Author : FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category : KDP NOVELS
koya mata yin hakan idan
tayi Sallah bata tashi akan darduma se tayi isha'i tsakanin magrib da isha'i bawani
rata sosai bane ne a wannan lokacin take samu tayita istigfari tana ambaton Allah
wanda hakan yanada kyau sosai seda tayi sallan isha'i sannan ta tashi ta naɗe
sallayan wuce wa tayi danufin ta kwanta dan tagaji sosai ba kadan ba yau ɗinnan
tayi aiki sosai tunda ta dawo daga makaranta bata huta ba kowani babban mutum iya
kaci ko abincin ma batajin xata iyaci sabida yanda tagaji bacci takeji gashi gobe
ma da wuri xata tashi kuma tanaso ta duba karatunta na makaranta ko xama batayi ba
sega munib ya shigo ita se alokacin ne ma tatuna da xasuyi wani assignment zama
tayi a bakin bed nata tare sukayi assignment ɗin tana nuna mishi har suka gama
sannan ya tashi ya tafi yana mata seda safe dan Anty batasan ya fita ba kwanciya
tayi akan gadon tafara sana'an nata wato tunani sabida inde har zata kebe ita daya
to bawani abun da zatayi face tunani batayi nisa da fara tunanin nata ba bacci yayi
gaba da ita sabida ta gaji sosai.... ASUBA TAGARI AYRA
DAHAKA NIMA NAKE CEWA ASUBAH TAGARI
🌹Mhizz teemah🌹
💥SAKAYYA DAGA ALLAH💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
𝐇𝐀𝐙𝐈𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐔𝐁𝐔𝐓𝐀
🌹(Mhizz teemah)🌹
*HAZIƘAN MARUBUTA*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
Dedicated to my beloved💔Mom💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wani ko wata a
𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 , 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶
rashi ne, idan kunga typing error ko wani mistake kuyi hakuri nima xan kokarta 🙏🥰.
𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝗦 . 𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵
3️⃣
Free Page
Washe gari da asuba ta tashi bawanda ya tashe ta tariga da tasaba ko ba'a
tasheta bama tana tashi toilet tashiga ta dauro alwala tafito dadduma ta shimfiɗa
ta tada sallan asubah koda ta idar ma mikewa tayi ta gyara gadon ta sannan ta fita
a ɗakin direct ɗakin Anty tawuce tana zuwa ta taras indo me aikinta ta ɗaura girkin
safe ganin haka se itakuma ta gyaran dakin seda ta gyara ɗakin tass duk Anty tana
Bacci gashi ba shiga mata cikin daki sukeyi ba kawai seta fita a ɗakin ta wuce part
ɗin mama lokacin har haske ya fara fitowa tana shiga nan ma de kaman dakin Anty
haka ta gyara shi tawuce cikin dakin ma ta gyara komai duk Mama na Bacci koma wa
tayi part ɗin Anty ɗakin da munib yake kwana tashiga nan tasa mesa se bacci yake
sha tashin sa tayi dan yaje ya fara shirin makaranta haka ko akayi mikewa yayi ya
shiga toilet ita kuma ta fito falo lokacin kusan karfe 7:00 fita itama tayi ta wuce
part ɗinsu don tafara shirin makaranta koda ta shiga bakowa a ɗakin duk sun tashi
basa ma part ɗin gaba daya suna tashi suka wuce part ɗin Mama gyara musu bed nasu
tayi duka ta gyara ko'ina sannan ta shige toilet wanka tayi ta wanke bandakin kana
ta fito tafara shirin dan bataso tayi latti Amma tasan yanxu Anty zata iya kiranta
idan munib ya tasheta sauri sauri ta saka uniform ɗin ta tana gama shiri ta fito
tsaf da ita wucewa tayi part ɗin Anty nan tasamu an sakawa munib abincinsa cikin
lunch box zama tayi ta fara cin abincin ta ko Spoon biyu bata yiba Bus ɗin su yazo
haka ta tashi ta bar abincin suka fita tana rike da hanun munib ga lunch box ɗinsa
a ɗayan hanun haka suka fita a cikin gidan tana ta Allah Allah su tafi kafun Anty
ta tashi dan kada tace setayi wani abun Bus suka shiga suka kama hanyar makaranta
suna isa duk suka fita ko wannen su ya wuce ajin su itama nata ajin ta wuce Eshall
bata jeba da Marwa sabida ita Eshall a ss3 take kuma yanxu suna third term sune
za'a yaye Marwa kuma jss 3 zata tafi ss1 shiyasa suke zaman su se Randa suka ga
daman zuwa se suje Ayra kuma zata tafi jss1 duk de abun yazo kusan lokaci daya ne,
kofan ajinsu ta tsaya ba malami a ajin Amma seda ta yi sallama sannan ta shiga su
ashfat duk sunzo kowane harkan gabanshi yakeyi bawanda ma ya kalleta zama tayi
gurin zaman ta suka gaisa da su ashfat daganan bata kara magana ba ta dauko
litattafan ta tana dubawa Karatu suka fara har suka fita break kaman jiya yauma
haka sukaci abincin su sukadai har suka koma class aka cigaba da karatu har aka
tashi tafito tafara duba munib shida yake primary 3 ta kama hanun shi suka wuce Bus
daze maida su gida koda suka isa munib ya wuce part ɗin anty ita kuma tawuce nasu
tana shiga ta taras ɗakin gaba daya ko'ina a hargitse kan bed nasu duk kaya sunfito
dashi basu mayar ba anan bakin kofan ta tsaya tana tausaya wa kanta domin kuwa
tasan yau bakaramin aiki zata sha ba nan take idonta ya ciko da hawaye Amma haka ta
danne ta shige dakin ajiye jakanta da takalmin ta tayi sannan tadauki kayan da zata
saka tawuce toilet dashi murɗa handle ɗin toilet ɗin tayi tana addu'an shiga
bandakin ko karasa addu'an batayiba nan ma ta tsaya cak kaman an tsaida ta toilet
ɗin kota ina a wargaje duk kuma yayi datti soson wankan ta a yashe a kasa kaf
mayuka da sabulun cikin toilet ɗin suna kasa wasu babu marfi ma ga sahun kafan
mutum nan gashi a jike ko'ina yayi kaca kaca komawa dakin tayi ta ajiye kayanta
sannan ta wuce toilet ɗin tafara tattare su sabida tunda taga haka tasan acikin
sune wani yayi wanka yayi duka wannan barnan Amma bayanda zatayi haka ta tattare su
gaba daya se asannan nema ta kalli pant ɗin dayake gefe a yashe a kasa tana gani
tasan na eahall ce sabida dama itake wanke musu kananan kayansu gaba daya su harda
Anty da mama duk ita take wanke musu wanke bandakin tafara yi sannan ta wanke pant
ɗin ma ta rataya shi gurin shanya duk ta hada zufa dazaran tayi aiki seta ringa
hada zufa fitowa tayi ta dauki kayanta doguwar riga ce dan kayanta duk dogayen
riguna ne ɗaiɗai kune ba doguwar riga ba wanka tayi tareda alwala tasaka kayan
sannan tafito Sallah ta farayi tana idarwa ta mike tafara tattare dakin duk kayan
da suka wargaza seda ta gyara tass ta share dakin tayi mopping sannan ta fita a
part ɗin gaba daya part ɗin Anty ta wuce dan tunda taga yanda part ɗinsu ya baci
tasan basanan ne ko sunfita anguwa tare da mama baza'ayi sati basu fita ba daga yau
suna gidan kawar maman nasu haka sukeyi basa taba zama guri daya shiga ɗakin tayi
bakinta dauke da sallama ƙasa ƙasa kamar kullum yauma Anty na zaune kan kujera
muhiba kuma tana wasa ita kadai se galantoyi takeyi gaishe ta tayi motsi da bakinta
kawai tayi kaman wacce ta amsa abinci ta kawai tace mata taje taci har mamaki ma
Ayra take yi yanda yanxu take ɗan bata abinci da wuri wucewa tayi ta dauki abincin
duk da kwata kwata abincin kotaci ba isan ta yake yi ba kuma bawai babu abincin
bane kawai de baxa ta bata taci ta koshi bane yanda aka samata Haka takeci zama
tayi taci abincin mikewa Anty tayi ta shige dakin ta binta a baya Ayra tayi dan
tasan idande ta mike toh tana nufin ta bita ne shiga dakin suka yi wani irin warin
wani abune ke tashi a cikin dakin kaman ba lafiya ba Amma me Ayra ko ajikinta da
alama ta saba da wannan warin ne dan ko gyaran duniya zatayi haka yanda take jinshi
ma sede tace karuwa yakeyi naɗe kayan kan bed ɗin ta fara yi tass tanade sannan
tayi shara da mopping bandakin ta bude da addu'a a bakinta ta shiga ai gaba daya
bandakin a kacame yake ga wani kalan Ruwa a kasan tails ɗin daya bushe Brown haka
ta wanke tanayi kaman zatayi amai domin kuwa ta tsani abun kyama tsikar jikinta ma
tashi yakeyi inde taga abun kyama jikin ta har girgiza yakeyi duk tabi ta rikice
tanada tsoro sosai wanke toilet din tayi dakyar sannan ta fito da pant ɗin da suke
toilet ɗin gaba daya sunkai Ashirin duk wari ma sukeyi wani harda jini a jikinsa a
cikin bocket ta saka su da détergent kanta a kasa ta fito kallon ta Anty tayi na
'yan sakanni ta kauda kanta daga gare ta sannan tafara magana cike da takama kaman
bataso ''ki tattara hada underwear da vest ki wanke su kuma ki tabbatar sun fita in
bahaka ba kinsan sauran'' takarasa maganan tana jan kwafa gyaɗa mata kai kawai tayi
kanta akasa haka ta buɗe kofan ta fita a cikin ɗakin wucewa bayan ɗakin tayi
baiwar Allah ashe harda kuka tayi idanunta sunyi jaa idan ta tuno dattin
banɗakin kaman tayi amai har wani irin hadiye zuciya takeyi kaman me shesheka tana
hana aman zuwa ruwa ta hada tasaka duk detergent ɗin da ake sawa tunanin yanda zata
fara wanki ma takeyi batason saka hannun ta sabida tsabar yanda panties ɗin sukayi
datti gashi wari ma suke yi halamun sunjima da dattin ajikin su wasu jini ne ma
ajiki duk ya bushe se wari yakeyi kayan de gaba daya ko kallon su mutum yayi idan
me kyama ne se yayi amai jika kayan ta farayi ko kallon suma batason yi kanta a
kasa tana kallon gefe guda da kyar tasaka hanun ta acikin ruwan wankin jijjige su
kawai takeyi ta cire haka ta jijjige gaba dayan su ta kara hada wani ruwan ma
tasaka su se asannan ne tafara wanke su tanayi tana hawaye da kyar ta wanke kayan
nan bada son ranta ba seda tayi kusan ruwa huɗu sannan ta dauraye ta shanya tagaji
ba kaɗan ba zama tayi tace bari taɗan huta sabida tsabar yanda ta gaji haɗa kai
tayi da guiwa tana hutawa domin ba karya harga Allah ta gaji ba kaɗan ba.....
'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
''''''''
Wani irin tamfa tsetsen gida ne ɗan uban su wanda kaf unguwan babu gidan da
yakaishi haduwa anguwa ne na masu kuɗi bana yara ba ko ina shiru ba mutane kaf
gidajen anguwan ba na raini Amma wannan gidan duniya ne gaba daya ma get ɗin gidan
ma kawai abun kallo ne.........
Ga me bukatan karanata littafinnan daga farko har ƙarshe ze iya nema na ta
wannan number 09060413321
🌹Mhizz teemah 🌹
💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story& writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
Dedicated to my beloved 💔Mom 💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wani ko wata a
𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 , 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶
rashi ne, idan kunga typing error ko wani mistake kuyi hakuri nima xan kokarta 🙏🥰.
𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝗦 . 𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵
4️⃣
Page
Wani irin tamfa tsetsen gida ne ɗan uban su wanda kaf unguwan babu gidan da
yakaishi haduwa anguwa ne na masu kuɗi ko ina shiru ba mutane kaf gidajen anguwan
ba na raini Amma wannan gidan duniya ne gaba daya ma get ɗin gidan ma kawai abun
kallo ne ya hadu iya haɗuwa, gida ne babba se kashiga cikin gidan ma zaka gane
wajen ba komai bane ya haɗu yanda baxan iya misalta muku bama idan nace zan tsaya
kiyasce muku yanda gidan ya hadu ma se mugama page nan har mushiga wani so kawai ku
ƙiyasce yanda yake irin gidan nanne da ake cewa aljannan duniya domin kuwa ya kai a
kira shi da fiye da haka ma part Uku ne a cikin gidan kowanne yanada tazara da ɗan
uwansa manya manyan part ne ba ƙanana ba kowani part yanada upstairs kowani part
ɗauke yake da ɗakuna Uku a down stairs Uku a upstairs ga wasu Flowers da kowani
part yake zagaye dashi ta bayan part kuma akwai lambu me ɗan girma yana ɗauke da
ƴaƴan itacuwa kaman ayaba dade sauran kayan fruits Sannan akwai katon fool ga kuma
kujeru na shan iska a jere ta gefen fool ɗin, gidan de ba'a cewa komai domin kuwa
ya hadu ba karya, mata biyu ne a gidan kowa da nashi part ɗin ɗayan part guda dayan
kuma na mazan gidan ne ko ina a tsare yake
Part din farkon na shiga falon yahadu ba karya yanada girma sosai mu haɗu a falo
ake kiran irin wannan falon bayan falon kuma kowani daki kashiga akwai falon sa
ɗan daidai da ɗakin shi da banɗaki, bayan dakuna uku na kasan kuma akwai kitchen
shikuma yana ta ɗan lungu a gefen kitchen ɗin akwai wani ɗaki wanda ina kyauta ta
zaton na masu aiki ne cikin kitchen ɗin kuma yanada girma a can ciki akwai wani
kofa shikuma store se kofan da xesada ka ta bayan gidan inda anan garding din part
ɗin yake,wata hamshakiyar mata ce zaune a kan daya daga cikin lumtsuma luntsuman
kujerun falon tanada ƙiba ɗan daidai irin na hajiyoyin nan farace tas tanada tsayi
Amma ba sosai ba a shekaru bazata wuce 42 ba kyakyawa ce kallo takeyi Amma bawai ta
maida hankalinta gaba daya akan kallon bane da alama ta tafi duniyar tunani ne wata
matashiyar yarinya ce ta shigo dakin bakinta dauke da sallama da kayan makaranta a
jikin ta da alama dawowanta daga makaranta kenan aƙalla zata kai 13 years fara ce
kyakyawa yanayin jikin ta irin na yaran Madara ne yarinyar akwai ƙugu dede da
shekarunta ɗass dashi ga breast nan da suka fara cikowa suma, zama tayi kusa da
wannan matar ta kwantar da kanta a kafadan ta''wai mommy mutum ya shigo ma har yayi
sallama baza kijishi ba kin fara sana'an naki kenan wai meyesa kike sa damuwa da
tinane tinane a ranki ne dan Allah kidena yawan wannan tunane tunanen inba haka ba
zaki iya sakawa kanki wani ciwon'' yarinyar tafada tana langaɓar da kai kaman
zatayi kuka domin kuwa harga Allah batason ganin mahaifiyar ta a haka, hmmmm dogon
numfashi Mommy taja tareda furzar wa sannan tafara shafa kan yar tata domin kuwa
ita harga Allah tana son ya'yan ta batason wani abunda ze bata musu rai yaranta 4
ne kuma duk maza ne daya ce mace itakuma Allah yayi ta da son yara ba kaɗan ba
mazan ma kuma gashi yanzu duk basa nan shiyasa kullum da ta zauna seta fara tunani
kaman basa kiranta kaf ɗin su kowanne yana kiran ta kullum Amma hakan ma duk be
mata ba tafiso taringa ganin yaranta kusa da ita,'' Ruma tashi kije kiyi sallah ki
ci abinci se ki huta nasan kin gaji ko'' tafada tana kallon yar autar nata gyada
mata kai tayi tana mikewa,
wucewa tayi wani ɗaki dayake ta gefe a ƙasan domin tayi wanka da sauran abubuwa
dakinta daban Amma shi dakinta baida falo iya bedroom ne da bathroom komai na yaran
masu kuɗi akwai kuma yan auta domin kuwa daga baban har maman suna ji da ita kai
harma da yayun nata, tana gama shirinta ta fito falon kasa direct dining ta nufa
anan ta zauna zamanta bada jimawa ba sega mommy ta karasa gurin zama itama tayi a
kujeran kusa da Ruma ita tayi saving nasu abincin suna ci suna taba hira kullum
idan ta dawo seta bawa mommyn ta labarin Ayra ita kanta Mommy harta kamu da son
Ayran tun bata santa ba domin haka kawai yanda Ruma take bata labarin yarinyar ta
fahimci tanada hankali sannan mahaifiyar ta tabata tarbiyya gashi kuma tana son
yara a rayuwar ta barin ma mata ita kuma 'yar ta mace daya shiyasa ma take ji da
ita sosai, suna gama cin abincin mikewa sukayi Ruma ta wuce ɗakin ladi me aikin su
don ta kirata su kwashe kayan aikuwa hakan akayi kwashe kayan sukayi ladi ta wanke
su ita kuma Ruma tana gefe tana kallonta suna taɗi dande itakam tanada surutu
bakinta baya iyayin shiru na wasu mintunan tanason tana zuwa gun ladi sabida tana
sata dariya sosai idan tana bata labari haka ta gama suka wuce ɗakin ladin dan anan
take wuni sabida kota zauna da mommy bawani hira sukeyi sosai ba inkuma ta zauna a
daki to karatu zatayi ko kuma bacci haka suka ta hiran su har lokacin daura girkin
dare yayi nan ma tare suka wuce kitchen ɗin Amma de ruma batayi komai ba tana tsaye
tana ganin yanda ladi take aiki suna hira kuma har ta gama komai suka jera a kan
dining sanna Ruma ta wuce dakin ta wanka tayi ta fito daure da towel kayanta tasaka
tayi sallah kana ta fito sukaci abincin dare itada mom tattare kwanukan tayi ta
kaisu kitchen bata ko kira ladi ba sannan ta wuce dakinta ta dudduba littatafan ta
tayi shirin bacci kawai ta kwanta Mommy ma kwanciya tayi dan already tasan ko abee
ya dawo ba shigowa zeyi ba tunda dare yayi seda safe suke gaisawa addu'o'in ta da
tasaba yiwa yaranta da ita kanta tayi, ta riga da tasaba ko acikin bacci ne tayi
juyi zata gyara kwanciyan ta setayiwa yaranta addu'a ko kuma idan ta farka cikin
dare wani uzurin ya tada ta kai itafa kome takeyi toh tanayiwa yaranta addu'a ne da
fatan Allah ya shiryar mata dasu ya karesu aduk inda suke ya kiyayesu daga cin
haram wannan addu'oin har sun zame mata jiki kuma hakan yanada kyau domin kuwa shi
(addu'ar iyaye yanada matuƙar tasiri a rayuwan 'ya'yan su saboda haka ina fatan duk
wanda ya karanta Wannan page nawa idan ma bayayi toh ya fara a kowani hali ana so
uwa ta kasance me yiwa yaranta addu'a sabida ze temakesu daga wasu abubuwan koda
wani ne yake nufinsu da sharri toh wallahi sanadin wannan addu'a da mahaifiya take
wa yaran ta dare da rana a cikin kowani hali Allah ze kare mata'ya'yan ta Allah
yasa mudace kuma ina fatan ku gyara idan da bakwayi yanzu ku fara) bacci ne me
daɗin gaske ya dauketa tareda yaƙinin aduk inda yaranta suke Allah natare dasu kuma
ze kare mata su ASUBA TA GARI MOMMY AND RUMA
''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
AYRAH
Wani irin wahalallen bacci ne yayi gaba da ita a gurin