Author : FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category : KDP NOVELS
abun tausayi ba zato ba
tsammani kawai se jin saukan duka tayi a jikin ta ta ko'ina a tsananin ruɗe ta mike
dishi dishi ta fara gani kafun ta fara kallon raɗas dukanta kawai anty takeyi ba ji
ba gani haka take sharba mata bulala a jiki se kuka take yi tana neman a gaji Amma
ina ba mejinta kuma kodama ana jinta ba wanda ze ceceta haka anty tahada mata
hawaye da majina sannan tafara magana tana haki domin kuwa itama kanta ta gaji se
haki takeyi ''Dan ubanki in saki wanki kifara bacci sannu Maji daɗi muna fuka yau
zakici ubanki a gidan nan!!'' taƙarashe maganarta tana hakadeta da kafanta seda ta
fado daga kan dakalin da take baiwar Allah se kuka take yi cikin kuka tafara magana
''Anty dan Allah kiyi hakuri bazan kara ba wallahi baccin ne ya dauke ni Amma
nagama wanki''tafaɗa tana sheshekan kuka hawaye da majina duk sun hadu sun bata
fuskan wani irin tsawa ta daka mata seda ta firgita ''dalla rufemin baki wawuya
kawai'' kama bakinta tayi irin kaman yanda taga a makaranta ake cewa su kama
wataran so take ta hadiye kukan Amma ta kasa sabida ko motsi tayi se taji jikinta
kaman ana fasa mata shi sabida zafin duka wucewa Anty tayi tana cemata ta bita
mikewa tayi da kyar kasa mike tsayin ta tayi sabide kugunta da taji ya rike
sanadiyan hankaɗata da Anty tayi a sunkuye ta fara tafiya kafin da kyar ta iya mike
tsayin ta nan ma da kyar take tafiya shiga cikin dakin suka yi Anty tasata Neel
down hanun ta sama a tsakiyan falon haka tayi tana kuka mara sauti wucewa tayi ita
kuma ta koma ɗakin ta ta kwanta abunta ko a jikinta seda tayi kusan 1hr sannan Anty
ta fito tana ganinta ta ja tsaki ta zauna a kan kujera tana danna waya Allah sarki
Ayra duk guiwoyinta sun sage har rawa sukeyi kaman zata dungura ƙasa seda ta gama
abunda zatayi sanna ta mike ta rankwashe ta tare da cemata ta bace ta bata guri da
kyar ta iya mikewa kafanta na rawa haka take tafiya da kyar da kyar seda ta kusa
fita daga dakin taji muryan Anty tana cemata gobe bazata je makaranta ba zatayi
mata aiki toh kawai ta amsa mata don Allah nagani ta ƙagu tabar dakin haka ta fita
ta wuce part ɗin su gashi yana da tazara da part ɗin Anty Amma haka ta wuce ɗakin
su tana shiga toilet ta wuce sabida ta samu tayi wanka ko zataji saukin abunda
takeji.....
Game bukatan karanta book na daga farko har ƙarshe ze iya nema na ta wanna
number via WhatsApp 09060413321
🌹Mhizz teemah🌹
💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
𝐇𝐀𝐙𝐈𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐔𝐁𝐔𝐓𝐀
🌹(Mhizz teemarh)🌹
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
Dedicated to my beloved 💔Mom💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sani ne,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏.
𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲
𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗳𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵.
5️⃣
Free Page
Wanka tasamu tayi da ruwan ɗumi tanayi tana share kwallan idonta dakyar ta
karasa wankan maida kayan jikin ta tayi sabida bata shiga da wani kaya ba a haka ta
fito direct bed nata ta wuce rigan baccin ta tafitar doguwa mara nauyi me laushi
toilet ta koma tasaka ta fito bata tasa hula ba hakan yabawa dogon gashin kanta
bamar bayyana wani irin gashi take dashi me ɗan uban yawa har gadon bayan ta baƙi
ne sosai gashi da tsayi da cika bata daure shi da ribon ba sabida yanda duk take a
wahale da alamun datti a jikin gashin dan yanda bata samu lokacin kanta bama balle
na wanke kai yawan gashin ma bazata iya wanke shiba dan idan tace zata wanke seta
ɓata more than an hour's dan sede kawai ta jagwalgwala kan takasa gyara shi shiyasa
ma take barin shi da dattin sa Amma kullum yana cikin hula dan gaba ɗayan shi take
turashi cikin hula in zata makaranta kuwa ɗaure shi takeyi ta naɗe shi duka a ribom
ɗin
Seda ta fito daga wankan nema sannan ne ma ta ankara da su Eshall da duk suka
baje a kan bed, bata tsayabi takansu ba sabida itama takanta takeyi already tayi
alwala darduma ta shinfida nan ta haɗa sallolin da batayi ba tayi su sannan ta haye
kan bed dinta takwanta dan tasamu tayi bacci ko zata rage abunda take ji koda ta
kwanta ma ta kasa bacci hawaye kawai take yi tana tunanin Ummin ta (haka take kiran
maman ta) tanajin ƙuna a cikin zuciyar ta batajin dadin abubuwa da dama yarinya ce
ita dole tana bukatan wanda zena ɗaura ta a kan hanya Amma bata samu ba, ba abunda
ta sani se wahala,ƙunci kiyayya ga rashin uwa a kusa kuma batasan wani abu wai shi
soyayyar mahaifiya ko jin daɗin Rayuwa ba, haka tayi shiru hawaye kawai yake zuba
mata kukan ma yadena fitowa shiru tayi likmau kamar me bacci tana haka har bacci
barawo ya sace ta, washe gari dakyar ta iya bude idanunta da suke duk a kumbure
sabida kukan da tasha kafun tayi bacci
bakinta dauke da addu'a ta farka dafe kanta dayake sara mata tayi fuskanta ya
kumbura abunku da farin mutum idanun nan sun ƙanƙance mikewa tayi direct ta nufi
toilet alwala tayi ta fito dadduma ta shumfuɗa Amma kwata kwata ta kasa tsaya wa
tsabar yanda take jin karta kaman ba'a jikin ta yake ba sede zama tayi tayi sallah
a zaune tana idarwa taɗan yi addu'o'i a gurin ta kwanta kan abun sallah sabida
taɗan huta kwata kwata bata jin dadin jikinta seda ta kara kusan 1hr kana ta mike
ta naɗe darduma ta ajiye shi inda take ajiye su Marwa ko suna ta shan baccin su da
idan ta tashi Sallah tana tada su Amma wataran ha duka take sha wataran kuma su
mata masifa hakan yasa ta dena tada su duk Time da suka ga dama sutashi,fita tayi
daga ɗakin tana tafiya tana ɗingishi fitan ma wallahi dan yazame mata dole ne Amma
da bazata fita ba bayanda ta iya ne kawai direct part ɗin mama ta wuce dan inde ta
riga da taje na Anty bazata fito da wuri ba shiyasa gwara ta fara gyara wa mama
nata shiga falon tayi bakinta dauke da sallama kasa kasa kaman yanda ta saba haka
ta fara gyaran tanayi tana huta wa dan Allah na gani tana wahala seda tayi tayi
komai tass tasaka turaren ɗaki sannan ta fice daga part ɗin dama sauri sauri tayi
sabida bataso mama ta tashi dan tasan zata iya sakata wani aikin wucewa tayi part
ɗin Anty,batasan meye sa tace baxata je school ba yau kuma bata ji daɗin hakan ba
batason fashin makaranta bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa kaman yadda tasaba haka
ta shiga ɗakin bakowa a falon da alama yau bata tashi ba Amma indo me aiki tana
kitchen jin halamun indo a kitchen se kawai ta karasa kitchen ɗin Indo na kallon ta
ta tallafa mata tana mata sannu dan tasan tabbas yarinyar tana wahala
kashe gas ɗin da take girki tayi ta kama ta suka wuce ɗakin indon wanda yake
gefen kitchen ɗin sabida ganin Anty bata fito ba suna shiga ta zaunar da ita a
bakin gadon ta shima ɗakin yanada ɗan girma se toilet a gefe shigewa toilet ɗin
tayi ta ɗibi Ruwa me zafi a cikin ɗan bowl ta fito dashi tare da towel karami zama
tayi gefen ta a ƙasa ta ɗaga kafan nata hakan da tayi ma seda Ayra ta ɗan yi ƙara
kaɗan dan ko ita idan tana tafiya jan kafan take yi sannu ta mata kana ta ɗaura
ƙafan a kan cinyan ta ta matse towel ɗin kaɗan ta fara matsa kafan kara Ayra ta sa
ai ba shiri ta cire towel ɗin ta ɗago tana kallon ta tare da tambayan ta meya faru
da zafi Ayra ta faɗa har hawaye ya taru a idon ta sannu tayi ta mata kana tace tayi
shiru kar Anty ta fito dan wallahi tasan inde Anty ta fito taga abunda take yi wa
Ayra to takara mata wani matsalan ne kuma itama kanta tashi ga matsala, seda ta
gama mata bayanin idan ta matsa mata ƙafan zataji daɗi zedena mata ciwo kana ta
kara ɗaukan towel ɗin tana matsa mata kafan nan ma ahankali take yi ba karamin
namijin ƙoƙari Ayra tayi ba duk da haka seda tayi hawaye sabida akwai zafi sosai ta
daure ba kaɗan ba nan Indo tayi ta gama maida bowl ɗin tayi kana ta dawo tace da
ita ta kwanta ta huta ita zata gyara ɗakin yau kam kawai ta huta zuwa an jima tana
ɗan tsoro da fargaba haka ta kwanta akan bed ɗin Indo kuwa fita tayi a ɗakin ta hau
gyaran ko ina ta gyara shi tass kana ta koma kitchen ta cigaba da girkin har tagama
gyaran ɗaki da girki duk Anty bata fito ba taji daɗin hakan sosai ganin Anty bata
tashi ba ɗaukan abincin da ta ɗiba zata bawa Ayra tayi ta koma ɗakin nan tasamu
Ayra tayi bacci Allah sarki baiwar Allah dama baccin be ishe taba abincin ta ajiye
a ƙasa kawai ta zauna tan kallon Ayra tana kuma tunanin Rayuwan mutanen gidan da
Allah ya jefota matsayin 'yar Aiki
A school kuwa yau da su Ashfat basu ga Ayra ba duk se suka damu sunyi wani
jugum jugum sunata tunanin kome ya hanata zuwa kowani malami/malama idan suka shiga
se sun tambayi 'yan class ɗin meya hana Ayra zuwa duk da ba yau tafara Rashin zuwa
ba idan yau tazo toh gobe bazata zoba haka take kullum tana cikin fashi tanada
ilimi sosai ga shiga rai shiyasa duk malaman suka shigo basu ganta ba sesun tambaya
har aka tashi de su Rumaisa kam basu wani ji daɗin karatun ba haka kowanen su ya
koma gida zuciya a cunkushe gashi ba waya take da shiba balle su kirata har su duk
suna da waya kuma sunɗan girmeta dan ita Rumaisa tanada 13 years itama Ashfat 13 ne
sun girmeta da kusan 2years
'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
A bangaren rumaisa kuwa koda ta koma gida bata samu Mom a falo ba dakin ta tawuce
wanka tayi tareda alwala Sallah tayi kana ta fito dan cin abinci dakin mom tashiga
nan tace mata ta dawo sannan suka fito tare dan cin abinci sabida ita mom din su
bata cin abinci se Ruma ta dawo na safe ma tare suke ci dining suka wuce mom tayi
saving ɗin su suna ci suna taba hira a nan ne ma take gaya mata ai yau Ayra bataje
school ba tanuna damuwanta karara har tana tambayan meya hanata zuwa Amma se Ruma
tace itama bata sani ba haka suka karaci cin abincin su suka tashi yau kam bata ko
shiga gurin ladi ba tunawa tayi da kwana biyu bata shiga gurin Ammii ba hakan yasa
ta fita daga part ɗin nasu dan taje ta gaishe da Ammii part din ta tawuce shiga
tayi da sallama dauke a bakinta tashiga falon Amma shiru taji wucewa cikin dakin
tayi tana kara doka sallama hakan yasa Ammii dake cikin daki tana bacci farkawa
fitowa tayi daga dakin ita kuma tasaka kai zata shiga kenan ribas taci ganin ta
fito da fara'a suka gaisa tare suka koma falon anan suka gaisa a shekaru Ammii zata
kai 30 bata taɓa haihuwa ba suna zaman lafiya da mom se suyi kusan satituka ma basu
hadu ba se ita Ammii ne sa'i da lokaci take shiga gurin mom ɗin suɗan taba hira duk
da ita mom bata sakewa da ita sosai haka kawai itakuma jinin su bezo daya ba
itakuma Ammii tanason shigewa Mom ɗin hakama yaranta domin kuwa taja yaran ajiki
sosai kuma suna sakewa da ita Amma banda babban ɗan shi ko kula ta ma ko shiga
safgan ta bayayi,
Sunɗa taba hira kadan kafin Ruma ta mike sabida tanaso suyi waya da ashfat
shiyasa tace mata zata tafi.....
🌹Mhizz teemah🌹
💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_________________________________________________________*
Dedicated to my beloved 💔Mom💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰
𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵
Free Page 6_7
Sunɗa taba hira kadan kafin Ruma ta mike sabida tanaso suyi waya da ashfat
shiyasa tace mata zata tafi cike da fara'a Ammii ta rakata har bakin kofa tana
tambayan ta yaushe zata dawo cewa kawai tayi idan tagama abinda zatayi zata dawo
aikuwa Ammii tace seta dawo haka ta wuce part ɗin su Ammii ma ta koma dakinta koda
ta koma part ɗin su a falo taga Mom kaman dama jiranta takeyi tana shiga dakin mom
ta mike tafara tambayan ta ina taje duk da tasan gurin Ammii taje hakan kuwa tace
mata daga gurin Ammii take girgiza kai kawai Ammii tayi tana taune labbanta na kasa
sannan ta wuce tabar Ruma tsaye tana kallon reaction ɗin mommyn nata, basar wa tayi
kawai ta wuce dakin ta wayanta ta daga ta kira Ashfat hira sukayi sosai kana daga
ƙarshe Ruma tace wa Ashfat ta gaishe mata da Mimi wato Mahaifiyar Ashfat ɗin kenan
sukayi sallama ta katse kiran tunani ta fara yi ko takira ya Ammar ko ya Ajeeb
tasan duk inda aka samu ya Ammar to ya Ajeeb ma yana gurin se kawai ta yanke
shawaran kiran ya Ammar ɗin inyaso se su gaisa gaba dayan su cikin sa'a kuwa tana
kiran number ya Ammar ya shiga har murna tayi domin kuwa idan basu suka ƙira ba
yana wahala a same su seda tayi ringing har takusa katse wa sannan taji an ɗaga ai
kuwa murna sosai tayi kafun ma tayi sallama wata murya me daɗi da sanyi tayi
sallama amsawa tayi dan tundaga jin yanayin muryan tasan ya Ammar ne gaishe shi
tayi cike da girma mawa kaman yana ganinta domin kuwa gaba ɗaya nutsuwanta ta haɗa
lokaci ɗaya sunɗan taba hira tana tambayan shi ya aiki amsa mata yayi shima yana
tambyan ta ina Mommy nan tace mai tana ɗakin ta a kaimata ne a'a yace sannan ya
ɗaura da faɗin ya makaranta dafatan de tana karatu alhamdulillah tace mai tana
tambayan shi ina ya Ajeeb mika wa Ajeeb wayan kawai yayi aikuwa yana karba
''Assalamu alaiki 'yar ƙanwata ta kaina'' yayi magana yana ɗan dariya aikuwa kaman
jira take suka shiga hira suna dariya ya Ajeeb akwai shi da abun ban dariya seda ya
tabbatar ya sata farin ciki Sannan ya tambaye ta ya mom take aikuwa tace tana nan
lafiya qlau ta ɗaura da cewa ''ya Ajeeb yaushe zaku dawo ina yaya Deen'' duk tahada
masa tambayoyin lokaci daya sautin dariyan shine ke fita daga cikin wayan itama
dariyan takeyi seda yaɗan tsagaita sannan yace ''zamu dawo soon inshallah ina fatan
kina mana addu'a?'' aikuwa cike da murnar sunkusa dawowa tace ''ina muku my
brothers'' toh kawai yace sake tambayan shi tayi ina yaya Deen yana dariya yace
''kai 'yar kan wata toh baya nan wani abu ne'' ya tambaya cike da neman tsokana
aikuwa nan take yanayin ta ya sauya tace ''babu komai kawai dama zamu gaisa ne''
haka suka cigaba da hiran su kana sukayi sallama ta katse kiran tana mejin kewan
yayun nata don harga Allah tayi missing draman su da ya Ajeeb ɗin nata dailing
number ya Deen tayi da tayi saving da Best Brother ringing yayi har ya katse ba'a
ɗaga ba kara kiran shi tayi nan ma yayi ringing ɗin shi harya katse ba'a ɗaga ba se
ana ukun ne nan ma seda ya kusa katsewa sannan aka ɗaga shiru akayi ba'ayi magana
ba sallama tayi seda tayi kusan minti biyu chan se wani daddaɗan cool Voice me
tafiya da hankalin duk wata Mace voice ɗin very Cool a kuma sanyaye cikin nutsuwa
yace ''wa'alaiki Salam'' gaida shi tayi bata ko jira amsan saba ta cigaba da tam
bayan shi ya aiki seda ya kara yin shiru kafun nan yace alhamdulillah shiru ne ya
biyo baya ta rasa me zata ce masa secan taji zazzaƙar voice nashi yana cewa wani
abu ne a'a kawai tace masa ba komai Mommy ya tambaye ta nan tace tana nan Lafiya da
alama de wannan ya Deen ɗin akwai shi da izza da jan aji,taƙama dan daga yanayin
maganan shima abun a bayyane yake da tarasa mezata ce kawai setace ''yaya yaushe
zaka dawo'' shiru be bata amsa ba hakan yasa ta kalli screen ɗin wayan gani tayi
yana jinta dan be katse kiran ba se kawai tamai sallama tareda katse wayan ta a
ranta tana cewa ya Deen ɗin nan ɗan rainin wayo ne wallahi shi idan beyi niyyan
bada amsa ba shiru yake yi gashi bala'in tsoron shi take yi haka ta fara danna
wayan tama rasa me zata yi se ɗaukan books nata tayi tafara dubawa se a lokacin ne
ma tatuna da zasuyi presentations a school ɗin nasu gashi za'a yaye su su wuce
jss 1 ga Exams da zasuyi yanxu kwata kwata bai wuce 2weeeks ya rage musu ba
'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
GOMBE
( DUKKU)
Wata tsohuwa nagani tana tafiya da ɗan sauri yanayin tafiyan su na tsofi da
kyar a haka taketa sauri tana rike da kwarya wani matsakaicin gida na marasa karfi
ta shiga wani dattijo ne tsaye a bakin kofan da alama ita yake jira tana shiga
gidan kwaryan hannunta ya karɓa suka ƙarisa cikin ɗan madaidaicin gidan nasu na
laka wata mata ce kwance akan tabarma kamar me bacci tana da duhu Amma ba sosai ba
da alama bata da lafiya ne siririya ce sosai ba komai ya ramar da itaba face