WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 19

21K to 24K   out of 57K words

dake gabanta ta ciro takardar daukar aikin ta mika
mata.
Momi ta sanya gilashinta tana dubawa, ta mika mata ta ce,
“Masha-Allah, yaushe za ki fara zuwa?”
Ta ce, “Sati mai zuwa”.
Ta ce, “Ga shi kuma za a yi auren Isma’il sati mai zuwan”.
Ta ce, “Wa zai aura?”

Ta ce, “Sujood”.
Sai Lailah ta vangale baki tana dariyar farin ciki.

Sujood diyar Yayar mominsu ce, tare suka taso da Lailan tun suna kanana. Ba za ta ce Sujood
kawarta ce ba, don ita ba ta kawance, to amma ‘yar uwarta ce da suka san juna suka fahimci
juna.
Sai da suka zo shiga jami’a ne suka rabu, inda Sujood ta tafi kasar ‘Syria’ ta yi karatu a kan
likitanci, Lailah kuma ta yi a nan Al-Azhar din Alkahirah.
Biki sosai suka yi irin na al’adarsu, Lailah na kan gaba a kan komi. Aka kawo Sujood nan gidan
su part din Isma’il, kasancewar gidansu katon gaske, mai sassa daban-daban.
Lailah ta shirya sassan sosai kai ka ce fadar wani gwamna ne kasancewar a al’adarsu miji shi
yake yin komai na kayan daki.
Musamman suka fita Oman don sayayyar kayan da za a zuba a gidan ita da Momi. Ganin irin
rawar jiki da wahalar da Lailah ta sha a shagalin auren sa ya sa ya soma sakar mata.
Amma ko an gode bai ce mata ba, duk da ya lura sayayyar da a kai ta zarta ta kudin da ya
bayar.
Ita kanta amarya Sujood ta lura da basar da Lailah da Isma’il ke yi a ‘yan kwanakin da ta yi a
gidan, amma ta ja bakinta ta yi shiru don ba ma’abociyar magana ba ce.
Bayan bikin ne Lailah ta mayar da hankali a kan aikinta. Wata rana idan ta fita tun takwas sai
shida na yamma.
A karshen sati ne kawai take zaman gidan, kuma zuwa lokacin Isma’il ya saki ranshi da ita. Ya
yarda ba wai sai mutum yana dan iska bane kawai yake yin iskanci ba, a’ah, dan kirki ma
kaddara da yanayin rayuwa kan kai shi da aikata laifi, ko ba da son ran shi ba.
Sai dai mu yi ta addu’a Allah ya sa mu fi karfin zuciyoyinmu. Ya raba mu da son zuciya, ya
nisanta mu da kaidin shaidan. Amin.
***
ko da jirgi ya sauke su Sa’eed da Hajiyarsa a garin Bauchi, basu kara ganin Mohd ba. Shi
Sa’eed ne ya yi masu shatar mota suka nufo Jama’are, don ya lura a yadda Yayan ke tunzure
da shi in aka ba shi wuka zai iya burma masa. Haka in yana da bindiga zai iya harbe shi har
lahira. Don haka salin-alin ya wuce Jama’are shi da Hajiya.
Mohd. yana kwance a sofa na falon gidan shi yana busa hayakin ‘Marlboro’, idanunshi a rufe.
Tiryan-tiryan yake tariyo rayuwarshi da Lailah, tun haduwarsu a babban filin jirgin saman Egypt,
sun rako mahaifinsu zai tashi zuwa Nijeriya.
Ya tuno gwagwarmayar da ya sha wajen neman auren ta, domin Hajiyarshi sam ta ki amincewa,
don a cewar ta ba ta son kwashe-kwashe da rore-rore.
Marigayi mahaifinshi shi ya tsaya mishi tsayin daka ya samu abin da ransa da zuciyarshi ke so.
Ya tuno irin soyayyar da suka gudanar a kwanakin amarcinsu. Wanda har gobe ba a samu
macen da yake so ya kuma ke kauna ya amincewa irin Lailah ba.
Ya kuma tuna cewa, tun daga wancan lokacin Lailah ba ta kara yin zaman farin ciki a gidansa
ba. Ta yi hakuri har ya kure ta domin ba shi da lokacin ta.
Idan har za a auna ne a mizani, to alhakin koma me Lailah da Sa’eed suka yi, to yana wuyansa.
Kuma nashi laifin zai rinjaya. Bai san yana son Lailah ba sai yau da ta kuvuce masa, zuciya ta

kuma tunkudo shi ta ce ya je ya dan huce a kan Sa’eed kawai ko ya rage asara.
Daga baya kuma ya ce,
“To don na daki Sa’eed me na yi? Yaro mai tsoron Allah da harshe daya, dukan da ba zai rage
komi daga suyar da zuciyarshi ke yi ba.
Ya tabbatar ya yi rashi tun da ya yi saken da ya rasa Lailah, mai kyautayi da hakuri da
tausasawa a gare shi.
Ko daya ba za a hada Lailah da Aisha ba. Ta fannin komai, shi dai kawai ya karvi aurenta ne
don ya faranta ran Hajiya.
Amma soyayyarta gaba daya in za a dora ta a sikeli ba ta wuce cikin cokali ba. Ai gaba da
gabanta... wai aljani ya taka wuta.
Me zai yi ya huce abin da Sa’eed ya yi masa? Babu, ya riga ya cuce shi. In ma kotu ya kai shi
karshe ma watakila shi zai je belinsa.
Idan ya doke shi bai huce ba, idan ya yi masa Allah Ya isa, idan alhaki ya lalata shi komai a
kansa zai kare.....
Bai ankara ba ya ji wata irin azaba a ‘yan yatsunsa, tuni tabar ta kare har ta soma cin yatsun
hannunsa.
Ya jefata ‘ash tray’ na silver dake gabansa ya bude idon shi sakamakon tsayuwar mutum da ya
ji a kanshi. A’isha ce.....
Ta ce,
“Majnoon na Lailah......!
Za ka iya tashi mu yi ‘break’ din ne ko Misra za ka koma a baka, tunda bikon bai yuwu ba?”
Ya valla mata harara ya ce,
“Idan komawar zan yi za ki iya hanawa ne?”
Ta kyave baki ta ce,
“A’a, ko bani da abin yi ba abin da zai kai ni inda ba’a so na.....”
Ji kake fauu! Ya wanke mata fuska da yatsunshi biyar...har sai da ta ga wuta da taurari. Ta
kama kuncinta duka biyu ta sunkuya tana neman kwayar idanunta da ta neme su ta rasa na
wucin gadi.
Da kyar ta ce, “Ni ka mara daga magana Mohd.?”
Ya yi tsaki ya yi ball da ‘center – table’ din gabansa na gilashi tsantsa, a take ya ragargaje. Ya
yi sama fuuu! Kamar zai bi ta kanta, ta yi kwafa ta mike ta ce.
“Wallahi ka mari auren ka”.
Ta yi dakinta tana kuka tana hada kaya. Azahar a Jama’are ta yi mata, ba ta nufi gidan Hajiya
ba don ba sulhu take nema ba, gidan iyayenta ta nufa.
Kwananta biyu Hajiya ba ta san ta zo ba, sai mahaifinta ne Malam Adamu ya zo yake gayawa
Hajiyar yadda aka yi.
Hajiya ta girgiza kai ta ba shi hakuri, ta ce, “Za ta dau mataki ita ma zata yarda da komai amma
banda duka. Amma ya yi hakuri ya turo mata A’ishar ta zauna a wurin ta kafin ta kira shi”.
Malam Adamu ya gyara zama ya ce, “Hajiya idan Muhammadu baya son auren nan ina ganin
gara a raba shi cikin mutunci ba tare da zumunci ya lalace ba.
Don ta fadi abubuwa da yawa, wadanda abin dubawa ne a cikin aure. Ta ce sai ta yi watanni
uku ba ta ganshi ba, kuma bai neme ta a waya ba.
Sannan in zai tafi ba ta isa ya yi mata sallama ba, sai dai ta ga kudi a kan tebur, haka in zai

dawo. Allah ya ga zuciyata ba don kudi na wanke A’isha na ba wa Mohammadu ba, sai zumunci
da mutuncin da ke tsakani”.
Hajiya kamar ta yi kuka, ta ce,
“Don Allah ya ba ta lokaci ta kira shi, in Allah Ya yarda za ta tsawatar”.
Kwana uku kenan Hajiya na buga layinshi ana gaya mata a rufe yake. A lokacin ma shi yana
‘Bangkok’. Daga can ya wuce ‘Austria’ yana yi wa jirgin Virgin Atlantic lodi.

Sai da ya kwashe watanni uku cur sannan ya yo Bauchi. Bayan motarshi fal da tsarabar Hajiya
da Sa’eed din da ba shi da yadda zai yi da shi.
Hajiya na sallar walha ya daga asabarin dakinta kasancewar ana zabga sanyi, kamshin
turarensa kawai da ta shaka ta san cewa shine.
Ya yi sallama ya shigo ya kwanta cikin kujera yana waya. Ba ta bi ta kansa ba sai da ta gama
sallolinta da laziminta, sannan ta aje mayafi gefe ta juyo ta dube shi kawai ba ta ce da shi komai
ba, don bakin cikin da yake shaka mata Allah ya yi yawa da shi.
Sai shine ya rufe wayar ya sauko kasa yana murmushi ya ce,
“Barkanku da safiya Hajiya, na same ku lafiya?’
Da da ne sanda yake yaro idan ya ba ta haushi irin haka carbinta za ta jawo ta tsutstsula masa,
to yau ma tunanin da ta yi kenan.
Sai dai kuma da ta dubi girmansa da haibarsa hadi da kwarjinin da Allah yai masa, sai ta rasa ta
ina za ta tsula mai carbin ya ji zafin shi a jikin shi?
Ko’ina guraye ne murdaddu na ingarman namiji, mai cikar halitta, ma’abocin haiba da kamala.
Sai birkitaccen hali da babu macen da za ta jure shi.
Dole ta aje carbinta a gefe ta dube shi cikin ido ta ce.
“Barka kadai”.
Ko a kwalar rigarsa, don shi ya manta ma da wata A’isha, ya soma ba ta labarin irin
tafiye-tafiyen da ya yi a wannan tafiyar.
Ta gaji da soki-burutsun da yake mata ta ce,
“Duk na ji, ka samo kudi ko?”
Ya ce,
“Sosai kuwa Hajiya, don na yanke ma can gidana na Bauchi za ki koma, ni zan koma Old
G.R.A”.
Ta jinjina kai ta ce,
“To iyali fa?”
Ya yi dan duru-duru na rashin sanin abin cewa, don shi tun lokacinda A’isha ta sha mari bai kara
tuno ta ba ya ce,
“Tana can Bauchi, don kai tsaye nan na yiwo ban je gidan ba”.
Haushi ya kashe bakin Hajiya Baida’u, ta rasa me za ta ce masa. Ta girgiza kai ta ce.
“Na tabbata ba haka kwarorin nan suka barka ba. Yanzu abin da kake yi wa aurenka ka kyauta
kenan?
Baka ma san takamaiman inda matarka take ba. Ka kama ‘yar mutane kuma ‘yar uwarka da
duka kamar jaka aka aura maka?
Tun da ka yi mata dukan ka haure ka yi tafiyar ka ba tare da ka damu da halin da take ciki ba,
balle ka binciki lafiyarta, wai sunan tana matarka....”

Ya katse ta da cewa, “Ni fa Hajiya ban doke ta ba, marin ta kawai na yi da na ga za ta kawo min
rashin kunya, wato zuwa ta yi ta ce na dake ta kenan?”
Hajiya ta ce, “Ungo naka....”
Ta yi masa umbola. “Wato marin ma kawai ne. Ka fada da bakinka ka doketan kenan. To sam
ba zan lamunci wannan rashin hankalin ba, ka je can gidansu ka ba ta hakuri ka sa matarka a
gaba ku tafi, kada na kara ji ko da tsinke ka tsikare ta dashi balle mari. Idan ba haka ba wallahi
zan dauke ta, in ya so ka koma in da ba a san darajarka ba ka je can ku karata, ni kuma in fidda
hannuna a kanka”.
Ya sunkuyar da kai, “Duk me ya yi zafi Hajiya? Ki yi hakuri zan je in ga Baba Adamun, zan ba
shi hakuri amma don Allah ki sa min albarka!”.
Ya ba ta tausayi matuka, Allah ya ba ta ‘ya’ya masu gudun zuciyarta, su biyu kacal amma
kamar goma ta haifa. Zurfin ilimin zamaninsu bai sa sun kangare mata ba, komi ta ce ‘eh’ ne ko
da bai yi masu ba.
Sai dai har yau ba ta kara tada zancen Sa’eed da Lailah ba, ga dukkan alamu ba ta son zancen
kwata-kwata, duk da ta amincewa ranta gaskiya ne tun da har Sa’idun ya furta mata da bakinsa.
Ya dai nemi gafararta ya kuma ce ta taya shi neman gafarar Ubangiji. In Allah ya yarda wani
abu makamancin wannan ba zai kuma faruwa da shi ba, insha Allahu.
Ya sa aka fiddo jakunkunan da ya zo da su, sittiru ne dankare, ya ware na Sa’eed. Hajiya ta ji
dadi sosai.
Sannan ya ce, “Sauran a rabawa dangi”.
Ta ce, “To, matarka fa?”
Ya ware wasu ya ce, “A kai gidansu ita zai ba ta nata daban”. Bayan shi tun da ya tafi ma ko a
mafarkan shi ba ta zo ba. Tunanin shi na LAILAH ne, sai dai ya ce Allah ya yaye masa.
Duk kawaicin Baba Adamu yau ya fitittike ya gwada masa shi ma yana son ‘yarsa. Bayan dogon
kai ruwa rana da ban hakuri sannan da kafa sharudda sannan ya yarda ya kira A’ishan suka tafi,
wadda ita kam kamar a kan kaya ta yi watanni ukun nan cike da nadamar fitowar ta, domin ta
tabbatar kafin ta sake samun wannan daular da tsadadden miji irin nata a matsayi da ajin
rayuwarta, abu ne mai matukar wuya. Ko ko a ce ba zai yiwu ba. Allah ne ya kashe ya ba ta,
wautarta za ta kwace mata.
Don haka tun a mota ta soma zuba masa hira, tun yana share ta har ya biye mata. Suna yi wa
Baba Adamu dariyar sharuddansa na duk ranar da ya kara dukan ta zagewa zai yi ya rama
mata, don bai fi shi karfi ba.

****
Tun zuwa Sujood, Lailah ta samu abokiyar debe kewa, duk sanda ba ta da darasi tana sassan
Sujood ko ita Sujood din na nasu vangaren. Ko su shiga gari idan Isma’il baya nan.
Cikin watanni biyar da suka biyo baya, account dinta ya yi nauyi, don ba ta tava komi cikin
albashinta, Isma’il ya dauki nauyin rayuwarsu gaba daya.
Kuma Egypt ba kamar London ba, ba ta biyan kudin haya, gida ne nasu na kashin kansu. Duk
da matsin tattalin arziki da kasar ke da shi wannan bai sa al’ummarta zama cikin talauci ba.
Egypt kasa ce mai dadin zama da albarkar abinci, da suttura da wadatar ilimi, da kwararrun
ma’aikata kiwon lafiya.
Kullum cikin kwanciyar hankali da wadata suke, ban da yanzu da suke fuskantar matsin

Amurka. Sai dai damuwar Lailah daya (ABBAS) ina za ta nemo shi?
KANO da girma, kai ita duk zamanta a Najeriya ma ba ta tava zuwa Kano ba, ba ta san ina take
ba.
Tana dai ji ana fada Kano-Kano a bakin Sa’eed da Mohammad, amma ba ta ma tava tambayar
su wani sharhi a kai ba. Ta kuma gwada nambobinshi na Britain an gaya mata ba a amfani dasu
sam.
“Watakila Allah ya rubuta iyaka haduwarmu kenan???”
Ta tambayi kanta cikin sanyin murya.
“Haduwar kan hanya ce ta zamo haduwar ZUCIYA…., aminci, kyautayi da abota ne suka hadu
suka yi gingimemen gini a ZUCIYA. Wanda hakan ya janyo ZUCIYAR take so, amma baki ya
gaza furtawa...... Saidai sau tari fuska kan gaza boye zahirin abin da ke ZUCIYA, domin
ZUCIYAR na ragaita....Sai dai kuma a rashin sani na ashe bani da ‘yancin wannan
al’amarin………
Ta tuno kalaman wasikarsa.

Idan ta yi wa wadannan kalaman fassara ta hankali....Abbas na son ta! Sai dai AUREN da ta ke
da shi ya zama shinge. Ta yi murmushi ita kadai, ta juya ta rungumi filo.
...... “Kana da ‘YANCIN Abbas, yanzu kana da ‘YANCIN, dukkanmu muna da ‘YANCIN. Allah ya
hada fuskokinmu cikin gaggawa”.
Idan ta ce tunanin Abbas da soyayyar shi da ta yi kane-kane a zuciyarta za ta dinga yi, lashakka
za ta samu matsala a kan aikinta.
Don haka take rufe ‘file’ din zuciyarta a duk lokacin da take tare da dalibanta, wadanda suke
kaunarta saboda karancin shekarunta da manyan kwalaye haka. Kuma a lokacin ne Jami’ar
Al-Azhar ta tura ta karo Karatu (in service) a Jami’ar Ummul-Kura da ke Madinah.

Duk yadda ta yi don ta cogewa hakan abin ya faskara, domin tsarinsu ke nan. Dole ka mallaki
kwalin PhD a matsayinka na ‘staff’. Wannan ne zai baka damar zama Dr. A ilimi. Sai dai aure da
iyali na sanyawa a barka a nan cikin Alkahira, wanda ba ta da ko daya.
Ta samu Momi da Isma’il take gaya musu batun tafiyarta Saudi-Arabia. Sujood sai ta hau kuka
ita ba ta yarda ba.
Isma’il na dariya ya ce,
“Haba Sujood sai ka ce wata karamar yarinya? Abin da za ta dinga zuwa ko mu muje?”
Budar bakin Sujood sai cewa ta yi, “Ni sai dai mu tafi tare”.
Lailah da Isma’il suka kwashe da dariya, Momi ba ta ce dasu komi ba.
Sai da Sujood da mijinta suka tashi Momi ta dubi Lailah sosai ta ce,
“Kina da yakinin cewa za ki iya rike kanki da mutuncinki tsayin wannan lokacin din?”
Kawai sai Lailah ta fashe da kuka. Ta rasa ranar da Momi da Isma’il za su daina yi mata kallon
wata mara imani.
Wane irin tuba suke so ta yi a kan kuskurenta wanda ba ta yi ba? Shekara guda har da doriyar
watanni sun kasa yi mata kyakkyawar shaida?
Momi ta saki baki tana kallon ikon Allah, ta ce,
“To mene ne abun kuka cikin maganata?”
Ta ce,

“Kun kasa yarda dani Momi. Da zinar halina ce da na yi ta inda babu mai ganin aibunta, kuma
da ban fada maku ba balle ku san na aikata.
Momi ki yarda dani, wallahi-wallahi ba zan kara ba, kuskure ne wanda ba wanda ya fi karfin
yinsa.
Ki yafe ni Momi, ki tayani rokon dan uwana ya yarda dani. Ku yi min kyakkyawan zato, kada na
mutu ba tare da shaidar arziki daga bakin ku ba....” Ta ci gaba da kuka.
Momi ta dube ta sosai ta ce,
“Kina tunanin da shari’ah ake bi a wannan zamanin da ba a jefe ki ba?”
Ta fiddo ido kwalala! “Momi duk da sahihancin tuba na da nadamata?”
Momi ta ce,
“Wannan ne dai ban sani ba, sai dai ki tambayi malamai. Lailah kin bani tsoro sosai, duk
tarbiyyar da na maki?”
Ta sa havar gyalenta tana share hawaye.

Hankalin Lailah ya kara tashi, ita ma ta kama kuka. Suna cikin kukan Sanah da Najat suka
shigo aguje suna kokawa a kan ‘yar tsana, dole suka share hawayen Lailah ta raba rigimar suka
fita.
Lailah ta dago jajayen idanunta ta ce, “Momi me zan yi ki yi farin ciki dani?”
Ta ce,
“Aure”.
Ta fyace hanci

8 / 19