SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah

Author :  FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category :  KDP NOVELS

Chapter   10 / 19

27K to 30K   out of 54.2K words

Alqur'ani
ita ma zama tayi kusa da maman ta ta buɗe Suratul Ah-qahf shafi na biyu nan ta
karan tawa mom ɗin duk inda tayi bata seta gyara mata har ta mata rabin shafi kana
ta tsaya anjima da yamma malamin lesson ɗin ta yana zuwa seda tayi ta maimaitawa
sosai ya zauna mata sannan ta rufe Qur'an ɗin ta maida shi inda yake dade Ammiii ta
gama zaman ta basu yi wani hira sosai ba dan Mom ɗin ma karatun ta take yi miƙewa
tayi ta koma part ɗinta bayan sunyi sallama ko kaɗan mom bata nuna mata wani abu ba
dan ita haka take ba ruwan ta ita ma ruma daƙin ta ta shige kafin malamin ta yazo
ta fara karatun sauran littattafan da yake mata su hadisi,fiqhu,Tauhidi, tajwid
dade sauran litattafan harda Azkar duka, Mom kuwa ci-gaba da karatun ta tayi,can ta
miƙe ta rufe Qur'an ɗin ta wuce ɗaki haka de har malamin yazo suka yi karatu wurin
ƙarfe 5 ya tafi yaude dad yana gurin Ammiii kwana biyu biyu suke yi se yayi 2 days
kafin ya dawo washe gari ya kasance Lahadi karatu Ruma take ba kama hannun yaro
tayi busy se karatu take ba kakkautawa malamin ta yazo sukayi karatu sosai na
islamiya dayake duk ranan asabar da lahadi kawai suke karatun har dare yayi dad
yana dawo ya ya shigo ya duba su ga ƴar babyn sa ta riƙe littafi karatu kawai take
yi Allah na gani bataso ta faɗi ko kaɗan seda yaɗan tsokane ta suka yi raha kafin
ya wuce Part ɗin Ammii har kusan 10pm takai tana karatu zasu shiga Exams by 8:30
paper biyu zasuyi sannan ta kwanta asuba ta gari Ruma.


🌹AYRAH🌹

Kallon Dad Anty tayi tafara magana cikin isa kaman Uwar shi ''kana ganin abunda
yarinyar nan tamin Amma kabar ni inata shan wahalan dukan ta kaduba fa kagani
wallahi kamata punishment ɗin da seta ji ajikin ta har ni zan mata magana taƙi bani
amsa kuma tafasa min kuloli harma da zubar da abincin'' ta kare magana tanayin
kwafa haɗe da nuna Ayrah dake kwance tana gurzan kuka da yatsa, sharɓebiyar bulalan
sa dad ya ɗauko daga ƙarƙashin kujera nan ya fara zuba mata dukan ta yake kaman an
aiko shi ƙasan zuciyar sa kuma yana jin zafin dukan daure wa kawai yake yi seda
yamata duka har seda ta suma ba irin haƙurin da bata bashi ba ta ƙira Mama su Marwa
da Eshall harda munib da muhhiba ba wanda bata ƙira ba na cikin gidan har indo ba
kalan haƙurin da bata bawa Anty ba Amma tayi banza da ita kaman bata jita ba seda
Anty taga ta suma kana ta dakatar dashi daga dukan baiwar Allah nan,zama dad yayi
yana maida numfashi suna hak sega Indo idanun ta sun ƙumbura ba ƙaramin kuka tasha
ba tazo zata shigo seta ga dad yana dukan Ayrah hakan yasa ta koma daga baya ta
zauna bata shiga ɗakin ba tayita kuka dan tasan idan ta shiga Anty zata iya cewa a
haɗa da ita shiya sa ta rufa wa kanta asiri tayi zaman ta a wajen,wasu kulolin
abinci ne a hannun ta wanda ta ƙara dafawa tundaa shi wance ya zube ajiye su tayi
kan dining kanta a ƙaa tazo zata fita Anty ta kira ta tace ''ki ɗauke min wannan
ƙazamar yarinyar daga nan idan ta farfaɗo tayi pim pim (up an down) harse na
shigo'' duƙawa tayi ta ciccibi Ayrah da bama tasan inda kanta yake ba suka bar
ɗakin direct ta wuce da ita part ɗin Anty ɗakin ta ta kwantar da ita kan ɗan gadon
ta ruwa ta tarfo a hannun ta yayyafa mata a fuska wani dogon numfashi taja tare da
fashe wa da kuka idon ta a rufe ta cigaba da cewa ''dad dan Allah kayi haƙuri bazan
ƙara ba na tuba dan girman Allah kayi haƙurin Antyyyyyyyy wallahi bazan ƙara ba
kiyi haƙuri'' haka tayi ta faɗa da alama har lokacin bata dawo hayyacin taba dafa
ta Indo tayi ta ƙira sunan ta a hankali cikin tausasa lafazi da iya magana irin ta
manya Indo ta shiga bata haƙuri tana gaya mata magan ganu masu daɗi jin muryan Indo
batasan lokacin da ta buɗe idon taba kawai se tafaɗa jikin ta ta ƙara rushewa da
kuka haka ta cigaba da kwantar mata da hankali har tayi shiru haɗa mata ruwan ɗumi
indo tayi tace taje tayi wanka zataji daɗin jikin ta haka kuwa akayi wanka taje
tayi da ruwan ɗumin duk jikin ta shatin bulala har fiskan ta,taɗan ji daɗin jikin
ta sosai ta dawo ɗakin tasamu Indo zaune ga plate na abinci da tasaka mata zama
itama tayi abincin Indo ta tura mata tace maza taci ba musu ta fara ci bawai dan
tana jin dadin shiba se dan yunwan da take ji Amma samm bakinta ba taste bata wani
ci sosai ba ta ture shi wanke hanun taje tayi kana tasha ruwa duk indo na kallon ta
kama hanun ta tayi suka fita falo bata ce mata komai ba ta zaunar da ita inda take
zama ita kuma ta tashi ta wuce bakin kofa dan tana gani idan Anty tazo zuwa seta ce
mata ta tashi ta fara abinda ta sata,seda tayi kusan minti talatin tana tsaye a
wajen kafin ta hango Anty na tahowa da sauri ta dawo cikin falon ta cema Ayrah da
ta tashi ta kama kunnen ta ta fara yin sama da ƙasa da sauri haka ta tashi indon
kuma ta tsaya tana kallon ta har Anty ta shigo balla mata harara tayi zama Anty
tayi ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya Ayrah kuma se yi take har ta fara gajiya tayi
kusan ɗari indo na ƙirgawa duk suna gurin kaman an tsikari Anty se ta tuno gobe su
Abdull suna dawo wa juyawa tayi ta kalle ta kana tace tasa gwiwowinta a ƙasa thats
tayi neel down haka ta tayi duk ta gaji ga wani gumi da yake tsatsaffo mata daga
nan Anty ta miƙe tabar ɗakin seda taje har bakin ƙofan kana ta juyo tace ''a haka
zaki wuni yau se dare zaki tashi daga nan'' ta juy ta fita abunta Ayrah kuma wani
irin kukan da take ta riƙewa tun ɗazun ne ya kubce mata kawai seta fara rera shi
cikin dishashiyar muryan ta da baya fita sosai da sauri Indo ta juya ta wuce ɗakin
ta dan batason ganin Ayrah na kuka haka gashi ba yanda zatayi,Indo ne yau tayi
gyaran ɗakin tass sannan ta ɗaura girki haka Ayrah tayi wuni churr a wajen sede
kuma idan har aka kira Sallah toh tana tashi duk da tana tsoron kar ta tashi Anty
tazo Amma haka take daure wa ta tashi toilet ɗin Indo take shiga tayi alwala ta
zumbuɗa hijab ɗin indo tayi Sallah sannan ta koma har indo ta gama girki har bayan
la'asar tana gurin Sallah kawai ke tada ita seda akayi magrib bayan ta dawo daga
Sallah kaman dama jira Anty take ta dawo kawai sega tanan ta shigo kallon arziki
bata samu daga gurin taba tace ta wuce tabar ɗakin zasu haɗu gobe ne da sauri ta
miƙe ganin Anty na nufi ta tayi waje da gudu tabar ɗakin part ɗin su ta wuce duk
agajiye take koda ta shiga babu kowa a ɗakin duk a wargaje dan yau besamu gyara ba
hakan yasa ta fara gyara ɗakin kafin ta ɗauro alwala dan gabatar da Sallah isha'i
tana cikin yi sega Eshall ta shigo toilet ɗin ta wuce darect alwala tayi ta fito ta
fara sallah la'asar da magrib da isha'i ta haɗa tayi su duk lokaci ɗaya Ayrah kuwa
har ta Idar ta ninke sallayan ta maida shi inda yake kwata kwata batayi mamakin
ganin Eshall na Sallah ba dan haka take yi wani lokacin seta haɗa duka salloli
biyar ɗin nan lokaci ɗaya tayi shi wataran cikin dare take tashi tayi su, ɗale wa
bed nata tayi tasan gobe bata da Time ɗin yin karatu hakan yasa batayi ƙasa a gwiwa
ba wajen ɗaukan books nata ta fara karan tawa abun mamaki Eshall na idar da Sallah
ita ma ta ɗale bed nata school back ɗin ta ta ɗauko ta fito da wasu takardu ta fara
dubawa ga wayanta tana dubawa tana kallon wayan ba komai bane a cikin wayan face
answers na questions ɗin da za'a tambaye su gashi nan wani malamin ta ya tura mata
daga amsan objective har na Essay haka ta gama duba littafin ta kalli questions ɗin
kana ta mayar da littatafan ta ajiye jakan a gefen bed nata Ayrah kam karatun ta
tayi sosai sannan ta rufe book ɗin ta ɗauki wasu ta karanta har seda ta fara jin
baccin ya fara cin ƙarfin ta sannan ta rufe book ɗin ta tasi taje tayi alwala tazo
tayi addu'an bacci se kawai ta kwanta se bacci kuma dan dama a gajiye take sosai,
Eshalla kuwa se dudduba answers ɗin da sir Emanueler ya turo mata take yi rants
fess ko yanzu a shiga Exams bata damu ba, sir Emanuel shine best teacher ta suna
shiri sosai sabida tana cika mai aljihu da ƙuɗi ba kaɗan ba kuma sonta yake yi shi
yasa can wurin past 10 Marwa ta shigo ko sallama babu ko wanka bata yiba tana zuwa
ta baje kan bed wani irin kallon banza Eshall ta watsa mata taja tsaki dan basa
shiri ko ƙaɗan duk da suke uwa ɗaya uba ɗaya abun yana ɓatawa Mama rai sede kawai
tana danne wa ne kuma tafi son Marwa sosai duk inda zasu tare suke zuwa tafiyin
abubuwan ta da Marwa yanzu ma tare suka dawo sun fita tun safe, itama Marwa tsaki
taja kana ta fara shirin kwanciya duk hatta kayan da ta tuɓe anan ta barshi ga
takalmin da ta shigo dashi har cikin ɗakin yana gurin shima wayanta ta ɗauka yau
tayi matuƙar gajiya tana buɗe data itama taga an turo mata answers questions nasu
duka subject ɗin shiga tayi ta gani sanna ta fita dan ita bama shi band a gaban ta
tasan sir Samuel ne ya turo mata malamin ya matsa mata sosai kawai tana biye masa
ne Amma ita baya gaban ta shine de dayake son shishige mata nan tafara danne danne
da wayan duk kowa yayi bacci ya barta se kusan 2 na dare ta kwanta wani bacci ya
ɗauke tana sawa a ranta gob dole Ayrah ta mata wanki dan ta tara sosai kuma tana
buƙatar su, washe gari...

*DAN GIRMAN ALLAH KU DIN GA TAYANI SHARING FISABILILLAHI 🙏🏼☺️
☺️☺️
☺️*

COMMENT
LIKE
SHARE
FISABILILLAH

🌹Mhizz teemah🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


Page 24_25

Washe gari bayan ta tashi tayi Sallah wanka ta shiga tass tayi ta fito kullum
kanta da hula bata buɗe shi se idan zata yi wanka itade batasan yanda zata yi da
gashin ba dan bazata iya wanke kan nata ba gashin ya mata yawa shiyasa kullum kan
yake a kulle kitson kanta ba ƙaramin jimawa yayi ba har kitson ya saje da gashin
kaman ba kitso ne akan ba se wanda ya lura ne ze gane toh bama barin kan takeyi a
buɗe ba kullum kai yana cikin hijabi ɗan ƙarami zuwa cikin ta, tsaf ta shirya cikin
doguwar rigar material me ratsin fari da baƙi tayi kyau ga shatin bulala raɗas a
fiskanta da shatin tafin hannun Anty data mare ta idonta ya faɗa sosai duk wannan
uban ayyukan da take sha bata rame sosai ba se wanda ya lura ne zega yanda taɗan
rame a fiska ba sosai ba nan ma,


fita tayi daga part ɗin nasu ta wuce na mama jiya bata shiga ta gyara mata ba hakan
yasa yau ta fara shiga nan tsaf ta gyara ɗakin ko ina yayi tsaff Mama tana bacci
har ta gama ta wuce part ɗin Anty bakin ta ɗauke da sallama kaman de yanda ta saba
ƙasa ƙasa a falo ta taras da Anty tana daddana waya kaman yanda ta saba har ƙasa
Ayrah ta tsuguna ta gaishe ta Amma bata amsa ba kuma bata kalle taba tashi tayi
simi simi ta fara gyara ɗakin tsaf har kitchen bata samu Indo a kitchen ɗin ba ta
leƙa ɗakin ta bata ganta ba sede taji ƙaran ruwa a banɗaki wanka take yi fita tayi
ta cigaba da gyaran ɗakin ta tsaf tayi shara da mopping da goge goge ɗakin munib ta
shiga yana bacci nan ta gyara har da banɗakin sa ta wanke


tana fitowa Anty ta miƙe ta shige ɗakin ta bin bayan ta tayi dan tasan abinda take
nufi kenan yau kusan kwanan ta huɗu ko fiye da haka ma bata gyara ɗakin ba tun
kafin dad ya dawo,ya ilahi ɗakin yayi datti ba kaɗan ba ga kayayyaki nan a baje a
kan bed ɗin ita Ayrah har yau tsoron ɗakin take yi tun ranan da tayi mummunan gamo
har yau abun be fita daga ƙwaƙwalwan taba,wajen mirror nan duk yayi datti ko ina ba
kyan gani ga wani ɗan banzan warin da ɗakin yake yi me hargitsa hanjin ciki kunsan
idan wari yayi yawa a guri yana saka murɗan ciki mutum ya rasa gane kansa toh haka
yake a gurin Ayrah ma warin yanzu ya fara fin ƙarfin tunanin ta yayi yawa over tun
tana danne wa bata toshe hancin ta har ta fara toshe wa, gyaran ɗakin ta fara tana
tottoshe hanci duk abinda take Anty na kallon ta hakan kuma ba karamin ɓata mata
rai yake yiba ganin yanda Ayrah take toshe hanci ita de Anty bajin warin ɗakin take
yiba shi yasa take ganin kaman toshe hancin da Ayrah take yi ta raina tane ko kuma
ita ɗince me wari,

haka Ayrah ta naɗe kayan kan bed ɗin nan tass ta buɗe drawer ta saka su sannan ta
fara shara tsaf ta share ɗaki ta dauko mopper ta haɗa ruwan mopping nan ma tayi ta
goggoge jikin drawers ɗin da suke ɗakin na jikin mirror dana gado duka tsaf ta gama
gyaran bata leƙa toilet bama balle taga abubuwan da suka fi ƙarfin idon ta har
tasaka su air freshener na ɗakin tazo zata fita har ta riƙe handle ɗin kofan Anty
da tun dazu haushi take bata jira kawai take tayi laifi dama ga kuma yanda ta ƙular
da ita ganin tana toshe hanci,ta daka mata tsawa tana miƙewa daga kwanciya da tayi
kan bed ɗin ta ƙara sa gurin kofan batai aune ba kawai taji wani masifaffen zafi a
bayan ta na dundun da Anty ta ɗirma mata sannan ta fara magana


''dan uwarki ni kika barwa toilet ɗin na wanke miki da bed ɗin da zaki kama hanyar
fita? wato raini ya fara shiga tsakanin mu kenan ki kiyaye ni ki fita a idona inba
so kike na nakasa kiba tamm!!!!'' da sauri Ayrah da ta sunkuya tana sosa bayan ta
tsabar yanda dundun ya shige ta ta miƙe bed ɗin ta fara shumfuɗa wa tsaf sannan ta
wuce banɗakin ta riƙe handle na ƙofan toilet ɗin ta tsaya tayi addu'a sannan ta
buɗe wani irin wari ne ya daki hancin ta seda ta ja baya se kuma ta daure ta shiga,
banɗakin ba kyan gani,ya ilahi wannan banɗakin se me ƙarfin imani ne ze iya shiga
wani irin wari yake yi me ɗaga hankali as usual datti ya manne a jikin farin tiles
ɗin yayi brown sosai cikin toilet (wajen yin kashi) wani kalan Maroon da Brown ya
haɗu ya bada wani kalan ruwan cikin,ruwa ta fara tara a bocket sannan tayi flushing
na wannan ruwan cikin toilet ɗin duk da haka jikin shi ya canza color seda ta tari
ruwa me ɗan yawa ta kwara a kasan banɗakin ta ƙara taran wani nan ta saka su hypo,
detol, morning fresh, duk wasu detergent na wanke banɗaki


seda ta saka ta fara wanke cikin toilet ɗin bayan tayi flushing sannan ta wanke
mirror da sink na cikin banɗakin seda ta gama tsaf sannan ta dawo kasan tiles na
banɗakin nan ma tafara wanke wa,ba ƙaramin wahala tasha ba wajen wanke banɗakin
tsaff ta wanke sa ya fita har wani shining yake yi warin yaɗan ragu sosai Amma be
fita duka ba baiwar Allah nan harda hawaye tayi wajen wanke toilet ɗin tana haƙi
kaman wacce tayi tsere da doki haka ta fito duk ta jiƙe da uban zufa,

miƙewa Anty tayi tace ta biyo ta haka ta bita simi simi fita

10 / 19