushi take ga kuma Ruma a bayan ta yasa ta yin murmushi tare da
kama haɓa ta fara magana ''ikkon Allah yau wa nake gani a gidan nan kaman baby wata
sabon gani'' ta ƙarashe da alamun mamaki da kuma barkwanci irin nata akan fuskan
ta, dariya Ruma tayi kana taje ta rungume Mami tace ''a wallahi Mami nice yau anan
zan wuni inaso kimin special girkin nan naki me daɗi'' kumatun ta Mami taja sanna
tace ''kai ƴar rigima ai nama gama abincin idan zaki ci se nasa miki'' girgiza kai
tayi tace ''a'a bayan zuba ciki na a koshe yake ina baffa Habib'' raba jikin su
Mami tayi sanna tace ''ai ya fita tun ɗazu se anjima idan ya dawo'' ''toh seya dawo
ai ina nan har dare'' wuce wa sukayi ita da Ashfat sukayi ɗakin Ashfat ɗin gyara
jikin su sukayi inda Ruma ta saka kayan Ashfat ɗin kuma sun zauna mata sunyi ciff
kaman nata, sun baza littatafan su akan bed ɗin Ashfat ɗin su a dole karatu zasu
yi, tare sukayi karatun nasu sosai sede suka gama suka shiga hira sunɗan taɓa kaɗan
sanna suka fito falo ana suka taras da Mami zama duk suka yi kusa da ita dayake
tana zaune kujera me zaman mutum Uku hakan yasa suka saka ta a tsakiya, Mami ne ta
fara magana tace ''Ruma ya gidan naku da Adda Nana na ina fatan kuna lafiya tunda
kika zo bamu zauna ba'' ta kai ƙarshen maganan ta tana miƙewa tace dasu suzo suci
abinci, tsaf seda suka zauna a dining tayi saving nasu Sannan Ruma ta bata amsa da
cewa ''lafiyan mu kalau'' ta faɗa tana shagwaɓe fuska kana ta ɗaura da cewa ''ni
wallahi Mami ki dena kiran Mom Adda Nana wallahi ba daɗi kawai gwara kema kin ƙiran
ta Mom ɗin'' ta ƙarasa a tsananin shagwaɓe dariya Mami tayi sannan tace ''toh ƴar
lelen Mommy ta zan dena kinsan in abu ya zauna a bakin mutum se a hankali'' cigaba
da cin abincin su suka yi Ruma ƙaɗa mata kai kawai tayi can bayan sunyi nisa da cin
abincin ne Mami tace ''ina yayun ki ne wai yaushe zasu dawo wallahi sun jima SHEED
fa yanzu ya kai kusan 8yrs kuma tunda ya tafi be dawo ba ko sau ɗaya har gwara
Ajeeb da Ammar suna

12 / 19