SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah

Author :  FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category :  KDP NOVELS

Chapter   11 / 19

30K to 33K   out of 54.2K words

suka yi daga part ɗin
wasu ɗakuna guda biyu wanda suke manne da juna ta ɓangaren Mama suka je ganin haka
seda cikin ta ya ƙulle ta fara tunanin karde a ce su ya Abdull ne zasu dawo,bata
gama tunani ba taga Anty ta ciro key ɗakin farko buɗe ɗakin tayi duk yayi ƙura
sabida ya jima ba'a shiga ba falo ne ɗan daidai se ɗaki haɗe da banɗakin sa kujerun
an rufe su da fararen abubuwan da ake rufe kujeru,nuna mata ɗakin Anty da ta tsaya
a bakin ƙofa bata shiga ɗakin ba tayi sannan ta fara magana cike da izza da halin
ko inkula

''gobe yayun ki zasu dawo sun ce ki gyara musu dakin su dan haka ki musu gyara me
kyau idan be fita da kema kinsan sauran ki gama wannan sannan ki shiga wancen duk
ki gyara su'' tana gama faɗan haka ta wuce ta koma part ɗin ta tabar Ayrah da tayi
suman wucin gadi tana tunani watan cin ubanta yayi kenan dan wallahi tana mugun
mugun tsoron yayyen nata, taɗau kusan minti biyar tana tsaye a gurin kafin kuma
kaman wanda aka tsikara tayi saurin dawowa tunanin ta shiga ɗakin tayi ganin yanda
duk yayi ƙura haka ta shige cikin ɗakin ko ina yayi ƙura ga datti ga kuma wasu daga
cikin kayayyakin su a zube a ƙasa wanda suka tafi suka barshi a gurin banɗakin ma
duk yayi kura ga datti tana nan de maƙale da hijabin nan nata kaman na gado dashi
take kwana dashi take tashi kullum ga zufa tana haɗa wa ba halin ta kunna fanka ko
AC tunda gyara zata yi ga ƙura zena dawo mata da aki baya ne tattare ɗakin ta fara
yi kayayyakin da suke zube a ɗakin duk tasa su cikin wash machine anan taga wani
hanky cikin drawer ɗauka tayi ta ƙulle hancin ta sabida protection ga kuma ƙura
aiki ta fara ba kama hannun yaro ta ɗauki kusan past 2hr tana gyara ɗakin ɗaya
kawai yayi ƙura ne na wuce misali sunyi kusan 2yrs basa nan shiyasa tsaf ta gyara
nan da nan sega ɗakin yayi kyau


ta gyara ko ina harda canza bed sheets ta wanke banɗakin nan tass har jikin bango
komai yayi clean seda ta gama sannan ta kunna washing machine ɗin tana tsaye a
gurin tsaf seda ya gama ta fito da kayan taje ta shanya su ta kunna AC falo dana
ɗakin duka ta saka Air freshener ɗakin ya ɗauki kamshi ba ƙaramin kyau ɗakin yake
dashi ba yayi tsaf tsaf kaman ba'a taɓa shiga ba ita kanta seda taji ina ma ta
kwanta ta huta Amma ba hali tunda bata gama ba saura ɗayan ɗakin lokacin azahar ma
tayi ta kashe wutan ɗakin AC kawai ta bari sabida ɗakin yayi sanyi Amma ta rage
power sa sannan ta fito daga ɗakin ta rufe harda key ta zare key ɗin ɗayan ɗakin ta
buɗe da ɗayan key ɗin dayake duk ajiki suke,shiga ɗakin tayi ta buɗe ko ina already
ta cire hanky data ɗaura tun a ɗakin chan ɗin ta wanke sa,bata taɓa komai a cikin
ɗakin ba kawai ta buɗe ne se tace bari taje tayi Sallah ta dawo seta ƙarasa gyaran,

part ɗin su ta wuce her heart is racing tana addu'a Allah yasa kar Anty ta leƙa
bata ganta ba dan tasan shima wani laifi ne da wannan tunanin ta shiga ɗakin su
direct ta wuce toilet alwala ta ɗauro ta shumfuɗa abun Sallah ta zumbuɗa katuwar
Hijab ɗin ta har ƙasa ta cire ƙaramin ta fara Sallah, Marwa da Eshall har lokacin
bacci suke yi tana idar wa ta miƙe ta cire hijab ɗin tasa ƙaramin naɗe darduman
tayi ta ajiye sa tare da hijab ɗin nata bata ko kalla inda su Eshall suke ba ta
fita a ɗakin tana sauri kar tayi wani laifin kuma,


seda taji sanyi a ranta ganin Anty bata zoba ƙarasa shiga cikin dakin tayi nan ta
fara aiki tattare kayan ta fara yi ta share ta kaɗe ƙuran tahau share share ta kaɗe
kujerun ba wani datti bane ajikin su kawai ta kaɗe ne dan a rufe suke gyara dakin
tayi tass ta shiga banɗaki ma ta wanke shi seda ta gama gyara ko ina ta saka kayan
datti a washing machine ya gama ta shanya ɗakin yayi fresh kaman ba'a taɓa shiga ba
air freshener ta sakawa ɗakin ta kunna AC nan da nan ɗakin ya ɗau sanyi ga ƙamshi
zama tayi tana hutawa har ta fara gyangyaɗi taji sanyi AC miƙewa tayi ta kulle
ɗakin da key bayan ta kashe wutan dakin tabar AC kaɗai ta rage power sa bata wuce
part ɗin Anty ba se ta wuce nasu lokacin su Marwa sun tashi basa ma dakin ajiye
keys ɗin tayi kan bed nata ta ɗauki wasu kayan duguwar riga shima ta wuce banɗaki
wanka tayi tana son wanke kanta Amma ba zata iya ba kayan da ta ɗauka ta saka ta
fito hijab ɗin ɗazu ta maida kana tayi Sallah la'asar dan ta ɗauro alwala tun a
bandakin tana idar wa ta ɗauki keys ɗin ta fita direct se part ɗin Anty bata same
ta ba dan haka se ta wuce ɗakin Indo yunwa take ji kuma tasan Indo ta ajiye mata
abincin tana shiga ta zauna gefen Indo abincin da ta ajiye mata ta bata karɓa tayi
ta fara ci indo kuma na mata sannu dan tasan aiki tayi,


kullum tana son tambayan Indo wai bata da waya ne Amma se ta manta yau ko tana
cikin cin abinci ta tuna ɗagowa tayi ta kalli indo da dara daran idanun ta se kuma
ta sauƙe kanta ƙasa ta buɗe baki cikin sanyi hali irin nata da zazzaƙar muryan ta a
kuma hankali cike da nutsuwa tace ''Anty Indo ina wayan ki ne ni ban taba ganin ki
da waya ba naga bakya ƙiran ƴan uwan ki da maman ki'' kallon ta Indo tayi cikin
basar da magana tace ''bani da waya'' se tayi shiru bata ƙara cewa komai ba kallon
ta Ayrah tayi ganin kaman bata son maganan se kawai tayi shiru dama ita ba gwanar
magana bace,har ta kare abincin tass ta wanke hannun ta miƙewa tayi ta fita a ɗakin
falo ta wuce ta zauna inda take zama tana jiran Anty ta shigo tayi kusan 30min
sannan Anty ta shigo tana ganin ta tayi ƙasa da kanta tace ''Anty na gama'' miƙa
mata hanu Anty tayi ganin hakan yasa ta gane key zata bata samata key tayi a hanun
seda ta juya ta fara tafiya sannan tace ''biyo ni'' binta tayi kaman yanda ta faɗa
ɗin hanya ɗakunan suka yi ta buɗe duk taga yanda tayi gyaran seda ta duba duka
ɗakunan duk Ayrah na biye da ita gyaɗa kai kawai tayi ta fito ta rufe ɗakunan bata
ce komai ba tayi hanyar part ɗin baba ganin hakan se Ayrah ta juya zata yi part ɗin
Anty,


har tayi gaba se taji kaman ba'a biyo ta juya wa tayi se taga Ayrah kam har ta kusa
shiga ɗakin ta,wani mahaukacin tsawa ta daka mata ''ke ina zaki ba cewa nayi ki
biyo niba'' da sauri Ayrah da har ta taka step zata taka na biyu ta juyo ta biyo ta
harda gudun ta part ɗin Dad suka ƙarasa nan ma wani sabon aiki ne dan seda ta gyara
ɗakin nan tas gaba dayan shi yayi part ɗin Mama da na Anty tsabar girman sa Amma
haka ta gyara shi ba ƙaramin gajiya tayi ba, ta aikatu iya aikatuwa yau ɗinnan ko
iya gyaran part ɗin Dad aka barta dashi ma aiki ne ballan tana tun safe bata huta
ba ta gyara part ɗin Anty tayi na, Mama, tazo tayi na yayyun ta wanda yaji ma a
rufe duk yayi ƙura,after that tazo tayi na dad ɗin ta, haba dole ma duk wanda yaji
irin aikin da tayi ya tausaya mata ta aikatu ta kuma gaji duk me zuciyar imani seya
ji tausayin ta a ƴan kananun shekarunta nan,


magrib aka ƙira hakan yasa ta baro part ɗin Anty wanda bayan ta gama gyaran part
ɗin Dad nan ta wuce munib kullum bacci yake sha abunsa kaman kasa baya wani wasa
toh ma dawa zeyi wasan bayan shikaɗai ne daga yaci abinci se bacci se kuma idan
yanada karatu yayi ko yaje gurin Ayrah suyi tare shi yasa bayan ta gama gyara part
ɗin Dad ta koma na Anty suka yi karatu da munib dan tasan idan ba ita ba bawanda ze
koya masa kuma gobe suna da Exams,

tana shiga part nasu bata taras da kowa ba alwala tayi tayi sallah as usual ta
zauna har seda tayi isha sannan ta tashi books nata ta ajiye kan bed sannan ta
ɗauki uniform nata da kayan ta da sukayi datti ta wuce toilet ta fara wanke su tana
cikin yi su Marwa suka shigo se a lokacin Marwa ta tuna zata bawa Ayrah wanki jin
ƙaran ruwa a banɗaki yasa ta nufi toilet ɗin ba ruwan ta da ko wanka take ko wani
abu haka ta banka ƙofan toilet ɗin seda Ayrah ta tsorita ta juyo da sauri ganin
Marwa seta cigaba da wankin ta ''ke'' Marwa ta faɗa da masifa miƙewa Ayrah da har
ta kusa gama wankin ta tayi tana kallon Marwa ''biyo ni''shine abinda tace haka ko
akayi ta bita kamn yanda ta faɗa ɗalewa bed nata Marwa tayi ta hakimce sannan tace
''ki haɗa kaya na ki wanke min su yanzu kuma sufita'' gyaɗa mata kai Ayrah tayi
kana ta wuce wajen drawer Marwa buɗe wa tayi a loka na ƙasa kayan suke haka ta ɗibe
su ta wuce toilet dasu seda ta gama wanke nata tass ta shanya su a banɗakin kana
tahau wanke ƙananan kayan Marwa duka su pant ne da bra se vest da underwear duka
haka ta wanke seda ta gama tass wajen past 9 sannan ta fito ta ɗale nata gadon ta
ɗauki books nata ta fara karanta wanda suke dashi gobe, tasha karatu ba kaɗan ba
kafin wani waha lallen bacci ya ɗauke ta already tayi addu'an ta tin kafin ta fara
karatun, su Marwa da Eshall ma duk sunyi bacci da wuri sabida Exams da zasuyi gobe
akwai zuwa school da wuri, washe gari

🌹🌹London 🌹🌹

Zaune suke gaba ɗayan su kan dining suna break fast Ajeeb yace ''wallahi na matsu
na koma nayi missing Mom da baby Ruma'' Ammar yayi sauri caɓe zance da cewa ''nima
na gaji da ƙasar nan like serious i wanna see me at home'' duk wannan magana da
suke yi gogan na jinsu Amma be sa musu baki ba ya cigaba da cin abincin sa kaman be
jisu ba Ammar ne yayi ƙasa da murya yanda daga shi se Ajeeb ne zasu ji magana da
yayi yace ''jibi sheed muna magana yayi kaman be jimu ba Amma yanzu da a gaban Mom
yake haka zasu ta taɗi harda dariya ma sabida mu ya rena wa wayo shi yasa yake
share mu wallahi'' ƙasa da murya sosai Ajeeb yayi yace kyale sa ai kafin mu tafi se
mun tsokano sa wallahi se mun sashi magana ne kaide barshi'' kaf wannan magana da
sukayi rass a cikin kunnen sa duk da haka be nuna musu yaji suba ya cigaba da cin
abincin sa kaman besan dashi suke ba su kuwa duk a zaton su beji suba gya ɗa kai
Ammar yayi yana murmushin da shi kaɗai yasan dalilin yin shi,tissue ya ɗauka ya
goge bakin sa ya haura staircase ya wuce ɗakin sa haka suma suka gama suka koma
cikin falo can bayan mintuna se gashi ya sauƙo sanye da uniform na sojoji yayi ɗan
banzan kyau yana taku cike da izza yayi bala'in kyau kamshin sa ya karaɗe ko ina na
cikin falon kafan sa na sanye black cover shoe gashin kansa ya kwanta luff har
bayan wuyan sa in a stylish way dayayi mugun mugun masa kyau kwayar idon san nan se
ɗaukan ido yake koya mutum yakai ga son haɗa ido dashi baya iya wa sabida kwarjinin
sa ga haiba tattare dashi yana da wani irin shiga rai yanda ko sunan sa mutum yaji
se yaji ya kamu da son me sunan koda kuwa be kalle saba hanun sa na ɗaure da
danƙare riyar agogon Rolex me ɗan uban tsada taka stairs ɗin yake cikin nutsuwa
daka ganshi kaga ƙaƙƙarfar meji da jini a jika har ya ƙarasa sauko wa su Ammar da
suka zuba masa ido suna ganin tsantsar kyau da Allah ya masa ga wani irin baiwa da
Allah ya bashi basu san ya sauka ba su kansu ya tafi da imanin su inaga duk wata
mace da tayi arba dashi kuwa su kansu da suke ƙannen sa yana musu kwarjini ga cika
ido,tsaya wa yayi a tsakiyar falon yana kallon agogon hanun sa ganin kusan 11 hanya
fita ya nufa seda yaje dab ze fita ya juyo ya kalle su yanda suka ƙure sa da ido
tun fitowar sa yasan kallon sa suke yi be kula su bane kawai wani mugun kallo ya
wurga musu kana yace ''take care'' ya ƙarasa ficewa daga falon already an shirya
masa motoci yana zuwa Mash ya buɗe masa back seat na dan kareriyar baƙar mota ƙirar
Lamborghini se Shining yake kaman yanzu aka bare sa daga leda,sauran sojoji se sara
masa suke yi be kula suba ya shige inda Mash ya buɗe masa duk suka shige sauran
nasu motocin suka tada direct suka nufi gate inda gard ya buɗe musu suka cilla
hancin motan su waje, seda suka ji fitan sa kana duk suka sauƙe numfashi Allah na
gani suna mstuƙar son yayan nasu ga wani irin kwarjini da yake musu su karan kansu
tunanin yanda zasu tafi su barshi anan kawai suke yi kusan 3yrs suna tare duk da
suna koma wa Amma shi tunda yazo ƙasar nan be wuce sau uku ya shiga 9j ba yayi
kusan 8yrs anan har ya saba da muatanen wurin ya shiga cikin su ya saje dasu in
kagansa zaka rantse ba ɗan Nigeria bane tsabar yanda ya saje dasu, gudu suke
shararawa kaman titin uban su har suka isa wajen aikin nasu parking sukayi da sauri
Mash ya fito ya zagaya ya buɗe masa yana sara masa yaɗan dauki mintina kafin ya
zuro kafan sa ya fito nan danan aka hau sara maa shi kuma tunda ys fito direct ya
wuce office nasa direct ya shiga duk masu manyan muƙamai kaf suna da office da ya
kasance nasu, duk wasu information daya haɗa kan aikin da zeyi ya tattara ya fito
ya wuce Office ɗin ogan su gaba ɗaya dan yana da tabbacin yau yazo nocking ya fara
yi daga ta ciki yaji ance ''yes'' shiga yayi can kasan makoshi yayi excuse yana
zaune kam hakimin kujeran sa se juyi yake yi tsaya wa yayi ya sara masa yana nan a
ƙame seda ya bashi izinin zama kana ya zauna gently ya buɗe ɗan ƙaramin bakin sa
cikin harshen turanci wanda a yanzu yafi zauna wa a bakin sa fiye da hausa da za'a
iya faɗa masa abu ma ya kasa gane wa da hausa da zazaƙar muryar sa ya fara magana
cikin sanyi normal yace''sir this is the information i get about that criminal on
what i see he is very dangerous yana da yara sosai a ko'ina yanzu haka ina tunanin
akwai abunda suke shirya wa'' seda ya sauƙe numfashi sabida yanda yayi maganan yayi
tsawo da yawa be kuma tsaya ya huta ba,jinjina kai Solomon (the general of the
army) wato ogan su, gently yace ''good my son i like this aikin ka yana kyau what i
want you t do now is ka zauna cikin shiri and ka sanar wa yaranka tun kafin su kai
ga abinda suke so ku gano location nasu ku farma kesu kawai i think zefi'' gyaɗa
kai yayi sannan ya miƙe ya ƙara sara masa yace ''okay sir''dama shima that was what
he is thinking about so yanzu he have full confidence on it juyawa yayi ya fita
cikin takun sa na zaratan maza Sir Solomon ya bishi da ido he really like this soul
haka kawai yaji yaron ya kwanta masa a ransa sosai ga kuma wani ɗan banzan kwarjini
da yake masa yanayin yanda yake komai nasa cikin tunani da lissafi yana ƙara burge
sa a ranshi yana ji ina ma ace Alex ne da seya fi kowa jin daɗi yana mutuwar son
yaron nasa Amma baya jin magana ko kaɗan se ya kwana a waje besan inda yake ba
kullum daga yau kaji sa a wannan ƙasar se gobe kaji sa a wancen ƙasan wai ya tafi
aiki aikin da shi kansa uban sa besan wani irin aiki ɗan nasa yake yiba, kawar da
tunanin yayi kawai yaci gaba da harkan gaban sa a ɓangaren Sheed kuwa bayan ya fita
waje yayi direct duk yaran sa da suke ƙarkashin sa yasa suka taru sabida magana da
zeyi dasu keɓewa suka yi a wani waje nan ya faɗa musu akwai aikin da zasuyi nan
bada jima waba su zauna cikin shiri dan a ko wani lokaci zasu iya jinsa a cikin
yaran nasa harda Mash da Byron, bayan ya gama sanar dasu se suka bar wurin, ayau
yake so ya gama binciken nasa dan ya haɗa target na yanda zasu tinkare su har suka
isa ya lumshe idon sa ya jingina kansa jikin seat yana tunani shi kaɗai yasan
abunda yake shirya wa yanzu parking sukayi Mash ya fito da sauri ya buɗe masa
marfin motan yaɗan ɗauki lokaci kafin ya zuro kanfansa ya fito gaba ɗaya beyi
hanyar shiga cikin gidan ba se ya nufi wata hanya ta gefe kaman lungu inda yayi wa
Byron da Mash alamun su biyo shi da sauri suka rufa masa baya hanya suka bi sunyi
tafiya me ɗan tsayi sannan suka isko wani ƙofa ɗan ƙarami hanu ya miƙa wa Mash
cikin sauri ya miƙa mishi key buɗe kofan yayi seda ya sunkuya sosai kafin ya iya
shiga su Byron suka rufa mai baya wasu computers ne a gefe guda a jere duk a kunne
ɗakin yana da fili sosai daga gefe guda kuma bindigogi ne kala kala na yaƙi a jere
gurin computers ɗin kujeru ne ajere daga ta ɗayan gefen kuma wani labule ne me ɗan
karan tsada an rufe wani fanni dashi nan ne gurin ajiye masu laifi idan an kama su
ana bincike akan su ko ana buƙatan bayanai daga gare su, wurin computers ɗin ya
nufa kaf gidan akwai Camera ta ko ina toilet ne kawai babu dama kuma yawancin manya
manyan soldiers zeyi wuya kaga gidan su ba Camera sabida tsaro kuma yawancin su
basa rasa abokan gaba masu son ganin bayan su balle kuma shi da yake ganin makiyan
nasa ƙarara ai dole nema yasa wa gidan da yake kwana tsaro badan tsoro ba sedan
tsaro tunani ma yake yi dole idan ya koma Nigeria yasa wa gidan su Camera sabida
yasan baza a taba dena bibiyan sa ba dashi da ƴan uwan sa so dole ya tsare su dole
su kasance

11 / 19