Author : FATIMA IDRIS UMAR Mhizz Teemah Category : KDP NOVELS
suka mata
liƙi murna sosai take yi kuma yaji haushin rashin zuwan Mami duk da kuwa cewa aki
take yi shi yasa ya wakilce su duka,
RUMAISA'U SULTHAN DAULA suka ji an faɗa hakan yasa Ruma saurin tashi ta miƙawa
Ayrah hand bag ɗin ta kana ta shiga filin jikin ta a sanyaye dan gani da tayi ba
wanda yazo mata, gabatar da kanta tayi ta kuma faɗi abunda zata yi Sannan tayi
shiru tana jiran a tambaye ta ta bada amsa ɗaga kan ta tayi da nufin ta kalli Abbu
ko zata ji kwarin gwiwa kawai se tayi turus ganin ya Ammar da ya Ajeeb, murmushi
suka sakar mata gaba ɗayan su Ajeeb ya ɗaga mata gira ɗaya irin yane, da sauri ta
kawar da kanta tana jin wani irin ƙwarin gwiwa yana zuwa mata nan da nan aka fara
tambayan ta tana bada amsa har ta gama ta shiga speech tayi ƙoƙari sosai bata carke
ko sau ɗaya ba hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi wa yayin nata ba dama su Ayrah sun
mata liƙi kam sosai kuma sun ji daɗi har ta gama ta koma ta zauna inda take aka
bita da tafi rungume juna suka yi se murmushi take yi dan tunda ta gama seta ji
wani daɗi gashi bata yi mistake ko ɗaya ba,
AYRAH BEDARUDEEN KAISAM jin an ƙira sunan ta yasa ta miƙe cikin sanyi da nitsuwan
ta ta isa inde aka tana da domin su toh ita de abu uku zata yi dan kaff abubuwan da
class nasu zasu yi perticipating zata yi, cikin nutsuwa ta gabatar da kanta da
abubuwan da zata yi nan aka fara tambaya tana ansa wa taron dubbani mutanen duk
anyi shiru ana sauraran dadda ɗan muryan ta inda take spelling duk wani word da aka
faɗa mata dalla dalla bako tsoro ballan tana fargaba, haka ta gama sanna ta ƙara
gaba tar da kanta a talk show nan ma ta fara tun ba'aje ko ina ba manyan mutane
suka fara mata kyauta ganin yanda yarinya ƙarama take zubo karatu kuma me amfani
sabida magana take yi akan gomnati da abubuwan da ake fama dasu yanzu idan take
cewa inda ita ce a wannan muƙamin ga abubuwan da zata yi da kuma matakin da zata
ɗauka, nan da nan jikin manyan ƙasan wa'inda yaran su suke makarantar yayi sanyi
wannan abubuwa da take faɗa wanda ita ma sir Richard ne ya bata a rubuce ita kawai
karanta wa take yi already yana kanta ta samu kyau tuttuka da dama kafin ta gama
yarinyar ba ƙaramin burge muta ne tayi ba ciki kuwa harda Ajeeb da Ammar sunji
matuƙar daɗi ta kuma burge su ganin yanda take zuba turanci me ma'ana, Abdull ne
kawai ya tashi ya mata liƙi dama shi ɗan ba ruwan kane ba ruwan sa da abubuwan
mutane sede kuma kowa na ciki na ciki a ƙasan zuciyan sa ji yake dama ace Marwa ne
ko Eshall tayi wannan abun,
Toh a ɓangaren dad da Anty kuwa dad de a ƙasan zuciyan sa ji yake yi kaman ya tashi
ya rungume ƴar tasa Amma kuma baze iya ba yaji daɗin yanda yaga tana ƙoƙari Amma
baze iya nuna hakan ba ( toh ko meye sa dad baze iya nuna hakan ba? Mhizz teemah ce
kawai zata iya warware muku komai) toh Anty ma de haka ne taɗan ji daɗi yanda taga
yarinyar tayi ƙoƙari toh kuma de kunsan dama ita Anty tana son karatu sosai barin
ma daya kasan ce ita bata yi karatun boko ba, shiya sa da taga yanda yaran suke yi
taji ya burge ta har tana jin ina ma ace Munib ne yake wannan karatun toh Amma fa
wani mugun haushin Ayrah ne taji ya ƙara nin kuwa mata a ƙasan zuciya tsanan tane
ya ƙara mamaye zuciyan ta, Mama kuwa ko ajikin ta dan harkan gaban ta ma kawai take
yi kaman bata san me ake yiba, Marwa kuwa da Eshall baƙin ciki kaman su shaƙe ta
suke ji barin ma da suke ga Abdull ya mata liƙi haushi kaman su mutu more
expecially Marwa da ta cika ta batse da baƙin ciki gashi kuma su ba wani abun da
zasu yi nan da nan haushi ya ƙara turnuƙe su take kuma Marwa ta fara dana sanin ta
kura wa su dad akan se sun zo se yanzu nema take ganin shirmen da tayi suda ba wani
abu zasu yi ba toh meye na zuwan su Mama iya result nefa za'a basu tana cikin
tunanin se kuma wani tunani ya faɗi mata toh ai ita ce zata zo na ɗaya a ajinsu
tuna hakan yasa ta yin murmushi Amma duk da haka taji haushi yanda Ayrah take zuba
karatu,
Seda ta gama koma daga ƙarshe tayi musu godiya ta koma inda ta tashi (karku manta
duk abinda tayi da turanci tayi shi) tun kafin ta ƙara sa su Ruma da Ashfat suka
taso da ɗan gudun su suka rungume ta dan su kansu ba ƙaramin burge su tayi ba Abbu
kanshi yarinyar ta matuƙar burge sa, ƙara sawa suka yi suka zauna Ayrah ta faki
idon su ta share ɗan gutun ƙwallan da ya tarun mata a ido tana ji ina ma ace Maman
ta tana raye,
Da sauri ta kawar da tunanin dan yanzu zata iya fara kuka shiru aka yi ana jiran
fito wan sakamako da kuma result da za'a raba dan dama Ayrah ce last daga ita an
gama se raba kyauta wa'inda suka yi ƙoƙari....
Manage This
💥THE BEGINNING 💥
🌹Mhizz teemah🌹
💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰
Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba
Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321
Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️
33️⃣
00️⃣ Page 3 0
Free
Kyau tuttukan presentations da suka yi aka fara raba wa tun daga wanda yazo na
biyar ha aka zo wanda ya kasance na uku ba kowa bane kuma face Ashfat taje ta karɓa
sannan aka ƙara kiran na biyu Ruma ita ma taje ta karɓa sannan na ɗaya Ayrah taje
ta ƙarɓa haka aka ta ƙira abubuwa ukun da aka yi duk Ayrah ne tazo na ɗaya hakan
kuma ba ƙaramin shiga ran muta ne tayi ba sosai aka jinjina wa ƙoƙarin ta,
Sannan aka zo na jss3 aka basu kyauta su banda ƴan ss3 sabida su weac suke rubuta
wa da neco yanzu haka basu gama ba, bayan an gama raba kyautan wa'inda suka yi
ƙoƙari da kuma faɗan wanda yazo na ɗaya se aka fara na Exams shi kuma daga na Uku
ne zuwa na ɗaya haka aka tayi tun daga ajin ƙasa da aka iso primary 3 Munib ne yaci
na ɗaya (ni kuma nace da taimakon Ayrah dan da nadan ita ba baze yi karatun ba so
da taimakon ta) zo kuga murna gun Anty kaman ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka taji
Dad ma yaji daɗin hakan sosai, haka aka ciga ba har aka zo primary Six anan kuma as
usual Ashfat ta fito a na uku Ruma ta fito na biyu Ayrah ta fito na ɗaya sunyi
murna sosai duk da ba sabon abu bane a gurin su haka be hana su farin ciki ba ita
de Ayrah ko a fuskan ta baza kace taji daɗi ba sede a ƙasan zuciyan ta taji daɗi
sosai kawai ta share ne tabar abun ta iya zuciya,
Koda aka zo ajin su Marwa ita ta zo na ɗaya bawai dan ilimin taba malamin ne yasa
ta haye wasu a cikin ajin nasu sunji haushi sosai sun yi mamaki kuma dan su kansu
sun san ba kullum Marwa take zuwa ba Amma ya aka yi kuma tazo na ɗaya, haka de tayi
ta murna ƴan uwan ta na taya ta har aka gama gaba ɗaya kowa yana zuwa wajen iyayen
sa Amma Ayrah kam zaman ta tayi ga kyaututtukan da aka bata a hanun ta, tawagar dad
de gaba ɗaya suka tashi zasu tafi tunda an gama taron toh daya ke shima babban ɗan
kasuwa ne nan suka fara gaisa wa da mutane wa'inda suka sansa dama wanda ya sani
suna kuma taya shi murna ƴar sa tayi ƙoƙari shi kuwa yake kawai yake musu su Mama
da Anty duk sunyi gaba harda du Marwa da Abdull shi kuma dad bayan sun gama gaggai
sawa da mutane ya juya ze tafi kawai suka yi ido huɗu da Abbu nan da nan kansa ya
wani sara masa da ƙarfi seda ya dafe kan toh shima de Abbu ganin dad da yayi seda
kansa ya juya da sauri dad ya ƙara sa barin wajen kaman zeyi tuntuɓe haka ya fita
suka wuce gida shida tawa gansa,
Ashfat da Ruma ne suka miƙe duk suka haɗa kyaututtukan su kana Ashfat tace ''Ayrah
kizo muje ki gaisa da Abbu na gashi can'' girgiza mata kai Ayrah tayi tare da cewa
''a'a kije kawai nikam base na jeba'' jin haka yasa nan take yana yin ta ya sauya
har zata ƙara magana se Ruma ta riga ta da cewa ''Ayrah ki taso muje mana ga yayu
na ma duk ba se ku gaisa ba'' haka de badan taso ba ta miƙe suka nufi gurin da Abbu
yake tare da su Ammar yana tambayan su yaushe a gari tun kafin ma su basa amsa suka
ga isowan su Ruma Ashfat ne ta faɗa jikin Abbu yayin da Ruma kuma ta fara rungume
ya Ajeeb sannan ya Ammar ita kuwa Ayrah tana tsaye kanta a ƙasa sede suka raba juna
sannan Ayrah tsuguna har ƙasa ta gaishe da Abbu sannan ta gaida su Ammar ma kallon
ta Abbu yayi kana ya amsa mata cikin sakin fuska Ashfat tace masa kawar suce tare
da faɗa musu sunan ta gyaɗa kai Abbu yayi yace ''Allah ya miki Albarka Ayrah ya
ƙara buɗa miki ƙwaƙwalwa'' kanta a ƙasa ta amsa da ''Ameen ngd'' haka suka shiga
hira kaɗan ita de Ayrah tana shiru Abbu ne yace ze tafi badan Ashfat ta gaji ba
haka suka wuce ita da Abbu Amma kafin ya tafi seda ya bawa Ayrah kyautan kuɗi shi
kansa besan nawa bane kawai ya miƙa mata ne Amma taƙi karɓa firr yayi da ita ta
karɓa Amma firr taki karɓa haka ya haƙura ya ringa sa mata Albarka,
Bayan tafiyan su Ruma tace ''yaya dan Allah yaushe kuka dawo baku faɗa mana ba ina
yaya Deen meya hana Mom da Abba zuwa'' duka wannan tambayoyin ta ringa jero musu
tana ya mutsa fuska kaman zata yi kuka Auren ne yace ''to rigima yanzu duka wannan
tambayoyin da kika jero ɗin wanne kike so a fara amsa miki yanzu de koma meye ne ki
bari semun je gida''ya ƙara sa faɗan hakan shide Ammar shiru yayi ya ƙure Ayrah da
ido gani yake kaman yasan me kama da fiskan nata Amma se yayi saurin kawar da
tunanin,
Ammar ne yace ''to Parrot kina ta zuba kin manta da kawar taki'' juya wa tayi da
sauri ta kama hanun Ayrah tace ''yanzu Ayrah baza mu sake haɗuwa ba se an dawo
hutu'' tun kafin Ayrah ta bata amsa Ajeeb yace ''Ayrah ke in iyayen ki naga banga
kowa ba ko basu zo bane'' ya faɗa fiskan shi ɗauke da tsan tsan mamaki, dajin haka
idon Ayrah ya cika da hawaye kawai seta ƙara yin ƙasa da kanta bata ce komai ba toh
shima ganin bata amsa masa ba yasa shi basar wa Amma a ƙasan zuciyan sa yana son
sanin amsan da zata bashi gashi kuma wani irin shiga ranshi yaji yarinyar tayi nan
da nan to haka yake a gurin Ammar ma nan da nan tun tana karatu yaji ta wani irin
shiga ransa matuƙa kuma yana son jin amsan ta, cikin son share maganan Ayrah tace
''Ruma barin tafi kar Bus ya tafi ya barni se mun dawo hutu bye'' ta faɗa tana juya
wa da sauri Ruma ta riƙo hanun ta juyo wa tayi gani tayi idon Ruma ya cika da
hawaye wai zata yi kewan ta dan har ga Allah tana son Ayrah sosai Allah ma ya sani,
rungume ta tayi sun ɗan jima kana ta sake ta su Ammar ma suka yi suka yi ta karɓi
kuɗin da suke bata Amma taƙi karɓa dan acewan ta ko ta karɓa ma me zata yi dashi
gwara kawai ta bar musu kayan su may be ze musu amfani da haka ta juya ta wuce Bus
da ze maida ta ta shige kusa da window ta zauna Ruma na ɗaga mata hanun ita ma seta
ɗaga mata hanun tare da mata murmushin daya mugun tafiya da imanin su gaba ɗaya dan
Ruma zata iya ƙirga sau nawa ta taɓa ganin murmushin Ayrah ita de baza kaga fuskan
ta a murtuƙe ba Amma kuma baza ka taɓa cewa tana murmushi ba,
Ita kanta Ayrah a ƙasan zuciyan ta zata yi kewan su gaba ɗaya kuma ita harga Allah
bata so bada hutun nan da aka yiba gashi zasu jima kan su dawo seda ta share ɗan
gutun hawayen ta abubuwa da yawa suna mata yawo a kanta,
Ruma kuwa bayan tafiyan Ayrah suma suka kama hanyan tafiya driver da ya kawo su
Ajeeb ya maida su dukkan su baya suka shiga suka saka Ruma a tsakiya tana tambayan
su yaushe suka zo, abunda ya faru bayan tafiyan Ruma Mom ta ƙira Dad ta faɗa masa
su Ammar jirgin su ya kusa landing toh da yake tun safe da ta tashi aiki take hakan
be bata daman zuwa taro suba Dad ne yaje shida driver bayan jirgin su ya sauka suka
gaggaisa da dad a nan ne yake gaya musu zashi school na Ruma yau suke abubuwan su
toh shi yasa suka ce gwara su wuce kawai,har zasu wuce makarantar su Ruma se aka
ƙira dad suna da meeting shiya sa yace driver ya kaisu shi kuma ya wuce gurin
meeting ɗin su kuwa ko gida basu yiba direct school na su Ruma suka wuce, taji daɗi
sosai da ganin su haka suka isa bakin tamfatse tsen get ɗin driver yayi hon aka
buɗe masa ya kutsa kai cikin gidan parking yayi duk suka fita Ruma ta ɗauka musu
Trolley nasu sauran kuma driver ya bisu dashi a baya, Ruma ce ta fara shiga falon
nasu suna biye da ita a baya ba ƙaramin kyau suka yiba duba da yana yin dressing na
jikin su tun kafin su ƙarasa shiga cikin falon Mom ta tare su side Hug ta basu haka
duk murna fal ransu gaba ɗayan su don sun jima basu ga juna ba sosai suka yi farin
cikin ganin ta har suka shige cikin falon suka zauna suka sata a tsakiya se kallon
su take yi, se a sannan suka gaisa sosai gaisuwa irin na uwa da ƴaƴan ta da kuma na
anjima ba'a haɗu ba take Mom ta ƙwala wa Ladi ƙira ta fara kawo musu abun sha ita
kuma Ruma ta wuce ɗakin ta don ta watsa ruwa ta kuma canza kaya, haka Ladi ta cika
musu gaba da abubuwa Mom da ta kalli bayan su bata ga gogan nasu ba tasan be dawo
bane kuma bata ji daɗin hakan ba ko kaɗan sosai suke shan hira abunsu se tambayan
su abubuwa take yi har da cewa ko zasu je suyi wanka su huta Ajeeb baki yaki rufuwa
yayi matuƙar farin cikin ganin mahaifiyar tasa sosai, miƙewa suka yi don su ɗan
watsa ruwa ga gajiyan hanya duka fita suka yi a part ɗin suka wuce nasu daya
kasance a tsakiya Mom da kanta ta fara jide musu trolleys nasu tana kai musu har
part nasu, su kuwa bayan sun shiga kowa ɗakin sa ya wuce suka watsa ruwa Ajeeb de
yana fitowa bed nasa ya ɗale ya gaji sosai shi yasa ze ɗan huta shi kuwa Ammar falo
ya fito se a Sannan ne ya samu ya ƙira SHEED dan ya sanar dashi sun iso,
🌹 LONDON 🌹
Kafin su Ajeeb su tafi sosai suka yi ban kwana da da su Mash da Byron harma da
sauran Sojojin gidan shi kuwa Deen yana ɗaki yana kwance suka shiga suka same sa
bacci ma yake yi lokacin haka suka ɗale bed nasan seda suka tada shi ya miƙe zauna
kallo ɗaya ya musu ya ja wani siririn tsaki ƙasa ƙasa Amma duk da haka seda suka ji
''whats your problem'' ya faɗa can ƙasan maƙoshi miƙe wa suka yi kana kaman haɗin
baki suka faɗa a tare ''zamu tafi Flight ɗin mu ya kusa tashi'' Okay kawai yace
dasu be ƙara cewa komai ba kallon juna Ajeeb da Ammar suka yi Ajeeb ne yayi ƙarfin
gwiwan cewa ''SHEED kazo mana ka raka mu airport ko haka zamu tafi ba muyi bankwana
ba ne'' ganin suna ɓata lokacin sune kawai yasa su juyawa suka nufi hanyar barin
ɗakin seda suka kusa fita kana ya miƙe sanye yake da pajamas launin Ash gashin
kansa a wargaje ya zubo har ta gefen fuskan sa, bed Room slipas nashi ya saka me
ɗan banzan laushi ya rufa musu baya basu ankara da yana bin su ba seda suka kusa
sauka daga stairs, cikin falon suka tsaya hugging na Ajeeb yayi haka shima Ajeeb
yayi hugging nashi back so tight shafa bayan sa yayi sunyi 1min kana ya raba jikin
su yayi hugging na Ammar same way da yayi na Ajeeb, akwai uzurin da