Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
kwalin apple da kwalin inibi, duk haka
yake ajiye mata ba ta kuma isa ta yi godiya ba, yanzun nan zai hau fushi da ita.
Ya hanata yava ajiyarta ta banki sam, tana mamakin wannan al’amari, kulawar da yake nuna
mata da kwarin gwiwar da yake ba ta ya wanke duk wani bakin ciki da ke zuciyarta, sai fatan
Allah ya raba ta da cikin da ke jikinta lafiya.
Cikinta ya shiga watanni na tara, ranar wata alhamis sun dawo daga awo a NHS. Abbas ya
mika mata waya ya ce lallai ta kira Mominta su gaisa.
Atleast ko ba ta fadi mata inda take ba, ta sanar da ita tana nan lafiya don hankalinta ya kwanta.
Yana mai nuna mata mace mai haihuwa a kan gava take, baya fata, amma in ta mutu a ya yin
haihuwa me za ta ce da Ubangijinta a kan mahaifiyarta?
Jikinta ya yi matukar sanyi da nasihohin sa, jiki a sanyaye ta soma dialling number Momin,
wadanda suke kamar karatun sallah a cikin kanta.
Bugawa daya- biyu Momin ta dauka, ganin bakuwar lambar ta kasar Ingila. Lailah ta yi sallama
Momin ta amsa, sai dai ba ta gane mai maganar ba.
Lailah ta kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata ta ce,
“Momi nice Lailah.....”
Momi ta ce,
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil! Lailah!! Ashe kina raye kika tafi da gangan kika barmu cikin
tashin hankali?”
Ta soma kuka. Ta ce,
“Wallahi ba da son raina bane Momi”.
Ta ce,
“Koma me ke damun ki Lailah da har ya sa ki barinmu na dauka kafin kowa ya ji ni za ki fara
nema ki fada min damuwar ki, amma ba ki tsallake ni ki barni cikin tashin hankali ba.
Da auren ki Lailah…….. ki tsallake mijinki ki tafi wata uwa duniya, kin san hakkin aure kuwa?
Amma tun da hakan kika zavarwa kanki ai shi kenan”.
Ta kashe wayar ba tare da ta sake sauraron ta ba.
Hankalin Lailah duk inda yake to ya yi kololuwar tashi, ta tabbata Momi ta yi fushi da ita, fushi
kuwa mai tsanani tun da har ta ki sauraron ta.
Ta mika ma Abbas wayar tana kuka sosai. Ya barta ta yi abunta mai isarta, bai katse ta ba. A
karshe tashi ya yi ya bar mata dakin don ta ji dadin yin kukan sosai.
Ya kuma cire layin ya sanya wani don shi ma yana ganin ba yanzu ne ya dace lokacin da Lailah
za ta koma gida ba.
A can Alkahira Momi zugum ta yi cikin kwanciyar hankali, ko ba komi yanzu hankalinta ya dan
kwanta tun da ta tabbatar Lailanta na raye, kuma cikin koshin lafiya.
Tun da har ta fara tunanin neman ta wata rana za ta yi tunanin dawowa. Ko da Isma’il ya shigo
ta gaya mishi Lailan ta yo waya cewa ya yi ta ba shi lambar.
Ya gane lambar ta kasar Ingila ce, amma bai san wane yanki bane. Yayi-yayi ya kama layin ya
kasa dole ya hakura.
A ranar Lailah ba ta yi barci ba, tausayin Mominta ya hanata barci na abin kunyar da ta jawo
mata da kuma tunanin yadda za su karvi abinda za ta haifa.
Don ba za ta voye ba gaskiya za ta fadi duk ranar da Allah ya mai da ita gida, don ta san
aurenta vatacce ne a addini.
Ga rashin Babansu ga rashinta, ta san abun ya yi wa Momin yawa, musamman yadda take
sonta fiye da sauran ‘yan’uwanta, take kuma nunawa karara.
Suka smu hutun makaranta har na tsayin watanni uku. A irin wannan lokacin yawancin dalibai
kowa kasarsu yake tafiya.
Ban da Lailah da Abbas, a wannan lokacin cikin ya yi katoto ya kuma yi kasa sosai, don haka
suka sa rainon cikinsu a gaba, baya awa biyu cikakku bai san halin da take ciki ba.
Yana kuma yawan jaddada mata cewa duk wani motsi da ta ji ba dai-dai ba ta kira wayar shi. Ita
har tausayi yake ba ta, ba shi ya kar zomon ba amma ya dauki rataya ya dora a kafadunsa.
Ranar litinin da daddare misalin karfe goma sha biyu na dare. Lailah na barci ta tashi da wani
irin azababben ciwon baya, kafin ta ce meye wannan ta ji ta sharkaf cikin wani abu da ke bin
kafafunta.
Ta soma salati nan da nan ta yi kokarin daukar wayarta a kan ‘bed-side lamp’ ta yi dialling no
Abbas, ba wani vata lokaci ya ce
“ya ya ne? Haihuwar ta zo ne?
Ta ce, “I think so.....”
Ya kashe wayar ya jefar da bargon da yake ciki ya kira hospital van, cikin ‘yan mintuna ta iso da
nurses ya yi masu jagora suka fito da Laila sai NHS.
Kwana daya, biyu Laila na cikin matsananciyar nakuda amma ta kasa, in ka ga kai komon
Abbas a wannan lokacin sai ya baka tausayi.
A kwanaki biyun nan kaf ba abin da ya sanya a cikinsa sai ruwa, kamar shine mai nakudar.
A karshe aka sanya mata ruwan nakuda har leda biyar amma duk a banza. Don haka suka
nemi shi mijinta (kamar yadda suke tsammani) da ya saka hannu ayi mata CS don ceton ta da
yaron gaba daya.
Ba tare da wani tunani ba Abbas ya rattaba hannu, nan da nan likitoci suka fara aikin ceton rai.
Ya samu ‘waiter chair’ ya zauna yana yi wa Lailah addu’ar fatan alheri.
Awanni biyu cur aka dauka ana aikin kamin wata nurse ta fito daga dakin da aka shigar da
Lailah.
Da sassarfar shi ya mike ya cimmata. Ta dube shi cikin tausayi ta ce,
“Am sorry, yaron bai zo da rai ba. Ya dade da mutuwa a cikinta”.
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi ya ce, “Lailan fa?”
Ta ce,
“Komi lafiya tare da ita”.
Ba ta rufe bakinta ba aka turo Lailan a kan gadon marassa lafiya zuwa dakin kwana.
Ya ja kujera dai-dai kan Lailah ya zauna, ba a jima ba ta bude ido sannu a hankali tana kallon
shi.
Ya dora sassanyan hannunsa a goshinta, abinda bai tava yi ba, yanzun ma bai san yayi ba,
rudewa ce. Ya ce,
“Are you alright Lailah?”
Ta girgiza mishi kai. Sannan ne ya samu nutsuwar zuciyarsa.
Kwanansu uku, wajen da aka yi wa Lailah ‘operation’ har ya fara kamewa, aka sallame su a
rana ta hudu. Bayan asibitin ta hadata da nurse da za ta dinga zuwa gida tana taimaka mata
har kwana goma sha hudu.
A kwanakin nan duka ba ta bar tsiyayar da hawaye ba, na asarar jaririnta. Hakannan Allah Ya
dauki kaunar yaron Ya sanya mata. To haka shi ma Abbas da ya dauki rai ya dora a kan abin da
Lailah za ta haifa. Ya gama yin duk shirye-shiryen tarvarsa.
Da ta murmure ta koma makaranta, kowa da suka sani tsammani yake ita da Abbas mata da
miji ne, daga su sai Allah suka sani.
Jegon Lailah a kasar England, ya zamo wani abin tarihi a rayuwarta da ba za ta manta ba. Haka
babynta da ya koma ga Mahaliccinsa har abada ba za ta daina tunaninsa ba.
Abbas ya ce, “Yana da kyau ta fara istigfari tun daga yanzu, domin yana ganin lokaci ya karato
da ya kamata ta soma shirin komawa gida, tunda karatun ya zo karshe.
Ba tare da musu ba ta bi shawarar Abbas, sai dai har yau ba ta san da fuskar da za ta dubi
Mohammed ba.
****
Watanni uku bayan nan suka karvi kwalin masters din su, shi kuma Abbas saura shekara daya
ya karvi na PhD. Jikin Lailah a sanyaye suka soma shirye-shiryen tahowa Egypt.
A ranar wata litinin Momi ba ta zata ba ba ta tsammana ba, kararrawar kofar shigowa ta kada,
mai sanar da su cewa akwai bakon d ake son a bude masa kofa.
Budewar nan da za ta yi suka yi arba da diyarta Lailah. Lailah ta rungume mahaifiyarta tana
kuka mai tsanani.
Sanah da Najat, suka taso cikin al’ajabi suka rungume ‘yar uwarsu. Tare suka rankaya falon
cikin yi ma Allah godiya maras iyaka.
Sai da murnar ganin Lailah ta lafa, take sanar dasu tana da bako, don haka Momin ta ba wa
Najat makullin sashen baki ta ce ta bude ma bakon Lailah. Akai masa ruwa da abinci.
Momi ta fiddo waya ta kira Isma’il daga wajen aiki ta ce ya zo yanzu-yanzu ya ga abin mamaki,
addu’arsu ta kwana da kwanaki farat daya yau Allah Ya karva.
Isma’il ya iso gidansu a sukwane, amma maimakon ya yi murna si ya rufe ido ya soma balbale
Lailah da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba a kan tashin hankalin da ta jefa su a
ciki har tsayin shekaru biyu cur.
In ban da sharar hawaye ba abin da Lailah da Mominta ke yi. Daga baya shi ma sai ya rungume
‘yar uwarshi ya fashe da kuka.
Suka yi kukan su mai isar su, kamin da Isma’il ya fiddo waya ya kira Mohammed, wanda
already ya yi aure.
Hakan bai hana shi tsallake aiyukan gabansa ba ya yi landing a Egypt. Suka tsaya cirko-cirko
shi da Lailah sai kallon-kallo, the one that is always hunting his dream….
A hankali jama’ar dake katon falon suka shiga zamewa, ya zamo daga Lailah sai Mohammad
dinta, wadanda suka yi cirko-cirko suka ci gaba da kallon juna kamar yau suka fara ganin juna.
Tsohuwar soyayya ta motsawa Mohammed, ya mika hannu ya kamo hannun Lailah, sannu a
hankali ya hadata da jikinsa ya kankame ta ya rungume, a hankali ya kama sakin wata irin
sassanyar ajiyar zuciya.
Wasu irin dumammun hawaye suke kwaranyo daga idanuwan Lailah, hawayen da ita kanta ba
ta san ko na mene ne ba, na nadama ne? Na tunanin gurvataccen auren ta ne? Ko ko na
tunanin da wane harshe, da wace fuska za ta fuskanci Mohammed?
A hankali ta soma zamewa daga jikinsa, ta durkushe a kasa kan gwiwoyinta ta soma girzar
kuka mai cin rai.
Shi ma binta ya yi ya zauna dirshan a gabanta, ya ce,
“Lailah duk kukan nan na mene ne? Kin tafi a bisa na yi miki laifi, ko ko don ni ba na haihuwa?
Kin kuma yi tunanin dawowa wanda mun yi farin ciki da hakan.
Don haka ban ga me zai saki kuka ba, illa mu yi tunanin matsalolinmu da neman hanyar
warwaresu domin cimma rayuwa mai amfani.
Sai dai ban sani ba ko za ki iya ci gaba da zama dani duk da rashin haihuwata ko a’a?”
Ta yi saurin cira kai ta dube shi, cikin muryar kuka ta ce,
“Ban tava tunanin in guje ka ba wai don ba mu haihu ba, illa don hujjoji nan da na ambata maka
cikin wasikar da na bar maka.
Sannan ni din wata mai babban laifi ce a gare ka da Ubangijina. Sai dai nima ban san me ya kai
ni ga aikatawa ba. Amma ina da tabbacin cewa na yi tsarkakakken tuba wanda Allah (S.W.T) ya
yi alkawarin karvar sa, wato tuba da tabbacin ba za a sake komawa izuwa zunubin ba”.
A hankali ya ce,
“Laifin me kika yi min Lailah? Gaya min komin girmansa.......”
Ta mike daga jikinshi ta ba shi baya, ta isa ga taga tana kallon harabar gidansu inda ruwan
sama ke sauka a kan korran ciyayin da suka yi wa gidan kawanya.
Ta vata shiru na lokaci mai tsawo, tana hango girman laifinta, hoton ranar da ta kira “bakar rana”
na gilmawa a idanunta.
Hawayen idanunta na tsiyaya duk da ta amince da tubanta. Ganin ba ta da niyyar cewa komi,
ya kara taku ya isa bayanta, ya dora hannu a hankali bisa kafadunta.
Ta juyo suka yi ‘facing’ juna idanunta sharkaf da hawaye, kafin ta mika hannu ta share su,
sannan cikin karyayyar murya ta ce.
“Za ka iya yafe min idan na fada maka cewa har haihuwa na yi da Sa’eed?”
Idandunan shi ne suka yo waje tamkar an busa masu barkono, ya kasa furta komai, kai kamar
ma bai ji dai-dai ba.
Ta share ambaliyar hawayen da suka shimfido mata ta ce,
“Aure tsakanina da kai ya haramta Mohammed.... shaidan ya rinjaye mu mun aikata cin amana
a gare ka.
Ni kaina ban san ya aka yi ba, sai da mai afkuwa ta afku. Ina cikin kunyar ka, ina cikin kunyar
Mahaliccina………
Ka yi afuwa a gare ni Mohammed, ko na samu sassauci wurin Ubangijina.
Na tafi domin ina ganin zaman nawa ba shi da amfani, aurenmu ya riga ya gurvata, na yi asara
kuma na ci amanarka, duk da kai ma kana da naka kamashon.
Tun da an tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa, “Kwana nawa ne mace mai aure za ta iya yi ba
tare da namiji ba?”
Ya ce, “Kwanaki arba’in”. To ni casa’in nake yi ban ganka ba.
Sai ya nuna shi yana da lokaci na, yana kula dani tamkar matarsa, yana kyautata min tare da
bin duk wata hanya don ya sama min farin ciki.
Sannan ka dauko baligi ka hada da matarka wacce ke cikin shekaru na kuruciya, alhalin kai din
baka nan. Ta ya ya varna ba za ta faru ba......?”
Tun da ta soma magana bai yi magana ba binta yake da ido, da zuciya. Jin al’amarin yake
kamar almara ko mafarki.
Idan ma Lailah ta kullawa dan uwanshi wannan sharrin ne don ta rabu da shi, wanda tuni ya
fahimci take-taken ta kenan, ko don ta hada shi da marayan dan uwansa da baya da ya shi a
duniya, to, ta yi karya, ta kuma yaudari kanta”.
Ta dai tafi ta yi gantalinta ta yi shegenta, ba zai tava yarda da wannan tozarci ga dan uwansa
ba.
Ya daga rinannun idanun shi da suka kada suka yi jawur suka kankance ya ce,
“LAILAH!”
Dagowa ta yi a hankali ta dube shi, har yanzu kuka take.
Ya ce,
“Mece ce hujjah? Ko shaidar da zan yarda da ke, wadda shari’a za ta yarda da shi ta
gurvata/haramta auren namu?”
A mamakance ta dube shi, wato duk irin bayanin da ta yi mishi bai yarda da ita ba. Ta ce, “Na
dubi Allah ne na fallasa maka sirrina da yake voye.
Wanda babu wanda ya sani daga ni sai dan uwanka, don in samu afuwa da yafiyar ka ko na
samu saukin hukuncin da Ubangiji zai yi min idan na ha’ince ka muka ci gaba da zaman
ZINA....”
Tare ta ya yi.......
“ZINA? Ai kin je kin yi abarki, wannan ke da Ubangijinki. Amma AURE NA yana nan ba abin da
ya same shi, ba kuma wanda ya isa ya sheganta min shi tun da ban gani ba.
Wace mace mai mutumci ce za ta tafi turai tsayin shekaru biyu ba tare da muharraminta ba, ta
ce wai wani wanda ke Najeriya ne uban shegen nata?
Kin ganni nan duk son da nake yi wa mace ba ta isa ta tozarta ‘yan uwana in kyale ta ba. Don
haka ki nemo uban shegen ki a inda kika baro shi, ba cikin zuri’ata ba”.
Lailah ta soma hasala, zuciya ta harzuko ta.
Ta ce,
“To me ya yi zafi Mohammed? Ka yar da kwallon mangwaro ka huta da kuda mana?”
Ya yi mata wani irin kallo wanda ta kasa fassarawa, domin kallo ne na kiyayya da rashin kauna,
wanda ba ta tava gani cikin kwayar idanunshi ba.
Ya yi wani irin miskilin murmushi ya ce.
“Ai hakan kike so. Na kuma ramfo ki yarinya. Sai ki sake dabara wadda kowa zai yarda dake ba
sai kin tozarta dan uwana ba. Don hakan ba karamar illa ba ce ga mutuncinki a idon duniya.
Aurenmu babu rabuwa.
Ba shege daya ba, ko dari ne zan karve su tunda ni musulunci ya baiwa. Don haka ki shirya
gobe mu wuce gida kawai cikin mutuncin ki.
Na yi alkawarin ba mai jin wannan katovarar taki daga bakina, sai idan ke kika sake furtawa.
Zan yi kokarin in gyara kuskurena kamar yadda kike so Lailah. Amma wannan magana, ki
barta.
Ki yi haka ki binne ta tunda baki da hujja ko shaida ko kotu ba za ta karve ta ba.......”
Ta katse shi,
“Allah shine shaida ta, kuma ba zan yi zama na zina ba. Da din ma soyayya ta rufe min ido
nake zaune da kai Mohd. Kana kwara ta, nake jure bakin cikinka har na kai kaina ga halaka.
Ba don Ubangijina ya yi gaggawar farkar dani ba, na san da har yanzu ina cikin halaka. Ka
tambayi duk malaman da ka sani.... babu aure tsakanina da kai, tunda na kwanta da shakikinka,
alhalin kana raye.
Mohammed na soka, na soka da zuciya daya, kuma har gobe ina sonka, ba zan iya komawa
aurenka ba muddin ina cikin hankalina.
Amma tun da ka ce sharri na yi wa Sa’eed, to muje a hakan, wata rana gaskiya za ta yi
halinta.....”
Da sauri ya katse ta,
“Ban sake ki ba Lailah.....ki kwana da sanin wannan. Ba kuma zan tava yin hakan ba, in dai
sunana “Mohammad!”.
Don haka na baki kwanaki uku ki yanke mai fissheki, za ki bini mu koma ne, koko zan ji
sammaci daga kotu........?”
Fuuu! Ya fita ya banko kofar har sai da Lailah ta razana, mamaki kam yau ta sha shi kamar ya
kashe ta, ta yadda mutum mai ilimi kamar Mohammed ya mai da kanshi katoton jahili cikin
addini, saboda soyayya da ta rufe mishi ido.
Ta dade tana sake-sake ita kadai, ko dai ita ma ta bar maganar ne kamar yadda ya ce a barta
ba tare da ta tozarta kanta ba?
Idan ta ce kotu za ta kai shi a kwatar mata sakin aure kanta za ta tozarta. Duniya ta ji abin da
WASA DA KANIN MIJI ya janyo mata.
Asirinta ya bankadu har Momi da sauran ‘yan uwanta su ji, ta kuma san har ‘ya’ya da jikoki ta
barma kanta abin gori.
Abu mafi a’ala dai shine a bar maganar, amma kuwa idan ta ci gaba