Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
ka ce
ba mijina ba, ban yi wani doki ba balle in yi wasu shirye-shirye domin tarbarsa.
To shima din bai damu ba, don ya san shi din har kullum mai laifi ne a gare ni, bayan a ganin sa
yana sauke duk wasu nauyi da Allah ya dora masa a kaina idan ya zo bayan kowanne watanni
ukku.
Ya rage nawa in dubi yanayin aikinsa inyi mishi uzuri ko kar in yi, don shi kan ga yadda ya nuna
ya gaji da kananan korafe-korafen da nake damun shi dasu a kan rashin sa cikin gidan, tun da
dai ba dauka na zai yi ya goya ya dinga yawo dani cikin duniya ba. Bai kuma iyakance min
zuwa ga ‘yan uwana a duk sanda na so ba. To amma mene ne auren? Ina da tambaya, ‘yan uwana mata. Shin wannan shine ginshikin
auren ko me? Ba na samun ginshikin aure, don haka am not satisfied with my husband.
Don haka Mohammed har ya gama kwanakin shi biyu ya koma bai samu wani edcellent
welcome daga gare ni ba, kamar yadda shi ma ya ke complaining(korafin) na hana shi hutawa,
na dauki vacin ran banza da wofi na daurawa kaina.
Idan bai fita ya nemo min ba me zai ba ni? Ko nufina shine ya jive a gida kada ya yi amfani da
damar da Allah ya ba shi na morar iliminsa? Mutane nawa ne suke neman ‘chances’ din
(damar) da yake samu basu samu ba?”
“Su ‘chances’ ba a hakura da wasu don a huta, a kula da bukata da rayuwar iyali?” Na
tambayeshi watarana.
Ya ce,
“Lailah you’ll never understand me, (bazaki tava fahimtata ba), tunda kin riga kin damu kanki.
Na gane ki, irin matan nan ne da suke so miji ya like musu kamar kaska, kin san da irin aikina
kika aure ni, a kan me yanzu za ki uzzure ni?”
Don haka har ya koma bamu yi rabuwar arziki ba.
Ta duba agogon hannunta kana ta dubi Abbas.
“Ya kamata mu tafi gida haka yamma ta yi sosai”.
Abbas ya zare kafafunshi daga cikin ruwan suka mike suna harhada kayansu.
Ya ce, “Ni dai na so ki karasa min labarin nan a yau”.
Ta ce, “Some other tym, bana jin dadin jikina sosai, sannan ga yamma ta yi”.
Suka jero suna tafiya cikin hirarraki kanana, sai ka rantse mata da miji ne”.
****
Abbas ne a kitchen din gidan yana kiciniyar daura masu sanwar abinda za su ci da daddare. Ba
komi bane ‘source’ ce da za a ci da biredin alkama.
Ya kammala y rufe komi ya gangara kantunan dake kasa ya mika ‘yan sisinsa (penny) ya sayo
biredin ya dawo kitchen din, ya dauki na Lailah da nufin ya fara mika mata kafin ya dawo ya
dauki nashi.
Ya iso jikin kofarta ya kwankwasa, shiru ba a amsa ba. Ya sake kwakwasawa a karo na biyu......
A wannan lokacin da ya dan saurara, sai ya jiyo tana kakarin amai kamar fitar rai.
Don haka ba tare da wani tunani ba ya murda kofar a sukwane ya isa gefen gadon da ta jike da
amai, ya aje plates din da ke hannunsa a gefe.
Ya ce, “Lafiya Lailah?’
Cikin tsananin tashin hankali da firgici bayyananne, zane varo-varo a kyakkyawar fuskarsa.
Ta yi mai nuni da ya ba ta ruwa, ya dauko gorar ruwa a ‘bed-side fridge’ dinta ya valle hancin ya
mika mata, ta kuskure baki ta wanke fuska. Ta koma jikin filo ta kwanta tana maida numfashi a
galabaice.
Duk abin da ta saka ma cikinta a yinin ranar ta amayar da shi, har da wani kore-kore cikin
aman. Sabida babu sauran abinda za’a amayar din.
Ya zage tukuru yana gyara wajen bayan ya tattara zanin gado ya jefa a bokiti.
Sai da ya gama aikin aman tas ya fesawa dakin ‘room-fresh’ mai dadin kamshi, zuwa lokacin
Lailah ta fara rawar dari, hakoranta sun soma karo da junansu.
Ta ce, “Rufa min bargon nan, Abbas sanyi...”
Ya dauki lallausan bargon ya rufa mata, amma ba ta daina rawar darin ba sai ma abin da ya
karu.
Don haka ya gangara kasa ya koma nashi dakin ya dauko nashi bargon ya kara mata. Ya koma
kan kujera daya kwallin-kwal dake cikin dakin ya zauna cikin kulawa ya ce.
“Za ki iya kokartawa muje asibiti?”
Girgiza mishi kai ta yi alamar “A’a, ba za ta iya ba”.
Lallai lafiya… uwar jiki, lokaci daya ta rafke Lailah a daki, shima ta hana shi hidimomin gabansa,
balle halartar ‘lectures’.
Ya je dai ya ba da edcuse a kan Lailah, amma shi ba shi da hujjar da zai bayar. Don haka ciwon
Laila tsawon sati guda ya shafi karatun sa ba da wasa ba.
Wannan ba shine a gabansa ba, lafiyar kawarshi, abokiyarshi, aminiyarshi Lailah ne.
A rana ta bakwai ne dai ya takura mata ala dole ta mike, duk ta rame ta zaizaye dama jikin ba
wani jiki ba.
Ya dauko jibgegiyar coat dinta ya jibga mata, ya manna mata bakar hula da socks na hannu.
A wannan lokacin na karshen watan January, lokacin da London ke fama da snow , har ya
soma tunanin rashin sabo da yanayin ne ya haifar ma da Laila wannan mugun zazzavi da
vomiting. Wato (amai)
To amma ina ruwan sanyi da vomiting (amai)? Haka dai suka gangara kasa, suka hau bus, ko
da yake daga nan ma unguwar da suke (Acton Town) za su iya karasawa NHS da kafafunsu,
sai dai don baya so ta jigata ne.
Abinki da dalibai ma’abota inshora, nan da nan su kai ‘booking’ ganin doctor, aka soma daura
Lailah a kan gwaje-gwaje, wanda ya kai su hard a su dibar fitsari, jinni, don binciken zahirin abin
da ke dmaun ta.
“Congratulations!”.
Siririyar Baturiyar ta ce da shi tun kamin ta iso kujerar da suke zaune. A tsammaninta su din
mamallakan juna ne (ma’aurata).
Ta sake cewa, “Congratulations, nan da watanni bakwai muna maka albishir din mallakar
bouncing baby”.
Daga shi har Lailah ba su fahimce ta ba. Don haka ya kama hannun Laila kada ta fadi suka
koma ofishin doctor.
Ya ce, “Meke faruwa ne doctor? Me ke damun Lailah?”
Ya washe baki shi ma cikin yi mishi albishir din cewa matar shi na dauke da juna biyu ne”.
Wata kara da Lailah ta saki ta kuma sulale a nan ta fadi sumammiya ta razana su. Abinka da
wadanda suka san muhimmancin patient, nan da nan aka yi rubdugu a kan Lailah aka kuma
umarce shi da ya fita.
Ya dawo bakin kofar dakin likitan ya jingina da bango, hankalinsa ya masifar tashi, ya rasa
dalilin suman Lailah don anyi mata albishir din kasancewar ta mai juna biyu.
Ba da auren ta ba? Me zai dame ta don an ce tana da juna biyu? Duk da can a karkashin
zuciyarsa wani dunkulallen abu ne ya tokare kirjinshi, tun sanda Lailah ta soma ba shi labarin
rayuwarta, ya kuma fahimci tana da aure, ya soma canja tunanin shi a kanta, ya kuma yi dalilin
da ya sa ya fara ja baya da ita, amma tun da ta fara ciwon ya samu kanshi da son taimaka
mata.
Amma bai ga dalilin da don an ce tana da juna biyu za ta daga hankalinta ba. Al’amuran
rayuwarshi gaba daya sun canja, tun haduwar shi da Lailah.
Yana fama da wani lamari mai girma cikin zuciyarshi a kanta, shi kadai ya san halin da yake ciki
a kan Lailah, dare da rana, wuni da safiya. Tun a ranar da ya soma dora idanunshi a kanta.
Hatta a marigayiyar matarshi bai tava tsintar kanshi a al’amarin dake faruwa da shi a yanzu
game da Lailah ba.
Ba ya tantama soyayya ce mai girma, kuma mara adalci. Tun da dai wadda ake mawa matar
aure ce ga wanin sa. Don haka ya san cewa al’amarin ba zai tava yiwuwa ba.
Kwanansu biyu a asibitin ana yi ma Lailah karin ruwa da kulawa ta musamman. Tunda Lailah ta
dawo cikin hayyacinta kuka take, wanda bai san dalilin sa ba.
Rarrashin duniya Abbas da ‘nurses’ sun yi amma kamar kara izata suke, har aka sallamo su
suka dawo gidan da suke zaune Lailah ba ta bar tsiyayar da hawaye ba.
Ya yi sallama a kofar dakinta dauke da plate na soyayyar ayaba (plaintain) da apple (tuffah) a
cikin leda, da fresh milk har da ‘ya’yan inibi.
Ya ja tebir ya dora mata ya sanya ta a gaba a kan dole sai ta ci, ta soma ci kamar mai cin
magani, ta rasa inda za ta sa kanta. Rabonta da abinci har ta manta.
Kuka take wurjanjan a lokacin da take rokonsa da ya taimaka mata a cire cikin da ke jikinta.
Abbas ya sa mata ido yana kallon ta, a ladabce ya ce.
“Lailah”.
Ta saurara da kukan ta dube shi tana shessheka.
“Ke fa da bakin ki kika gaya min cewa kina da aure?”.
Ta daga mishi kai bayan ta sa havar kallabinta ta fyace wata matsiyaciyar majina.
“To ‘why’ (meyasa) za ki ce a kashe rai alhalin da ubansa?”
Maimakon ta ba shi amsa sai ta kara tsinkewa da kukan, na yau har ya fi na kullum, tamkar
wadda aka yi wa bushara da rasuwar uwa da ubanta.
“Allah-kareem!”
Ya furta cikin zuciyarshi. Ji yake kamar ya dauko damuwar Lailah ya aza ma kanshi don ta huta.
Shi bai ga dalilin da za a cire cikin da yake da uba ba. Koma babu uban shi a haife dan a ba shi
yana so.
Babban burin shi kenan a duniya, ya ganshi da dan kanshi, wanda kuma gurin haihuwar ne
Allah ya karvi ran matarsa.
“Lailah idan ba kya son dan ne ni ki haife ki bani, wallahi Lailah baki san yadda nake addu’ar
Allah ya bani da ba.
Idan Ubangiji ya baka da ya yi maka kyautar komai, wadda wani ko wata bazasu tava baka ba.
Ki tuna ke musulma ce, wadda ko ba dade ko bajima za ta tadda Ubangijinta.
Shin me za ki ce da Ubangiji a bisa wannan muhimmiyar kyauta da ya yi miki kika butulce? Baki
da tabbacin cewa wannan shine kadai kwanki a duniya. Wasu suna nan suna nema ruwa a jallo
koda zasu karar da dukiyoyinsu, amma Allah bai basu ba
A matsayina na dan uwanki musulmi ina mai tunasar da ke cewa, idan kika zubar da ciki kamar
kin kashe rai ne, kuma wallahi Allah ba zai barki haka ba.
Idan laifi uban dan ya yi miki za ki huce a kan dan tayin dake karkashin mahaifa kin yi babban
kuskure, wanda ko ba dade ko ba jima wata rana za ki yi nadama.
Idan bakya so ina mai shawartarki ki daure ki haife, ni Abbas ina so, ki bani. Zan yi mishi uba,
idan bakya son uban shi, ko idan wani laifi uban nashi ya yi miki har ta kai ki ga yin wannan
gurvatacen tunani.”
Lailah ta juyar da kai cikin matse hawayen idanunta. Ga dukkan alamu ranta ya soma sanyi. Ya
ci gaba da yi mata nasiha hadi da ba ta misalai kala-kala, har ta saddakar da tana son
fayyacewa Abbas dalilinta na yin hakan.
A ganinta idan ya ji dalilinta shine mutum na farko da zai goya mata baya ta yi abin da take da
nufin yi.
[12/17/2019, 17:51] Takori: ****
Matsala ta biyu da muka kara cin karo da ita ni da Mohammed, ita ce matsalar rashin haihuwa.
Shekarun mu biyar tare amma haihuwa shiru, babu ita babu alamunta.
Daga baya ma Mohammed ya zo yana zargina da yin ‘planning’ a voye, bayan kuma a zahiri ba
hakan bane.
Muka koma biye-biyen teburin likitoci suka yi ta zakule-zakulen su har suka tabbatar matsalar
daga gare shi ne.
Idan har yana son haihuwa to yana bukatar ai mishi aiki, don haka daga ni har shi muka tattara
maganar haihuwa muka yi watsi da ita. Sai dai duk inda Mohd ya ga ‘ya’ya sai ya karar da
lokacinshi a kansu.
Na lura Mohd na matukar jin dadin yadda alakata take da Sa’eed, domin dan gaban goshinsa
ne, su biyu kacal iyayensu suka haifa kuma mahaifinsu ya jima da rasuwa.
Yana so ya zo ya tadda mu a falo muna ta nishadi, tunda dai shi baya da lokacin mu.
A wani weekend Sa’eed yake yi min zancen yarinyar da zai aura Zaliha, ajinsu daya ne a
makaranta, yana son in fadawa Mohd. don gidan su Zalihan sun takura idan ba zai fito ba za su
bawa wani. Shi kuma yana son yarinyar sosai.
Na ce,
“Sa’eed da rigima kake, kana fafutukar kwalin karatun farko za ka hada ma kanka aure?”
Ya ce,
“Wallahi da gaske nake Antina, ina matukar son Zaliha, idan kuma ban same ta ba ban san ya
ya rayuwata za ta kasance ba, ku taimaka mani”.
Na ce, “Ni don ta ni ai mai sauki ce, amma Yayanka ka fi kowa sanin shi”.
Ko da Mohammed ya zo, bayan wasu watanni kamar yadda ya saba, na yi mishi zancen, bai
wani ba zancen muhimmanci ba, don haka ya koma ta vangaren Hajiya.
Na ke jin ita ce ta tusa Mohammed din a gaba sai da ya amince aka yi ma Sa’eed baiko da
Zaliha, amma aka ja lokacin sosai zuwa sanda za su kammala karatun su.
Sa’eed ya dauko Zaliha har gida ya kawo min ita, yarinyar kyakkyawa amma ta waye da yawa.
Na yi mishi maganar hasashe na ya ce “haka nan nake son abata”.
Gab da kamawar watan bikinsu muka samu wani mummunan labari, wato hatsarin Zaliha da
iyayenta a kan titin Abuja, duka babu wanda ya tsira.
Hakika Sa’eed ya shiga matsanancin tashin hankali wanda ta kai shi da furucin babu shi babu
aure a duniya.
Shekarun mu biyar da aure Sa’eed ya tafi NYSC jihar Cross-river. Don haka sai na kasance
cikin kadaici da kewa. Da dai kadaici ya isheni sai na tattara na tafi Egypt wajen mahaifiyata,
bayan na nemi izinin Mohammed ta waya.
Zamana da ‘yan uwana sai ya zamo magani ga dimbin damuwar da nake ciki. Momi ta kasa
daurewa don ganin muguwar ramar da nake yi. Ta sani a daki a wani maraice tana tambaya ta.
Ban voye mata komi ba na zayyane mata matsala ta. Momi ta ce,
“Tun farko ke kika kawo yaron nan Lailah kika ce kina son shi, alhalin kin san yanayin aikinsa,
ban ga dalilin da za ki daura ma kanki damuwa yanzun ba.
Idan har kina ganin ba za ki iya ba, to tun wuri ki nemi da ya sauwake miki”.
Na yi jim! Ina tauna maganar Momi, in ce Mohammed ya sake ni? Abune da ba zan tava iyawa
ba, domin dai auren soyayya muka yi, duk da halayen sa na rashin kulawa da soyayya a gare ni
‘still’ ina son kaya na.
Don haka har na koma Bauchi ban yankewa kaina shawarar komi ba, tunda dai 100% na yarje
ma zuciyata ina son mijina.
Ginshikin aure kam ba na samu, wato auratayya. A hankali dai na fahimci jinsin mu ba daya
bane, yana cikin jinsin mutanen da seduality wato auratayya bai dama ba, ya yin da ni kuma
nake a rukuni akasin hakan.
Dole haka na daure ina ci gaba da cin dan uban hakuri. Da dadi ba dadi muna zaune a hakan.
Rashin Sa’eed sai ya zamo min kamar rashin babbar aminiya. Ya shiga jikina sosai, mun
amincewa juna, duk wata matsalar junanmu da junanmu muke shawara, na kuma lura sosai
Mohd ba karamin jin dadin hakan yake ba.
Ta duba agogon ‘swatch’ dake daure a fatar hannun ta, ta dubi Abbas, “lokacin sallah yayi, mu
je mu sauke farali”. Ya sauke tagumin da yayi da hannayenshi biyu yana sauraronta, ya mike
yana duba nashi agogon shima.
****
Kwance yake a mike bisa doguwar kujerar da ke karamin falonshi yana nazarin jaridar
‘Daily-Trust’, sai dai da ganin irin kwanciyar da ya yi ka san ba ta lafiya ba ce, alal hakika yana
cikin matsananciyar damuwa.
A karo na wajen dari da hamsin kenan, ya sake ‘dialling no Lailah, kamar yadda computer ta
saba yi mai vavatu yau ma vavatun ta shiga yi mishi, cikin sanar da shi layin a rufe yake.
Kararrawar shigowa falon ta yi kara, da kamar ba zai kula ba, ya dai daure ya mike ya isa ga
kofar ya bude.
Ya bayyana a falon cikin kyakkyawar shiga ta caftan na farar shadda mirrow, suka yi ido hudu
da dan uwansa da baya da ya shi a duniyar baki dayanta.
Ya matsa kadan ya ba shi hanyar wucewa suka zauna a tare cikin kujeru masu fuskantar juna.
A saluve Sa’eed yake kamar wanda ya sha duka, ya ce, “Yaya har yau ba labari?”
Bai saurari amsar shi ba ya ci gaba da cewa.
“Ni ina ganin a kai zancen cigiya kafafen yada labarai”.
Mohammed bai amsa ba, illa ya mike ya isa ga kitchen ya fiddo ma dan uwanshi abin sha mai
sanyi na’ya’yan itacen ‘tropical juice’ hade da tambulan, don ga dukkan alamun shi a gajiye
yake da uwar tafiyar da ya niko tun daga jihar Cross-river.
Hakika yana tausaya ma dan uwanshi halin da ya shiga a dalilin vatan matarshi, wanda kuma
shi ne sila.
Anya idan Mohd ya ji irin cin amanar da ya yi mishi zai tava yafe mishi? Idanuwansa suka kada
jajir, amma sun kasa tsiyayar da hawaye.
Ya tashi tsamo-tsamo da shi ya nufi hanyar baskwata, don ganin ga dukkan alamu Mohd din bai
son damu yanzu cikin halin da yake ciki.
Wayar shi dake gefe ta yi ruri, ya mika hannu a kasalance ya dauka. Isma’il ne yayan Lailah.
Bayan sun gaisa ya ce,
“Babu labari a nan Bauchin har yanzu? Mu ma nan mun baza cigiya har a sauran kasashen da
ke makotaka damu wadanda take da kawaye a can, ba amo ba labari”.
Mohammed ya ce
“Nan din ma babu, amma yanzun nan Sa’eed ya kawo min wata shawara a kan na baza cigiyar
a