Author : FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category : KDP NOVELS
gashi ko yaje hankalin sa yana wani gurin a
ƴan kwana kin nan ma abun yafi yin worst dan kwata kwata an dena gane kanshi shi
kansa yanzu ba gane kansa yake yi ba haka kawai yake ji kaman akwai abunda ya rasa
me mahimmanci a rayuwar sa Sannan kuma yana ji ajikin sa akwai wasu abubuwa da suke
shirin faruwa dashi gashi kullum fama yake da ciwon kai abunde ba sauƙi.
Kwance Mommy take kan kujera me zaman mutum uku tayi shiru kanta na kallon sama
idon ta a buɗe da alama wani tunanin take yi Ammar ne ya shigo bakin sa ɗauke da
sallama yayi matukar kyau cikin wata yadi baƙa da layi layin fari Amma farin beje
har can ba ɗinki half jamfa da gani base an faɗa maka ba kasan yadin me tsada ne
kanshi ba hula gashin kan yasha gyara sosai normal aski ne da gyaran fuska gashin
yayi kyau se sheƙi yake yi zama yayi kujeran dake kusa da Mom ɗin ganin yayi
sallama kamar bata jiba gashi yanzu se ƙiran sunan ta yake yi Amma ina tayi nisa
cikin tunanin da take yi seda ya ƙira ta da ƙarfi sannan ta farga miƙe wa tayi daga
kwancen da take ta zauna ta jingina da jikin kujeran kallon ta yayi cikin nutsuwa
yace ''Mommy Please me yake damun kine kwana biyun nan duk kin canza kaman kina
cikin damuwa Amma idan na tambaye ki se kice ba komai kinsan bama jin daɗin ganin
ki cikin damuwa ko'' ya ƙarasa fiskan sa da alamun damuwa tattare dashi shiru tayi
kaɗan
kafin ta fara magana sega Ajeeb ma ya shigo bakin sa ɗauke da sallama kayan su iri
ɗaya sak da Ammar komai iri ɗaya shima zama yayi kusa da Ammar ɗin bayan ya gaishe
da Mom ɗin magana ta fara kamar haka
''ba komai kawai de ina kewar Ruma ne kaga ta tafi gidan baffan ku acen zata yi
hutun ta tare da ƴar uwar ta Ashfat gashi kuma yanzu zaku tafi can Meduguri wajen
kakan ku nasan kuma zaku ɗan yi kwana biyu tunda kun jima baku jeba ai dole na
shiga damuwa dama kukam baku jima da dawowa ba bayanda zanyi ne tunda Abban kune
yace kuje Amma ni bason zuwan naku nake ba''
Shiru suka yi shide Ammar be yadda wannan shine yasata cikin damuwa ba tunda ai
idan tana so zata ce Ruma ta dawo inyaso ko ita da Ashfat ɗin base su dawo tare ba
yasan ta faɗa ne kawai dan ta kawar masa da wannan tunanin shi kuma Ajeeb daya ke
bada shi aka fara maganan ba se ya yarda kewan su da zata yi ne yasa.
Be nuna mata be yarda da abunda ta faɗa ba sema cewa da yayi ''Mommy Please ki
kwantar da hankalin ki ko munje baza mu wuce sati ɗaya ba zamu dawo kinga ai a
satin zamu zazzaga dangi kidena damuwa Please''
Ajiyar zuciya ta sauke kawai ba tare da tace komai ba har ga Allah a cikin ranta ba
wannan bane yafi damun ta abunda yake damunta yanzu be wuce canzawan da Abba yayi
ba ko tana masa magana sama sama yake amsawa yanzu wani kalan canza wa yayi in
magana ze mata haka zena basarwa baya dawo wa gida se dare yayi sosai baya dawowa
da rana ma don cin abinci kwata kwata ta dena gane kanshi duk daren da yake kaiwa
kuwa baiwar Allah tana zaune a falo zaman jiran shigo wan sa Amma daya ganta se
yayi kaman be ganta ba idan kuma a gaban yaran nasu ne baya nuna mata komai shi ya
tada tafiyan su Ammar wai suje su zaga dangin su na Meduguri mahaifiyar sa ma tana
can shi da kanin sa ne kawai anan Abuja suma kuma aiki ne ya kawo su nan se kuma
ɗan matsaloli da suka ringa fuskanta a can ɗin yaso ɗaukan mahaifiyar tasa ma su
dawo tare Amma se taƙi fir tace baza tabar tushen taba ya barta anan hakan yasa ya
barta.
Wani hanzari ba gudu ba anan shine ƙanin Dad ɗin ba kowa bane se baban Ashfat
sannan Maman Ashfat ɗin kuma ƙanwar Mommy ne a taƙaice de Auren dangi suka yi da
Abba da Mommy dan mahaifiyar Mommy ƙanwa ce ga mahaifiyar Abba Amma ta rasu a hanun
mahaifiyar Abba Mommy ta girma wannan a taƙaice kenan se lokaci yayi zaku ji komai
dan gane da su Abba.
Sun gama shirin su dama already driver ne ze kaisu so sun shigo ne domin su yiwa
Mommy sallama kayan jikin su kuwa mussaman Abba yasa aka ɗinka musu dan acewar shi
baza suje da ƙananan kaya ba haka yasa aka yi musu ɗinki masu yawa kuma duk kala
ɗaya kaman wasu ƴan biyu komai kala ɗaya hatta takalma sabbi Abba ya saya musu su
kansu da suka saka kayan seda suka ga ya musu kyau dan kwata kwata basu da irin su
gashin kansu ma Abba yayi magana har ya gaji kan su rage yawan shi Amma suka ce ya
bar musu shi haka yayi shiru ya kyale su (niko nace ai bega na oga SHEAD bane shi
yasa).
Addu'a Mom ta musu sosai da fatan isa lafiya sannan ta basu saƙon gaisuwa su kaiwa
dangi har baƙin mota ta raka su inda driver yake jiran su dan har ya zuba trolley
nasu a bayan motan haka ta musu addu'a sosai irin wanda uwa take wa ƴaƴanta sanna
ta kuma ce musu su tsaya a hanya su sayi kayan abinci wanda zasu kaiwa ƴan uwan da
toh kawai suka amsa sannan suka shige motan driver ya tada ita suka kama hanyan
Meduguri yayin da ita kuma Mommy ta koma part ɗin ta duk abunda suke yi Ammii tana
kallon su ta window ɗakin ta wani irin daɗi taji ganin sun tafi yanzu plan ɗinta ze
fara aiki cije leɓen ta na ƙasa tayi tana girgiza kai haɗe da yin wani shu'umin
murmushin da ita kaɗai tasan ma'anar sa sake labulen tayi ta zauna bakin gadon nata
dama ita ta bawa Abba shawarar ya tura su suga ƴan uwan su sabida ta samu abunda
take shirya wa ya tafi yanda taso hmmm Amma fa bata san da dawowan SHEAD bane shi
yasa take wanga zance muje de zuwa .
GOMBE
DUKKU
Bari mu koma baya domin kuji abubuwan da suka faru,
Jikin matar nan kullum ƙara tsanani yake yi ga baba Malam jiki duk ya tsanan ta
shima shide yasa abunda yake damu shi Amma ba bakin yayi magana ga kullum idan
megari yazo seya masa karatu har takai idan megari yazo ze fara masa karatu se ya
kasa dan ji yake kaman ana shaƙe masa maƙoƙoro tun hakan baya damun sa har yakai
yanzu ya fara tsorata da lamarin dan fa shima ciwo yake yi a tsaye ya rame sosai
wannan ahalin ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba ga baba sadiq baya nan har
yanzu be dawo ba inna bata bar yiwa matar magani ba kullum seta bata Amma duk a
banza anje har gonan da baba sadiq yake zuwa Amma ba'a ganshi ba jin wanan labarin
kuma ba ƙaramin ɗaga hankalin ahalin yayi ba gade su musa basu gaji uban nasu ba
balle su iya gane abunda yake damun shi su kansu ba ƙaramin tashin hankali suka
shiga ba dama baba sadiq ɗin ne da beyi Aure ba yana zaune da baban nashi toh shine
ya koya masa kuma kunsan gado ba karambani ba se ya zama na kaman baba sadiq ɗin
yafi baba Malam sani sosai a wannan harkan duk ƴaƴan sa sun duƙufa ne wajen kula
dashi kullum se sunje kauyen da baba sadiq yake Amma basa ganin sa,
A yau ne suka tashi da wani kalan tashin hankalin da basuyi tsammani ba dan gaba
ɗayan su majinyatan yau jikin yayi tsanani abun mamaki kuma yau jikin matan nan se
rawa yake yi abunda be taɓa ba, gaba ɗayan su zagaye suke da baba Malam da jikin ra
yake ta ƙarƙarwa gashi yayi wani bala'in zafi dukkan su da ƴaƴan sa harda jikokin
sa suna zagaye dashi duk an rasa wanda ze iya taɓa shi sabida yanda jikin nasa yayi
zafi sosai duk ya rame sosai kuma ya haɗu da jikin tsufa inna ne ta fara magana
cikin tashin hankali take ƙiran sunan baba malam ɗin Amma ina ko idon sa baya iya
buɗe wa nan take jikin sa yayi sanyi kaman ba yanzu jikin yayi zafi sosai ba take
ya fara kafewa take kuma bakin sa ya buɗu kalamar shahada kawai ya iya furta wa
daga nan kuma tsit kake ji ya dena motsi nan take kuma ya sandare kaman wanda ya
jima da mutuwa take kuma suka fara kuka wasu kuma suna faɗin innalillahi wa'innan
ilaihir rajun inna kuwa miƙewa tayi da sauri ta fita a gidan dan bata maso ta ƙara
kallon mahaifin nata ba rai aikuwa tana fita tayi wani mummunan ji ihu ta kurma nan
su Ibrahim suka fito suka nufi gidan nasu dan daga nan suke jin ihun suna shiga
koridon ita kuma tana fito wa da gudu ba kowa bane face wannan matar tunda baba
Malam ya ɗauke ɗipp ta kurma wani ihu se kuma ta miƙe ta fito da gudu toh anan ne
suka gamu da ita kuma se aka rasa wanda ze bita duk se suka tsaya a yanda suke dan
ba ƙaramin shock suka shiga ba ganin matar da suka bari kwance ko motsi bata yine
ta fito kuma harda gudun ta matar da ta kwashe shekaru bata iya motsawa duk se suka
tsaya sun afka duniyar tunani seda inna ta musu magana wanda dawowan ta cikin
hankalin ta kenan sannan suka fita da gudu suk fara neman matar Amma sun zaga ko
ina basu ganta ba kaman wanda ta bace batt haka suka nemeta basu ganta ba suna
cikin haka kuma matar megari tazo hankalin ta a tashe ko magana ta kasa kawai se
jansu tayi suka bita aikuwa suna zuwa cikin gidan megari suka tarar dashi kwance
baya motsi ga sauran matan sa zagaye dashi da sauri musa ya ƙarasa kusa dashi Amma
se gani yayi baya motsi ya rasa ma me zeyi a halin yanzu ga baba Malam ya rasu ga
wannan baiwar Allah ta fita da gudu kuma basu ganta ba ga kuma megari ma ya rasu
shikam yau yana cikin tashin hankali mahaifin sa ya rasu abokin mahaifin nasa kuma
amininsa kuma surkin sa shima ya rasu ga matar da take gurin su ita ma ta gudu
wayyo shi ina zesaka kansa ne ga baba sadiq an neme sa ba'a gansa ba (innalillahi
wa'innan ilaihir rajun nima de wannan tashin hankalin ya ishe bi yau ni ina zan
saka kaina ne gwara de na koma wajen SHEAD maybe kafun mu dawo zamu tarar ya samo
😭
inda matar take ko kuma ya samu solution ɗin yanda zeyi )
LONDON
Tsaye suke a compound na gidan shirye cikin kayan aikin su duk sunyi shirin fitan
SHEAD ma sanye yake da nashi kayan aikin yana ƙara gaya musu yanda zasu yi yanzu
gurin ƙarfe 3:30 na dare dama haka suka tsara zasu fitan dan lokacin ne mafi
dacewan farmaki gari yayi shiru ba wanda zeyi tsammanin wani abun suna gama magana
kowa ya ɗale mota inda shima ya shige nasa motan shida su BYRON trolley su kuma
yana bayan motan dayake fitan na sirri ne se basu tada jiniya ba shiru suka fita
gudu kawai suke zubawa a titin har suka isa wani ɓoyayyen guri can ta bayan gari
wata hanya ce da bakowa ne ya santa ba tana iya fitar da mutum har yabar ƙasar daga
nesa da gurin suka yi parking dama basu kunna wutan motan ba haka duk suka dira
daga motan suka fara kutsawa wajen a hankali SHEAD ne a gaba kowannen su hanun sa
riƙe da manyan bindigu ga kuma ƙananan a gefe da gefen wandon su ga manyan bullet
da suka rataya a jikin su chan ta baya suka fara hango haske haka suka ta zuwa a
hankali har suka iso gurin nan suka tsaya inda ba wanda ze gansu mutane ne sunkai
su ashirin a filin gurin ga wasu manya manyan kwalaye da suka zuba a gurin kowannen
su hanun sa riƙe da bindiga wasu kuma suna shiga ɗan tamfol ɗin suna fito da sauran
kwalayen sun jima suna tsaye basu da niyyan fita kuma duk umarni ne na SHEAD shi
kaɗai yasan abunda yake shirya wa kallon su kawai yake yi seda suka gama fito da
duka kwalayen sannan suka ɗanyi wani magana kana suka bubbuɗe su kwalaye ne da suke
cike da kayan maye kala kala se kuma wanda yake ɗauke da Guns manya manya da ƙanana
suna gama ganin duka sanna suka rufe kwalayen suka fara shigar dasu babban motan
dake gurin ganin hakan ne yasa SHEAD bawa sojojin sa umarni su fita su zagaye gurin
sannan suyi shirin harbi haka kuwa suka yi seda yaga sun gama shirya kwalayen cikin
babban motan sannan ya fito fili kana yabawa sauran umarni da zasu iya fara harbi
ta hanyar daga hannun sa sama nan fa suka fara musanyar wuta hakan kuma yazo mawa
miyagun mutanen nan a baza tane dan basu taɓa tunanin akwai wanda yasan shirin suba
shiyasa duk sun sakankance shikuma SHEAD dama yasan basu shirya wa hakan ba shiyasa
seda ya bari suka gama shigar da kwalayen cikin motan sannan ya bada umarnin harbi
haka shima ya ringa harbi ba ƙaƙautawa suma suka fara nasu take guri ya hargitse
aka fara musanyar wuta harbi kawai kake ji guri fa ya hargitse sosai inda har wa
lokacin ba'a harbi ko mutum ɗaya daga cikin sojojin ba danfa kwararune wajen iya
harbi suɗin ba ƙananan kwari bane daɗin daɗawa kuma shine bazatan da suka musu basu
shirya ba shi yasa sun samu nasara kashe su kusan daka nan SHEAD ya ɗauki mutane
uku cikin sojojin sa ya basu umarnin shiga cikin babban motan sanna ya basu umarni
su tafi dashi suje su ajiye motan a gurin aikin nasu za'ayi bincike akan shi haka
kuwa akayi suka wuce da motan, seda suka zagay ko ina ganin babu wanda ya rage yasa
SHEAD ɗin juya wa dan subar gurin haka sauran sojojin suka wuce shine na ƙarshe
yana rufa musu baya ba zato ba tsammani kawai yaji an kwala masa ƙira ta hanyar
cewa ''sirrrrrrrrrrrrr'' juyawan da zeyi kawai se ganin bullet yayi daga nesa ta
kusa iso shi kafin ya samu wani dama na kauce mata har ta iso (oh ni ko ina ba
sauƙi kai innalillahi bari mu leƙa AYRAH maybe kafun mu dawo anyi wani abun 🥱)
ABUJA
Tunda Anty ta bata wannan abun tasha take jin kanta na sara mata wani kala take ji
bata jin daɗin jikin ta dan ko tsayuwa tayi setaji kaman zata faɗi dan wani kalan
hajijiya take ji shiyasa tana shiga ɗakin su ta ɗale bed nata ta kwanta nan da nan
bacci ya ɗauke ta Anty kuwa AYRAH na fita ta ɗauki wayan ta ta ƙira wani banji
abunda suka tattauna ba se ji kawai da nayi tace nan da 1hr sannan ta kashe wayan
ta, Indo baiwar Allah yau tunda ta tashi bata jin daɗi haka nan take jin kaman wani
abu yana shirin faruwa da ita ko kuwa wani abu ya faru da ita dan haka nan jikin ta
duk ba ƙarfi tunda ta tashi take kwance takasa miƙewa zuciyan ta yana mata zafi
sosai kuma ta rasa dalili duk abunda tayi yau ba ƙarfi a jikin ta haka nan take yi,
bayan 1hr, zaune Anty take kan kujera ta kwala wa Indo ƙira da sauri Indo ta fito
ta tsuguna ƙasa ko kallon Arziƙi bata samu ba Anty tace ''kije ki ƙira min yarinyar
can'' haka take faɗa bata ƙiran sunan AYRAH miƙewa Indo tayi tace ''toh'' sannan ta
fita a ɗakin hanun ta rike da wata ƴar ƙaramar paper da number ta a jiki tana so ta
bawa AYRAH sabida ko basa tare zata iya ƙiranta haka nan yau ta tashi da son bawa
AYRAH number nata dan tana ji a jikin ta kaman akwai abunda ze faru dasu da wannan
tunanin ta shiga part ɗin su har cikin ɗakin su ta shiga kwance taga AYRAH tana ta
sharɓan bacci har bakin bed nata taje ta fara tashin ta da yake bata da nauyin
bacci se kuwa ta farka miƙewa tayi zaune haka nan kanta kuma be dena ciwon ba
''AYRAH kizo Anty tana ƙiran ki'' shine abunda Indo tace miƙewa AYRAH tayi da sauri
bata ko amsa ba tayi hanyar barin ɗakin da sauri Indo ta rufa mata baya seda suka
zo dapp zasu bar ɗakin Indo ta tsayar da AYRAH ta tsuguna sannan tace ''AYRAH ga
number na ki riƙe a gurin ki idan buƙatan ƙiran nawa ya tashi'' cikin sanyi ta
ƙarasa maganan idon ta na cikowa da kwallan da ta rasa na meye ne karɓa AYRAH tayi
itama haka nan se taji wani iri ta rasa meke mata daɗi ''Anty Indo toh a ina zan
ɓoye'' ta faɗa a hankali karɓan paper Indo tayi da sauri dan ƙar Anty tace sun jima
hulan da yake kan AYRAH ta cire ra saka mata paper a ciki tana kallon gashin AYRAH
dan tunda suke da ita bata taɓa ganin gashin taba ganin yanda take da gashi sosai
gashi ya tsufa sosai har ba'a gane kitso ne akan nata ko meye ne da sauri ta kawar
da tunanin da take yi ta mayar mata da hulan sannan ta maida mata da hijab ɗin da
yake jikin nata suka fita tana ce mata ''idan na samu Lokaci zan gyara miki gashin
kanki sannan karki yarda wani yaga paper nan kinga na samiki shi cikin hulan ki''
da ''tohm'' kawai ta amsa a haka har suka shiga ɗakin Anty aikuwa sun gudu basu
tsira ba dan seda Anty tayi masifan ta son ranta sannan ta miƙe ta shige ɗakin ta
ita ma Indo wuce wa tayi nata ɗakin can ba jimawa sega Anty ta fito hanun ta riƙe
da kuɗi ta miƙawa AYRAH sannan tace ''kije waje zaki ga wasu a mota ki basu kuɗin''
a fisge tayi maganan kaman ba ita tayi ba ko kallon inda AYRAH take bata
yiba,karɓan kuɗin AYRAH tayi tace ''toh''sannan ta fita haka nan da zuciya ɗaya ta
fita inda tunda take ba'a taɓa aikan ta waje ko wai ta fita haka kawai bata taɓa ba
se idan Bus ya dawo da ita daga makaranta nan ma bata